MAHREEN

By HAERMEEBRAERH9900

1.5K 423 71

A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na... More

MAHREEN PAGE 1
MAHREEN PAGE 2
MAHREEN PAGE 3
MAHREEN PAGE 4
MAHREEN PAGE 5
MAHREEN PAGE 7
MAHREEN PAGE 8
MAHREEN PAGE 9
MAHREEN PAGE 10
MAHREEN PAGE 11
MAHREEN PAGE 12
MAHREEN PAGE 13
MAHREEN PAGE 14
MAHREEN PAGE 15
MAHREEN PAGE 16
MAHREEN PAGE 17
MAHREEN PAGE 18
MAHREEN PAGE 19
MAHREEN PAGE 20
MAHREEN PAGE 21
MAHREEN PAGE 22
MAHREEN PAGE 23
MAHREEN PAGE 24
MAHREEN PAGE 25
MAHREEN PAGE 26
MAHREEN
MAHREEN PAGE 27
MAHREEN PAGE 28
MAHREEN PAGE 29
MAHREEN PAGE 30
MAHREEN PAGE 31
MAHREEN PAGE 32
MAHREEN PAGE 33
MAHREEN PAGE 34
MAHREEN PAGE 35

MAHREEN PAGE 6

39 14 0
By HAERMEEBRAERH9900

💅 MAHREEN  💅





WRITTEN BY HAERMEEBRAERH





PAGE 6:




"Matsalar da ke tattare da ke mana ! Wannan ai babbar matsala ce a ce mace ta na tsallaken jinin al'ada, ya kamata a shawo kan matsalar tin kafin ta girma"

Kallon na fahimci maganar ki na mata, damuwa ta kuma sai ta qara yin gaba, saboda ina tunanin wad'anne kalolin matsala ne nake tattare da su? Ina ma zan samu me yi min bayani ya fayyace min komai, lallai da na samu nutsuwa, amma babu komai, a yau ba sai gobe ba zan tinkari Mama da maganar.

Bayan na koma gida da dare kamar yanda muka saba kwanciya, cikin duhun da d'akin ya yi sakamakon kashe k'wan wutar lantarkin da mu kai,na d'aga kai ina kallon Mama da ke ta jan carbin ta, domin ta saba da hakan dik daren duniya sai ta yi tasbihi ba adadi sannan ta dora da ayatul kursiyyu cikin carbi ko kuma bacci ya dauke ta ta na tsaka da yi, gani na yi hankalin ta na can kan abinda take yi,ina jin nauyi da shakkar tambayar ta game da wannan matsalar tawa, duba da cewa a wannan lokacin ba cikakkiyar shaquwa a tsakanin mu da ni da ita, ba ma fayyace wa juna yanda muke ji game da junan mu na soyayyar dake tsakanin uwa da 'ya kamar yanda ya kamata,iyaka na san ta na iya qoqarin ta na ganin ta yi mana duk wani abu da ya zama dole ta min shi a matsayin ta na uwa, tinanin ranar da na fara yin period ne ya d'arsu a raina.....

Bana mantawa ina makarantar boko aji hud'u na dawo gida zan yi fitsari se na ga jini, na hau kuka a sirrance ina cewa na ji ciwo a wajen, Addah Ummu ita na samu da maganar ina ganin jini, nan take ta hau dariya ta na cewa na girma, Addah Ummu ita ta koya min yanda zan kula da jiki na, da yanda ake wankan tsarki, sannan ta sanar da Mama, da dare muna kwance kamar yanda muke a yanzu Mama ta kalle ni ta ce,

