A SOYAYYAR MU

By hijjartAbdoul

4.1K 74 0

Be tashi ya ga mace a gidan su ba, rayuwar su gaba ɗayan babu mata idan kaga mace a gidan to auro ga akayi ha... More

Shimfiɗa.
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50

27

60 1 0
By hijjartAbdoul

Sauke ajiyar zuciya tayi, sannan ta taka a hankali taja kujera ta zauna tana ƙara kalle office ɗin da kyau, idan ta ne ya sauka akan gwangwanin madarar da ke kan table ɗin hakan yasa ta tashi tare da zagayawa tana dubawa ga kuma kuɗi a ciki nan tana iya hangowa, ajjewa tayi da sauri jin ana alamar buɗe ƙofa ta dawo ta zauna harda kwanciya da kifa kai irin ace baccin tayi shiyasa ta kifa kan ta saboda kada aga idan ta na ƙiftawa. Dukan table ɗin yayi ne yasa ta tashi tana wani yatsine fuska irin baccin nan nake aka tashe ni, duk da ba'a ganin fuskar ta saboda face mask ɗin da ta saka, amma ya ga alamar kamar bacci take.

Beyi mata magana ba kamar yadda itama ba tayi masa ba, wayar ta kalla taga time, ashe lokaci ya ƙure haka. Tana nan zaune sai ga wani nan ya shigo da Mug da cookies kamar de kullum, ajiyawa yayi ya fice, wani ya kuma shigowa.

"Ka nuna mata Office ɗin ta".

"Yau Farida bata zo ba".

"Me ruwa na kuma?

"Da kace na je na same ta?

"Ohh! Yi haƙuri na manta".

Jinjina kai kawai yayi, daga nan babu wanda ya kuma magana. Sectary ɗin sa ne, wanda a yanzu ya koma ƙarƙashin Yusuf kasancewar Matar Hafiz ce sectary ɗin su, su duka biyun, yanzu kuma Nilah ce ta maye gurbin nasa. Binsa tayi aka nuna mata nata office ɗin, daban a gefen nasa amma nata be kai ko rabin girman nasa ba, sai dai yana da kyan shi sosai, sai wata ƙofa da ya nuna mata wacce zata shiga ta shiga ta office ɗin sa, sai kuma secrets abubuwa da ya nuna a office ɗin. Godiya tayi masa ta zauna ta fara dubawa sai dai babu system, Allah yasa ta taho da system ɗin companyn su, amma bata zo da ita ba yau. Cigaba da tayi da duba office ɗin tana duba ko wanne file dake gefe daban a cikin shell ɗin su, ta je maida wani file ɗin ya faɗi takardun suka watse ta tsugunna tana kwashewa ta ci karo da wani hoto, Jibrin ne da Sagiru suka ja hankalin ta hakan yasa ta ɗaukan hotan ta ware daban, ta ajje komai ta koma kan kujerar ta, tana nazarin hotan duka mutanen bata san su ba sai su Jibrin ɗin, sai kuma wasu mutane guda uku suma da'alama manyan mutane ne su ɗin. Wayar ta ta ɗauka ta kira Faisal ta sanar dashi abinda ta gani sannan ta tura masa hotan.

"Naji kuma suna cewa za su haɗu anan Abujan".

"Ko suna ɗaya daga cikin baƙin da za su zo?

"Ka sa ido akan su sosai dan Allah".

"In Sha Allah kar ki damu".

"Nagode".

Daga haka sukayi sallama, gashi ta baro system ɗin a gida, tana nan zaune sectary ɗin ya dawo ya fara mata bayanin aikin ta ya kuma faɗa mata duk wani schedules na su na yau ta fahimta iya fahimtar ta duk da ba duka ta gane ba amma ta gane wasu abun.

"Oga baya dan ɓata lokaci, baya jira, baya san magana da yawa duk naga ke ɗin kamar baki da hayaniya".

Ya ƙarashe da tsokana, ɗan murmurshi tayi masa duk da har yanzu tana ƙunshe da face mask.

"Nagode".

"Sunana Sadiq".

"Ni kuma Hauwa'u".

Har zai tafi sai kuma yaga ya dace ya sanar da ita. Hakan yasa shi ƙara zama yana fuskantar ta ganin haka ita kuma ta nutsu taji me zai ce.

"Hauwa'u".

