YADDA NA KE SO

By Dijen-sy

918 100 44

YADDA NA KE SO burin Ummi ta auri mijin novel ,Mai arziki ba ta son talauci ya rayuwa zata juyawa mata a sand... More

Shafi 1
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Page 22
Page 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29

Page 2

27 6 1
By Dijen-sy

YADDA NA KE SO🌺

BY DIJENSY

Page 2

       


      Yashe ta tarar da Ammyn  a parlor Ummi tayi kanta tana jijjiga ta "Ammyy ,je ki kira Nasiru Yusrah dakko wayarta na kira Baba na shiga uku Ammy na ki tashi".

  

1hr later

  Tsaye suke sunyi carko carko a bakin gadon ,banda Ummi da ta ke tsugune bakin gadon Ammyn tana hawaye.

  "Ummi ki tashi Ammynki tana bukatar hutu anjima kya dawo d'akin kafin nan ta tashi.

  Baba ya fad'a ta taso gwiwa a sanyaye suka fito ,dai dai nan yaya Abdul ya karaso hankalinsa duk ya tashi .

" Baba ya jikin nata?"

  "Tana samin sauki ,yanzu hutawa take anjima idan ta farka zaku ganta waya fad'a maka?"

Ummi ya kalla ta sunki da kai hakan ya tabbatar masa itace ta fad'a"Ke ba na ce miki kar ki kira wani ba".

Shiru tayi ba amsa Baba yace"Ina fatan dai baka kira sauran Yan uwanka ba?"

Kai Abdulbasit ya jinjina baba ya ce "Samu guri ki zauna ,zan sanya Nasiru ya kawo muku kayan Ammynki ,gida Zaki koma anjima akwai Yaya saa (Yayar Ammyn da take zawarci mijinta ya mutu ya barta da yara) zata zo ta zauna da ita".

  Can ta hangi Shaheeda ta k'arasa gunta "Kiyi hakuri zata samu sauki".Ta fad'a mata tana dafa bayanta Shaheedan Ummi ta jinjina kai.

  Ammy wajen karbe 9:30pm ta farka,suka shiga duba ta kowa gwiwarsa a sanyaye ,murya kasa kasa sukai magana da ita Abdulbasit yake tambayar tun yaushe ne bata da lafiy haka don ya lura ba yau ne rashin lafiy ya kamata ba Baba bai masa wani cikakken bayani na kawai dai yace masa ulcer ce me tsanani a lokacin ganin Ummin a gurin.

  Lubabatu ta kawo kayan Ammy   Anty saa ta zo , Abdulbasit ya maida su Ummi gida aka sauke Shaheeda kofar gidansu.

    Kusan daren kwana tayi bata yi bacci ba Ummi ta kaisa washegarin tayi ta koma asibiti dukda akwai makaranta kuwa ,safiya nayi ta shirya Lubabatu ta gani har ta yi girkin karyawa ta sa a flask ,ta duba yaya Abdulbasit a daki shima ya shirya yace makaranta fa tace sai ta je dubata tukun a ranta kam ta niyyata bazata ba.

  Shi ya kaita bayan Lubabatu ta sanya abincin a mota.Jikin nata da sauki ,gefen gadon ta zauna ta hau tambayarta kadan kadan take amsa mata.Suna zaune nurse ta shigo take sanar mata zasu je da ita ayi mata gwaji ,daga Ummi har Abdul din Basu San ko na mene ba ta dai fita da nurse.Baba ne ya tashi ya kirawo Abdulbasit din waje Ummi na ciki sai Anty sa a ,wayarta ta bud'e data nan ta d'an yi chat da kawayenta take sanar musu jikinta da sauki sannan tayiwa Yusrah gaisuwa.A lokacin Khalil ya kirata ya ke mata ya me jiki basu wani dade ba sukai sallama ta sauke wayar.

  
Baba  gefe ya ja Abdulbasit ya soma fada masa sababin ciwon Ammyn.Tunda ya soma gwiwarsa ta kasa rike kafarsa  kwakwakaran motsi  ya kasa jin anbaton cancer maihaifa.

  "Addua zakuyi mata ,a cikin sati na gaba zamu fita ,so idan hutu ka dauka zamu iya tafiya da kai Ummi sai Anty saa su zauna gida idan Kuma zata koma wajen Hajiya (Kakarta) to kafin dai mu dawo".

Kai kawai yake jinjinawa ,kafin nan suka koma ciki.Ta dau tsahon lokaci kafin ta dawo Ammyn ,nan Anty saa ta zuba mata dankalin da liver source da luba tayi kadan ta iya ci Ummi ma ba ta ci sosai ba ,da Baba ya mata maganar ta tashi ta tafi school ta sanya rigima tana shagwa'be wa a jikin Ammy  ya girgiza kai Ammy tace ya rabu da ita.Anty sa a kam tabe baki tayi ta ga tabara irin ta Ummi kamar zata sha nono ta nanike ma Ammyn uwa ba mara lafiy ba.