'To Mahreen na ji labari wajen Ummu cewa kin fara jinin al'ada, ina so ki sani a yanzu kin tashi daga yarinya kin koma babba, alqalami ya hau kan ki, aikin ladan ki daidai yake da irin aikin ladan da zan yi, aikin zunubin ki daidai yake da aikin zunubin da zan aikata,yanda Allah zai bani lada in na bauta masa da gaskiya, kema haka Allah zai baki lada in kin bauta masa da gaskiya, yanda Allah zai bani zunubi ya sani a wuta in na aikata zunubi kema haka Allah zai maki, yanzu an bud'e maki littafi a wajen Allah, idan ki ka furta kalma d'aya sai an rubuta ta, idan ki ka fad'i me kyau a baki lada, idan ki ka yi mara kyau a baki zunubi, sannan ki sani kamar yanda zan d'auki ciki in haihu, haka kema duk sanda ki ka tsaya mu'amala da namiji wanda ba mijin ki ba kema zaki dauki ciki ki haihu, ki tsare mutuncin ki, ki kare martabar ki, kar ki zama ki na wasa da maza ko ki na bari maza na wasa da ke, namiji in ba muharramin kin ki bane(Mahaifi, yaya da ake uwa d'aya uba d'aya, ko wanda aka had'a uba kawai, ko wanda aka had'a uwa kawai,ko qanin uwa ko qanin uba, ko kakannin wajen uwa da uba, wanda a yanzu zamanin nan da muke ciki su kan su ba abin yarda bane)ko hannu kar ki bari ya tab'a maki, saboda had'uwar hannun ku waje d'aya kamar aikata zina ne kuma aikata zina babban haramun ne,Mahreen ki ji tsoron Allah a dik inda ki ke a kuma duk halin da ki ka samu kan ki, sai Allah ya so ki, kuma ya kiyaye ki daga dikkan sharri, kina ji na ko? Na ji ta ce ta koya maki yanda ake kulawa da jiki, da kuma wankan tsarki, akwai wasu abubuwan da zan koya maki a hankali inshaa Allahu, Allah ya muku albarka baki d'aya'

'Ameen' shine abinda na amsa da shi a wancan lokacin, to yanzu gashi an ce akwai matsala idan bana yi akai akai anya in sanar da Mama kuwa ko dai na yi shiru, ko na bari sai na je gidan Inna ta se na fad'a mata tinda ni na fi shaquwa da ita sama da kowa, ba abinda nake b'oye mata duk wani sirri na da ya kamata Mama ta sani da Innata nake yin shi sai dai in bama tare, shahada na yi na tashi zaune sosai na ce,

"Mama? Ko kin yi bacci?"

"Na'am ido na biyu, ya aka yi?"

"Uhmmm damaaa...damaaa ina so immmm na maki wata magana ne,"

Hankalin ta ta tattaro ta miqo min dika, tare da juyowa saitin inda nake muka fara fuskantar juna.

"Uhumm ina jin ki, akan menene?"

"Mama dama wannan watan ban ga period d'ina ba, kuma ya na min tsallake shine Maman Ihsan ta ce na sanar da ke akwai matsala"

Shiru ta yi kamar ba zata yi magana ba, can na ji ta ta na cewa,

"Iya sanin da na maki ba kya shashanci balle a ce ciki gare ki...."

"Ciki?? Ciki na me?"

Banza ta yi da tambaya ta, sannan ta ci gaba da magana,

"....Amma inshaa Allahu zai daidaita ai da yake kin fara ki na da qarancin shekaru wataqila shi yasa yake hakan"

"Ok kenan ze daina? Amma mama na ji kin ce ciki"

Bata sake kula ni ba ta juya ta ci gaba da jan carbin ta, ni kuma da tinani na kwana a raina.

Washegari mu na magana da Maman Ihsan nake mata bayani, ta ce.

"kwarai, nima ba dan na san halin ki ba sai na ce ciki ne, amma kuma sanin ke wacece shi ya sa ban ma kawo maki wannan maganar ba, tinda ba lallai ne ma ki fahimci me nake magaba akai ba, kamar yanda ki ka yi a yanzu"

Na sha mamaki sosai da na ji cikakken bayani akan idan mace ta dena jinin al'ada ya na iya yuwa ciki ne, wannan shine babban kuskure da aka tafka tin asali na qin tsananta bincike akan matsalar rashin yin jinin al'ada da bana yi a jere yanda ya kamata.

