SAUYIN RAYUWA ✅

By divaadoveysdiaries03

2.9K 299 4

labari akan yadda rayuwa ta kan sauya wa Dan Adam.yadda abubuwa sukan juya su rikice su firgice har mutum yag... More

(1)
Sauyin rayuwa (2)
Sauyin Rayuwa (3)
(4)
(5)
(6)
(7)
(8)
(9)
(10)
(11)
(12)
(13)
(14)
(15)
(16)
(17)
(18)
(19)
(20)
(21)
(22)
(23)
(24)
(25)
(26)
(27)
(28)
(29)
(30)
(31)
(32)
(33)
(34)
(35)
(36)
(37)
(38)
(39)
(40)
(41)
(42)
(43)
(44)
(45)
(46)
(45)
(46)
(47)
(48)
(49)
(49)
(50)
(51)
52
53
54
55
56
57
(58)
59 (tarewan queen)
60
(61) haduwar masoya
(62)
(63) Za end

(9)

31 2 0
By divaadoveysdiaries03

SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(9)

_______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Bayan dogon kuka da jinyar zuciya ta bawa kanta hakuri Dan ba yau farau ba ,shekara nawa ana Abu daya kullum ba sauyi?

Se sauyin da ita ya same ta?

Kuna mamakin inda iyayen Abida suke da duk kaunar dake tsakanin su,da suka bar yar su tana ta wahala a gidan Hashim?

Ku biyo ni cikin wannan labarin na sauyin rayuwa,zaku ga yadda komai ze dafi .

Cikin Abida ya samu watannin shi bakwai .Kuma a har lokacin C's ake mata .shi yasa ma likitoci sun bata zabin hutu daga wannan haihuwa tata saboda gudun matsala.

Sannan a har yau Babu abunda ya chanja daga rashin kula da lafiyar ta daga wajen Baban Abul.

Shi yasa ma har yanzu ba ko yaushe take zuwa antenatal ba,se sanda ya ga dama ya Bada kudin Mai Tai zuba a motar ta.

Mai har na dari uku  zuba Baban Abul ya bayar ta zuba a mota.yarinyar da ta Saba yawo da full tank a cikin gata ga askafuna.

Yanzu kuwa ana Saka Mai na dari uku da dari biyar Yaya za'a kunna wata Ac?,da taci sa'a ake bata na Mai ma ai se ta gode wa Allah..

✨✨✨✨✨

Tana kwance a dakin ta tana ta Jin kwadayi a ranta..kwanaki dama da suka je gidan Hajiya ne fa suka hadu da yaya () wan  su Hashim shine ya ba wa Yara dubu hudu.

Duk suka bata suka ce basa so,hatta Nabila bata nata tayi.

Kawai se ta ce bari na fara gwada yin meat pie me suna chofe Wanda ake yin shi fale fale da naman shi kamar hanjin bera din nan me garas garas ..

Bata hi shawara da Baban Abul ba domin shi Kuma Wani Hali nashi ko dubu miliyan zata samu baya taba dora idon shi a Kai ,kunga dai in mutum yayi a fada.ko da ta gaya masa an bawa su Abul kowa dubu guda ba abunda ya shade shi.

Shidai nashi ne baze bayar ba.

A cikin unguwa aka siyo mata komai na bukata ta fara chofe,dake akwai Yara a anguwar rututu tunda akwai Yan gargajiya sosai a anguwar ,se ta bawa Sarauniya ta Kai islamiyya ta ajje a kofa.shi kenan ta fara cinikin chofe

Hashim na gani ya hau masifa da bala'i yace tana zubar Mai da kima a cikin unguwa ta wulakanta shi ace duk girman gidan nan da kudin shi da komai,Kuma se tayi Wani Sana'a?

Ba dan ranta yaso ba dole ta Daina ,dama shi baya so ana zuwa Mai gida bare wasu Yan unguwa .

Dan sau daya aka Kai islamiyya shikenan da an tambaya se suce a gidan su ne ,dama ta bayar an Kai islamiyya ne dan mutane su gani..toh Malam Hashim dai yayi Karan tsaye ya Hana .

Allah ya sawwake..

💞💞💞💞💞💞💞

Saudatu wato proff na daya daga cikin daliban da ake ji dasu a primary five saboda kwazon ta .

Wannan dalilin yasa sanda suka zo zana entrance examination aka Saka sunan ta a jerin sunayen mutum biyar na makarantar su da aka zaba zasu zana scholarship exams

Abul Akai wa wannan bayanin sukai ta murna ance musu Indai suka ci za'a dauki nauyin karatun su ..