     ★★★

 
   Bugun kofar su Haydar ne ya sa shi bude ido daga kwance,yana tashi ya bud'e musu sunyi cirko cirko "Yaya kud'in makaranta".

  Suka fad'a sun shirya cikin uniform ya juya wallet dinsa ya duba Yana zaro 500 ya mika musu tare da musu Allah kiyaye.

  
    Komowa yayi ya zauna duba agogo yayi 10am ya daga gira da mamaki don bai cika yin bacci haka dayawa ba.Toilet ya shiga yayi wanka ya fito ya shirya cikin jean blue da riga grey t shirt ya dakko waya ya fito.A kasa ya iske Hassana "Je ki gyaran d'aki na".

     Amsawa tayi ba taso ba ba yadda zatayi ,ta rasa wani irin lalaci Yaya yake ji dashi yana yin duk wani aikin gida ya iya sai dai ba abinda yake masa wuya irin gyara katifa da share d'aki ,amma girki da shirya yara kuma bai bashi wuya.

     A parlor ya iske Umman ya gaisheta ta amsa "Abincin gidannan ya kusa karewa kuwa ,Abeed Bai da lafiya ina son kai shi asibiti".

  "Me yake damunsa?"Ya tambaya tace "Ina tunanin dai malaria ce amai yake da zazzabi".

     
"Allah bashi lafy".Ya fad'a tare da zaro dubu biyu ya mika mata ta amsa tana jujjuyata tayi zaton dubu uku ne "Anjima zan gani ,idan na dan samu wank abu sai na taho da kayan abincin".Ya fad'a sannan ya fice daga gidan  , matsalolin goma da ashirin sun tsaya masa a rai ga matsalar gidannan ga jiya da daddare Rasheeda kanwarsa ta kirasa take fad'ar tata matsalar za ai ma yaronta aiki a ciki.

   'Allah ka kawo min daukii ya furta a zuciyarsa.

  Cafe ya wuce kai tsaye ,dukda abokin nasa yasan rashin maganarsa sai  dai yau ya kula tunda ya kafa idonsa a system bai dauke ba kala baya cewa ana ta hira a gun.

"Mutumin me ya faru ne yau naga ka dauke wuta?"Abokin nasa ya tambaya.

Jingina Mukhtar yayi da kujera "Shafiu bazaka gane bane abubuwa sun tarar min aka na rantse".

  "Toh ya za ai sai hakuri ka daina d'orawa kanka damuwa ka dinga ajje ta a gida ,wanann rayuwa mutum ba zai kashe kansa ba fa mutumina".

  Murmushin ya'ke yayi kawai don sam abinda shafiun yake fad'a bazai yiwu ba,maida kallonsa yayi ga system din yana karasa project din wata da yake yiwa.

 
  *****

   Kwanan Ammy uku a asibiti aka sallameta ko da suka dawo gida ,tunanin yadda zata sanar wa da Ummi take zuwansu India ,ba ta sani ba Baba ya fad'a mata sai dai bai sanar mata da ciwon da ke damunta ba duk ta bayar ulcer din ce.

    Damuwarta daya shine ba da yarinyar zasu tafi ba ,Umar da Hafiz sun sanar dasu sai dai dukansu basu da labarin ciwon da ke damunta.Ana e gobe tafiyansu suka zauna dukansu hudun a parlor sunyi hira wacce suka dade basuyi ba har ma Ummi take jin ina zasu dawwama a haka don rabon da a hadu sun jima, don ma ba su Umar sai to 11 Baba ya ce ta je kowa ya kwanta sabida around 9am washegari jirginsu zai tashi.

 
    Tun da sallahr asubah yau Ummi ba a koma bacci ba dukda cewa weekend ce ,sai ta ya Ammy shiryawa take motsi kadan tace Ammy zanyi kewarki sai kawai ta ce nima.Bata lura da hawayen da yake kwaranya idanun Ammyn ba gabadaya ta tsorata da ciwon ,a yanzu haka wani bleeding take yi.Har airport sai da ta raka su ta dubi Ammy "Allah Kara sauki Ammy nasan me magunguna kawai za a baki ku dawo don dai Baba ya matsa anan ma zaa iya baki maganinki dole sai dai ya sani kewarki , shikenan ai Allah kiyaye hanya yasa ki dawo da wuri".

  "Ameen ,Khadija ki kula da kanki kinji ,be a good girl kamar yadda na sanki banda bari bari a dinga Jin magana Kuma Ake zuwa makaranta exam is approaching two weeks ya rage ko?

Kai ta girgiza "4 Ammy da saura ai".

