DARE DA DUHU

By nimcyluv

3.2K 168 53

Labari Rayuwar Abra da Mahaifinta. More

Shimfiɗa
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10

Chapter 5

223 14 5
By nimcyluv


Wani irin kallo Captain ya bi Faruk da shi, yana son gazgata abun da kunnuwansa suka jiye masa ya fito daga bakin Faruk.

"Do you mean my Abra?" Yai maganar yana nuna kansa da yatsansa.

Faruk cikin damuwa yace "eh, Abra ba'a ganta ba, na duba duk in da ya dace a cikin barrack ɗin nan ba'a same ta ba"

"Shhhhhh, kar ka gayamin maganar banza mana Faruk, ya za'ai ace yarinyar nan ta ɓata how comes? Kaga, i have no option for now am going make sure you bring back my daughter"

"Haba Captain, ta ya zan maka ƙarya, Wallahi a.....

Be ƙarasa maganar ba Captain Khamal ya ɗaga masa hannu yace "na gama Magana, duk in da 'ya ta take ka tabbatar ka nemo ta ka kawo min a bata"
daga haka ya cigaba da takunsa sannu a hankali me kama da na ƙasaita yaa bar Faruk a tsaye a gurin.

Faruk yace "ya salam, Madam Halima kin kashe ni ina kika bar yarinyar nan ta tafi? Ya a kai ta ɓata?" ya ƙarasa maganar yana sauke wani irin nannauyan numfashi, kafin daga bisani ya juya cikin sassarfa ya nufi wani sashi na barrack ɗin.

Zaune take a kan gwiwonwinta, ta zubawa kyakkyawar yarinyar me kama da 'yar larabawa idanu, hawaye ne kwance akan fuskar yarinyar, hannunta ɗaya riƙe da teddy bear, ta zura yatsanta ɗaya a baki tana tsotsa kamar me shan nono.

"Hey look up, kina son chocolate?" Tai Maganar tana kallon idon Abra.

Shiru Abra tai tana binta da kallo, dan sam ba ta ji me tace ba.

"In baki chocolate, ai zaki sha ko?* Still Abra bata amsa ba, kallonta kawai take kamar wata gunki.

Salima ta tashi ta ɗakko jakarta,ta ciro Chocolate ta miƙawa Abra, maimakon Abra ta karɓi Chocolate ɗin, se ta fashe da kuka tana kiran "Abbi, Abbi".

"Shhhhhh, is ok i will take you to your Abbi, amma ki yi shiru, I have plenty chocolate and teddies, zan baki idan ki kai shiru"

Ƙaro sautin kukan Abra tai, tana kiran sunan Abbi.

"Ji min makirar yarinya zata ɗaga min hankali, will you shut up?"

Babban abunda ya bawa Salima mamaki, be wuce yadda sam Abra ba ta responding ga Maganar da duk za tai mata ba, kukanta kawai take yi.

Salima tace "what so ever, da ke zanyi amfani in cika burina, se na nunawa matar Khalid bariki iyawa ce, sena rusa gidan da mijin da take taƙa ma da shi.

TWO DAYS BACK. Kwana biyu da suka shige!

tun bayan faɗan nan da Salima sukayi da Naima, Salima ba ta sake komawa gurin Khamal ba, se ta fita waje ta kama Hotel tai zamanta, sakamakon rashin posting ɗin su da ba'a yi ba.

Tun abun da ya faru a tsakanin ta da Na'ima matar Khamal, tace se ta ga abunda ya turewa buzu naɗi in dai akan Khamal ne, se ta gwadawa Na'ima kalar nata rashin mutuncin da iya barikanci.

Khamal kuwa da ƙyar ya rarrashi Na'ima, kasancewar ta mace me tsananin kishin tsiya, ba ta da haƙuri ko kaɗan akan kishi, ita da ta zo dubiya ƙarshe se da su kai faɗa da Khamal akan Salima.