*******************************

Kasancewar asalin tushen Innata shine garin Daura muna yawan zuwa da ita lokacin da nake hannun ta sun sanni na san su sosai, haka ne ya sanya Innata tafiya da ni ana biki na saura wata d'aya, tafiya ce da ba zan tab'a.mantawa ba a rayuwa ta, saboda gata da qaunar da dangin mahaifiya ta suka nuna min, na sha addu'o'i da fatan alkhairi, ga abubuwan azziqi da akai ta bani a matsayin gudummawar aure na, abu d'aya Innata ta hana a bani shine kayan mata, bana tina sha ko cin komai da ya danganci maganin mata, illa tukud'i da na sha da madarar shanu tabbas na sha madarar shanu sosai da kindirmo ba iyaka, kasancewar  Sana'ar Inna Habi ne saida tukud'i kusan kullum sai an daka shi, nono da madara kuwa kusan ko ina muka je ana kawo mana da fura, ni ba ma'abociyar shan fura bace sosai a da,shi ne dalilin da ya sa nake shan nonon ko madarar na bar furar, haka muka gama zaga dangi muka juyo ana biki sauran sati biyu.

Direct gidan mu Innata ta maida ni, Mama na kwashe shanya a inda muke shanya wanki, ko shiga gidan Inna bata yi ba kasancewar magariba ta yi, a tsaitsaye mama ta leqa suka yi sallama a lokacin Addah Ummu ta zo biki na da cikin ta na fari wanda in ba ka kula ba ba zaka gane akwai shi ba, a tare muka qarasa nad'e shanyar kayan da Mama ke nad'e wa kafin zuwammu, muna kwashewa ina zuba mata hira da irin abubuwan da aka bani, da nasiha da addu'o'in da na sha a wajen manyan mutanen da muka je wajen su.

"Tabbas ga kaya nan niqi niqi an dawo da su Allah ya saka masu da alkhairi, Allah kuma ya amsa addu'ar su ya biya su da alkhairi"

"Ameen" na furta muka shige cikin gida, na tadda Addah Ummu kwance kamar ruwa,dan kuwa cikin ba qaramin wahala yake bata ba, hira muka fara sosai ina ta mata tambayoyi ita kuma ta na amsa min ba tare da gajiyawa ba, inda take sanar da ni Addah Firdaus na nan tafe itama, murna na dinga yi ina kumawa, baqin ciki na d'aya da ya kasance Addah Babba ba zata samu damar zuwa ba saboda tsohon cikin da take dauke da shi.

Tin da na tafi muke waya da Mansoor, shi kuwa Yah Maheer be damu da kira na ba, hakan kuma na mugun qona zuciya ta, ta ya za a yi ka zo rumi rumi ka nemi auren yarinya ya zamana ba ka kiran ta sai sanda ka so? 'yar I love you d'in nan tinda aka fad'e ta sau d'aya ba a sake ba, duk sanda zai kira waya har na harda ce abinda zai tambaye ni akai.

"Assalamu alaikum"

"Da fatan ki na lafiya?"

"Ya mama da baba da su Ummu Salma? (Qanne na kenan)"

"Ya makaranta? Allah ya bada sa'a,"

"Sai anjima a gaida mutanen gida"

Wannan shine hirar mu a kullum,gefe d'aya kuma ga Mansoor da kowa da ya sammu ya shaida irin qauna da soyayyar da yake min, qarshe dai har gida na kaiwa qanwar shi da muke qawance katin aure na, sannan na bashi nashi a hannu da na abokan shi, Mansoor ya shiga matsananciyar damuwar da fad'in ta ma zai zama kamar na tauye yanda yake ji akai na.

