NAZLAH

By Salmeert

245 32 2

Labarin Wata Fitinanniyar Yarinya da bata barin bashi, ko mai ka mata sai ta rama, har sai ta ci gyara, gata... More

CHAPTER 1-2
Chapter 3-4
CHAPTER 5-6
chapter 7-8
chapter 9-10
chapter 11-12
chapter 13-14
chapter 15-16
Chapter 17-18

Chapter 19-20

33 3 0
By Salmeert

19-20.

"""""""""""Harararshi tayi tare da cewa "duk ma yarda aka mata dai-dai ne, tunda tona min Asiri kake da niyyar yi", "uhmmmmm ba zaki gane bane Adda girman bukatata ta wuce na Yar 20years ma balle 15, kaya kawai zaku haɗani da shi", ya fada yana mikewa.

        "ngd kuma ba sai ka gwadamin ban isa da kai ba", ta fada tana haɗe fuskarta alamar tayi fushi, matsawa ya yi kusa da ita, tare da riƙe hannunta yace "Adda na Amince..!", yana fadar haka ya fice daga bedroom din, cike da murna ta fito itama, haɗa baki suka yi gurin cewa "Adda ya amince?", wani kallo ta musu irin na wasa tare da cewa "ko yake jira sai kun amince", ta fada tana zama, dariya duk sukayi dan susan dole ma ne ya amince.

         Washe gari gaba dayansu suka tafi Saloon , sai da suka je kafin Adda Zainab ta sa driver ya je ya taho da Nazlah  , cikin minti kaɗan ya je gidan, kafin ya je ma Nazlah ta shirya dan sun kira Ummu ta Yar kwararraɓar wayarta sun sanar mata,cikin shiga mai kyau Nazlah ta fito sai kamshi take ,mota Driver ya bude mata, shiga tayi ta hakimce a baya, sai da ya rufe kafin ya koma mazaunin driver, ya kunna motae suka kama hanyar shagon saloon din.

       15minutes ne ya sadasu da ƙawattacen shagon Saloon din da yake kan Hanyar Kano road , shago ne mai kyau da tsari , na masu kuɗi, bayan sun karasa ya bude mata motar ta fito, jagora ya mata har ciki, da Sallama ta shiga cikin shagon, duk juyowa sukayi da murmushi kan fuskarsu suka amsa mata, ƙarasawa tayi ta ɗuka har ƙasa ta gaishesu, Jaan ta Adda Zainab tayi jikinta ta rungumeta, tare da cewa "kina lafiya Ƙanwar Adda?", ta fada da murmushi kan fuskarta.

        jinjina kanta tayi alamar lafiya lau, rungumeta suka shiga yi daya bayan daya suna tambayarta lafiyar ta, Haleesa da take mata murmushi tace "Sannu Amaryar Auta..!", dan murmushin yaƙe ta mata dan sam bata fahimci kan maganar ta ta ba, karɓar Ƴar Adda Zainab tayi ta zauna kusa da Haleesa tare da fara ma wasa.

         Wata Yar siririyar Mata ce ta fito daga wata yar kofa tana cewa  "Ayya kuyi hakuri na barku kuna jira na, yanzu me za'a fara muku kuma da wa za'a fara, "ta fada tana dan murmushi.

          Nuna Nazlah Adda Zainab tayi tare da ce wa "ita zaki fara mawa gyaran jiki zaki mata da gyaran kai, sai ki wanke mata ƙafa , " kallon Nazlah tayi tace "kina son kitso?", da sauri ta girgiza kai alamar bata so, "mai yasa ba za'a miki ba? , zai fi fito da ke", dan kwaɓe fuska tayi tare da cewa  "kaina namin ciwo in aka min", ta fada tana matsawa kusa da Mai gyaran jikin.

         wankin ƙafa aka fara mata, duk da cewa ƙafarta tsaf take ga laushe da tsantsi, hakan yasa da aka wanken sai ta kara kyau da tsari, kumba ta gyara mata ƙafar tayi tarrr² har wani jaa² take kamar jini zai fito, wani ɗaki suka shiga  anan aka mata dilka da halawa, komai binshi da ido Nazlah take, dan ita wannan abubuwan bata sansu ba, sai kallon jikinta take, tana mamakin wai ita ce ta koma haka, jikinta ya koma kalar na jarirai, sai shinning yake gwanin burgewa, bayan an gama turara mata jiki da turaren jiki mai kamshi da zama cikin jiki suka fito.