"Tohm fatan Alkairi a rayuwa yayi albarka I love you daughter "

Ta kare kalmar tana rau rau duk irin dauriyarta Ummi ta kwabe fuska tana so tayi kuka Baba ya kira Nasiru "Zo ku wuce ai anyi rakiya yayi haka ,Anty sa a sai mun dawo ko?"

  "Tohm Allah tsare ya sa ayi a sa a ".Ta fad'a.

  Kamo hannunta tayi suka wuce mota ta shiga zuciyarta a cunkushe Nasiru ya ja su ,Ammy kuwa  suna tafiya ta fashe da kuka Abdulbasit ya bita da ido "Haba Ammy mene hakan ki shiru please komai zai zo da sauki".

  Har suka shiga jirgi tana sheshekar kuka ,Ummi ta koma gida ta hau gado sai kuka kawai take yi ,ranar yini guda a daki tayi sai bayan Maghreb ta fito parlour ta iske Anty saa na parlor ta zubo abinci "Yan Ammy kin ga dama kin fito kenan,kodayake yunwar cikinki ta fito dake ".
  
   
  Kitchen ta shiga ta debi abincin ta fito parlour banda wasa da cokali ba abinda take ta mayar kitchen ta ajje ta koma daki.

    Isarsu India Ya Abdulbasit ya kira ta ya fad'a mata Nan ya hadata da Ammy sukai waya ,ta dan ji relief jin muryar tata".

   ★★★

   Duk yadda ya so ya kwammata ya samu kudin da zai iya fito da lissafinsa Allah bai yi ba haka ya hakura iya na abinci ya siya shima ba komai ba ,ya bawa Rasheeda hakuri tana da aure sai dai mijin sam ba wani motsi rabin matsalolinta yaya ke yi mata hakuri kawai take tana lanjarawa don ta taba yin yaji kuma zaman yaki dad'i ita da Umman su Haydar din  dole ta hakura ta koma gida.

     A wajen me shayi ya tsaya ya amshi  ruwan bunu da bread don yasan ba wani abun zai samu a gida ba ,ya shiga gida ya haye sama a binsa .

   Sako ne ya shigo wayarsa yana daf da loma biredinsa ya duba ya ga "Safna"

_Na kira ka ba ka amsa kirana Mukhtar ni kam mai na maka? Please let me know I can't bear the pain dan Allah kayi hakuri I love you reply my message_

  "Ke bazaki fahimta bane wai ? Na rasa gane kan yarinyarnan tun dare bai miki ba ki je ki aurenki ina zan kaiki ina fama da kaina ina zan iya , ana ta kai wa yake ta kaya"Mukhtar ya fad'a a ransa yana soma typing kamar haka.

_Please Safna kiyi hakuri bana son bata miki time just move on because I am not ready for marriage a yanzun kiyi hakuri_ Yayi sending Yana ajje wayar ya cigaba da cin biredin sa.
  
    
    *****

A firgice ta tashi daga baccin da take wani irin mafarki tayi mara dad'i ,ta tashi zaune fitilar wayarta ta kunna tana motsa kafa ta tashi ta kunna light na d'akin 5:20am ta gani ,alwala tayi  ta daure ta zo ta gabatar da sallah ta idar ta yiwa Ammy addua sauki.

   Data ta bude ta ga chats da bata bude ba da yawa , contact Yaya Abdulbasit ta duba ta ga ko yana online bata gani ba ta duba Baba shiru.Zama tayi tayi jugum tana tunanin mafarkin da tayi.Karfe shida ta fito parlour Bata ga Anty saa ba taje dakinta ,gaisheta tayi ganinta kan sallaya ta Dan Yi shiru ,Anty saa ta mata nuni da gado.

  "Ammynki anyi aiki wajen 1 mukai waya da Babanki anyi mata aikin ,ki taya da addua in sha Allah anyi a saa.

  "Aiki?"

  Waiwayowa tayi Anty saa "Ehman ba ki sani ba ai aiki aka  mata ".

  Nan ta soma tunanin ko boye ma yarinyar akai "Aiki aka mata in sha Allah ta samu sauki".

  "Ca sukai min doctor zata gani".

  "Basa so ki shiga damuwa ne Mamana ,addua Zaki mata".Anty saa ta fad'a.

  Kai ta jinjina hawaye na silalo mata ,kasa komawa d'akin tayi kadan suka taba hira da Anty Sa a sannan da gari ya washe ta fita kitchen ta tarar da luba tana aiki.

"Luba kinsan wai aiki aka wa Ammy ?"

Kirji ta dafe da mamaki "Ke Dan Allah Ina na sani ? Na bayar likita zata gani a can d'in".

"Wai boyen sukai kar ma damu duk ma ni sun tsoratani ".

"Zata samu sauki in sha Allah ".