Haka zalika nima na sha kuka da baqin cikin rabuwa da shi a lokacin da nake dawowa gida, a hanya muka had'u da Baba zai je masallaci dan yin sallahr magriba, ina sanye da dogon hijabina da niqabi na ina kuka a cikin shi, shiga ta da yanda na nutsu a cikin hijabi na ya ba wa Baba sha'awa har sai da ya tsaya ya min wasa sannan ya wuce, da a lokacin ya kula da kyau da ya gane kuka nake amma sam be fahimta ba ko da na shiga gida na tarar da Mama ta je kasuwa an yi min siyayya sosai ta na can ta na sallah a d'aki, nima bathroom na fad'a na yi alwala na zo na tada sallah, cikin sallah ta nake ta addu'ar samun nutsuwar zuciya, da fatan Allah ya yaye mana son junan mu da muke ni da Mansoor, ina idarwa na tadda Addah Ummu ta zauna gaban kayan ta na ta nuna min ta na murna har qasan raina nima na ji dad'in ganin kayan amma hawayen da ke sintiri a kunci na sun kasa tsayuwa, a zaton ta tsabar farin cikin ganin kayan ne, tinda kowa ya sanni da saurin kuka, ga wake da shinkafa ta dafa ta zuba min, kai loma kawai nake amma zuciya ta a quntace take, a hankali na shanye duk wani baqin cikin da ke taso min a raina saboda ganin kayan nan sun faranta min rai,mu nan a haka har Baba ya dawo daga masallaci ya shigo gida,muna zaune da shi a parlourn Mama Ummah ta kira ni, ina shiga na ga manyan tukwane baqaqe masu kyau da marfin glass da Silva,ban taba ganin irin su ba a lokacin nan, da sauran tarkace na kitchen Umma ta bani ta ce nawa ne,na yi farin ciki sosai sannan na mata godiya,Baba ma da ya shigo ya gani sai ya yi mata godiya sannan na koma d'aki na kwanta a gado, ina ci gaba da sharar hawaye na,ina matuqar son Mansoor amma dole zan yi hakuri da shi, tinda ko aure ma bai tashi yi ba da ace zan kammala secondary ne wataqila da min yi aure, amma hakan ba mai yuwa bace, dan haka zan bi zab'in iyaye na inshaa Allahu mai kyau ne a waje na, tinda ni kaina shaida ce akan kyawawan halayen Yah Maheer,mutum ne da zai wahala ka zauna da shi be burge ka ba, abu d'aya na sa wa zuciya ta shine .

Zan yi hakuri, zan zauna da shi a duk halin da yake ciki, ko da be iya soyayya ba kamar yanda na kula, zan yi zaman hakuri har Allah ya sa watarana na so shi.

Ana sauran kwana takwas biki da dare Yah Maheer ya kira, bayan na amsa sallamar shi na gaishe shi kamar kullum, ya min tambayoyin da suka zama kamar karatu, na amsa mishi, sai na ji ya na magana kamar ya na jin kunya ta, cikin murmushi na ce,

"Yah Maheer kamar ka na so ka yi min magana akan wani abu ko?"

'Eh Young lady, baki ji me na ce ba?'

"Ah ah ban ji ka ba, maganar ta yi can qasa qasa"

'Ke dai ko ki na so na maimaita ne shi yasa'

"Allah da gaske ban ji ka ba"

Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce,

'Ok shi kenan...sanda aka kawo ki gida na a ranar zan maimaita maki.me na ce, a ranar ne ma za ki fi fahimta ta, yanzu ko na fad'a ba zaki gane ba'

"Try me, ka fad'i abinda za ka fad'a ka dena boyewa"

"Ohhhh i should try you haa? Kar ki damu veeery sooon ma kuwa, bari na barki haka a je a kwanta i love you so much, na matsu ki zamo mata ta, mallaki na, halaliya ta, na matsu na gammu a inuwa d'aya a matsayin miji da mata, Allah ya nuna min wannan rana"

Ji na yi kamar ya d'ora min dala da gwauron dutse a kaina, dama yana magana haka? Dama ya iya kalamai haka? Ikon Allah, mutumin da kamar kunya ta yake ji?

