A SOYAYYAR MU

Galing kay hijjartAbdoul

4.1K 74 0

Be tashi ya ga mace a gidan su ba, rayuwar su gaba ɗayan babu mata idan kaga mace a gidan to auro ga akayi ha... Higit pa

Shimfiɗa.
1
2
3
4
5
6
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50

7

82 4 0
Galing kay hijjartAbdoul

Ganin ta tashi tsaye yasa shima Sajjad tashi yana kallan ta sannan ya kalli mutumim, ganin ya fara matsowa inda suke yasa ta ɓoya a bayan sa.

"lafiya?

Sajjad ya tambaya dan ganin yadda ta ɓoya sai tabbatar da cewa tsoron sa take.

"Ni kake lafiya? Ka taɓa min matar da zan aura gobe kuma sannan kake cewa lafiya?

'aure?

Ya maimaita a zuciyar sa, lokaci guda kuma abin ya faɗo masa sanda Muftahu na faɗa masa, rumtse idan sa yayi ƙarfi, lokaci guda kuma zuciyar sa na karyewa yana jin wani irin zazzaɓi a jikin sa da taɓa ji ba, kafin kuma ya buɗe idan a hankali, jin wasu irin kalamai da mutumin yake jifan sa da su, a halin da yake ciki ba zai iya buɗe baki ba bare kuma yayi faɗa daman kuma shi can ba mutum ne me faɗa ba shidai a barshi da taƙalar ƴan uwan sa da kuma abokin sa Mahmud shima dan yasan halin sa ne.

Sa kai yayi zai tafi, ya riƙe bayan rigar sa gam, hakan yasa shi kasa tafiyar.

"Daman ba yau na saba ganin ku da tare ba saboda shi nace a dena barin ki kina fitowa amma dake bakya jin magana shine kika fito ko?

Hausar kawai zai baka tabbacin bahaushe ne ko kuma de ya iya Hausa sosai domin baza'a taɓa kiran sa da yare ba.

"Wuce mu tafi gida".

Ya daka mata tsawa, maimakon ta sake shi, sai ta ƙara ƙanƙame shi sosai. Kallan ta Sajjad yayi yaga ta dena hawayen hasalima idan ta a rufe yake, jikin ta kuma ya dena karkarwa da ya ɗauka, a hankali ya juyo bayan ya cire hannun ta ta baya yana kallon ta har zai kai hannu ya taɓa ta sai kuma ya maida hannun sa ya ajje yana kallon ta, duk kallan da yake mata sai yau ne ya ƙare mata kallo, gashin dake lulluɓe da goshin ta shine zai tabbatar maka da cewan tana sa suma ga kuma gashin girar ta mai kyau gwanin ban sha'awa dashi bakin ta shape ɗin love ne da shi motse shin da tayi ne yasa shape ɗin fitowa sosai hancin ta ma ɗan sirit da shi mai kyau, babu abinda ya burge shi a fuskar ta irin girar ta, haka nan yaji yana so ya shafa amma yasan babu hali babu kuma dama babu ma rana, idan har ya sake ganin ta ma kenan.

Ya buɗe baki kenan da niyyar yin magana yaji an buga masa wani abu a kai ƙara ya saki tare da dafe kansa ya tsugunna a ƙasa yayin da ita kuma ta ƙwalla ƙara da ƙarfi ganin sun zagaye shi zasu dake shi yasa ta rugawa da gudu domin kiran wani a gidan su dawowar sa kenan daga tafiya yagan ta a firgice.

"Lafiyan ki kuwa?

"Ga...ga..ga..ga ..".

Ta kasa faɗa, sai nuna bayan ta take tana haki.

"Waye?

Ya faɗa yana kamota wai ko zata nutsu sai ƙacewa tayi.

Babar Garko ne ya fito dan yana sama yana kallon ta ta ɗakin sa, shine ya fito.

Yace, "Muftahu kuje da ita mana tunda ta kasa magana".

Ai kuwa bata jira cewar sa ba ta kama hannun sa, tana jan sa  kafin suje sun yi masa duka laga laga duk da basu bar shi a haka ba wani daga cikin su ne ya ɗaga gorar hannun sa zai maka masa a ciki Allah ya kawo su Muftahu ya ture shi ko sauraran sa be yi ba ya kama shi ya ɗaga shi. Banda kuka abin da Nilah take ita ce ta ɗauko masa wayar sa da ta faɗi ana daukan sa da takalmin sa suka tafi, duk inda suka wuce kallan su ake kasancewa magriba tana daf da yi mutane wasu na dawowa wasu kuma na fitowa hakan yasa ake kallan su, har suka zo gida.