Na'ima ta daɗe da sanin Salima na bibiyar Khmal, amma tafi kowa sanin halin mijinta, mutum ne kamili da be ɗau duniya da zafi ba, sam ba shi da wannan ɗabi'ar ta kule kulen mata, hasali ma mutum ne me tsare gida, wanda ba'a kawo masa wargi, amma Salima ke ta cusa kanta a wajensa.
Tun kan ya Auri Na'ima, Salima take son sa, amma kasancewar Salima ba mutuniyar arziki ba ce ya sa ko saurararta ba ya yi sam, ya sha yi mata gargadi da jan kunne, akan ta fita daga rayuwar sa amma taƙi, se da ta ƙure shi ta kai ga ta sa ya gaya mata miyagun maganganu, amma still ta ƙi barin rayuwarsa, sannan tai alwashin se ta ga bayan Na'ima, se ta raba shi da ita.

A ranar da Na'ima su kai faɗa da Salima, washegari ta shirya tace ba zata cigaba da zama ba, tafiya za tayi gida.

Captain yace "dear, yanzu tafiya zaki ki barni a nan, nika ɗai?"

"To zaman me zan cigaba da yi, ka san EDD ɗina ma ya kusa, gara ina gida haihuwa ta zo min, tun da suna kula da kai kuma an kusa sallamar ka"
Haka ya ƙyaleta, tai shirinta ta juya Kanon dabo.

Washegari da safe wajen ƙarfe sha ɗaya na safe, Salima tai wanka ta shirya ta koma gurin Khamal, a hanyar da zata sada ta da ward ɗin da yake, ta haɗu da Faruk hannunsa ɗauke da Abra.

Ta tsaya suka gaisa, ta kalli Abra tace "ina ka samo wannan cute Babyn haka?"
Nan Faruk yai mata bayani yace "a gurin operation Captain Khamal ya tsinto ta, tana gararanba a cikin daji, Kuma ikon Allah, Allah ya haɗa jininsa da ita sosai"

Salima tace "ita ma kidnapping ɗin nata a kayi?"

Yace "Sanin gaibu se Allah"

Tace "ikon Allah, to an gano iyayenta?"

Yace "A'a, ba'a gano su ba, tana gurin wata staff ɗin mu ne, Madam Halima matar Captain Abdussamad Goza"

Tace "ok, Allah sarki shes cute Masha Allah, to yanzu ya za'ai da ita? Tun da ba'a samu iyayenta ba?"

Faruk yace "Ai da kyar ne idan ba Captain ne ze ɗau yarinyar nan ba, dan kamar sun daɗe da sanin juna, yana son yarinyar sosai dan har ya raɗa mata suna, it ma Abbi take ce masa, kamar sun san juna,. Se dai be gayan abun da ya yanke ba amma nafi kyautata zaton da ita ze koma, ya riƙeta kan a ga iyayenta"

Ɗan shiru Salimaa tai kan daga bisani tai ajiyar zuciya tace "thats good" daga nan ta wuce zuwa in da Khamal yake.

A wannan karon ma bata samu kulawa daga Khamal ba, sema tijarar da yai mata ya koreta daga ɗakinsa.
Idan da sabo ta saba da wannan abubuwan na wulaƙanci da hantara da yake mata, amma sam ba ta damuwa, ita dai burinta ya amsa yana sonta.

Washegari ta koma cikin barrack, cikin ikon Allah ta bi ta compound ɗin su Madam Halima, abun mamaki ta ga Abra a tsaye hannunta da teddy ɗinta, tana rarraba manya manyan idanunta tana ƙarewa gurin kallo.

Ƙarasawa in da take Salima tai, ta durƙusa a gabanta tace "cute baby, how are you?"

Ɗan ja da baya Abra tai tana kallon Salima.

Wani tunani ne ya faɗowa Salima, ta kuma matsawa kusa da Abrar tace "ina da sweet, ai zaki sha ko in baki?"

Still Abra ba ta amsa ba, saboda ba ta iya jin abunda Salima ke faɗa.

"Ok, zomuje in kai ki gurin Abbi"

Bakin Salima ta ƙurawa ido, taga kamar Abbi tace.