Kallan sa tayi alamar inaji, shi kuma ya ɗan sunkuyar da kai, kafin ya ɗago ya kalle ta.

"Ki sani cewa duk abinda zakiyi kiyi gaskiya a ciki. Na sha samun hare-hare daga mutane da dama da kuma na zauna nayi tunani sai naga duk mutum ɗaya ne ke kawo min harin shiga hallaka ma'ana na ci amanar Sir. Sajjad".

Ɗan murmurshi takaici yayi.

Yace, "Sun sace min Mahaifiyata, saboda naƙi amincewa da ƙudirin su".

"Ehhh....?

Ta faɗa tana wani ƙwalalo ido.

Yace, "Ehh, amma ta dawo, idan zaki gane cewar suna da mutane da yawa kenan ba. Kada ki yadda da kowa kada ki sake da kowa".

"Su waye mutanen?

"Mugayen mutane mana".

Shiru tayi tana cigaba da kallan sa, bata ce komai ba, yana bata labarin yadda aka zo aka same shi, ta riga shi ji amma bata nuna masa ta sani ba har ya gama, sukayi sallama ya tafi. Wato ita yanzu wani jan aiki ne a gaban ta bata sani ba. Jin an buɗe ƙofa an shigo yasa ta buɗe ido tana kallon Sadiq.

"Zaku shiga meeting ki tashi kije ki sanar da shi".

Ya faɗa yana ajje mata files ɗin da ya shigo da shi a hannun sa, ya nuna mata.

"Kar ki manta fa, kar ki haɗa takardun kowanne daban yake".

Jinjina kai kawai tayi, ta shiga toilet watsawa fuskar ta ruwa ta goge da towel ɗin da ta gani, sannan ta zo ta saka saban face mask bayan ta gyara idan ta, ta kwashi jakar ta da takardu ta fice. Yana zaune a office yana danna system kai kace aiki yake nan kuwa ba wani aikin da yake yi, kawai tunanin ya lula.

"Assalamu alaikum. Yallaɓai muna da meeting".

Wani irin ɗaure fuska yayi, batare da ya kalle ta ba. Ya rufe system ɗin yayi gaba da sauri ita dake kusan ƙofar ma ya wuce ta ya fita, da sauri itama ta bishi sai dai me kafin taje ya shiga elevator ya barta a tsaye saura kaɗan ta rufe tayi wuf ta shiga tana haki dan ɗan ƙaramin gudu tayi, banda haki babu abinda take yi kamar wanda tayi tsare. Suna fita ma da sauri ya wuce ya barta, da sauri ta bi bayan sa har da gudu take haɗawa kafin ta jefa ƙafa ɗaya ya jefa shida, bata lura ba ashe ya ja ya tsaya tana zuwa sukayi gware da shi da sauri taja tana mai da numfahi, shi kuwa ba komai bane yasa shi tsawa ba, face ganin da ya yayiwa yarinyar a kwance a kusa da motar sa, an shimfiɗa mata ɗankwali ta kwanta.

Inda yake kallo Nilah ta kai idan ta ganin kamar yarinyar ɗazu ya sa ta maida hankalin ta taga kuma yanzu be zai yi musu? Ganin tayi yaje ya finciko yarinyar da ita da ɗan kwalin ya wancakalar daman ita yarinyar ba jiki ba, ga rashin lafiya kuma sai abin ya taru yayi mata yawa, saura ƙiris yarinyar taje ƙasa Nilah ta tsugunna ta tare ta, gaban na wani irin faɗuwa, dai-dai nan Zainab ta zo da abinci a take away ta ƙaraso da gudu dan taga abinda yayi.

"Ke wacce irin dabba ce? Ke a cikin jeren dabbobin ma na lura ke koya musu dabbanci".

"Dabba".

Ta maimaita a ran ta, kafin ta rungume ƴar ta tsam a jikin ta tana jin wani irin zafi da raɗaɗi a ran ta, lumshe idan ta tayi hawaye ya samu nasarar zubowa tana wani irin ƙunjin kuka.

"Idan ba jahilci ba taya..."

Tas! Tas! Tas! Tas!

Kake ji an wanke Sajjad da wasu zafafan maruka guda huɗu, da kallo ya bi wanda ya mare shi ɗin. Tsabar firgice da mamaki bakin sa har wani rawa yake yi wurin furta sunan, kafin hawaye ya zubo idan sa.