Baba Garko na ƙofar gida yana safa da Marwa yana tunanin mene zai biyo baya kuma mene yake faruwa, duk abinda zai firgita ta yasan abu ne ba ƙarami ba. Yana haka sai ga su kuwa da saurin sa ya biyo shi.

"Subhanallahi waye, su waye suka masa wannan abu? Me ya faru?

Muftahu dake kame dashi yana tafiya.

Yace, "Baffa Likitan nan ne fa".

"Innalillahi".

Ya iya faɗa kawai ya tsaya yana kallon su suka wuce da shi, suma matan gidan duk tashi tsaye sukayi ganin an shigo da wani da basu san shi ba jina-jina da shi. Be iya tattakawa da shi ba benin ɗakin da zai kai shi yana sama hakan yasa shi kai shi ɗakin sa ya kwantar sai a lokacin Bana Garko ya iya shigowa ganin an cika ɗakin hakan yasa shi cewa kowa ya fita.

Ruwan ɗumi da kanta hanky ɗin ta ga ɗauko mai kyau aka goge masa jinin da shi aka gasa masa inda ya kumbura a fuskar sa da hannun sa, duk abinda suke besan ana yi ba dan kuwa ya jima da suma. Sai da Muftahu ya fita Masallaci yaga Mahmud yake sanar da shi abinda ya faru amma basu san abinda ya haɗa su ba, sosai hankalin sa ya tashi jin cewan wai anyiwa Sajjad duka be ƙara tada hankalin sa ba sai da ya gan shi. Sai da Baba Garko ya ɗan bashi baki sannan ya ɗan nutsu.

~~~~~~~

Yau ne ranar da za'a shiga koto, kowa yana fatan shine zai yi nasara duk wani hujja Ƙarami ya tana da wanda ya kamata ace ya yi sai dai duk abinda yake ba sanar da kowa komai ba har yau da aka zo za'a gabatar da shari'ar kuwa. Kafin a fara sai da koto ta dakatar da shi daga aiki sannan kuma aka ƙwace license nasa, sannan aka fara gabatar da shari'ar sai dai tun ba'aje ko ina ba aka fara daƙusar da  Ƙarami ganin amma da yake yana da hujjoji sai ya fara fitowa da su, ganin haka yasa lawyern gwamnati ƙara fito da wani abun wannan yasa aka ce sai an ɗaga Shari'ar nan zuwa kwanaki uku bayan an bada belin Daada.

Yana zaune a office ɗin sa yana duba wani case aka shigo batare da anyi sallama ba bare kuma a ƙwanƙwasa. Ɗago da kan sa kawai yayi yana kallon sa har ya ƙara so ya zauna ne ɗauke idan sa a kan sa ba.

"Ka koma gida ka zauna kayi kallo da iyalan ka. Ɗaya kenan.

"Ko kuma ka zauna ka zama ɗan kallo. Biyu".

"Ko kuma de zakayi nesa da wannan garin ne ka tafi can inda babu wanda zaka kare. Uku kenan".

"A cikin ukun nan to dole zakayi ɗaya".

"Wai ma shin? Nawa ya baka ? Da kake ta faman ƙoƙarin kare shi? Za'a baka Billions kawai saboda ka cire hannun ka a wanna shari'ar".

"Wanne ka zaɓa?

Tunda ya fara kafe shi da ido be ɗauke ba, yana kuma yin rubutun a lokaci guda, sai da ya bashi damar yin magana sannan ya ɗago papern ya karanto masa tas abinda ya ce ko harafi ɗaya be tsallake ba, sai da ya kai ƙarshe ya sauke papern tare da yin wani munafiki murmurshi na gefen baki.

"Idan kuka sa nayi ɗaya daga cikin wannan abun to tabbas kune kuka ga alamun nasara a tattare dani".

Murmurshin ya ƙara yi.

Yace, "Tunda na fara shari'a ban taɓa samun faɗuwa ba kullum nasara nake".

"Koda na faɗi nasan nasara ce ta ƙara yawa ba kowa ba".

"Kai har ka isa..."

"Shiiiii".

Ya ɗaura masa hannu a kan bakin sa alamar yayi shiru, shirun kuwa.

