A SOYAYYAR MU

By hijjartAbdoul

4.1K 74 0

Be tashi ya ga mace a gidan su ba, rayuwar su gaba ɗayan babu mata idan kaga mace a gidan to auro ga akayi ha... More

Shimfiɗa.
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50

37

63 1 0
By hijjartAbdoul

Babu abinda ya ke sai safa da marwa a cikin ɗakin sa tun dawowar su daga asibiti bayan sallamo ɗan sa. Abin duniya gaba ɗaya ya haɗu yayi masa yawa, be taɓa tsammanin aikin su zai samu matsala ba a cikin ƙanƙanin lokaci ba sai a yanzu da komai yake nema ya cakuɓe masa. Ga rashin lafiyar ɗan sa da yake jin ta har cikin zuciyarsa, be san ya zai yi ba, be san cewar haka ake jin fargaba sai jiya da yaji labarin kama su Sagiru sa akayi shima Jibrin ne ya faɗa masa abun ba ƙaramin razana shi yayi ba, ko da aka kama su Dr. Ismail hakan be ɗaga masa hankali ba kamar yarda aka kama su Sagiru.

Samun waje yayi ya zauna kafin ya fara lissafin iya adadin dukiyar sa, ganin lissafin bame ƙarewa bane yasa shi tashi salin alin ya haɗa muhimman takardun sa tare da ɗaukan passport ɗin sa ya yi parlour, yana zuwa yaga matar sa da Ɗan nasa a parlour alamar ba su shiga ɗaki ba kenan.

"Ina zuwa haka?

Be je ga bata amsa ba aka yi knocking, zuwa tayi ta buɗe ƙofar batare da ta tambayi waye ba. Wasu irin murɗaɗan samudawan Sojoji ne, suke neman sa, ita kan ta, ta tsorata bare kuma shi kan sa da yayi laifin, bata je ga ja ba tace yana nan, ta basu hanya suka shigo, basu yi wata wata suka ɗaga shi sama shi dukan sa, babu tsayawa wani You are under arrest ko wani takarda ko wani abu, tsayawa magana wannan sai ɗan sanda abokin kowa amma banda soja aikin su kawai suke da cika umarni doka ɗaya ce idan ka karya ta shikenan hukunci za su dauka babu ruwan su. Yanzun ma haka ne, suna zuwa sukayi sama da shi dan kada ya ɓata musu lokaci. Haka iyalan sa da masu aikin sa  suna ji suna kallo aka sanƙa mashi a mota suka tafi.