Ta miƙawa Abra hannu, aikuwa ba musu ta bita, saboda ganin laɓɓan Salima sun ambaci Abbi.

Salima ta ɗauki Abra ta tafi da ita.

Yadda a kai Abra ta fito kuwa shine Madam Halima ce t fita  tare da Abra, da suka dawo ne, taga Abra ta tsaya tana kallon murguza murguzan karnunkan da ke kaiwa suna komowa a compound ɗin, ta ɗauke Abra ta shiga da ita gida, a zatonta ko tsoronsu take ji, sedai bayan shigarta wanka, Abra ɗin ta sake fitowa tana kallon karnukan, wanda a nan ne Salima tai awon gaba da ita, tare da ƙudurce wani abu a ranta.

Tun da Madam Halima ta farga Abra ta ɓata ta shiga cikin tsananin damuwa da tashin hankali, saboda Abra ta shiga ranta matuƙa, sannan da ya zata fara bayanin yarinyar da aka bata ajiya ta ɓata?.

Captain Khamal kuwa ji yake tamkar zuciyar sa zata fashe, maimakon yai murna ze koma garinsa da yai wata da watanni baya nan, amma ya kasa farinciki saboda ɓatan Abra, ji yake kamar 'yar cikinsa ce ta ɓata, haka nan yaji yana ƙaunar yarinyar, dan har a wani sashi na zuciyar sa yana jin idan iyayenta suka bayyana be san ya zeyi ba, sakamakon tsananin ƙaunar yarinyar da yake yi.

Shiru yai yana tuna innocent face ɗinta,tana kiransa da Abbi, wanda har cikin ransa yake jin sunan da take kiran na shi da shi. Tunani yake akan how taje Wannan dajin? Waye ya kaita? A yaya ta rayu? Suwaye iyayenta? Gashi tun da ya tsince ta shi dai be ji tai wata magana ba, da zata ba shi haske game da ita ba, Abbi kawai shi ne abun da yaji bakinta yana faɗa.

Wata zazzafar iska ya furzar daga bakinsa, yana jin tamkar ya koma Naija State, tabbas ba dan an riga an gama shirya dawowarsa ba, da ba in da za shi se an nemo masa Abra ɗin sa, amma a yanzu ma ba ta ɓaci ba, nan da 'yan awanni idan ba'a ganta ba, dole ya koma Naija state, jikinsa ya na ba shi Akwai wani al'amari me girma game da Yarinyar.

Faruk kansa ya shiga damuwa da tashin hankali, akan ɓatan Abra, balle Madam Halima da megidanta, sun fi ɗaga hankalinsu akan kowa, nan da nan aka baza cigiyarta a cikin barrack ɗin.

Salima kuwa Abra ta addabeta da kuka, fafur yarinyar nan ta ƙi jin rarrashi, gashi maganar duniya ta ƙi sauraron Salima.

Salima ta ɗauketa ta fita da ita, wani babban shop ta kai Abra tai mata siye siyen, kayan ci da na wasa, se dai duk da hakan Abrar ta ƙi sakin jikinta da Salima, yadda take nunawa ma kamar tsoronta take ji.

Salima ba ta damu da hakan ba, burinta kawai take fatan ya cika, ta tafi da Abra gurin wasan yara, ta din ga yiwa Abra ɗin hotuna.

Sai magariba Sannan suka koma masaukin Salima, sedai  suna komawa Abra tace ba ta san zace ba, ta ɗora da kukanta a in da ta tsaya tana kiran "Abbi"

Salima tace "Ohh God, this pikin want spoil ma plans"

Ta kaɗa ta raya, amma Abra ta ƙi bacci, kuma taƙi yin shiru, tai rarashin tai shouting ɗin, amma kamar ta na yi da gunki.

Ba shiri ta ɗau Abra ta nufi cikin barrack ɗin, kai tsaye ba tare da shakkar komai ba, ta nufi gidan Madam Halima, ai kuwa ta tarar da su a ƙofar gida tare da Faruk, da wasu sojoji, Faruk ya rasa in da ze sa kansa, saboda yadda ya sha kiran waya a gurin Captain Khamal akan Maganar Abra.