"Tunda ka fara ban katse ka ba, nima kuma bance ka katse ni ba. Ga hanya zaka iya tafiya na gama da kai".

A fusace ya tashi kamar ya tashi sama kafin yayi murmurshi tare da girgiza kai alamar Allah ya kyauta. Lawyern da suka gama Shari'a ne da shi shine ya biyo shi ba wato ya ci kuɗi, da'alama kuma kuɗi bana wasa ba tunda har yake masa maganar Billion. Shima da gaggawa ya tashi ya wuce gida, yana zuwa direct wurin Daada ya wuce dukan su suna zaune shida Abba da Baba a parlourn sa ya same shi ya gaida shi.

"Daada ina so dan Allah ka yi magana, kayi magana ko na samu wasu evidences ɗin".

"Ina ka samu waɗan nan da kayi amfani da su?

"Daada bincike nayi".

"Ƙarya kake Ƙarami".

Ɗago da kan sa yayi ya kalle shi jin ya ƙarya tashi lokaci guda.

"Daada na same su ne da kai na".

"Waya baka clue?

"Aliyu".

"Waya bashi?

"Sajjad".

Daman yasan amsar kenan, amma domin ya kuma tabbatar yasa shi tambayar sa.

'Sajjaaad'.

Ya faɗa ba zuciyar sa.

Abba yace, "Sajjad ya san wani abu ne?

Ƙarami yace, "A'a be san cewan an kama Daada ba amma yana suspecting wasu daga cikin mutanen da suke aiki a asibitin Daada, Daada kuma ya ƙi yayi magana".

"Nayi magana nace me?

"Bana so kuke shiga irin wannan sabgar sai me? Ƙarshen ta a kaine prison na gama rayuwa ta a can shikenan fa? Meyer rayuwar idan babu bakin ciki? Meye rayuwar idan babu hassada?

"Amma Daada ya kamata ace kasan zuwa yanzu abinda ya dace da wanda be dace ba, akawo adalci asa a inda babu amma taya za'ayi a fara adalcin kayi shiru? Ehh Daada?

Yana dire maganar sa shima Daada na dire hannun sa kan fuskarsa.

"Wannan ya zaman karo na ƙarshe da zan ke faɗa kana faɗa har kana ɗaga min murya, kaine zaka yanke ko ni?

Be iya cewa komai ba, domin zuciyar sa ya kai ƙarshe zai iya yin komai muddin ya cigaba da zama, ya fi Daada zuciya amma shi kafin yayi za'a jima idan kuma yayi to babu kan ta.

Abba yace, "Abinda kayi ka kyauta, kayi dai-dai".

"Kai ko tunanin mu baka yi? Baka tunanin halin da zamu shiga? Idan baka tuna mu ba da muke ƴan uwan ka ka tuna matar ka, ka kuma tuna ɗan ka da har yanzu ake ɓoye masa wannan al'amarin".

"Kan ka kawai ka sani? Ko dan farin cikin mu ai ka fito ka fadi komai ko?

"Yaya wallahi baza ku gane ba, Mutanen haɗari ne da su fiye da yadda baka zato, sune fa suka tura Sajjad wancan garin? Imagine, Ina san ɗa na Yaya duk san da nake masa baka fini san shi ba, idan wani ya same shi wanne hali zaka shiga?  Wanne hali  Yaya Kabir zai shiga? Wanne hali ne Aliyu ne zai shiga? Haka ma Mahaifiyar sa?

"Da'ace iya ni abin ya shafa babu abinda zan yi, amma Yaya ku nake gudu idan wani abu ya faru da shi, kaine zaka fara shiga damuwa".

Ya faɗa ƙarashe cikin kuka hawaye na zubo masa, Baba daman a koto sai da yayi kuka yanzu ma shine ya fara yin kukan, kawai tashi yayi fice daga ɗakin domin shima Allah ne kaɗai yasan irin son da yake yiwa yaron, amma duk da haka sai da aka san yana sa shi? Yana nunawa ne yana san nasa?

Abba kam be iya yin komai ba banda shiru da yayi jikin sa yayi mugun yin sanyi da aka ambaci Sajjad dole ne Daada yayi shiru, domin Sajjad shine soyayyar su shine farin cikin su, amma shi yaron kan sa be sani ba.

