MAHREEN

By HAERMEEBRAERH9900

1.8K 437 71

A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na... More

MAHREEN PAGE 1
MAHREEN PAGE 2
MAHREEN PAGE 3
MAHREEN PAGE 4
MAHREEN PAGE 5
MAHREEN PAGE 6
MAHREEN PAGE 8
MAHREEN PAGE 9
MAHREEN PAGE 10
MAHREEN PAGE 11
MAHREEN PAGE 12
MAHREEN PAGE 13
MAHREEN PAGE 14
MAHREEN PAGE 15
MAHREEN PAGE 16
MAHREEN PAGE 17
MAHREEN PAGE 18
MAHREEN PAGE 19
MAHREEN PAGE 20
MAHREEN PAGE 21
MAHREEN PAGE 22
MAHREEN PAGE 23
MAHREEN PAGE 24
MAHREEN PAGE 25
MAHREEN PAGE 26
MAHREEN
MAHREEN PAGE 27
MAHREEN PAGE 28
MAHREEN PAGE 29
MAHREEN PAGE 30
MAHREEN PAGE 31
MAHREEN PAGE 32
MAHREEN PAGE 33
MAHREEN PAGE 34
MAHREEN PAGE 35

MAHREEN PAGE 7

35 13 0
By HAERMEEBRAERH9900

💅  MAHREEN  💅




WRITTEN BY HAERMEEBRAERH






PAGE 7







Ba kowa bane ya sakko daga motar nan face babban abokin Yah Maheer da suka saba zuwa zance waje na tare mai suna Alhaji Younusa, ya kafe fa sai Amarya ta fita daga motar Alhaji ta shiga tashi wanda shi ma Alhajin abokin Yah Maheer d'in ne,ja in ja aka fara a tsakiyar hanya, gudun kar a b'ata lokaci sai Alhajin ya hakura ya ce mu je mu shiga motar wancan duk d'aya ne, ba haka mu kammu muka so ba a mana juye a tsakiyar hanya, amma dole muka sauka muka shige motar aminin Yah Maheer ya ja mu zuwa bauchi, gudu ya ke shararawa kamar za mu tashi sama, ni kuma kuka nake kamar zan cire ido na,ta cikin farin mayafi na nake hango unguwanni da gidajen da muke wucewa, mu na wuce unguwar su Mansoor na ji wata iriyar kewa ta kama ni, sabon kuka na bud'e murya ta ina yi, Aunty na (Matar qanin Baba) ta juyo ta na bani hakuri, Goggon su Yah Maheer ta ce,

"Aysha batta ta koka, ko ke ce aka dauke ki daga cikin 'yan uwan ki za a kai ki wata uwa duniyar dole ki kuka, balle ita da ta shaqu da mutan gidan su da iyayen ta,za ta dena ne da kan ta ai hanyar ba qarama bace da nisan ta"

Jin haka ne ya sa na fara rage sautin kuka na, ina ta shessheqa da sauke manyan ajiyar zuciya, har muka je wudil ido na na zubar da hawaye, a hankali bacci ya fara diba na, na kuwa gyara zama na na jingina da kujera na lumahe ido na, bacci ne na gajiya da kum bashin wanda bana yi kwana biyu ya d'ebe ni, ban farka ba sai da muka kusan shiga jigawa, a wannan lokacin mayafin nawa kan shi baya saman kai na, Ina d'aga ido mu ka yi ido  hud'u da Alhaji Younusa yana kallo na ta mirror murmushi ya min sannan ya ce,

"To amaryar fa ta farka,an sha bacci,ni yarintar ta na bani dariya fa"

Dariya suka sanya baki d'ayan su, ni kuma na tura baki na ina d'an murmushi sama sama,na ji kunya sosai a lokacin, kuma da alama na jima ina baccin dan kaina a saman kafad'ar surukata(Innar Yah Maheer) na tadda shi mayafi a saman wuya na ya bar kai, hannaye na na dunqule su waje guda kamar me jin sanyi, hira suka ci gaba da yi wadda na kula tin ina bacci suka fara ta,