           duk tsura mata idanu sukayi suna kallon zallar kyau irin na Nazlah dan haskenta ya kara fitowa sosai , dan in kai mata kallo daya ba lallai je ka iya gano daga wace ƙasar ta fito ba, dan kwata² batayi kala da Yan nigeria ba, zaunar da ita tayi gurin da zata wanke mata kai, dan kwallin kanta da tunda tazo bata cire ba Matar ta kama ta fara warwarewa, kyakyawan gashin kanta ne ya fara warwarewa daga gammon da ta mishi.

           tana zare gammon gashin ya warware gaba dayanshi ya zubo akan bayanta, faɗowa Haleesa ta kusan yi sa boda tsananin mamakin irin yawan gashin kan Nazlah, duk da Ahalinsu na da gashi sosai Amma bata taɓa ganin mai yawan gashi da kyan gashi ba irin na Nazlah, matsawa tayi gurinta jikinta na rawa ta kama kasan gashin tace "Duk wannan naki ne..!?", gyaɗa kanta Nazlah tayi.

          su Adda Dariya suka fara wa Haleesa dan sosai take zuba santin sama nata ne gashin, duk kuwa da cewa suma sun cika sa matsanancin mamakin yarda Yarinyar ta tara abubuwa da yawa, na daukar hankali.

            gyaran gashin aka shiga yi mata, cikin kankanin lokaci aka gama, dan gashinta yana da taushi kamar na jarirai gashi da suɓi uwa-uba bashi da cunkushewar nan,a yaryare yake, duk kuwa da cewa yana da yawa amma bai cunkushe ba, bayan an gama Adda ta bada Ribbons guda huɗu aka daure mata kanta dasu.

         izuwa lokacin idanun Nazlah sunyi jaa, dan gaba daya hankalinta ya fara tashi da yarda ake jaan gashin kan nata , dan bata son abun da zai taɓa kan, dan ma tana jin kunyar su Adda ne ba zata iya musu, musu ba da tuni ta mike .

           lokacin kuma Yan taya mai shagon aiki suka zo, umarnin fara hakafarawa ta basu, hakan yasa suka farawa su Adda Zainab, Nazlah kuwa Abin ci Adda Zainab ta sa aka kawo mata , ta zauna chan  bayansu suna ci ita da Yar Adda Zainab.

             ba a dau wani lokacin mai yawa ba, aka gama musu dan nasu bai dauki lokaci kamar na Nazlah ba dan wankin kai ne kawai da wankin ƙafa, bayan sun gama, suka tafi gidan su Nazlah gaba daya, lokacin Yan Uwan Iya duk sun hallara gidan ana ta hada ², ana gyaran kayan miya da sauran kayan Abinci.


.

           Tara ta mutunci aka musu , aka kawo musu Abin ci da Lemu wanda Iya ce ta bada aka karɓo musu, bayan sun gaisa suka bawa Ummu haƙurin kayan lefe da ba'a kawo ba, sai taje chan zasu bata kayanta, murmushi  Iya tayi tare da ce wa "Ba komai ai gwara ma da baku kawo ba kuka barshi chan, dan wahala za'a sha sai an kawo kuma a mayar", basu wani jima ba sosai suka tayi suna godiyar karamci irin na Yan gidan.

           Washe gari, Nazlah da rigama ta tashi,wanda hakan ya haddasa mata zazzaɓi , sai dai Iya ce ta dauketa zuwa gidanta, domin chan ne mai rangwamen  hayaniya.

        Tun 10 mutane suka fara daddala, zuwa gurin daurin Auren duk kuwa da cewa ba wata Gayya sukayi sosai ba, dan Bangaren su Nazlah Yan uwa kawai suka gayyata, Chan gidan Ango ne suka yo gayyatar mutane, 12 bata  ƙarasa ba Adda Zainab da Haleesa da Hameed duka zo gidan .


            lokacin da Hameed ya fito, ya yi mugun mamakin ganin Abokanshi a ƙodar gidan , dan shi kanshi jiya yaji zancen Auran, bai kuma fadawa kowa ba dan har Sadiyya bai faɗa mata ba, gurinshi duk suka tattaso suka zo, Khalil ne ya dan duku ƙafadarshi yace "Buddy ashe dama shirin shigewa kake daga ciki, amma ka bari ciwo zai kashe ka, amma wallahi ka shammace ni,kawai sai dai Invitation card naga yana yawo a media , na nemi wayarka kuma shiru ba'a samunka", dafe kanshi ya yi, tare da  cewa "yi hkr pls kasan yana yin abun ne sai a hankali, dadin media din kenan ai, amma naji dadin ganin ka wallahi, na gode maka".


               Ammar ne ya dan duki kafadarshi daga baya yace "mu da baka ji dadin ganin mu ba, ba komawa zamu yi ba ai", juyawa ta yi, yana dariya suka rungumi juna, fira suka ci gaba dayi irin ta Abokai, Adda Zainab da Haleesa kuwa tuni suka shige ciki.