"Allah sarki".

Ya furta a zuciyarsa.


******

A hankali ya fara buɗe idan sa da yaji sun yi masa wani irin nauyi da kuma kan sa dake sara masa sai da ya buɗe idan tarwar sannan ya shiga ƙarewa ɗakin kallo, daga kan rufin da yake ɗakin ya fara dake shine yake facing, fanka ya ga tana juyawa kafin ya maida kallan da ga gefen sa inda aka sa inverter ga kuma switch ɗin bulb nan a jiki, sai wata wardrobe babu wani tarkace a ɗakin sai gadan da yake kai, hannun sa ya bi da kallo jin zai tashi allura ta soke shi, abinda kuma ya bashi mamaki ɗakin ƙasa yake gani fa. Koma yayi ya kwanta ya rufe idan sa, sai kuma abinda ya faru ya dawo masa har aka zo aka ɗauke shi, hakan yasa shi ƙara buɗe idan sa, sai yanzu ya hango ta a zaune daga can wurin bakin ƙofa a bayar ɗazun ce a jikin ta tayi wani iri da ita.

Tashi yayi zaune daƙyar yana zare drip ɗin hannun sa, ganin haka yasa ta tashi zata fita.

"Zo".

Ya faɗa yadda zata iya ji domin baya da ƙafi ko na sisin kobo dama ya iya ɗaga muryan ya kira ta. Dawowa tayi ta tsaya a kusa da shi.

"Ka tashi?

Ta iya fada tana kallon sa, jinjina mata kai yayi.

"Waya kawo ni nan?

"Bakayi sallah ba".

Zai ƙara magana Baba Garko ya shigo.

"Masha Allah, ka tashi?

Jinjina masa kai kawai yayi yana ƙaƙaro murmurshin dole.

"Ya kamata ka tashi kayi wanka sai ka ji ƙarfin jikin ka ka ci abinci sannan kayi sallah".

Be jira cewar sa ya Umarce ta da ta kira Muftahu amma sa wani yare da be gane ba fita sai ga Muftahu shida Mahmud. Ruwan wanka ya aka kai masa bayi da kujerar zama, besan haka ruwan yake ba sai da ya taɓa yaji wani irin zafi na bala'i gaye kuma a ruwan sai kace mai wankan jego gashi babu wani ruwan. Haka ya saɓa sabulu yayi wanka da tafasasshen ruwan nan babu yadda ya iya sai dai ba ƙaramin daɗi ya ji ba, yana fitowa alwala yayi itama da ruwan zafi yayi kayan sa ya gani da'alama Mahmud ne ya kawo masa yasa sannan ya yi sallah yana idarwa Baba Garko ya kawo masa abinci cikin wata irin silba mai kyau da ita, ya kawo masa shayi da kunu shayi da kuma sirace, siracen ya fara yi ya bashi shayin ya sha ganin ya fara gumi yasa Baba ɗaukan mafici ya fara masa filfita duk da akwai fanka sai da ya  nutsu ya fara ɗan jin sanyi sannan Baba Garko ya miƙa masa abinci. Da kama zai yi musu amma ganin irin kallan da yake aika masa yasa shi sa hannu ya fara cin sakwara da miyar da be sani ba amma test ɗin ya masa daɗi ya ƙoshi amma ganin irin kallan da Baba Garko ya ke masa yasa shi cinye ɗaya daƙyar a hankali ya ajje kwanon yana kallan Baba Garko, be yi masa magana ba ganin ya ci dayawa ya miƙa masa kunu kaɗan ya sha yaji zai yi amai saboda ya ƙoshi magani ya miƙa masa da ruwa ya sha.

"Ina ke maka ciwo?

"Kaina".

Ya faɗa a hankali.

"Shi kadai?

Girgiza masa kai yayi yana nuna masa ƙafar sa wurin gwiwar sa sa kuma hannun sa da ya kumbura. Jinjina kai kawai Baba Garko yayi ya tashi ya fita, shi kuma a yanzu bacci kawai yake da bukatar samu, hakan yasa shi hawa gado ya kwanta duk da ya san yanzu ya ci abinci amma baccin dake idan sa ya fi ƙarfin sa.