Ko da suka zo gida da wannan bayanin ba karamin dadi Abida taji ba.

Da yake saura two weeks se suka dikufa yi mata lesson a gida bayan na makarantar su da ake musu.

Saturday ta kama ranar da za'ai exams din.exams din da ta hada Yara sa'oin su Saudatu da Wanda suka Fi su da shekara daya haka.

Yara ne daga makaranta mabanbanta wanda aka zabo su a cikin sauran dalibai Wanda suka kasance zakakuran ciki Wanda baza'ai asarar daukan nauyin su ba.

Abida ita ta Kai Saudatu gun exams din Wanda office ne na scholarship board .

Se da Baban Abul ya shaka musu bakin cikin shi kafin suka fito.dama Abida ta shiga watan haihuwar ta .

Da Allah ya taimake tana da karfin zuciya ,haka a amu ta Kai proff tayi jarabawar ta tana ta murna tana gaya wa Maman ta ko daya Bata fadi ba.

Murna suka dingi yi inda aka ce musu anan zasu zo su duba Sakamako sati biyu a gaba.

Da wannan suka dawo gida murna ma agun Yan uwan ba'a cewa komai da proff take gaya musu ko Daya bata fadi ba

Sati biyun da aka Basu suzo su duba result yayi dai dai da ranar da za'a yi wa Abida C's..

Hakan yadan daga mata hankali Amman tace babu komi Allah ze kawo yadda za'ai.

A dan tsakanin tana ta dan yawan tuna wa Baban Abul maganar C's ,Dan haka ba abun da yake se jaraba da masifa matukar aka ce yana gidan.

Gashi Yara sunyi hutun makaranta,se ya zamana kullum suna yi masa Dan abu kadan ze fara jaraba yana babatu .ko fa ba laifi bane in gaya muku se ya maida shi laifi ta hau fadace fadace.

Memakon hutun da akayi ya zama musu dadi se hutun duk yabi ya gundure su se Allah Allah suke a koma makaranta.

✨✨✨💞💞✨✨✨

Zaune take cikin kaguwa a layin asibitin  har kawo sanda layin ya zo kanta.

Mace ce har mace me jini jikin ta wadda take a team din da zasu wa Abida C's.ta Santa dama sosai tunda kusan duk haihuwa tana gamuwa da matar .

Dr Farida Abdullahi kenan.cikin fara'ah take cewa Abida" ba komai Abida,wata ranar se labari,ki Kara hakuri akan yadda kike yi kinji,batun C's Kuma na Kara Miki 3 days kamar yadda kika bukata.zanyi batun dasu doctor Mu'azzam Dan Kinga ya kama Tuesday team din su ke aiki.."

Abida ce tace "kar na katse ki Aunty Farida,Amman don Allah a mayar 4 days wallahi mafi son team dinki don Allah"

Dariya tayi ganin yadda Abidan ta marairaice saboda tafi son Farida ta mata aikin"

Cewa Dr tayi "wannan shi yafi komai sauki Abida,Allah ya Bada sa'a ,Amman kizo akan time kinsan Kuna da yawa ranar"

Cewa Abida tayi "Insha Allah zan zo da wuri Aunty Farida nagode nagode Allah ya Saka da alheri."

Sallama sukai da juna Abida ta tafi cikin farin ciki da Jin dadin turawa Hashim aniyar shi da tayi.

Kawai fa daga tace dan Allah ya daure ya je dubo result din proff shine yake ta zage zage ,wai shi an Raina shi an maida shi Dan aike ya dungi zabga rashin Albarka.

Murmushi tayi ta tafi gida ,dama ce Mai tayi ance tazo ranar shine fa ta samu ya bari da kyar ta fito.

Ranar da da zasu dubo result da safe ,da yake karfen nasara bayada tabbas.haka tazo tayi ta kokarin tashin motar Amman motar nan Taki tashi.

Ba sarki se Allah suka dauki kafa har titi suka samu Adaidaita sahu ,gashi Abida ta tsani wannan gwamutsen da ake a Adaidaita sahu maza da mata.

Cikin sa'a Wanda suka tare ba kowa ,ta gaya Mai inda zasu yace mata dari biyu.

A Adaidaitan Addu'a ta ruga yi Allah yasa kar ya samu Namiji.

Koda Allah ya duba zuciyar ta ya sa be ma samu passenger ba har ya sauke su.

Suna zuwa suka duba list dai Babu ma sunan Saudatu Hashim .ba Saudatu ba ko S din sunan ta Babu.