               Ko da suka shiga ciki ,cikin  girmamawa ake gaishesu har ƙasa, har suka shiga Ɗakin Ummu da take cikin shiga mai kyau shar³ da ita sai murmushi take, nuna wa Adda Zainab kusa da ita tayi, zama tayo suka gaggaisa, fira suka shiga yi da dangin Iya, da yake duk fara'a garesu ga saurin sabo yasa, suke firarsu cikin jin dadi, da tattauna yarda zancen Auren yazo, Haleesa ce tace "Ummu ina Amaryar Auta,da Iya?, naga ban gansu ba", dan murmushi Ummu tayi tare da cewa "Suna gidan Iya ko asa a raka ki chan din ?".


          dan gutun murmushi tayi tare da ce wa "Laaaah Ummu nasan gidan bari na je", ta fada tana mikewa, Amsar Yar Adda Zainab tayi ta fice da ita zuwa gidan Iya.


            Da Misalin karfe 1pm na ranar Juma'ah , aka daura auren Hameed Abubakar da Nazlah Lawal akan sadaki naira dubu dari biyu, wanda Adda Zainab ce ta bada kuɗin sadakin, Daurin Auren sosai ya samu halarta mutane Manya da ƙanana, kowa ka gani fuska washe dan an wadata kowa da komai abin ci da lemuka   har ba'a magana.

         bayan an gama daurin auren Hannu Yah Haleem ya mikawa Hameed cikin yar fara'a yace "ina taya ka murna, Allah ya sanya Alkhairi", dan murmushin da bai kai ciki ba Hameed ya yi, tare da ce wa "Na gode, uhmmm Haleem ko , Yayan Nazlah?", gyaɗa kanshi Yah Haleem ya yi, murmushi ya ƙara sakar mishi, kafin su zauna cikin Abokan Hameed din ,hannunshi kuma na rike da na Yah Haleem,sai da kowa ya watse Hameed ya rage daga Hameed sai Abokansa ,Adda Zainab ta fito daga cikin gidan, suna haɗa ido ya dan kauda kanshi.

       Yar dariya tayi tare da ce wa "Ango kasha kamshi..!", Yar harararta ya yi, tare da dauke kanshi, dan matsawa kusa da shi tayi, tare da cewa "Allah in baka saki fuskar nan ba sai na ɓata maka rai" ta fada cikin raɗa.

          kamar zai yi kuka haka yawa fuskarshi, dan wani kalar yanayi yake ji, shi dai ba zaice farin cikin Auren yake ji ba,kuma ba zai ce Yana jin baƙin ciki ba, kawai dai yana yi yake ji , shi ba sama ba shi ba ƙasa ba, gadai shinan.


        riƙe hannunshi tayi tare da cewa "Muje ciki ka gaiyar da mutane", ta fada tana fara takawa, bin bayanta suka yi  duka da Abokanshi, sai baza kamshi suke, har ƙasa suka ɗuƙa suka gaisar da mutanan dake cikin gidan kafin su shiga  ɗakin Ummu, itama har ƙasa suka gaisheta, Adda Zainab ce ta kalli Ummu tare da nuna mata Hameed tace "Wannan ne Hameed din", "Hameed wannan ita ce Ummun Nazlah", bai ɗago kanshi ba, sai dai zuciyarshi tayi wani mugun bugawa, Ummu kuwa dan murmushi tayi bata ce komai ba, yar dariya Adda Zainab tayi dan tasan kunyarshi Ummu take ji, sai dai ita ta tabbatar wata rana sai ta daina jin kunyarshi  dan duk ranar da Ya fara son  Nazlah sai ta bani da rashin kunyarshi , dan baya iya boye abun da yake so.

         mikewa sukayi zasu fice , Ummu ce tace "Zainab...!", juyowa Adda Zainab tayi ta dawo baya tace "Na'am Ummu..!", "a raka su gidan su Iya", ta fada tana dan kallonta, murmushi tayi tare da cewa "Yanzu kuwa ai ni zan rakasu ma",,ta fada tana ficewa.


        tana fitowa Khalil yace "Adda wai ina Amaryar ne?, naga ban ganta ba", ya fada yana dan murmushi, "kai kuwa Khalil mai kake ci na baka na zuba, yanzu zan raka ku gidan Kakarta tana chan ai" ta fada tana yin gaba, duk bin bayanta sukayi, anan suka bar motocinsu suka bi bayanta.


        Da sallama Adda ta kutsa kai cikin gidan , Iya da take tsakar gida ta Amsa mata, tare da cewa "Zainabu ce? shigo mana...!", ta fada tana kara buɗe taburmar da take kai, jin ance Zainab yasa Haleesa dan leqowa ganin Adda Zainab ce yasa ta fito.