Da asuba daƙyar ya tashi yayi sallah ya koma,saboda wani irin ciwon jiki da ya tashi da shi, yayi niyyan yin bacci dayawa amma fara baccin sa babu wuya ya fara jiyo hayaniya duk da baya da agogo ya san safiya ce to me zai tashe su da wannan sassafen? Yayi wa kan sa tambayar.

A wurin Baba Garko kuwa tun jiya yake sarrafa abinda   Mudassir ya faɗa masa da kuma wanda Nilah ta faɗa masa yasan ta bazata taɓa masa karya ba amma kuma ya san halin shi Mudassir ɗin ne? Jiya da daddare kasa bacci yayi yana juya naganar su har yau be samu mafita ba. Jin ana bubbuga masa ƙofa yasa shi zama yana cewa a shigo, Muftahu ne ya shigo tare da sallama.

"Baffa da Mudassir ɗin za'a ɗaura mata auren?

"Nima shine bansani ba".

"Baffa me zai hana tunda yana zargin Likitan nan da ita kawai a ɗaura mata shi".

"Kasan idan haka ne dole sai an yi musu wasa duk wanda ya cinye shine wanda za'a aura mata".

"To me zai hana ayi?

"Muftahu amma baka da hankali ko?

"Baffa zargi fa? Baffa nifa daman can wannan mutumin be min ba, be min ba Baffa".

"Kuma wanda bamu sani ba?

"Baffa shekara guda zai yi anan, a wannan shekarar ni zan yi yadda nayi na nemi inda yake zama yace min a Kaduna suke kuma su ƴan Bauchi kana da ƴan uwa a Bauchi asalin su ne can ɗin Baffa".

Shiru yayi yana nazarin kalaman Muftahu, yayin da shi kuma ya cigaba da faɗa masa halayen Mudassir wanda daman can tun sanda ya zo a matsayin shine wanda zata aura yaji be masa ba be kwanta masa ba, kawai de yaƙe yayi sai a jiyan yaje shi amsar wayar Sajjad a wurin ta yaji zancen su da Sadiya tana kuma cewa shi take so hakan yasa shi yanzu zagewa yana nemar Sajjad wurin zama. Ganin maganar sa tayi tasiri a zuciyar Baffan sa yasa shi ficewa.

Sajjad kuwa kasa baccin yayi dan daga ya fara sai yaji an fara surutu sai ya tashe shi, a bankuna sauko da ƙafar sa da niyyan ya fita yaji an turo ƙofa an shigo ko be kalla wanda ya shigo ba yasan Baba Garko ne.

"Ina kwana".

Ya faɗa yana ɗan rinsinawa, Murmurshi ya ɗan yi masa.

"Ya ƙarfin jikin?

"Alhamdulillah".

Ajiyar zuciya ya sauƙe, kafin yace.

"Har yanzu kan yana ciwo?

"Ya dena, jikina ne kawai yake ciwo".

"Shima in Sha Allah zai dena".

"Abu ne yake tafe dani bansani ba ko zakayi ko baza kayi ba".

"Meye shi?

"Jiya wanda ya sa akayi maka dukan nan ba kowa bane sai Mudassir wanda Hauwa'u zata aura".

"Hauwa'u?

"Nilah".

Ya bashi amsa da sunan da yake ganin ya santa.

"Bansan yaushe ne ka fara mutunci da ita ba".

Sajjad yace, "jiya ne kawai mukayi doguwar magana da ita".

Daga nan ya kwashe yadda sukayi da ita tun daga farko har jiyan da suka haɗu da kuma dukan da akayi masa. Jinjina kai Baba Garko yayi.

Yace, "Yanzu idan nace ka aure ta zaka aure ta?

Maganar ta zo masa a bazata, hakan yasa zuciyar sa bugawa da sauri haka ya zaro ido cikin razanar abinda be taɓa ji ba ko ya kawo.

Jinjina masa kai Baba Garko ya kuma yayi cike da tabbatarwa.

"Amma kafin nan sai kunyi wasa da wanda zata aura ɗin da kuma kai".

"Taya kenan?

"Zaka iya indai ka sa abun a ran ka zaka aure ɗin, kodan ya wanke zargin da yake muku da kai da ita sai ka tabbatar masa da zargin sa ba haka bane".

"Ya ilahi!

Ya furta.

"Ka dena hango ciwon dake jikin ka".