"Wa nake gani haka kamar Abra?" Yai maganar yana kallon in da Salima ke tahowa. Duk da dare ne amma ko ina da hasken fitilu.

Salima ta ƙaraso tace "lafiya na ganku a tsaye haka?"

Faruk yace "wacce irin magana ce wannan, kin ɗagawa mutane hankali, a zatonmu Yarinyar nan ɓata tayi".

Salima cikin ko in kula tace "No, na zo wucewa ne na ganta, na ɗauke ta mukaje na sai mata ice cream, that's all"

Mijin Madam Halima yace "amma haka akeyi, ki ɗau yarianya ba excuse ba wanda ya sani, duk kin ɗaga mana hankali, yarinyar nan fa ajiyar ta aka bamu"

Salima tace "to ai ni banga wani laifi da nayi ba, yanzu ba gashi na dawo da ita ba"

Abrar kuwa Faruk take miƙawa hannu, tana maimaita Abbi.

Ya karɓeta tare da rungumeta a jikinsa yana faɗin "Am sorry dear" se jera ajiyar zuciya take.

Ban da Allah yasa Faruk da mijin Madam Halima na gurin, da se sun bawa hammta iska, dan ba ƙaramin haushin abunda Salima ta aikata ba Madam ta ji, yadda ta ɗaga musu hankali da yawa.

Faruk kuwa ya dudduba Abra ya ga ba abunda ya sameta, dan haka ya ƙudurce, a gobe zuwa jibi ze gaggawar zuwa Kano, ya danƙawa Khamal Abra, idan ya so koma ya ze da ita yayi, tun da Salima ta fara ɗaukarta ba wanda ya sani, nan gaba be san me za tai mata, saboda ya san Salima farin sani, sun taɓa aiki tare, ya san irin yadda take faɗi tashin samun abunda zata samu shiga a gurin Khamal.

Labarin da aka tashi da shi yau ne, yai matuƙar girgiza al'ummar ƙasar, 'yan ta'adda sun tare manyan motocin cike da ɗaliban jami'a masu zuwa excution, sun yanka wasu daga mazan ciki, sun yi awon gaba da 'yan matan da malaman su zuwa cikin daji, a can Jihar Kaduna.
   Lamarin ya girgiza al'umma da dama dake ƙasar Nigeria, kasancewar ba a warke daga jimamin, ɓatan ɗalibai 'yan makarantar Sakandire da aka kwashe ba, wanda sojoji suka ƙwato su da kyar, katsam se ga wannan mummunan labari ya sake cika gari.
A ranar da aka sace 'yan makarantar washegari 'yan ta'addan suka saki video suna demanding 200millon as a ransom, a cikin kuɗin da gwamnatin tarayya za ta karɓa na tallafi daga ƙasashen turai, suka bada sati guda cewar idan ba'a biya kuɗin ba, za su dinga yiwa matan Fyaɗe suna yanka su ɗaya bayan ɗaya, kuma muddin aka tura sojoji za su kashe su baki ɗaya, Innalillahi wa Innalillahi raji'un.

Tun bayan dawowar Khamal, 'yan dubiya da 'yan Sannu da zuwa suka cika gidan, aka dinga tururwar zuwa duba Khamal, Na'ima se rawar kai take gami da taraiyar sa, da yi masa hidima iya iyawarta, dan a duniya ba ta da burin da ya wuce ganin ta sanya Khalid farinciki, saboda tsananin soyayyar da take masa.

Duk da tsufan da cikinta yai, shima da raunin da ke jiinsa, da batun ɓatan Abra da yake damunsa, be hana su nunawa juna tsantsar soyayya da yadda su kai kewar juna ba.

Faruk kuwa se farinciki yake, akan yadda ze  mayarwa da Khamal amanarsa, ya san ze farinciki ƙwarai.
 