"Yaya Aliyu?

Zainab kuwa firgicin da ta shiga baya faɗuwa, ita kan ta marin be mata daɗi ba komai fa laifin ta ne, ada ta san yayi mata biyayya ya so ta ya kuma ƙaunaceta sunyi zaman lafiya sun yi zaman tare amma kuskuren da ta tafka a rayuwar ta ƙwara ɗaya tal da harshen baki ya sauya komai, furuci bala'i furuci masifa ne ina ma zata iya rewarding da tayi ta goge komai. Bata tsaya taga ya karshe abin zai kasance ba ta ja ƴar ta da take da tabbacin suma ne tayi na tsoro.

Nilah marin da aka masa yayi daidai da sakin files ɗin hannun ta suka zube a ƙasa, yadda yaji mamakin marin haka itama taji matuƙar marin, yadda yaji zafi a zuciyar sa zata iya cewa ta fishi jin zafin, bata san me ya haɗa su da wannan baiwar Allahn ba, amma haka kawai ta yarda da mijin ta, bata san tana kuka ba sai da face mask ɗin ta jike jagab da hawaye. A lokacin kuma ta dawo hayyacin ta daga suman wucin gadin da tayi jin wani marin ya kuma sauka a kan fuskar Mijinta.

"Yaushe ka lalace har haka?

Hawayen baƙin ciki ne ya zubo a kan fuskar sa, batare da ya dafe kuncin sa ba ko ya nuna jin zafin marin, a,a takaicin sa da baƙin sa sune wai Yaya Aliyu ya ɗaga hannu ya zabga masa mari? Ba ɗaya ba, ba biyu ba, har dayawa?

"Magana nake maka".

Ya daka masa tsawa.

"Kayi haƙuri".

Kalmar da ta samu fitowa daga bakin sa kenan. Hannu ya ɗaga zai kuma kwaɗa masa wani marin Al-ameen yayi saurin riƙe hannun.

"Haba Aliyu meke damun ka?

"Barni na koya wa wannan sha-shan hankali".

"To muje".

Ya faɗa yana jan sa alamar muje.

"Alameen ka barni na koya masa hankali, ace mutum baya da hankali shashanci yayi masa yawa".

Shi dai Al-ameen jan sa yake batare da ya sake shi ba.

"Yaya Al-ameen me ya faru?

Su Hafiz suka tambaya, suna ƙoƙarin dakatar da su.

"Ku ja shi ku maida shi ciki".

Ya basu amsa, umarnin sa suka bi kuwa kama shi kamar de wani marar lafiya suka maida shi ciki. Itama Nilah jiki a wani irin mugun sanyaye zata bi bayan su.

Al-ameen yace, "Ina sectaryn da za su shiga meeting tare?

Jin abinda yace ne ta tsaya, tare da amsa sunan ta na ita ce. Sannan yace kowa ya watse ganin mutane sun taru suna kallo.

"Muje mu shiga meeting ɗin".

Ya faɗa yana nuna mata hanya, shima yayi gaba, kasancewar yana sauri meeting be wani ja lokaci ba suka fito, direct office ɗin sa suka wuce har ita tana bin sa a baya saboda zata ajje masa wani file koda ta ajje lungun da zai sada ta da office ɗin ta ta shiga tayi lakur da ita tare da jinjina bayan ta, bayan ta cire face ɗin hawaye na sake zubowa fuskar ta, da jimawa ta sani cewar akwai wani irin connection a tsakanin sa da Yayan nasa ko baki ba faɗa ba tasan shine Ya Aliyu. Har lokacin kuma Sajjad be dena zubar da hawaye ba, idan ya tuna akan me aka dake shi sai yaji wani hawayen ya zubo masa wai Zainab. Babu yarda ba su yi da shi ba akan ya dena kuka amma yaƙi.

"Wai Sajjad ba zaka dena kukan ba?

"Akan Zainab ya dake ni fa?

Yusuf yace, "Kaima meyasa kake yawan shiga harkar ta?

"Saboda na tsane ta, bana san ganin ta".

Ya faɗa da ihu har a sannan hawayen kuma be dena zuba ba.

Al-ameen yace, "Amma kasan ai yarda yake san ta ko? Baka san dalilin rabuwar su ba, baka sani ba ko shi Aliyun ne mai laifi? Kada kayi judging akan abinda baka sani ba Sajjad".