Ka fito kayi wanka.

Daga haka ya fice ya bar shi, da ido kawai ya bishi yana kallon sa, meke faruwa da shine? Ko kuma shine abinda zai faru da shi daman yake jikin sa wani irin a cikin satin nan ? Duk a tunanin sa wani abu ne ya faru da ƴan gidan su ashe a kan sa abin zai faru.

"Ka fito kayi wanka".

Muftahu ya sanar da shi, a hankali ya tashi ya fita duk da ya ɗan ji sauƙi sosai ba kamar jiya ba, yau ma da ruwan zafin yayi wanka da kuma wannan gayen a ciki yana fitowa yaga wasu kaya akan gado, yasa haka ƴar shara ce da wando wandon be kai kasa ba sannan ya wuce gwiwa kuma buje da ne kayan ba ƙaramin kyau suka masa ya sa ya zauna kenan a kan gado Muftahu ya zo da wasu abubuwa a hannun sa.

"Wacce ƙafar ke maka ciwo?

Nuna masa yayi, yana gani yasa abubuwan nan ya ɗaure masa hannun ma haka wanda ya kumbura, kan sa ma inda ya aka buge shi ya kumbura shima ya daure masa.

"Yau naga ta kaina irin wannan ɗauri haka?

Sajjad ya faɗa yana jin sa a wani irin ɗaure. Murmurshi yayi masa yace.

"Yanzu zaka iya tsare dani ma".

"Ina ni ina tsare da mai lafiya".

Ya faɗa ya ɗaga ƙafar sa, kamo shi yayi suka fito, suna fitowa Mahmud na zuwa.

"Hey! Ya jikin?

"Alhamdulillah da sauƙi".

"Sai yanzu zaka zo bana so".

Ya faɗa yana kumbura fuska, dariya Muftahu yayi.

Yace, "Da shi akayi jinyar ka jiya fa".

"Da ka yi shiru baka san halin wannan mutumin ba".

Banza yayi masa suka ci gaba da tafiya yaga sun fito gida sun nufi hanyar Mai gari.

"Wai ina zamu je?

"Kai de biyo ni".

Be kara magana ba dan shi kam Allah ya gani ya gaji, har ya suka ƙara so inda aka tara dan dazon mutane dayawa ana ganin su aka basu hanya suka shiga, Muftahu yaje ya tsayar da shi a inda aka tsayar da Mudassir da yake wata dariyan mugunta alamar amma rena masa hankali ɗin nan.

Sajjad be san abinda ake ba kallan Muftahu kawai yake da alama neman ƙarin baya ni yake.

"Ga Mudassir ga kuma Likita, duk wanda a cikin su ya yi gudu ya wuce ɗan uwan sa yaje wancan dutsen ya hau shi ya kuma sauko sannan ya shiga ruwa yayi iyo ya fito shine wanda zai auri Hauwa'u Nela".

Suka ji wani mutum da'alama shine mai sanar da komai ya faɗa, wata irin juwa Sajjad yaji tana daukan sa a yadda yake ɗin nan? Daman barshi akayi yayi ta kuka da wannan abun. Kallan inda aka ce zasu bi yayi har zuwa Dutsen ba wani nisa amma kuma gudun fa?  Hawa dutsen fa? Da shi ya iya ruwa ma? Yaushe raban da yayi gudu a rayuwar sa?

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un".










Ipagpatuloy ang Pagbabasa

Magugustuhan mo rin

1.7K 210 8
Ana kiranta Jidda Sufi, ƴar auta ga Governor Sufi Adam. Duk da jindadi haɗe da tsaron da suke dashi a matsayinsu na iyalan Governor bai hana wani mum...
55.8K 6.4K 37
Rashi ba shi kaɗai yake samar da giɓi a rayuwa ba. Wani yana doron ƙasa amma dalilai kan sa wanzuwarsa ta kasa amfanar da makusantansa. Me zai faru d...
12.5K 431 56
labari ne data kafu aka kadara🙇🙇 Kubiyoni ku ji yanda LabariDr. Essha Ahmad zata Kaya da Young Tycoon Namji Mai ji dankashi Aliyu Umar Tycooon 💃...
367K 27.3K 39
ပဲပြုတ်သည်ငပြူးနဲ့ ဆိုက်ကားဆရာငလူးတို့ရဲ့ story လေးတစ်ပုဒ်