Cikin tsananin tashin hankali da kaɗuwa, Captain Khamal yake kallon labarai, da tashin hankalin da al'ummar wannan ƙasa suka tsinci kansu a ciki, su gasu da su kai wannan opretion ko warkewa ba suyi ba, an kuma kai wani harin, wanda wasu sojojin za'a kuma ɗiba suje fafutukar karɓo su, babban abunda ya sake ɗaga masa hankali be wuce yadda ya shiga tunanin ya akai 'yan ta'adda suka san za'a bawa gwamnatin tarayya tallafi? Bayan ba aji hakan daga bakin gwamnatin ba, anya babu haɗin bakin wanda suke jikin gwamnatin? Yanzu iyalan su Jamil da aka kashe, babu wani tartibin abu da Gwamnati za tai wa iyalansu, da ze rage musu raɗaɗi, wanda gwamnati zata nuna damuwarta da rasa ɗan ƙasa da akai, a bakin aikin kare ƙasarsa, haka za'a kuma kwasar wasu a kai su daji.
Wani mugun sarawa kansa yai, tare da tunanin meye mafita akan wannan lamari da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.

Ƙarfe huɗu daidai, Faruk yana cikin garin Kano tare da Abra, shima ya warke daga harbin da ke hannunsa.

Khamal yana kwamce akan 3seater, Na'ima na jikinsa a kwance tana rarrashinsa, ganin yadda ya shiga damuwa, saboda wannan abu da ya sake faruwa mara daɗin ji, se ƙoƙarin kwantar masa da hankali take, saboda ya shiga damuwa sosai.

Knocking ɗin ƙofar falo aka fara yi, Na'ima tace "Baby bari in buɗe ƙofa"

Khamal yace "No dear, zauna inje in buɗe ki huta, kar ki wahal da kan ki da babyna"

Murmushi tai tace "My sweet, kar ka damu dama ance in dinga exercise, bari in buɗe"

Ya jinjina mata kai, ta miƙe tsaye tana tafe sannu a hankali, cikin salon tafiya irin ta masu juna biyu.

Tana buɗe ƙofar ta ga Faruk tsaye, cikin ƙananan kaya, murmushi yai tare da sara mata.

Ita ma murmushin tai tace "kai ne a tafe ba sanarwa? Ya jikin naka?"

Faruk yace "Alhamdilillah"

Ba shi hanya tai ya shigo, se yanzu ta lura da ƙaramar kyakywar yarinyar da yake tafe da ita.

Abra na hango Khamal, ta ruga da gudu ta nufe shi tana kiran "Abbii"

Da azama ya tashi zaune, duk da haryanzu yana jin ciwo a in da aka harbe shi.
Abrar ta faɗa jikinsa ta ruƙunƙume shi, Captain ya rungumeta sosai a jikinsa yana faɗin "My daughter, i missed you" ta ɗago tana bin idon Khamal da kallo, tana murmushi.

Faruk ya sarawa Khamal sannan ya zauna yana faɗin "Yallaɓai ya jikin?"

Khamal yace "jiki Alhamdilillah"

Na'ima kuwa kallonsu take cike da rashin fahimta, ina Captain ya samo 'ya har ta ke kiransa da Abbi, ta daɗe da sanin sa kenan?.

Khamal ya kalli Na'ima yace "Madam, a kawo musu ɗan abun taɓawa"

Ta miƙe ta nufi hanyar kitchen, zuciyarta fal wasi wasi da tambayoyi.

Khamal ya kalli Faruk yace "ya akai aka ganta?"

Nan Faruk ya gayawa Khamal duk abunda ya faru, Captain Khamal yai shiru tare da jinjina kai yace "Salima again?"
Shiru ya ɗanyi yana nazari, sannan yai ƙwafa, yana sake rungume Abra a jikinsa.

Ya nisa yace "Faruk, ashe abunda ya kuma faruwa kenan, an kuma kwashe ɗaliban jami'a?"