Da yake Abida ba duhun Kai a tattare da ita tunda A level 3 tayi deferring semester shine har yau Bata koma ba.

Da rashin duhun kan na ta ce su shiga office din suyi tambaya.

A office din sun tadda mutane kalilan kasancewar ranar Saturday ce

Gaishe su tayi sannan tace "Dan Allah na kawo yarinyana ne tayi entrance examination ne aka ce muzo mu duba result yau,sedai na duba naga kamar ba sunan ta ne "

Kallon su aka tsaya yi kamar wasu zombies har seda Abida ta kagu da kallon.dama a rayuwar ta Bata son kallon ko daga yayan ta ne in taga ana kallon ta se tace meye dalilin kallon.

Wani ne yayi karfin halin cewa "Toh ta fadi kenan tunda kika ga ba sunan ta a ciki ai hajiya"

Dan kallon shi tayi se tace "Kayi hakuri Baba,Amman a board din naga list din Wanda suka fadi ita Kuma Babu nata ne ma kwata kwata"

Wani ne a cikin su ya sake cewa "Toh abunda za'ayi ku dawo Wani satin ku sake duba wa ko akwai Wanda za'a sake kafewa "

Godiya ta musu ta fito daga office din .A hannunta tana Jin yadda jikin Saudatu yake rawa alamun kuka "

A jikin wata mota suka jingina sabida bacin rai se taji cikin na juya mata .tace zo Saudatu mu dan huta a jikin Motan nan banna Jin dadi.

Suna Tsaya wa se Saudatu tace "Sannu mama kinji"

Kallon ta Abida tayi se tace "Sannu Saudatu kema,Kuma kiyi hakuri Dan kin fadi exams ba Wani Abu bane,kin San kowa da rabon shi a duniya ,tunda kika ga kin fadi Baki da rabon wannan ne,muyi Addu'a se kiga Allah ya kawo Wani Alherin a gaba,share hawayen ki kinji diyar Arziki,insha Allah se kin zama professor kamar yadda kike so kinji?"

Daga Kai Saudatu tayi kwalla na zubo mata a fuskar ta ,cewa tayi "Ameen mama.Amman mama wallahi duk na amsa questions din nan,kin tuno ma rannan har nace Miki ba Wanda ban iya ba,Allah mama naci ban San meyasa na fadi ba"

Kallon ta Maman tayi,a ranta take raya ko Kila se an biya wasu kudi su Basu sani ba balle su yi fafutika su samu?

Girgiza Kai tayi kafin yanzu ta fara ciwon Kai saboda tunane tunanen da ba mafita gareta ba tunda lokaci ya kure,sannan tasan sun ce su dawo ne kawai Amman ba Wani maganar sake kafe Wani list din.

Ita ba ma abunda yake Bata mamaki se rashin ganin sunan Saudatu gab Daya,ce wa tayi "Saudatu toh ko dai kin manta garin saurin amsa questions din Baki rubuta naki sunan ba?"

Shiru Saudatu tayi alamun tuanani sannan tace "Allah mama na rubuta ,kinsan uncle Ola (Wani malami ne a makarantar su irin masu dukan Yaran nan akan gyara) in mutum ya fara rubutu ba sunan sa,ko date da topic bulala yake yi,ai ko Dan shi ma se da rubuta duka.

Dan shiru Abida tayi tana Jin yadda kafafun ta suke mata zugi.

Chan Kuma tace "Toh yanzu dai Saudatu Kinga bamu da yadda zamuyi,se mu fawwala Allah dukkan lamuran shi ze mana maganin duk abunda zamu iya da Wanda ma baza mu iya ba.zo mu tafi kinji"

Har sun fara tafiya se Wani mutum ya fito daga motar da suka jingina sakamon tint Babu San da mutum a ciki ba ya fito .

Kiran Abida yayi da cewa "Maman saudah zo man"

Kallon shi tayi a second guda ta fuskanci ba mutumin banza bane .

Dawo wa sukai ta gaishe shi Saudatu ma ta gaishe shi.

Kama hannun Saudatu yayi yace mata "Saudatu,kin tabbatar jarabawar nan da kikayi Baki fadi ba?"

Cikin sauri ta ke daga Kai tace "Wallah uncle Baba duk na iya amsa wa"

Cewa "Zo to muje "

Yan ruke da hannunta suka nufi office din suka tadda wayannan Mutanen dai ..

Wani ne yace "Alhaji afuwa yanzu nake kokarin kawo wa na kammala hada su "

Shima da yake result yazo amsa na yarinyar sa.