Ko a mota idan sa yayi tsilli tsilli yana cilla idanu, shi kam yau yaga tashin hankali, mai suna tashin hankali to da shi waye ya kai shi? San kuɗi ko kuma me? Ba kowa ne ya je fasu a halin da ake ciki ba sai su Dr. Ismail acewar sa kenan. Ganin basu ɗauki hanyar airport ba yasa shi sanin lalle kashin sa ya gama bushewa shi yaushe raban sa da yayi tafiya mai tsayi irin wannan, jide Kaduna yarda ya mayar ta kamar me nan da nan yaje ya dawo, sauƙin sa ɗaya sun bar shi yayi bacci san ran shi har suka ƙara so Kaduna.


~~~~~~~

Yusuf da Hafiz kuwa ba su san cewar an kama kowa ba a companyn su, kuma an sallamo Anty, daman su washegari kasancewar Jummu'ah ce ba su ba za su aiki ba, shiryawa suka yi za su je Bauchi. Dan haka da asuba suka fita, suna yin Sallah suka ɗauki hanyar Bauchi, sun yi gudu sosai dan haka suka isa sa wuri, tara ma a can tayi musu daman su idan suka zo Jigawa kamar sun zo ne, kai tsaye gidan su Bintu suka nufa suka nemi a aurawa Yusuf ita dan ko ƙudurin Inna akan auren Sajjad da ita Bintun, baban Bintun be wani ja ba ya yarda dan Mahaifin Bintun mutum ne mai fahimta da  dattako. Suka siyo goro da alawa da kuma dabino, sai da suka jira aka yi sallar Jummu'ah sannan suka ɗaura auren, ba ƙaramin daɗin hakan yayi musu ba, daman da zulumin zai yarda ko kuwa ba zai yarda ba, sai da suka kamo hanya kuma ya fara zulumin ita kan ta Bintun nan ɗin ma Hafiz ne ya cigaba da ƙarfafa masa gwiwa.

Kasancewar a wannan tafiyar sun yi tsaye-tsaye tsayawa yin Sallah yasa ba su dawo da wuri ba ga kuma hold up, sai bayan Isha suka dawo, gida suka wuce domin su sanar da su Abba, sai dai abinda basu sani ba shine, suna tafiya Mahaifin Bintu ya kira ya sanar da shi komai. Suna zaune suka tarar da su a main parlourn na gidan kowa da kowa ƙwan su da kwarkwatar su kowa ya hallara an zo dubiyar Anty. Mata sun yi gefe abin su haka ma mazan a gefe a bin su yara ma haka.

Yusuf na shigowa suka fara ango kasha ƙamshi, tsayawa yayi kawai yana kallan su, kafin ya samu waje ya zauna.

Yace, "Yanzu waye ya faɗa musu wannan abun dan Allah?

"Kai a tunanin ka baza mu ji ba?

Al-ameen ya faɗa.

"Yaya Al-ameen yaushe kuka shigo garin?

"Wallahi bari kawai, Hajiyar su ce ta zo ta ɗauki Unaisa wai ta kusa haihuwa shine fa muka dawo muma".

"Kuma aikin fa?

"Ina da Yaya Aliyu ai".

Ya faɗa yana kallon Aliyu. Ɗan girgiza kai kawai Aliyu be ce da su komai ba. Ganin kowa na magana babu Sajjad ya su kallan sa, ya wani uban zuba tagumi hannu biyu be masa me suke cewa ba.

Hafiz yace, "Sajjad ƙalau kuwa?

Mustapha yace, "Wanne ƙalau kuwa? Inna tace bata yarda da auren su ba, sai an sake, sannan kuma sai anje har garin na su an tambayi auren ta idan sun bashi a karo na biyun shikenan, idan ba'a bayar ba kuma shikenan, shine yake cika yake batsewa kamar de yarda ka gani".

"Kuma shine me?

Shidai be tanka musu ba, daga ƙarshe ma tashi yayi ya fice abin sa, dan gefe ɗaya kuma murnar auren Yusuf da Bintu yake at least de Inna ta haƙura kuma da wani auren sa da ita.