"Haka akwai wani zuwa da muka tab'a yi da Maheer, ta sha ado da purple material yanda ki ka san 'yar india masu duhun fatar nan,ni kin san Goggo har yau mamakin bawan Allahn nan nake? Dik cikin mu fa shi kad'ai ne bai da budurwa ko irin ta wasan nan,sai gashi ya yi taking d'in mu by surprise ya dakko me kalar larabawa,ranar da muka je ai mun ci taliya me shegen dad'i ( ba ni na dafa ba Addah Ummu ce😂) na jima ban ga yarinya me kunya ba kamar wannan, kud'i fa muka bata amma sam ta qi karba, next kuwa da za mu zo na ce to ai kuwa dole ki Karbi kyautar masoyin ki yarinya, muka siyo turaruka masu kyau, (Rose of love saman turaren wanda yake marfin turaren ne wata kwalba ce da aka yi ta kamar furen flower amma turare ne a ciki shima) sai shower gel da salt of bath, da tarkace na gyaran jiki a cikin wani box na katako me kyawun burgewa, ko da mu ka kai wannan d'in ma da kyar da sid'in goshi yarinyar nan ta karb'a tin anan na ce tooooo lallai Maheer ka yi sa'a,ka yi dacen matar aure ka riqe ta da kyau, gashi kuma da alama ta na son shi ta na mutunta shi,"

Wata harara na yi a cikin ido na da ke a rufe, a raina ina ayyana,

'Wannan bawan Allah akwai shegen surutu, wataqila shi ya sa ya nace se ya kai mu, dan ya yi ta tona asirin zancen da ya ke raka Yah Maheer d'in, wannan ko an kai ni muka gan shi zama za mu yi kamar kurame kar ya d'auki magana ya qara gaba da ita'

Hira suka ci gaba da yi Auntyna na basu labari na dan su san cewa 'yar tasu ta jiqu da tarbiyya, Goggon Yah Maheer banda gasgata ta ba abinda take kamar ta sanni dama can, (ta yi imani da cewa indai ni 'yar babana da mamana ce to kuwa za a same ni da tarbiyya, shine dalilin gasgata maganar da take yi)

Ba mu yi aune ba sai ganin mu muka yi a Ningi, dan kuwa ba qaramin gudu yake zabgawa ba,a wannan lokacin kowa baya ganin kowa sai fitilar mota dake haske gaban mu, duhu ya yi sosai, mun so matuqa a tsaya a yi sallah a hanya amma ya ce mu yi hakuri in mun isa ma had'e da isha'i, haka kuwa aka yi, mu na shiga cikin garin Bauchi ya zabga hamdala da qarfi ya daki sitiyarin motar ya kunna fitilar cikin motar sannan ya ce,

"To alhamdulillah amarya ta fara jiyo qamshin angon ta da alama, dan na ga ta ja mayafi ta rufe fuska"

Dariya aka sanya min, se na ji kunya ta sake kama ni, wai shi komai akai sai ya yi magana ne?

"To yanzu za mu wuce Wintin Dada,inda za a yi yinin biki gobe in Allah ya kaimu, shi yasa na dage se ni zan kawo ku, saboda Alhaji bakano ne be san wajen ba,wahala kawai za ku sha har shi, amma alhamdulillah ya fahimce ni, Allah ya kaimu lafiya, mun gode wa Allah da ya sa muka shigo garin yakubu lafiya"

"Ah alhamdulillah gaskiya dole a jinjina maka irin wannan gudu da ka ke laftawa haka, gaskiya a dinga rage wa saboda halin rayuwa"

"To Goggoji inshaa Allahu za a rage gudu, na yau ne ai, na dakko amaryar Maheer ai dole na zuqa gudu Goggo"

"Ahhh lallai kam...to Allah ya kaimu lafiya"

"Ameeeen"

Gani na yi muna barin cikin gari muna yin wajen gari, ashe Wintin dadan wajen gari ne? Haka mu ka dinga ratsa duwatsu da kwazazzabe dan kuwa hanyar ba a gyara ta ba, hanya ce ta babban titin da ake tafiya garin Jos,manyan motoci duk sun halaka ta, Alhaji Younusa be zame a ko ina ba sai a qofar gidan Yayan Yah Maheer, nan fa aka bud'e mota ana ta murna, gida ya cika da jama'a kamar rana, Goggon Yah Maheer da Auntyna ne suka kama ni muka shige cikin gidan, nan da nan fa aka hau gud'a ana shewa da murna ga amarya ga amarya, wani d'aki aka nufa da ni ina shiga na ga Yayar mu babba a dangin Mamana (Yaya Hadiza)da cousins d'ina wanda suka riga mu tasowa tini, wata murna na sanya na nufi Yayar mu na rungume ta, se na saki kukan farin ciki kuma, na ce,

"Na zaci ni kad'ai ce Yaya"

Dariya ta yi ta sa hannu ta na bubbuga baya na da sigar lallashi, ta ce,

"Kin san kema ai ba za mu barki ke kad'ai ba, ina nan tare da ke kin ji?"