Se yace "toh ba laifi.sedai yanzu kan Saudatu nake magana , result dinta ne ba'a gani ba shine take kuka"

Suna Jin sunan Saudatu se aka hau kallon kallo.

A zuciyar su suke  cewa "Ashe ita ce mighty Saudatu da ta samu star amsar da ta iya cinye ko Wani amsa.dole ta sa aka hanata ma scholarship din gaba daya.

Wannan na dazun da ya yi magana shine yanzu ma ya sake cewa "yallabai wannan ai ta fadi ne gab Daya.."

Da sauri Saudatu tace "Wallahi Baba duk na amsa su ko Daya fa ban kasa ba,duk na iya harda Wanda Yaya Abul yayi ta koya mun "

Se mutumin yace toh sedai idan ki rubuta wata yanzu,in kinci shi kenan in fadi Kuma ba sauran kuka"

Cikin tsalle. Farin ciki tace zata yi..ba Bata lokaci suka Bata paper baya ga haka suka kora uwar ta waje,sannan suka zagaye ta .a kasa da minti 50 ta amsa questions guda dari irin waccan dai da tayi..

Me za suyi ba mamaki ba ,se ga shi suna ta yabon ta hadi da dogayen Addu'oi na fatan samun nasara a rayuwar ta .

Abida na waje bata San me ake ciki ba,sedai bakin ta be bar yiwa Saudatu Addu'a ba.ilai kuwa Addu'ar nan ta amsu,Dan Saudatu na ciki ba iya secondary ba hatta jami'a an dauki nauyin ta.

Farko dama abunda yasa suka Hana ta scholarship saboda sun San cewa satar amsa aka bata,Ashe yarinya ce kawai gifted gata yar ficila da ita da yake Bata da garin jiki.

Da gudu ta fita taje ta rungume maman ta tana cewa "Mama dama na gaya Miki ban fadi ba na cinye duka wallahi"

Cikin farin ciki suke Hamdala ga Rabbil Aalamina me kowa me komai ,a gefe kuwa Uncle Baba da ya tsaya musu se godiya suke Mai.

Abida harda hawaye se ta ganshi kamar ubanta mahaifi.

Tare suka juya Dan gata schools ne a jere sun Kai goma aka ce Saudatu ta zabi inda take so taje junior secondary school dinta.

Se Abida tace "Ah ah Uncle Baba ya zabar mata.."

Yana duba wa yace "Toh a Saka mata crescent ko"

Cikin Jin dadi da murna aka gama komai ,shi uncle Baba yace ze Bada gudunmawar shi.

Se yace wa Abida me kike so na taimaka Miki da shi? Ki dauke ni tamkar mahaifin ki,kin ganni dai tsoho ne Amma Amina (yarinyar da yazo amsar wa result) ita ce ya ta ta fari Kuma itama seda tsufana na same ta.

Dan haka karkiji kunya ta me zan taimaka Miki dashi,Kinga dai komai za'a mata kama dag kan books , uniform , school bag da komai so se ya zamana ban San dame zan taimaka ba"

Shiru Abida tayi tan jaddadda girman Uncle Baba a idanun ta.

Se tace "Da komai ma yayi"

Ya lura bazata iya fada ba.amman alamu sun nuna suna bukatar a tallafa musu .

Se yace toh idan zan Kai Amina siyayya se suje tare su siyi abunda suke so.hakn yayi?"

Dan shiru tayi tana tuno Dan iskan Uban na Saudatu.se tace Baban ta ne ba lallai ya yadda ba "

Yace in Kuma ke Zaki kaita fa? Se na Bada kudin?

Kallon shi tayi kadan ta kauda kai.se tace "Ah ah se muje din a Siya "

Murmushi yayi Yana cewa "Toh shekenan yayi,se Kuma nake so na dau nauyin transportation din ta? Haka ma yayi ?

Kallon shi take ..yayin da ni Kuma na gaji nace bari na tsaya a nan mu hadu a next page ....

TBC........

Continue Reading

You'll Also Like

264K 19.3K 23
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
170K 6.3K 80
Not many people understood 12 year old Jessica, as a person and an individual. That doesn't include, however, her older sister, who Jessica adores w...
928K 26.8K 43
Athena is trying to adjust in her newfound freedom but she is forcefully ripped away from it. But sometimes bad things happen for better!
583K 20.2K 167
The young lady from the Xue family was talented and beautiful, and married the dream husband at the age of 16. They had a loving and harmonious relat...