Kasa cewa komai na yi duk da magiyar da ya dinga min akan in ce ina son shi ko sau d'aya ne, kunyar shi ma ni nake ji yanzu, ya yi taking d'ina by surprise with his golden words da suke kad'an amma masu tasiri a zuciya ta, domin a da ni ina tantamar soyayyar da ya ce ya na min, tinda baya nuna wa, amma a yau na yarda da ya na so na, akwai dai abinda ya ke hana shi bayyanawa. (Ba tare da na sani ba ashe jira na yake na shiga hannu)

Hidimar biki ta kankama here and there, kowa ka gani da abinda yake yi, biki na ba a tsara kashe kud'i ba, in fact ba ma a kashe kud'i sosai ba kamar yanda akai wa yayu na, amma fa kowa ya yaba ya kuma sanya albarka a ciki, dan kuwa kowa da ya samu halartar bikin ya ci ya sha ya tafi da na riqewa a hannu,a gidan kakata ta wajen uba akai kamu, a can Fagge makarantar Malama Fati aka so yi, ba a samu yi a can ba se ta wakilta manyan d'aliban ta suka zo har gidan kakata aka yi kamun cikin d'aliban har da aminiyar Mama wato Baaba Binta,a nan mata sukai waqe waqen su na islamiyya da duk wani abu da suka saba yi in ana kamu, turare kam na sha shi, ga jan qunshi da baqi da aka yi min, ga laffaya ta kalar green da na sanya, sai na fito sak irin matan nan na sudan irin 'yn kub'ul kub'ul d'innan, ranar kusan kwana mu ka yi da qannen Babana da muke kusan sa'anni da su, duba da cewa ina da qawaye amma sakamakon rashin zuwa gidajen su da bana yi ba wanda ya bini nima wajen kamun daga ni se dangi na, (Alhamdulillah muna da yawa dan haka ban yi kewar rashin qawaye ba da biki na), da sassafe aka maida ni gidan mu dan yin dinner.

Amarya dai ga ta nan ba kwalliya daga hoda se kwalli, amma babu mai cewa ba a min kwalliya ba, saboda yanda fuskata ke sheqi, domin ni ko irin gyaran jikin nan da ake wa amare ba a min ba, hasali ma wasu gani suke shekaru na sun yi qanqanta a min aure,Mama kuwa ko dabino bata bani ba a matsayin wai za ta aurar da 'ya ta ce ga maganin mata, haka nan nake sungul hamama kifin gwangwani,Addah Ummu da qawata  'yar uwa ta kuma aminiya ta Widad sai su Aunty Ruqayyah da Aunty meenah sune tsaye akan komai kafin daga baya Addah Firdaus ta zo, kuma sun yi matuqar qoqari dan ganin komai ya yi yanda ake son shi.

Kamar abun wasa ana tsaka da dinner ne Mansoor ya zo da qannen shi guda biyu, Ikleema na riqe wa hannu a lokacin da na hango ta, ban damu da me za a ce ba ganin na bar wajen zama na na nufe ta.

A kunne ta sanar da ni cewar tare suke da Mansoor ya na can baya wajen flowers, ban bata lokaci ba wajen tuje gwaggwaron kai na na maida d'ankwalin leshi na kalar coffee na bi duhun dajin unguwar ina neman shi, can na hango shi nesa da wajen da ake dinner, ya na zaune ya kife kan shi a jikin motar da suka zo da ita, ina zuwa sai na fashe da kuka, domin ba qaramin tausayi ya bani ba, kuma ko ba komai nima ina son shi kamar yanda yake so na.

Kasa magana ya yi kawai se ya sa hannu a aljihun shi ya zaro hotunan mu da muka dauka a lokacin da na je kai musu katin aure na a wani gidan hoto na Tonye wasu couples ne yoruba, ina kallon hotunan ina murmushi da ya ga na gama kallon su ina qoqarin riqewa sai ya sa hannu ya karba ya yaga su, a lokacin ji na yi kamar ya ci mutuncin soyayyar da na yi shekaru ina yi masa, kuka na sake fashewa da shi, har a wannan lokacin be iya furta kalma d'aya ba, illa hannun shi da ya sake sanya wa a aljihun shi ya dakko hankici ya hau goge min hawaye na da su, a hankali na yi shiru na dena kukan da nake, cikin dasasshiyar murya ta fuska ta d'auke da murmushi na ce masa,

"Zo mu je na nuna wa 'yan uwa na kai"