D'aga mata kai na yi cike da shagwab'a na ce,

"Ni dai Yaya in kun tashi komawa ku tafi dani na fasa zama anan"

Nan take hawaye ya balle min,sanin zan iya d'aga mata hankali ya sa ta ce,

"To kar ki damu bari a gama bikin, Addah Ummun ki ma na nan tafe ai da Addahn ki Firdous kar ki damu kin ji? Ki zaman ki ki huta gajiyar hanya, ki sallah ki ci abinci ki baccin ki"

"Yayah a ina zan yi wanka? Mutane sun cika a gidan, ni kuma gaskiya bana iya bacci in ban wanka da dare ba, kuma ba zan iya shiga bayi da mutane haka ba"

"Zuwa anjima in kowa ya tafi ko an kwanta zan raka ki"

Zama na yi a gefen yayar mu na jibga mata kusan rabin.nauyi na a jikin ta, ba tare da ta damu ba suka hau hira da sauran 'yan uwa na, cousins dina su Hafsat da Ladidi sai qannen babana su Zainabu da Shafa, sai Aunty Safiyya muka hau hira sama sama, can na duba waya ta da na manta da ita, messages ne na fatan alkhairi daga mutane daban daban har da wanda ban da No su, dubawa na dinga yi ina karantawa, inda daga qarshe na miqe qafafu na saboda zogin da na ji suna min,na cire mayafi na, ba tare da na sani ba ashe an taru ta window ana kallo na, yara na fad'in,

"Ashe matar Yah maheer fara ce lutuya,('Yar lukuta)"

Jin haka ne ya sanya Yayar mu wurga min mayafi na ta ce,

"Ke rufe jikin ki, ko har kin manta muna gidan surukan ki ne,"

Tura baki na yi na ce,

"Zafi nake ji Yaya,"

Wata mata ce ta shigo da tsohon ciki (d'aya daga cikin matan yayan Yah Maheer) hannun ta dauke da madaidaicin bokitin qarfe mai dauke da shinkafa, sai wani bokitin da be kai wannan ba miya ce a ciki, wata matar na biye da ita da plates da ruwan pure water da maltina, da cokula.

Ajiyewa suka yi aka gaisa sannan suka bar abincin suka fita, Yayar mu ce ta dauki plates d'in ta yi serving kowa abincin nima aka aje min, hankali na na can na duba messages ban san me nake nema ba, amma na kasa dena kallon saqonnin, ji nake kamar akwai saqon da nake jira be iso gare ni ba, kamar daga sama na ga saqon Yah Maheer mai sanyaya zuciya, saqo ne da ba zan tab'a mantawa a rayuwa ta ba,

"Assalamu'alaikum Hayatee..kun iso lafiya? Ya gajiyar hanya? Allah ya hutar da gajiya, kar ki damu my young lady zan cire maki gajiyar da ki ke tattare da ita d'aya bayan d'aya very soon, can't wait to set my eyes on you Baby"

"Whattttttt !!!!!!!"

Shine abinda na furta da d'an qarfi, idanu na a waje kamar wadda aka turowa mugun saqo,

Hayatee and Baby are new words from him to me, be tab'a ce min wani baby ba, se dai young lady, yau har da wata hayatee, Zainabu ce ta matso ta na so ta ga me na rikice wa haka na yi sauri na boye wayar ina zaro ido, abincin da aka jima da ajiye min ban tab'a ba shi na ja gaba na ina zare ido, yau nake jin sabon salo kiran sallah da husur, dama ya iya magana haka shima?

Shinkafa na dinga dannawa, duk so na da naman kaza ban tab'a ba, coz ina cikin rud'anin me yake nufi da zai cire min gajiya.

Ji nayi abincin ya shaqe ni, na duba gaba na na ga maltina na dauka na sha, sanan na yi hamdala na koma gefe,

Sallamar Yah Maheer ce ta karad'e d'akin, inda ya durqusa ya gaishe da Goggunaye na da Yayarmu, suka amsa cikin mutunta juna, kallo na ya dinga yi, ni kuma na yi lamo kamar me yin bacci, ta qasan ido na ina hango shi, ina hango yanda ya yi wani kyauu kana ganin shi ka ga ango.

Kiran qanne na ya yi suka fita da qannen Babana da muke kai daya, dan su ne a matsayin qawaye na, basu jima ba sai gasu da leda da gasasshen nama da multina da exotic juice da dai sauran tarkace, se chocolates da Yah Maheer ya damqa hannun su ya ce a bani nawa ne.