Suna zaune a su Abba suka shigo, Yusuf da Hafiz suka je suka same shi, Hafiz ne ya zayyana komai da komai har kawo auren sa da Bintun, sosai Abba yayi musu faɗa akan abinda ya aikata musamman ma sakin da yayiwa matar sa, da kuma auren. Haka shima Daada ya ɗaura nasa daga inda Abba ya tsaya Baba ne de baya da faɗa sosai. Suna gama na su Hajiya Mama da Ummi suma sukayi na su suka yi suka gama, sude kan su a ƙasa basu ɗago ba, bare kuma su tanka sai da aka gama tsab sannan suka bada hakuri suka da cewar in Sha Allah hakan ba zai kuma faruwa ba.

******

Nilah da Barrister kuwa, suna zaune har shaɗaya na dare suna hiran su, sam ba su gaji ba, bama sa jin bacci ba. Hira suka sha shi wanda ba su taɓa sakewa ba irin yau tunda suke a rayuwar su. Ganin sun yi shiru yasa Nilah cewa.

"Mahaifin Maryam fa?

Kallan ta kawai Barrister tayi, tare da yin murmurshi tana kallan da yaran da suka jima da yin bacci abin su.

Tace, "Mutanen da kake tare da su idan sun nuna basa san ka Nilah zaman me zaka ci-gaba da yi kuma?

"Mommy kamar ya?

"Ada suna sona, musamman da na haifi Maryam, tunda suka ga shiru ban kuma haihuwa ba shikenan suka tsaneni, ni kuma ba zan iya cigaba da zama a inda ba'a maraba da ni ba, ba zan kuma maimaita abinda nayi ina yarinta ba, ban je ga aikata hakan ba kuma shi akaran kan sa ya sauwake min domin farin ciki na".

Jinjina kai kawai tayi tana kallan ta.

"Shine dalilin da yasa na dawo, yace kuma na tafi da Maryam kada na barta a wurin su".

"Duka familyn sa suna can ne?

"Acan suke".

"Wannan gidan ma na shi ne ya bani".

"Allah sarki".

Kawai ta iya faɗa.

"Amma Mommy zaki koma wurin Abbanah?

Ta faɗa cike da marairai cewa. Murmurshi Barrister tayi kawai tana kallon ta, batare da ta bata amsa ba. To da me zata ce? Ta cigaba da duba takardun da ke gaban ta. Sam bata da burin sake zama da Mukhtar Abieyola, baya san ta ita ma bata san shi ba, biyayya ce tayiwa iyayen ta, to baya jin zata sake zama da shi kuma a karo na biyu.

Washegari tunda sukayi asuba suka koma suke bacci daga su har yaran dan suma ba laifi akwai bacci. Knocking da ake yi ne ya tashe su, wayar ta ta janyo ta duba time taga yaja sosai, ta duba taga Mommy da alama itama tashin ta kenan, sai yaran da suke ta juyi suna haɗa ido, ba su tashi daga gadan ba.

Barrister tace, "Ki tashi kije ki buɗe mana nasan ba zai wuce Sajjad ba".

Hijabi kawai ta janyo ta saka ta fita, a bakon ƙofar ta tsaya.

Tace, "Waye?

"Mijin ki ne".

"Ai ni bana da wani miji".

"Wanda zaki aura".

Murmurshi kawai tayi, ta buɗe masa, tana buɗewa yana zabga mata harara.

"Ina kwana?

Samun waje yayi ya zauna.

Yace, "kije ki cewa Mommy Yaya ƙarami yana jiran ta a waje".

Amsa tayi taje ta sanar da ita, lokacin ta shiga wanka, yaran suna ƙarami parlour sanar da su tayi cewar Daddyn su na parlour hakan yasa su zuwa wurin sa ita kuma ta wuce kitchen, shayi kawai ta dafa mai kayan ƙamshi ta soya ƙwai ta ɗauko bread ta fito, a ƙaramin parlourn ta ajje lokacin Barrister ta fito cikin shirinta.

"Zuba min shayin dan ba zan tsaya ba ina sauri".

"Toh".

Tace tana zuba mata.

"Ki kula da Maryama tunda ga ku ba sai na fita da ita ba".

"Toh. Allah ya kiyaye".

"Ameeen".

Ta faɗa tana barin wajen da mug ɗin ta a hannun ta, gaisawa sukayi da Sajjad sannan fita waje.

"Kin tashi lafiya".

Ƙarami ya faɗa sanda ta fito.

"Alhamdulillah".

"Yanzu ta ina za mu fara?

"Abba yace mu miƙa case ɗin hannun ƴan sanda. Ni kuma gaskiya bana san a miƙa shi hannun su. Saboda ba za su rasa mutane ba a wurin".