Murmurshin takaici yayi ga kuma hawaye na zuba a idan sa batare da ya ce komai ba.

Yusuf yace, "Sajjad yanzu kayi haƙuri ka dena wannan kukan, bana san abinda zai ɗaga maka hankali".

Hafiz yace, "ka kuma dena shiga harkar ta".

"Ba za ku gane ba ne ba, na tsane ta".

"Ka kashe ta to, nace ka kashe ta".

Ya faɗa yana shigowa, kafin su yunƙura su tashi kuwa ya cakumo shi ya fara kai masa duka. Al-ameen ne ya samu ya ɗauke Aliyu da mari, sannan ya tsaya daga abinda yake yi yana kallan Al-ameen da mamaki. Tsawon shekaru basu taɓa ko faɗan baki ba a junan su amma yau shine ya mare shi?

"Mamaki kake ji na mare ka?

Ya faɗa da dukkan muryan sa.

"Alameen?

"Yarda kaji a zuciyar ka shima haka yake ji. Mamakin marin da nayi maka ba? Shima haka yaji".

"Mari fa?

"Shi dutse ne?

Kulle idan sa Sajjad yayi tare da zuwa da shigewa cikin office ɗin Nilah batare da ya kula da ita ba, idan sa har wani rufewa yake yi, ya kuma dafe ƙirjin sa da yake masa wani irin ƙuna da raɗaɗi, ganin yanayin sa ya sata saurin bin sa baya.

"Dan Allah Yaya Aliyu kuyi hakuri komai ya wuce".

"Kasan abinda yake yiwa yarinyar ne?

"Bansani ba, ba kuma na son sani. Dan haka kayi hakuri Meye"?

"Amma...."

Al-ameen ya rufe masa baki da hannun sa.

"Kayi haƙuri da marin da nayi maka".

Kasa haƙuri sukayi kawai suka rungume juna kowa na zubar da ƙwalla, sune suka dukan, amma kuma sun fi wanda aka daka jin zafi da ciwon abun. Yusuf da Hafiz kuwa kasa yin komai sukayi kawai suka tafi gida.