Nan fa aka zo aka baje aka ci nama aka qoshi aka sha lemo, dare na qara yi damuwa ta na qaruwa saboda ban yi sallah ba ni kuma ina jin jiki na duk ya yi datti ina so na yi wanka,qarshe dai dole na hakura da wankan nan na je na yi alwala a waje, yara da manya haka aka tattaru ana kallo na, ni kuma kunya ta hana ni sukuni, saboda idon mutane da ke kai na.

A haka na idar na fad'a daki na tada sallah, ban tsaya ba se da na yi dika sallolon da ke kai na na qara da nafila na yi addu'o'i na shafa, anan na takure saboda na san ko na kwanta ba wani baccin azziqi zan yi ba, akwai mutane da yawa a d'akin dan ma sauran Goggonaye na sun tafi gidajen 'yan uwa d'akin ya ragu, (kar ku manta garin bauchi ne tushen Babana) akan dole na bar inda nake saboda Yayar mu da ta takura sai na tashi daga qasa.

Washegari da safe aka kai min ruwan wanka, na yi wanka na yo alwala, na tsara kwalliyar da na jima ban yi irin ta ba, duk wanda ya kalle ni a wannan lokacin sai ya yaba, saboda yanda na yi kyau sosai, Yayar mu da sauran Goggonaye na Aunty Safiyya da su Addah Ummu sune suka tafi yi min jere da safen, dan haka daga ni sai cousins dina da qanwata Amina ita ke bi wa Ummu Salma,muna manne da juna muna hira, tare muka ci abinci tare muke komai, haka aka fara yinin bikin,mata na ta shiga ana ganin matar da Maheer ya aura, masu mamaki na yi, masu ganin ai dama irin su haka suke sun iya zab'e.

Se da na kwana biyu ana biki a gidan Yayan shi kafin a na uku da dare aka kai amarya.

Wani sabon babin kuka na bud'e saboda gaba d'aya messages d'in da Yah Maheer ke tura min a kwanakin nan ba masu sauqi bane, hankali na a matuqar tashe yake, ni kad'ai na san me ke faruwa dan ko qanwa ta ban nuna wa ba.

Da qafar dama Aunty na ta umarce ni da na shiga gidan baki na dauke da addu'ar neman tsarin Allah daga dikkan sharrin zaman da za mu yi, da neman alkhairin Allah wanda Aunty na ke sanar da ni duk abinda zan fad'a, ina shiga parlourn gidan ta qofar baya aka kacame da rangad'a gud'a ta parlour muka bi aka kai ni d'aki na aka aje a bakin gado, mutane na ta shiga ana ganin waje, sai santi ake, wasu ma cewa sukai daga dubai aka yi min kayan d'aki na (made in kano ne aradu) a hankali gidan ya rage daga ni sai Yayar mu Addah Ummu da Aunty Safiyya,sun gyara waje se qamshi yake, Yayar mu ce ta fasan madara gwangwani biyu ta ce in shanye ta kula ban ci abinci ba, duk da kajin da aka dinga kawo mana da abinci kala kala, na ce,

"Yauwaa yaya kamar kin san yunwa nake ji"

Murmushi ta yi, ta na bi na da kallon tausayi wanda ya ke huda jiki na, bana taba mantawa da idanun ta har a yau, sai washegari na gane tausaya min d'in da take a wannan lokacin, wajen matar da muke maqota da ita Yayar mu ta kaini ta damqa mata ni amana matar da mijin ta da qannen ta ke kira da Addah tace ta karbi amana ta Allah ya bamu zaman lafiya, yaya ta kama ni muka koma d'aki ta zaunar da ni, ta ce in dinga karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakel da duk tasbihin da ya zo baki na, na ce mata to.

A gurguje suka shirya mota ta zo ta dauke su dan kai su gidan Baffan mu dake garin kafin da safe su zo su min sallama su koma kano, ina nan zaune ko minti biyar ba a yi ba na ji ango ya shigo, ni kuma na fara had'a zufa saboda wani irin mugun bayan gari da ya matse ni, saboda tinda na zo dama ban taba yi ba saboda qarancin tsaftar bandakin gidan biki,zufa nake ina danne tusar da ta matse ni saboda na tabbata na sake ta a wajen se na rub'a d'akin nan da wari, hannu na sanya na yarfe zufar da ta karyo min ta na d'iga, kafin na bud'e ido na da na lumshe hawaye na zuba ya yi sallama, hannun shi riqe da manyan ledoji guda biyu.