Faruk ya girgiza kai yace "bari kawai Captain, abun akwai tashin hankali, kullum abun ƙara worst yake, matsalar sake yawa take, kalli uban wanda muka kashe, da wanda muka kama, amma bayan ransom ɗin da suka buƙata har da se an sakar musu yaransu da muka kama, within seven days"

Khamal ya cije laɓɓansa na ƙasa, yana wani irin huci yace "Why? And When? Yaushe zamu samu 'yan ci, hankalinmu ya kwanta na 'yan ƙasa ya kwanta, har ɗan ta'adda yasan za'a bawa gwamnati tallafi, ya buƙaci wani abu a ciki, wannan wane irin abu ne, idan da gwamnati suke faɗa meye laifin innocent souls da suke sacewa suna cin zarafin su, yaushe hankalinmu ze kwanta? Gwamnatin mu na iya ƙoƙarin ta, mu kanmu jami'am tsaro muna namu ƙoƙarin, to a ina matsalar take? Waye me laifin?" Ya ƙarasa maganar yana huci.

Faruk yace "hakane, kowa yana ƙoƙari, amma akwai buƙatar mu gyara mu sake zage damtse gaba ɗayanmu, mutanen nan 'yan uwanmu ne, a cikin mu suke, meyasa za su zage su dinga kashe mu? Me mu kai musu? Akwai wani abu a ƙasa da yake buƙatar dogon Nazari".

Captain yai ajiyar zuciya yace "hakane, kuma idan aka tsaida hankali guri ɗaya, za'a a iya samo bakin zaren"

Faruk yace "hakane, Allah ya iya mana"

"Ameen" Khamal ya amsa.

Na'ima ta dawo Falon ta kawowa su Faruk snacks, da ruwa da lemo me sanyi.

Abra tai ta bin abunda ta kawo ɗin da kallo, Captain ya ɗakko donut ya miƙa mata. Ta karɓa maimakon ta kai bakinta, se ta hau leƙa ɗan ramin nan na jikim donut ɗin tana dariya, a zatonta abun wasa ne.
Sai da Khamal, ya ɗauka ya ci sannan ita ma ya nuna mata yadda za ta ci, sannan Abra ita ma ta fara ci.

Faruk da Khamal suka shiga hira abunsu, suna cigaba da tattaunawa akan matsalar tsaro, Abra na jikin Khamal tana ta kaɗa ƙafa tana ciye ciyenta.

Faruk ya miƙe tare da cewa "to Yallaɓai, ni zan tafi and Alhamdilillah na dawo da amanar da aka bani, ina fatan Ubangiji Allah ya taya riƙo, sannan ya ƙara maka lafiya"

Captain yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, nagode ƙwarai Faruk, ka gaida gida".

Faruk ya juya ze tafi, Na'ima tace "a'a ya na ga kuma ze tafi ya bar yarinyar?"

Khamal yace "karki damu zan miki bayani"

Faruk ya juya tare da ɗagawa Abra hannu, itama ɗaga masa hannu tai tana masa murmushi.

Na'ima ta dawo da dubanta kan Khamal tace "Nifa ban gane ba, bayanin me za kai min?"

Khamal yace "Calm down baby, ki zauna mana"

Zama tai tana tura baki tace "Gaya min, meye ma'anar wannan abun? Wacece wannan yarinyar?"

Khamal ya gyara zamansa, ya gayawa Na'ima komai, tun daga tsintar Abra da yai har zuwa yanzu, sannan ya ɗora da cewa "A hukumance ma, hukumar mu sun san da zaman Abra a hannu na, za'a cigaba da neman iyayenta, in Allah yasa an samesu shikenan, idan ba'a same su ba ina son Abra ta cigaba da zama tare da mu a nan, mu riƙe ta tamkar 'yar da mu ka haifa".