A office ɗin Nilah kuwa, kasa yin komai yayi zaman ma kasa yayi hakan yasa shi tafiya zai faɗi ta tare shi, jin an tare shi yasa shi kallan ta cikin ido da ido suke kallan juna idan sa yayi jajur da kuma hawaye a jikin sa, haka itama nata idan yayi jan, kasa riƙe shi tayi hakan yasa ta tafiya ƙasa da shi ta zauna a ƙasa har a yanzu kuma be ƙara sa rufe idan sa ba, yana kallan ta, ƙwallar cikin idan ce ta shiga cikin nasa hakan yasa shi rufe idan, duk san sa na sake buɗe idan hakan ya be samu ba, daga ƙarshe ma wani irin numfashi yake saukewa kafin ya tsaya cak numfashin nasa. A hankali ta kwanta a saman sa tana sakin kuka mai tsuma zuciya gami da ɗaci.

~~~~

Yusuf kuwa na zuwa gida yaji abinda ya kuma tayar masa da hankali, dangane de da matar sa tana waya da Yayar su, wannan karan kasa ignoring yayi ya shiga a hankali batare da ta sani ba ya jingina a jikin ƙofar ɗakin nata bayan ya rufe, ya lumshe idan sa. Sai da ta gama tsaf.

Yace, "A SOYAYYAR MU babu hassada a cikin ta".

Gaban ta taji ya faɗi sam bata ji shigowar sa ba bare kuma taji ƙamshin turaren sa sai maganar sa da taji. A kiɗemi ta juyo taga tagan shi a jingine a jikin ƙofa idan sa a rufe.

"A SOYAYYAR MU. Soyayya ce tsantsan da muke yiwa juna, A SOYAYYAR MU babu tsana a ciki. A SOYAYYAR MU babu ɓoye-ɓoye, A SOYAYYAR MU bamu san wani abu ba wai shi tsana, A SOYAYYAR MU babu tashin hankali a cikin ta. Ba mu san baƙin ciki da hassada ba, bawa iya kan mu hakan ya tsaya ba har ƴan uwan mu sa iyayen mu. Shin laifin ne dan mun so junan mu yarda ya kama ta? Shin laifin mu dan A SOYAYYAR MU, muna yin ta yadda za'ayi a kwantancen mu da ita?

Sai a lokacin ya buɗe idan sa, ya fara takawa inda take kasa zama tayi ganin yarda idan sa ya rine da ɓacin rai, duk maganar da yake yi kuma a hankali yake yin ta babu hayaniya a cikin ta, tashin da tayi ne yasa shi bin ta har ta je bakin gado.

Yace, "shin a soyayyar da muke yiwa juna ma ta tare miki dashi? Me ta rage ki da shi? Laifin yin haka? Ko kuma laifi ne dake mu so ƙaramin ƙani a wurin mu? Baza ki gane cewar shine ƙarami kuma auta? Sannan mafi soyuwa a gare mu? Ba zaki gane cewar bayan annabin mu da iyayen mu shine farko ba? San da nake masa bana yiwa kai na, sanda nake masa bana yi miki shi, san da nake masa kuma zai iya sawa na rabu da ke".

A gigici ta kalli ƙwayar idan sa, taga ko da wasa yake? Amma sai dai bata ga alamar wasa a cikin wannan idan ba.

"Idan kuma kina tantama ki cigaba da furtawa bakya san wani nawa ki gani. Zan nuna maki waye Yusuf Kabir Sani".

Daga ya banka ƙofar ya wuce, ɗakin Aman ya nufa ya fara haɗa kayan sa duk wani abu da ya sani sai da ya haɗa a cikin a kwati ya shirya duk wani kayan buƙatar sa, ya ɗauko laundry basket ya juye kayan cikin ya zuba kayan wasan sa a ciki, ya shiga kitchen ya nan ma ya haɗu kayan sa na amfani. Sannan ya kai mota ya dawo yayi wanka ya ci abinci, ya bari akayi sallah sannan ya je gidan Hafiz inda ya ke da tabbacin cewar yaron yana can, ɗaukan sa yayi.

Tace, "Kabar shi mana to, tunda ba kuka yake ba".

"Yaye za'a kai shi wurin Mama".

Hafiz yace, "Wacce Maman?

"Maman da ka sani de".

Farida tace, "Akan me za'a yaye shi?

"Kika sani ko little Princess zamu samu?

"Ahh Masha Allah"

Sunkuyar da kai kawai yayi.

Hafiz yace, "Gaskiya zaka kaiwa Mama wahala".

"Ka bari mu haihu sai a haɗa akai su mana".

"Matata zata sha wahala".

"Masu mata".

Shi dai bece komai ba ya tashi ya fice, be kuma nunawa ba kowa komai ba kamar yarda basu gane ba, kuma alƙawarine ya ɗaukawa kan sa ba zai nuna musu komai ba. Koda yaje gidan daƙyar ya samu ya sanar da Mama abinda ya kawo shi wai shi kunya, to Allah ya taimake shi sun gane matar tasa ciki ne da ita. Anan ya san shirye-shiryen da ake na zuwa Bauchi ranar Jummu'ah domin aje ayi walimar dawowar Daada idan an dawo kuma sai a haɗa na abokan sa da mutanen arziƙin da ba zasu sami damar zuwa ba.



~~~~~


A zaune suke su uku kowa riƙe da cup ɗin da aka zuba lemu a ciki sun haɗa suna chess irin nishaɗin nan. Sagiru ne da Jibrin sai Ogan sa mai suna Saminu wanda ya kasance wanda shine yake basu wani umarni da suke kai.

"Yanzu sunyi faɗa. Komai zai fara lalace musu".

"Amma bakwa ganin za su shirya kuwa?

"Ina Jibrin?

"Gani yallaɓai".

"Shi baya san ake sanar da shi laifin ƙaninsa akan tsohuwar matar sa, mu kuma laifin zamu yi ta faɗa ko yayi ko be yi ba".

"Ku ce mun alaƙa ta rushe".

Sai suka kece da dariya su dukan su har da ɗaga ƙafa.

"Ai ba iya alaƙa ba Soyayya ta rushe.....

Continue Reading

You'll Also Like

166K 11.9K 17
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
345K 26K 38
ပဲပြုတ်သည်ငပြူးနဲ့ ဆိုက်ကားဆရာငလူးတို့ရဲ့ story လေးတစ်ပုဒ်
266K 7.6K 76
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...
183K 19.5K 29
Labarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci...