A SOYAYYAR MU

By hijjartAbdoul

4.1K 74 0

Be tashi ya ga mace a gidan su ba, rayuwar su gaba ɗayan babu mata idan kaga mace a gidan to auro ga akayi ha... More

Shimfiɗa.
1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50

19

54 0 0
By hijjartAbdoul

Koda ta koma gida babu abinda ta ci haka ta zauna tana tunani duk surutun da Jiddah take mata ba jinta take ba sai dai kawai tayi ɗan murmurshi alamar tana ji amma ba ji ba take, har dare ya tsala tana warwara tana ƙullawa ta rasa ya zatayi da wannan mutanen guda biyu, idan ta juya nan sai ta juya nan ganin ba yi mata zai yi ba yasa ta zuwa tayi alwala ta fara sallah raka'a biyu tayi, tayi addu'a sannan ta dawo ta kwanta, ko addu'a bata gama ba bacci ya ɗauke ta. Washegari kamar kullum suka shirya suka tafi amma yau Jiddah ta so rashin mutuncin ta wai ba zata je ba yau, sai da ta mata jan ido sannan ta fito suka tafi ita ce ta makarar da su amma da, da wuri zasu je, ta rasa wannan wani irin hali ne da Jiddah ta kwaso ita de ta san kwata-kwata batayi wannan abun ba, maybe shine yayi ko a ƴan uwan sa, ita ina taga ƴan uwan ma da zata yi musu wannan abun ko uwar da zatayiwa haka, komai da kaga mutum yana yi samun waje ne.

"Mammy dan Allah wannan satin   ki kaimu wajen wasa dan Allah".

Jiddah ta faɗa, yayin da Abie shima yace.

"Ehh! Mammy kullum sai Ameel ya bamu labali duk Fliday sai Abban su da Momyn su sun kai su".

"Waye Ameer?

"Kaiiii!

Jiddah ta faɗa irin mamakin nan na daban baki san shi ba.

Sultan yace, "Wani abokin Abie ne a Islamiyya yake basu labari".

"To zan duba na gani amma babu tabbas ɗin za muje".

"Dan Allah. Birthday fa zai yi".

Kallan Abie ɗin kawai take, shi da Abokai basu dame shi ba, amma shine yake maganar wani Ameer duk yadda akayi akwai alaƙa sosai a tsakanin su tunda har suka saba haka ya yarda yake bashi labari.

Abie yace, "Shine fa labalin da nace zan baki? Kuma kike ta tafiya aiki".

Ɗan murmurshi kawai tayi masa.

Yace, "Be jima da kawo shi ba, shine wani Pilifect ya dake shi, kuma daman ko? Kuka fa yake".

Suka saki dariya Shida Jiddah.

Jiddah tace, "Kuma kullum da kuka ake kawo shi, nice ma na faga gaggashin sa, tukunna ya ɗan yi shigu fagkon zuwan sa".

Haka sukayi ta bata labari har suka iso makarantar su, mai Napep ɗin kuwa jinjina kai yake yana mamakin wannan surutun na yara, ita kuma tana gane abun ta, dan shi ba kalmomin duka yake gane wa ba musanman na Jiddah da take mai da R, G sam bata da R ba kuma ranar da za tayi da alama. Itama sauke ta yayi a wurin nata aikin. Yau kam babu mutane da yawa ba kamar jiya ba, a hankali take takawa har ta iso build din su kallo ɗaya zaka mata ka gane bacci be ishe ta ba saboda yadda idan ta ya kumbura ga kuma kukan da ta sha jiya sai abun ya haɗe mata yayi mata yawa.

Jin tana jin yunwa yasa ta tana ajjewa jakar ta, ta fito domin zuwa cin abinci taga wannan sectary ɗin na jiya yana ta sauri ya nufi inda suka haɗu da wannan mutumin, da sauri itama ta bishi a baya ba tare da tana making sound ba, ganin zai juyo yasa ta ɓoyewa a bayan bishiya tare da sauya hanya ta nufa inda suka haɗu jiyan, aikuwa de shine, yana jiran sa yana zuwa taga ya miƙa masa flash ya juya ya tafi, shima fitowa yayi ya tafi, wanda aka bawa flash ɗin ta fara bi har taga sun zo building ɗin su  a kusan tare suka shiga da ita dan haka ta wuce shi, shi kuma yana gaisawa da mutane, tsaye tayi tana kallan sa kamar tana neman wani abu a office ɗin nata ta riƙe file tana ta duddubawa har ya zo ya wuce kafin ta bishi ganin inda ya shiga yasa ta dawowa ta zuba ta buɗe drawer ta ɗauko flash da yawa different colors ta zuba a jakarta  da file a hannun ta, ta nufi  corridorn su na individual office, nashi opposite ɗin na Faisal ne hakan yasa ta dai-dai ta kan ta, tare da aro wani murmurshin ta yafawa fuskar ta, ta yi knocking.

Izinin ya bada ta  shigo da sallama a bakin ta ya amsa, yana kallan ta tare da bata wurin zama, tana murmurshin sosai ta ƙara so ta gaida shi sannan ta miƙa masa file ɗin hannun ta, tana kallan flash ɗin da ya ajje shi kusa da shi ga kuma system a gaban sa da'alama sawa zai yi kuma ta shigo. 

"Sir! Ance na kawo maka kasa hannu".

"Waye ne yace ki kawo min?

"Rabi'u messenger ne".

"Ohh! Anyi haka jiya yace idan nasa hannun daman ke yake kawo wa ko?

Ɗaga tayi.

"Shine yace zaki kawo nasa hannu. Wallahi sam na manta yi hakuri zauna mana".

Ya faɗa yana ƙara nuna mata wurin zama, looking so innocent ta sami waje ta zauna, a ɗan ɗosane ma ta zauna irin ta nuna tana da tarbiyyar nan, tana kallan ƙasa shi kuma yana sa hannu yana satar kallan ta, yarda ta wani nuna tana da tarbiyya ba ƙaramin burge shi tayi ba. Abu ta fara nema a jakar ta, kamar tana neman wani abu, be san kuwa kakan flash din take nema ba, wanda zai yi dai-dai da wanda aka bashi, aikuwa ta samu, har kala da size sak iri ɗaya babu wani banbanci. Ta zaro ta riƙe gam a hannun ta, ganin kamar ya dena satar kallan yasa ta yasa hannu zata ture takardun dake kan desk ɗin su faɗi aka kira shi a waya, ganin mai kiran nasa yasa shi ɗauka yana barin wajen, batare da wani  jinkirtawa ba kuwa tayi wuf ta sake ta sauya wanda ko sallamae da yake yi a waya be gama bere ya juyo yana kallon ta hakan ta faru, aikuwa yana amsawa ya juyo yana kallan ta, sai wasa take da hannun ta.  Yana gamawa ya zo ya ƙara sa sa mata hannun ya bata, harda ɗan durƙusawa ta amsa tana godiya sannan ta fita, ya jinjinawa kamalar ta tarbiyyarta ko ƴar waye ta fito daga gidan mutunci haka ma mijin ta yayi dace da ya same ta a matsayin mata.

Tana fita ta sauke wata irin ajiyar zuciya kafin tayi sauri ta maida komai a wurin sa, sannan ta hau system tayi copy guda uku, ita bata ga komai ma da aka tattauna ɗin ba, kodan ita ba ganewa na zatayi ai, har ake wani neman sa da muhimmanci, taɓe baki tayi kafin tayi masu shaidar da ita kaɗai zata gane sannan ta watsa biyu a jakarta ɗayan kuma tayi masa kyakkyawan tanadi a office, yayin da ta fara tunanin yarda za'ayi ta maida masa ɗayan batare da ansani ba.

~~~~

Jiddah ta shigo cikin companyn tana wani irin ware ido ganin wuri mai kyau, sai kalle-kalle take abun ta, batare da yi la'akari da ina take jefa ƙafar ta ba, sai ji tayi karo da mutum ta ɗago kai mana taga basamuden mutum na kallan ta, ai tuni idan ta ya ciko da ruwa tana ƙara ware ido tana kallan shi, kafin ta kai kallan da sauran sojojin da suke kallan ta, ƙara damƙe jakar ta tayi idan ta nayi ƙwale-ƙwale. Ɗaya daga cikin sojojin ne, yace.

"Ke! Me kike anan?

Jin wani irin mashahurin fitsari tayi ya zo mata, tuni ta fara matse ƙafa, tsawar da suka daka mata ne yaja hankalin Sajjad ya juyo yana kallan yarinyar da ta kafe Sojan da yayi mata magana da ido tana kallan shi, wayar da yake yi ya kashe tare da dawowa kusa da ita, ya durƙuwa a gaban ta, haɗa idan da sukayi yasa shi wani irin lumshe ido da be shirya ba, ta ƙure da kallo tana kallan sa haka kawai taji kamar ta san shi.

"Me kike yi anan?

"Fitsagi nake ji".

Ta faɗa hawaye na zubo mata, hannun ta ya kama, ganin kamar basa sauri yasa shi ɗaukan ta ya riƙe, yayin da ita kuma ta saƙolo da hannunta tana cigaba da kallan sa shima ita yake kallo yana kallan hanya, har suka hau Elevator zuwa hawan ƙarshe ya shiga office ɗin da aka gyara masa, ya kai ta toilet ya ajje. Shi kuma ya fito ya zauna a kujera, shiru shiru bata fito ba, shi kuma be shiga ya duba ba, sai ji yayi tana cewa.

"Na gama".

Da irin ƙarfin nan, to be rufe ƙofar ba, hakan yasa shi jin abinda ta faɗa, ko ya rufe ma wannan ihun da tayi yasan ai zai ji, da mamaki ya tashi yana mamakin to me tayi? Karde kashi tayi? Yana shiga kuwa ya tarar kashin tayi, girgiza kan sa yayi za wanke mata.

Tace, "Mammy sai ta faga wanke hannun ta take wanke min".

Kallan yarinyar yayi sosai yana so yaga no wani abu daga jikin ta amma ya rasa ganewar, wanke hannun nasa yayi kamar yadda ta buƙata sannan ya wanke mata yayi flushing.

"Nima wanke min hannu".

Ta faɗa tana haɗa hannun ta biyu, hand wash yasa ya wanke mata har yanzu mamakin yarinyar be barshi ba. Jakar ta da hijabi ta ɗauka a tare suka fito da shi, akan carpet suka zauna daga shi har ita ganin ta zauna shima yasa shi ya zauna.

"Anan wurin ake sai da ɗan yago?

"Yago kuma?

"Ehh mana ɗan yago".

"Ni bangane ba".

"Yago fa".

Ta faɗa kamar zata sa masa kuka, shi kuwa harga Allah ba ganewa yayi ba.

Yace, "wai me kike nufi?

"Ɗan baby fa".

"Wanne irin baby kike so?

Ya faɗa yana buɗe wayar sa, domin yayi searching.

"Mai kyau".

"Zaɓi wand kike so".

Ya faɗa yana matsowa kusa da ita sosai, kan sa ta hau tana karɓan wayar kafin ta miƙa masa tana kwaɓe fuska.

"Ba wannan bafa".

"To igin wanne?

Yanzu kuwa ya fahimci R ce bata da shi, tunda ya gane me take nufi, ɗazu ma da tace Fitsari be san ya akayi ya gane ba.

"Irin wanne?

"Kamag ni fa. Irin tana macen nan, idan ta gigma ta dawo kamag ni zan yi mata kitso".

"Wai jaririya kike so?

Ɗaga masa kai tayi, ɗaga kai ya fara yi yana kallan ta.

Yace, "Ina Mamanki?

"Tana wajen aiki".

"Ke kuma kika gudo daga makaranta ko?

"Ai ba gudowa nayi ba".

"Me kika yi?

"Ai de ƴag jagigiya zan siyowa Mammy".

"Mammy naki ta sani ne?

"A'a".

"To meyasa...."

"Kaga lokacin da akayi haihuwa a gidan da muke ne fa, sai muka je a bamu ɗan yagon shine sai aka hana mu nida Abie aka ce baza'a bamu ba. Hag dukan mu akayi, shine na cewa Mammy ta siyo mana, kuma daman Ummi itama ta siyo nata, shine muka ce Mammy muma siyo mana tace wai, wai sai ta taga kuɗi dayawa zata siyo mana".

"Kuma har yau bata taga kuɗin ba".

"Kiyi haƙugi sai ta taga kuɗin".

Ya faɗa yana ɗan sakin murmurshi, turo baki tayi gaba zata tashi daga kan shi yayi saurin taro ta yana bata hakuri tare da ƙunshi dariyan dake cin sa. Kallan sa tayi tana wani irin waro ido tare da taɓa dimple ɗin sa.

Tace, "Igin na Abie".

Faɗaɗa murmurshin sa yayi shima yana taɓa nata.

"Daman manya suna da shi?

"Gashi kin gani kuwa?

Ɗan murmurshi tayi tare da tashi ta ɗauko jakar ta, ta buɗe ta ciro bounty mai ɗaya ta bashi ita kuma ta ɗauki milky.

Tace, "buɗe min".

Karɓa yayi ya buɗe mata, ta ciro gwangwanin madara.

Tace, "anan nake zuba duk wani kuɗi na da Mammy ta bani ko ƙawayen ta, ko Ummi ko Abban Sultan".

"Shine na siyan jaririn?

Tana shan milkyn ta, ɗaga masa kai.

"Ehh man".

Tace, "Nida Abie muke tarawa".

"Abie kuma?

"Ehh!

Shi ya zaci Abie Baban ta. Hakan yasa shi ƙara tambayar ta, suna zaune tana ta zuba masa labari har ya fahimci Abie ɗin ɗan uwan ta ne, ba Baba, a labarin nata kuma sai dai tace Abban Sultan yayi musu abu kaza da kaza.

Yace, "Ina naku Abban ke da Anje?

"Muma bamu sani ba".

Ta faɗa tana yin kalar tausayi.

Tace, "Amma Mammy tace yana nan kuma yana da kigki sosai da sosai ya fi ta kigki".

Tausayi yaran suka bashi duk da bega Abie amma yasa shima yana kewar Mahaifin nasa.

Yace, "Daga yau na zama Abban ku keda Abie".

Wani irin waro ido tayi sosai har bata san ta ɗale shi ba tsabar murna ta wani irin rungume shi sosai, shima rungume yayi yana jin wani irin farin ciki na musamman yana taso masa, sosai yake jin wani irin na daban da be taɓa ji ba. Kan yake shafawa cike da kulawa.

"Ba'a miki kitso?

Ɗagowa tayi amma bata tashi daga jikin sa ba, yarda zata ke ganin shi.

"Ana min mana ka iya ne?

"Kina so nayi miki?

"Ai ba kifiya".

"Zan siyo kifiya sai na yi miki ko?

"Kifiya nace".

"To naji kibiya".

Ɗaga masa kai tayi, suna ahaka Abdulmaji da Mustapha suka shigo, da mamaki suke ganin sa, ganin yarinya a baje a jikin sa, ga kuma school bag ɗin ta da hijabi suma a baje.

"Ina ka sami yarinya".

Yana murmurshi sosai.

Yace, "Nima tsintar ta nayi".

"Sai ka mayar ta makarantar su kada a tashi azo ake neman ta"!

Mustapha ya faɗa.

"In Sha Allah".

Abdulmajid yace, "Zo ya sunan ki".

Kirmisisi taƙi zuwa ya kaɗa ya raya amma ina a banza, haka ma Mustapha shima Sajjad yayi yayi taje ƙi kawai da ido take bin su, har suka haƙura suka ƙyale ta, sukayi maganar da ta kawo su akan ɓatan flash suka fita.

"Meyasa ki ka ƙi zuwa wurin su".

"Nima bansani ba".

"Baki sani ba?

"Ehh man".

"To ai haka muke nida Abie idan Mammy ta je wani wajen da mu, sai mu ƙi muyi magana ko kuma mu cukume muyi shiru".

"Meyasa ku ke yin haka?

"To ai muma bamu sani ba".

"To ni meyasa kika yarda da ni?

"Kawai gani nayi kamar na san ka. Irin na taɓa ganin ka, kamar de da na san ka".

Murmurshi sosai yayi.

Yace, "Nima haka naji dana gan ki ai".

"Yunwa nake ji".

Waya ya ɗauka ya kira Abdulmajid akan a kawo masa cookies da cake da lemo, ba'a fi minti ashirin ba aka kawo masa, yana gani ta raba dai-dai da dai-dai a uku. Ta ɗau ɗaya ta zuba kashi biyun a jaka.

"Wa zaki kai wa?

"Na Abie da kuma na Sultan".

Jinjina wannan ƙaunar ta su yayi, yana kuma mamakin ta.

"Ita kuma Mammy fa?

"So kake ta duke ni?

"Meyasa zata duke ki?

"Saboda na kagba abin ka mana".

Be ƙara magana ba yana kallan ta tana ci, tana gamawa ta dawo jikin sa ta lafe abinta.....

Continue Reading

You'll Also Like

KASHI By stuckinatale

General Fiction

376K 18.9K 42
"So, Mrs. Kashi Abhay Pratap Singh..chalte hai. Goodbye..". Saying this, he left her broken in this world of betrayal. ~~~~~~~~~~ Kashi, a simple gir...
234K 6.4K 33
What if Harry feels out of place after the war? What if he gets a visit from Death and Death takes him away from the wizarding world. Because by all...
1.7K 209 8
Ana kiranta Jidda Sufi, ƴar auta ga Governor Sufi Adam. Duk da jindadi haɗe da tsaron da suke dashi a matsayinsu na iyalan Governor bai hana wani mum...
9.8K 452 9
Labarin sarqaqiyar rayuwa...💫💕Na NAFI ANKA DA MISS XOXO (2016)