Ba tare da ya min musu ba kuwa ya bi baya na, tafe muke shiruuu ba me cewa kowa komai a tsakanin mu har muka isa inda yayu na suke tsaitsaye suna hira, na hau introducing din shi gare su,Yayana Abdul (My twin💕) ya kama ni a gefen hannun shi na dama ya ce,

"Shegiya ashe ki na tsoro na, ai da baki taba fad'an ki na da saurayin da ku ka shaqu haka ba se yau, to kai aboki na ba dan qanwata ta yi aure ba ai da an yi ban gishiri in baka manda, nima na gani ina so"

Qanwar Mansoor ya kalla wadda take da kyau sosai kamar yayan ta,murmushin yaqe kawai Mansoor yake yi kuka kuwa ya sha shi har ya gaji ya dena, dare ya fara yi dan haka qannen shi ne suka yi gaba tare da abokin shi da ya rako su,mutane ana ta tattafiya gida har da qawaye na na makarantar Army day da suka zo.

Shi kuwa ya samu wani waje mai duhu da ciyayi ya zauna ya zura qafar shi a ciki ya na hawaye, d'aya daga cikin aminan su Addah Ummu ce ta same shi a haka, (Aunty Meenah) ta ce masa,

"Kai kuwa bawan Allah ka yi hakuri mana, inshaa Allahu Allah zai baka wadda ta fi ta"

D'aga kan shi ya yi ya kalle mu,sai a sannan ya samu bakin magana ya ce,

"Anyaaa? Anya kuwa zan tab'a samun wadda ta fi ta kuwa?"

Aunty Meenah ta ce,

"Allah fa na ce,"

"To na yarda tinda kin ce Allah,"

Daga nan be sake magana ba, haka ya kama hanya ya tafi, ganin da na masa kenan ba tare da mun sake yi wa juna bankwana ba.

A haka aka gama dinner aka tattara muka koma gida aka dasa sabuwar hira a qofar gida, sai da dare ya raba sosai sannan kowa ya nemi wajen kwanciya.

Washegari tin da asuba da na shiga alwala na tarar da ruwan wanka an kai min, dan haka wanka na sheqa abuna na daura alwala na fito, shiryawa na yi cikin wata atampa mai ja a jikin ta da ratsin baqi, ta yi min kyau matuqa ainun, ta yanda tin kafin na yi kwalliya kowa ya ganni sai ya yaba kyawun da na yi.

Kafin goma na safiya gidan mu ya qara d'inkewa da mutane ba masaka tsinke, ana ta yinin biki, abinci kawai ka ke gani ko ta ina, kowa ka kalla bakin shi washe saboda farin ciki, da azahar bayan sallar juma'a ina tsaye a tsakar gida sanye da leshin da na sauya kalar blue me haske wanda Addah Babba ta aiko min daga Lagos na jiyo muryar maroqa da maza a waje ana sanar da tabbatuwar  d'aurin aure na da ni da Yah Maheer.

Nan take na durqushe a wajen na fashe da kuka, mutane aka yo kaina ana ta min dariya, masu yi min waqa irin ta amare na yi, masu cewa kukan gulma ne na ga na samu miji bafulatani son kowa qin wanda ya rasa, in bana so su na basu shi.

Haka dai na samu na zame zuwa d'akin Ummana nai kwanciya ta a gado.

Ba jimawa Yayah Babba da Goggo Maryama suka shigo suna cewa na tashi na sake yin wanka na shirya cikin wannan shaddar yanzu za a tafi.

"Za a tafi ina?"

"Gidan ki mana, can bauchi, tinda an d'aura aure zaman me zaki yi?"

Kuka na sake fashewa da shi, ina cewa ni ba zani ba, Goggon Yah Maheer ce ta ratso cikin mutane ta na lallashi na, cikin jin nauyin ta da kunyar ta ya sa na miqe na shiga bathroom, na hau wanka, ina yi ina kuka, a haka na gama na yi alwala na fito.

