chapter 7-8

19 3 0
                                    

☘️☘️NAZLAH☘️☘️


       *DAGA ALƘALAMIN*

SARAUNIYAR YAƘIN MARUBUTA / ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️.

*WANNAN LITTAFIN GABA DAYA SADAUKARWA NE GA YAYATAH (MARYAM YUSUF)WANNAN LITFAFIN WAKE NA RUBUTASHI, KI YI YARDA KIKESO DASHI, ALLAH YA RAYA MIKI ZURI'ARKI , YA KUMA KARA RUFA ASIRI , DUNIYA DA LAHEERA........*








بسم الله الرحمن الرحيم




7-8.



"""""""""""""Yana tafiya Jamseey ta tattaro kayanta gaba daya ita da Ƙanwarta Jasmin suka dawo gidan, tunda suka dawo komai a gidan sukeyi, basa ko dan zuwa gidansu su zauna, sai dai su ɗibi abin ci su bada akai,basa mata aikin komai, kwana biyu kawai gida ya fita daga hayyacinshi, mai aikin  da take zuwa tana gyara palon ma Jamseey ta hanata zuwa, Sadiyya kuwa kamar wadda aka Asirce bata iya yin komai, kullum tana tule, duk abi da suka ce mata shi takeyi, bata son ganin bacin ransu ko kaɗan biyayya take  musi kamar uwarsu...........



            *********

            

             Tsabar kukan, Ummu ko leqowa waje bata yi ba saboda kawar da kai ga Yaranta, haka Nazlah ta mike ta shiga ɗakin tana kuka, kan jikin Maryama ta zauna tana shasheƙar kuka , tare da nuna mata hannunta, hannun ta rike tana dubawa, bata san sanda hawaye ya zubo mata ba ganin hannun gaba daya ya tashi, sharw mata hawayen idanunta ta shigayi, ita kuma nata na zubowa, ganin Ummu na kuka yasa itama ta kara fashewa da kuka, dan duk da bata wuce shekara daya da rabi ba amma gaba daya batason ganin Mamarta na kuka..............


           yakice Labulen dakin Lawan ya yi, tare da cewa "wane shege ne yakeson mayar min da gida filim mutuwa, kumin shiru ko na tattaka ku gaba dayanku", ya fada yana daka musu tsawa................



             Shiru Ummu tayi, kanar ruwa ya cita, Nazlah kuwa kara fashewa tayi da kuka tana boyewa jikin Ummu dan gaba daya bata son ganin Lawan ko kaɗan dan kallon mugu take mishi, "dan Ubanki rufemin baki ko nazo na tattaka ki", ya fada yana shirin shigowa ɗakin ,da sauri Ummu ta sanya tafi hannunta ra rufe mata baki, (Allah Sarki Mahaifiya, bata son duk abunda zai faru ga Ɗanta, tana iya jure dawainiyar Yaro tun daga ciki har izuwa haihuwa da raino, kashinka futsarinka, da komai naka ita take gyarawa, ko dan ciwo kaɗan bataso kaji, balle ta kai ga wani yaci zalinka, sai dai kawai tayi kawaici ta kyale bawai dan bataji ciwo a ranta ba, kawai dan mutunci da zaman tare, Allah ka tsare mana Mahaifanmu ka shirya mana Mahaifanmu sannan kaji ƙansu, ka gafarta musu zunubansu, Alfarmar Annabi da Al-qur'ani , Ameeen).



             sakin labulen ya yi, tare da ficewa yana banbamin bala'i, ganin ya fice da sauri ta dauki, Nazlar ta daurata akan gado tare da fara bincikar in da zataga maganin wuta, tasha wuya sosai kafin ta nemo maganin, tana kuka, Nazlah na kuka haka ta ciccire mata fatar da ta tashi, ta barbada mata maganin, bayan ta gama, feeding dinta ta fara yi tana shafa,mata kai tare da busa mata iska a hannunta, bacci mai nauyu sosai ya dauketa, ganin bacci ya yi awon gaba da ita yasa ta sauke numfashi da karfi, tunanin rayuwa ta fara yi, batayi aune ba taji ana kiran Magrib..............



                 Sallah tayi, lokacin da zata gama Haleem ya dawo daga aikin kanikancin da aka sanyashi, cikin murna ya matsa gareta tare da cewa "Ummu kalli, Oga na ya bani wannan", ya fada yana nuna mata wata sabuwar naira Ashirin da ya fitar a Aljihunshi, murmushi tayi tare da cewa "Allah ya mata Albarka, kaima Allah ya maka Albarka dama Ƴar uwarka," ta fada tana shafa kanshi, "Ameeen Ummu", ya fada yana jingina da jikinta..............




NAZLAHWhere stories live. Discover now