       Gaisawa da Iya tayi kafin tace "Iya da Anguna muke tafe", yar harararta tayi kafin tace "shine kika barsu a waje, ke Haleesa jeki ki shigo dasu, bari na karo taburma", ta fada tana mikewa, Haleesa kuwa tayi waje, ison shigowa ta musu, kafin ta juyo .

         kafin su shigo Iya ta shimfiɗa musu Taburma, Adda Zainab kuwa ta shige cikin ɗaki Gurin Nazlah, zama sukayi kan taburmar tare da gaishe da Iya Amsa musu tayi da fara'a,kafin tace "ina Angon nawa yake?", ta fada tana kallonsu.

         Khalil ne ya nuna Hameed da hannu tare da cewa "gashi nan Mama", murmushi tayi tare da cewa " , kar ka yarda a baka nunar rana, a bar ni, dan wannan dan fari²n duk rana ce ta duketa, ni kuwa ka gani  fess da ni , gani dakwau ," ta fada cikin yar tsokanar jika da kaka, Dan murmushi Hameed ya yi, tare da cewa "Haba Iya ai sabuwa ake so mai jini a jika", ya fada yana yar dariya.


           Bangaren Adda Zainab kuwa, tana shiga ta nufi Nazlah da take fitar da numfashi sama², sosai zazzaɓin ya yi zafi, matsawa tayi gareta  ta sanya hannunta akan wuyanta, da sauri ta cire saboda wani mugun zafi da ya daki fatar hannunta, "Nazlah!", ta dan furta da ruɗu, idanunta da suka mata nauyi ta bude tana kallon Adda Zainab bata iya Amsa kiran da ta mata ba.

         ganin tana jin jiki sosai, yasa ta fito tare da cewa "Iya zazzaɓi ne sosai a jikinta, akwai magani a bata kafin a tafi da ita Asibiti",,ta fada cikin yar damuwa, shi kuwa gogan taɓe baki ya yi.

         "Maganin ya ƙare dama shi kenan ta ƙarasa shanyeshi ɗazun, ban san mai yasa wannan zazzaɓin nata ya ke yawan taƙura mataba kwana biyu ga,zafi ga naci ",ta fada cikin tausayawa Nazlah.

      Kallon Hameed Adda Zainab tayi tare da cewa "taso ka dauketa mu tafi hospital dan jikin ya yi zafi sosai har na fara jin tsoro", ta fada tana kallonshi, shi kuwa shiru ya yi kuma bai tashi daga in da yake zaune ba.

         "Wai ni kam ba da,Hameed nake magana bane?," ta fada cikin yar tsawa, mikewa yay, yana jin Adda ta fara shiga haƙƙinshi da yawa.

            bin bayanta ya yi suka shiga ɗakin, sai da suka shiga tsakiyar ɗakin kafin yace "ina take?", ya fada yana dan duddubawa , nuna mishi Nazlah da take kakkafewa tayi, ido ya fitar waje kafin yace "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, wannan Ƴar Abar Adda mai yasa zakimin haka ne?, yanzu wannan ni ba abin kunya bane na nunata a matsayin mata, lallai da sakyal dan kuwa anyi bonono rufin ɗaki da Ɓarawo, dan wlh wannan ko bata mutu ba, zata sha wuya, kaji abu kamar mage, ji yarda,ta wani lafe tana futar da numfashi kamar,zata mutu k.......


07033371851

'''DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROYAL STAR'''

Continue Reading

You'll Also Like

295K 19K 48
The story of two souls who have experienced utmost love as well as heartbreak. What happens when two of them collide accidently? Will they heal each...
707K 101K 38
Yaduvanshi Series #3 it is a book under yaduvanshi series. But it could be read as standalone too. Nitya Raghavendra is a telugu businesswoman earnin...
249K 7.3K 44
စဝ်ခွန်နောင်= မင်းလူသတ်ရင် ကိုယ်ကအလောင်းဖျောက်ပေးမယ့်မဲ့ကောင်ပါ baby Gumkino =ကျွန်မက ပန်းကိုင်ရတာထပ် gunကိုင်ရတာပိုသဘောကျတဲ့မိန်းကလေးတစ်ယောက်မို့ ရှ...
212K 7.2K 56
ရိပ်ချေ ကိုကြီးကိုချစ်တယ် ။ ကိုကြီးလည်း ရိပ်ချေကိုချစ်လာရင် ဖွင့်ပြောပေးနော် ။ နွေဦးရိပ်ချေ 🍀 နေမခန်း & နွေဦးရိပ်ခ...