Ajiyewa ya yi ya matso inda nake ya na kallo na, gani ya yi na had'a uwar zufa kamar wadda aka kara a gidan biredi, murmushi ya yi mai sauti, a zaton shi duk a tsorace nake da shi,

"Young lady ya aka yi ne? Ki kwantar da hankalin ki, taso ki zo nan"

Ban motsa ba gudun kar tusar da nake matsewa ta kufce min na kad'a masa kai alama ah ah.

Jarumtar da nake yi ne ta qare min cikin sauri na miqe na ce masa,

"Toilet nake so na je"

Se ga hawaye shaaaaarrr, nan take ya miqe tsaye shima muka fita a tare,ko da na fita na ga duhu sai na sake rikicewa,hannu ya sa ya bud'e qofar da ta raba mu da tsakar gida inda kitchen din Addah da toilet yake sai tap a tsakiyar wajen, ina shiga na ga mage ta fito da gudu da ga cikin bayin ta yi waje, wata qara na saki, na matse jiki na saboda yanda na ji kamar zan saki fitsari da bayan garin da ya matse ni a jiki na,nan da nan jiki na ya hau rawa,hawaye kuwa kamar an bude tap,ina yada hasken waya ta na  yi arba da manya manyan tsaka a jikin gani su na ta shawagi kusa da kwan fitilar wutar lantarki, da alama jira suke a kawo wuta su fara cin kwarin da ke zuwa wajen fitilar.

Kasa shiga na yi hawaye da zufa na ta karyo min, ganin haka ne ya sa Yah Maheer raka ni har cikin bayin ya ce,

"Tsugunna ki yi lalurar ki, ina nan ba zan tafi ba se kin gama, kar ki ji tsoro"

Cikin rawar murya na ce masa,

"Kashi fa zan yi"

"Eh zan juya baya na ki yi abun ki"

"Tohh"

Shine kawai abinda na ce, na hau kiciniyar kunce zani na tsugunna, ina tsugunnawa kuwa kamar jira ake na dinga kasayar da duk abinda na aje na kwanaki da ke ciki na.

Waje ya kid'ime da shegen wari, amma ko hannu ban ga bawan Allahn nan ya sa ya toshe hancin shi ba, ni da kai na zani na na sa na toshe hanci na, ganin ba zai toshe hanci bane ya sa na ce masa,

"Na dena jin tsoron ka je in na gama zan shigo"

"Are you sure? I can wait till you are done with your business"

"No you can go please, zan shigo da kai na"

A hankali ya bud'e qofa ya fita, Allah kad'ai ya san kalar iskar 'yancin da ya shaqa bayan fitar shi, ni kuwa bayan na gama sabulun maqociya ta na dauka na wanke jiki na da hannu na, na yi addu'ar fita daga band'aki wadda a take na tuna anya na yi ta shiga ma kuwa?

Murmushi ne ya kwace min na bud'e qofar shiga cikin gidan na shige na sake rufewa da kyau sannan na shige kitchen d'ina na ajiye buta a gefen drum na tsaya a wajen na kasa shiga d'aki na...........

Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all.

Continue Reading

You'll Also Like

119K 15.8K 34
#Book-3 Last book of Hidden Marriage Series. ๐Ÿ”ฅโค๏ธ This book is the continuation of the first and second book "Hidden Marriage - Amazing Husband." If...
5.5M 229K 68
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally โฃ๏ธ Cover credit...
4.3M 287K 61
"Why the fuck you let him touch you!!!"he growled while punching the wall behind me 'I am so scared right now what if he hit me like my father did to...
226K 17.2K 24
"ู…ุง ู‡ููŠ ุฑูŽุบุจุงุชููƒ ุงู„ู…ูุธู„ู…ุฉ ..ุฏูƒุชูˆุฑ ุฌูŠููˆู†ุŸ" "ู„ูŽุฏูŠ ุบูŽุฑุงุฆุฒ ุชุงูŠู‡ูŠููˆู†ุบ ..ู„ุง ุฑูŽุบุจุงุชุŒ ูˆูŽ ู‡ูู†ุงูƒ ููŽุฑู‚" ุขุฏุช ุฃููƒุงุฑ ุชุงูŠู‡ูŠููˆู†ุบ ูˆูŽ ูุถูˆู„ู‡ ุญูŽูˆู„ ุฑูŽุบุจุงุช ุงู„ุฃู†ุณุงู† ุงู„ู…ูุธู„ู…...