"Dan Allah ɗan saurara mana Khamal, wai shekaruna nawa ne yanzu a duniya da har kake tunanin zaka iya raina min hankali? Wato ka mai da ni ma wata nusarar mahaukaciya, wadda ba ta san me take ba, kaje karuwa ta haifa maka 'ya, kuma ka ɗakko kace in riƙe kana cikin hayyacinka kuwa? Kai ina zaton sautin ƙarar bom da ka saba ji a daji ya taɓa maka ƙwaƙwalwa ba ka sani ba.
To bari kaji in gaya maka, wannan 'ya Wallahi ba zan riƙeta ba, ka mayarwa da uwarta can da kuka haifeta tare ta riƙeta, dama aiku sojoji ba wanda za'a bawa amana bane, wato uwarta na gudun abun kunya ba zata riƙe ba se ni, karkatacciyar bishiyarka me daɗin hawa, ni zan riƙe 'yar karuwa to Wallahi da sake"

"Shut up Na'ima!" Tsawar da Khamal yai mata se da ɗan cikinta ya juya, saboda tsabar razana da ta yi.

"Ni kike cewa na haifi 'ya da karuwa a waje? Na'ima yanzu shedar da zaki bayar a kaina kenan? Kin fi kowa sanik ni ba mutumin banza bane"

Cikin tsiwa tace "Abu na ɗan Adam kowane lokaci ai yana iya canzawa, kuma in da kake zuwan tunda ba wani ne yake binka ya ga me aikata ba, ai Allah kaɗai ya san me kake yi, dan haka Wallahi ba zan riƙe 'yar karuwa ba, ka maida ita gurin uwarta tun da wuri".

Khamal yace "Na'ima, nan gidana ne, kuma ko 'yar karuwa na kawo nace ta zauna, gida na ne ba naki ba, idan ba zaki iya riƙe Abra ba, zaki iya tattara kayanki ke ki koma in da kika fito".

A razane ta kalli Captain Khamal tace "yanzu zaka iya rabuwa da ni, da ɗanka na sunna da zan haifa akan 'yar da karuwa ta haifa maka Khamal?"

Yace "yes of course, idan ba zaki zauna da Abra ba, ni zan iya rabuwa da ke, kuma ko ki yadda tsintar Abra nai, ko kar ki yadda ki cigaba da zama akan bakanki cewar 'ya ta ce da na haifa a waje, wannan ke ta shafa amma Abra a nan zata zauna tare da mu".

Fashewa Na'ima tai da kuka, ta wuce bedroom ɗinta, ta cire wayarta da ke caji, ta shiga neman lambar Ammi, wato mahaifiyar Khamal, Ammi na ɗagawa Na'ima ta sake fashewa da kuka tace "Ammi dan Allah ku zo gidanmu akwai matsala, Khamal yaiwa karuwa ciki a waje, ta haihu tace ba zata riƙe ba, shine ya kawomin ita wai in ban riƙe ba ze sakeni"

Ammi tace "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Khamal ɗin?"

"Wallahi Ammi da gaske nake, dan Allah kuzo, kar baƙi ciki ya kasheni, dan Wallahi se da ya zaɓa ko ni ko ita, ba zan zauna da 'yar zina in raineta ba!".

COMMENT AND SHARE

BRIGHT PENS
NIMCYLUV
AYSHECOOL
ZEE KUMURYA

Domin ƙarin bayani, ku tuntuɓe mu akan
07063065680
09047871750

Continue Reading

You'll Also Like

5.5M 224K 67
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally ❣️ Cover credit...
197K 15.3K 35
𝐕𝐈𝐇𝐀𝐀𝐍 ♡ 𝐑𝐔𝐇𝐀𝐍𝐈𝐊𝐀 Ruhanika, a quiet introvert with a passion for books and study. She thrives in the world of words, finding solace in...
257K 17.9K 55
ABHIMANYU RATHORE :- Rude , workaholic CEO of Rathore Empire .Devilesing hot , every girls drools over him .But loves his family to dearest . . SAKS...
803K 8.1K 67
𝐢𝐧𝐜𝐥𝐮𝐝𝐞𝐬 𝐚𝐥𝐥 𝐨𝐟 𝐭𝐡𝐞 𝐛𝐨𝐲𝐬 ✦ .  ⁺   . ✦ .  ⁺   . ✦ don't forget to vote, share and comment. 🤍