"Ameen,nasan bazasu dawo da wuri ba".Ta furta.

   Yau for the first time ta ce zata soya kwan nata da kanta don idan ba Ammy ba bata mata dad'i.

  
Da wajen 12 suka yi waya da Abdul nan take masa complain yaji ta san aiki akaiwa Ammy hakuri ya bata ya tabbatar mata da ta farfado ma anjima zai bata wayar su gaisa idan ya sake shiga dubata.Da toh ta amsa sannan sukai sallama.

   Gidansu Yusrah ta shirya ta je domin debe kewa tayi ta duba wayarta ko ya Abdul zai Bata su gaisa da Ammyn shiru ,da misalin 4pm sai ga me aiki su Yusrah ta kirata.

  "Wai kije inji Hajiya".

Tashi tayi ta fita ,a dakinta ta tarar da ita "Yusrah,yanzu abbanku ya min waya sunyi waya da babansu Ummi Hajiya Rabia lokaci yayi".Mommy ta fad'a muryarta na rawa.

Wata iriyar razana tayi Yusrah  ta tsuguna tana dafe gwiwoyin Mommyn nata "Innalillahi wainna ilaihirajiun,Mommy kawata na shiga uku ya zatayi!"

  Hannu ta mata nuni da tayi shiru kar ta jiyota Ummin,mikewa tayi ganin Yusrah ta gigice tana kuka a ciki ciki ,a d'akin ta isketa ta tsurawa TV ido ba kallon ne gabanta ba hankalinta sam baya gun.

  "Ummi ,abbansu yayi kiranta ko Zaki je gida anjima zata shigo suna magana ne".

  Murmushi tayi ta mike "Daman yanzu nima nake son tafiya kaina ciwo yake zan Sha magani".

  Murmushi yake tayi cikeda dauriya zuciyarta na bugawa ta ga yarinyar ta fita ta zauna hawaye na silalo mata , bayan fitar ta sai ta Yi tunanin kirawo Abbansu Yusrahn  idan da hali ma kar su sanar mata yanzu sai sun dawo.

Waya ta daga ta kira Abbasu Yusrah ya tabbatar mata ba su fadawa ko Anty Sa 'a din ba.Tunda ta shiga gidan ta kwanta kamar an zare mata kuzari ta kira Abdulbasit waya kashe ta hakura.
 
 
   Har dare yayi bata ga alamar Yusrah ba tayi tunanin ko wani abune ? Halin da take jinta bazata iya kawo koma mene ba daga baya ta yi wannan tunanin.Da wuri bacci ya dauketa sai cikin dare ta farka ta kasa bacci da ta juya tunani Ammynta.Sai wajajen 4am ta sake bacci asubah Anty Sa a ta zo ta tasheta "Mamana tashi ki sallah"

  Mikewa tayi a sanyaye tana hada ido da Anty saa ta ga idanunta sun wani yi ja kamar gauta ,saurin dauke ido tayi ta shiga bayi alwala take amma bata san me take ba ta rasa me take ji a jikinta ta fito ta shinfida sallaya ta soma gabatar da sallah.

  "Innalillahi wainna ilaihirajiun"Bakinta yake furtawa sanda ta idar ita kadai take ambaton haka faduwat gabanta na karuwa ta mike taji   an  bud'e gate  mota ta shigo yar hayaniya taji sai kuma taji muryar wata cikin yayyin Ammy  "Innalillahi wainna ilaihirajiun Sa'a  munyi rashin 'yar uwarmu"

Kai ta shiga girgizawa   duhuwa take ta  lullube mata ido ta rike madubin d'akin tana ji kafarta ta kasa daukanta ta yi kasa ,shigowa d'akin taji anyi bata gane ko wace ba ta baya ta rikota "Ummi ta shi Ummi hakuri zaki  Ammynki lokaci yayi Allah ya mata rasuwa!"

    Ta ke ta sulale kasa numfashinta ya dauke ,Anty Sa a ta hau kiran yan uwanta su taimaka mata.

   *Your comments are very important and watpadians a dinga vote da follow please.Zaku iya searching Dina da suna Dijen-sy ,zaku ga ya banbanta da na da as there was a serious issue da na samu da tsohon account dina couldn't recover it so help your sister and follow the new account.*

Dijensy
 

Continue Reading

You'll Also Like

509K 32.6K 41
Let's see how different personalities mends with each other to form a beautifull bond together. Where the Eldest is calm and cold, Second is aggress...
140K 6.8K 28
Hooked onto drugs, no family, no guidance or sanity until she met HIM. Cover Creds: @Triceynexttdoor ❤️ -BLICKY.
333K 10K 81
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...
58.8K 1.4K 40
standalone ~ mafia siblings series "You can't make me stay here! I will get an emancipation." I yell. Flashbacks of the gun in my hand, the almost-de...