"A'ina za'ayi Shari'ar?

"Ta Yahaya Sabo de Abba yace ayi a Abuja, saboda ba ɗan Kaduna bane ba da shi da Mukhtar Abieyola".

Ɗauke mamakin ta tayi na jin an ambaci sunan Mahaifin Nilah.

Tace, "Shi kuma waye?

"Shi wannan case ɗin sa daban, ƴar sa yasa aka sace".

"Aka sace?

Ta faɗa cike da mamaki, bata taɓa sanin san kuɗin Mukhtar ya kai haka ba. Aka sace fa? Anya kuwa? Sai dai wani dalili nasa amma ba zai iya aikata wanna abun ba, shidai a bar shi da kasuwanci da siya gami da san kuɗin amma ba zai yi haka ba, ta san da haka kuma zata yabe shi akan haka.

"Taya hakan ta faru?

"Shine muke son ji daga gareshi, gashi ba mazaunin nan ba. Kuma kinga shi case ɗin sa daban ne, idan ƴar sa ta yafe shikenan idan bata yafe ba kuma sai kotu tayi hukuncin ta".

"Anga yarinyar ne?

"Shine bamu sani ba".

Jinjina kai kawai tayi.

Tace, "Mai zai hana a ɗauko shi to? Kamar yarda aka ɗauko Yahaya Sabo?

"Wannan be ta so bafa, case ɗin ƙaramin case ne. Muji da abinda ke gaban mu. Idan mun samu anyi anan ɗin hutun mune, idan bamu samu ba kuma zuwa Abuja ya kama mu".

"To shikenan".

"Mu tafi mana to".

Ta faɗa tana kallan shi ganin be tashi ba.

Yace, "Ni ba ki sa a bani shayin ba?

"Kace kana so ne?

"Sai nace ina so?

"Kaje ka karɓo".

Kallan ta kawai yayi, yayi ƙwafa.

"Mutum sai rowa".

"Ba'a ƙasa na dauka ba".

Be kuma magana ba ya yi reverse ya bar compound ɗin. 

A cikin gida kuwa ganin Barrister na fita yasa shi yin wuf ya shiga inda yaga ta shiga, anan yagan ta tana jera abinci a ƙaramin table ɗin dake wajen.

"Kiyi sauri ki shirya yaran zamu fita".

"Ina?

Ta tambaya tana kallon shi.

"Nace kiyi sauri ki shirya, bana san tambaya".

"Ka kira yaran ku ci abinci. Bari nayi wanka".

Beje ga kiran na su ba suka shiga wurin, dakan sa ya zuba musu komai, Hauwa'u kuwa dakan sa yake bata,bayan ya ɗaura ta akan cinyar sa.  Sanda suka gama har tayi wanka, bata shirya ba sai da ta gama yi musu wanka tsab ta bi ta shirya su, dukan su kayan Maryama aka sa musu sanda tana ƙarama. Kayan ba ƙaramin kyau yayi musu ba kamar yau aka siyo su tsabar kyau da sabinta. Amma banda Abie da sai da aka je aka siyo masa tukunna yace ba zai sa kayan mata ba. Ita kawai suka jira ta ci abinci sannan ta wanke kayan, suka rufe ko ina sannan suka fito.

"Ina motar taka?

"Napep zamu hau".

Ita de bata kuma magana ba, har suka fita daga compound ɗin gidan suka nufi titin da sai sada su da babban titi suka tare suka hau, bata ji ina yace ba sai ganin su tayi a airport ta kalle shi.

Tace, "Wani zamu tara?

"A'a Taraba zamu je".

Kawai tsayawa tayi tana kallon shi tsabar mamakin sa. Wai Taraba, haka ake tafiyar daman ? Ba su ɗauki komai ba daga su har yaran, gashi kuma sun taho da yarinyar mutane kenan har ita?

"Amma to Hauwa'u fa?

"Yaya Nilah bana san tambaya".

Daga nan bata kuma magana ba taja bakin ta ta tsuke.....







Continue Reading

You'll Also Like

9.8K 452 9
Labarin sarqaqiyar rayuwa...💫💕Na NAFI ANKA DA MISS XOXO (2016)
268K 7.7K 77
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...
419K 15.4K 192
Won Yoo-ha, a trainee unfairly deprived of the opportunity to appear on a survival program scheduled to hit the jackpot, became a failure of an idol...