Shadda ce kalar dark blue sai farin mayafi da farar jaka da farin takalmi, nan fa 'yan uwa na suka hau shirya ni, ana feshe ni da turaruka, nan take na fito sak amarya, Innar Yah Maheer da Goggon shi sai 'yan uwana su ne ke riqe da ni, ko da na fito sai na ji suna fad'in bari a kai ta wajen Mama ta mata nasiha, daga bakin qofa Mama ta ce,

"Ai ni fatan alkhairi da sanya albarka ne a tsakanin mu, iya shekarun da ta yi da ni in bata ga yanda nake zaman aure ba ta je ta yi duk yanda ta so,ni dai yau na san gado da kujera ta sun huta, Allah ya baku zaman lafiya ya had'a kan ku ya baku zuri'a mai albarka"

Dariya aka yi saboda yanda take maganar da barkwanci amma duk wanda ya saurara sosai ya san cike take da kewa tin kafin ma na tafi.

Muna isa zauren gidan mu fa na birkice se mun kusan fita daga soro na ruga gida ina kuka, haka za a bi ni a kamo, se da na yi haka sau uku ana hud'un ne Baba ya iso gaban mu ya kama ni ya rungume, ina jin Babana ne ya riqe ni sai na riqe farar babbar rigar shi na sanya kuka mai tsuma zuciya, hawaye Babana ya dinga sharewa shima ya na furta,

"Shikenan yau Uwar tuwo na za ta tafi gidan ta,ki yi hakuri ki dena kuka,da haka kowa ya fara ya gina iyalin shi,ki yi hakuri ki je ki yi zaman ki a gidan mijin ki cikin amincin Allah, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka,inshaa Allahu zaki yi farin ciki a cikin wannan auren"

A haka muna tafe ya na rad'amin kalaman shi masu sanya ni nutsuwa ya bud'e marfin motar da Innar Yah Maheer ke zaune ciki ya saka ni, mota ce ta d'aya daga abokan Yah Maheer d'in,ina shiga Goggon shi ta zauna a d'ayan gefen nawa matar qanin Baba na gaban motar, ina kuka a hankali Mama ta leqa kan ta ta window ta ce,

"Maza a tafi gado na da kujera ta sun huta Allah ya kiyaye hanya"

Goggon Yah Maheer wadda take matsayin qanwa ga Baban mu ce ta yi wa Mama daquwa ta ce,

"Ka ji shashashar uwa, ke ana kukan rabuwa da 'ya ke ki na murna ki duba ki ga Yaya yanda yake kuka"

Mama ta sake saka dariya ta ce,

"Ai ni kyale ta na yi da niyya ta ma se na rama lotsa min kujeru da ta yi da wannan tuma tuman mazaunan nata"

"Kai d'annan jamu mu tafi ni ban tab'a ganin irin wannan uwar ba,"

Mama na dariya wadda da kowa zai kula zai gane cewar yaqe kawai take, haka aka ja mota mu ka yi gaba, mu na tsaka da tafiya muka hango wata mota a guje a gaban mu, gudu take kamar wadda bata da burki,da sauri Alhaji abokin Yah Maheer ya taka burkin motar,muka tsaya a tsakiyar unguwar mu shima mamallakin waccan motar ya taka burki ya bud'e marfin ya fito............

Mutanen k'warai masu albarka in an karanta sai a dangwala min yatsa a star din nan hilis...sannan a Yi sharing da abukkai....se a zuba sharhi saboda shine taki na... love 💕 all.

Continue Reading

You'll Also Like

1.4M 35.2K 47
When young Diovanna is framed for something she didn't do and is sent off to a "boarding school" she feels abandoned and betrayed. But one thing was...
592K 49.1K 24
Indian Chronicles Book III My Husband, My Tyrant. When Peace Becomes Suffocation. Jahnvi Khanna has everything in her life, a supporting family, a hi...
867K 72.2K 34
"Excuse me!! How dare you to talk to me like this?? Do you know who I am?" He roared at Vanika in loud voice pointing his index finger towards her. "...
467K 13.9K 61
Silent, unforgiving and strikingly gorgeous, Rylan Parker is a cold-hearted businessman. An intimidating CEO, perfectly fitted in tailored suits and...