Lawh-Al-Mahfouz

By TajawwalAlRuwh

2.6K 672 265

Ina hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da ku... More

01: Hadiza.
02: 1996
03: 1996
04: 1996
05: Ibrahim
06: 1996
07: 1996.
08: 1996.
09: Hadiza
10: Ibrahim
11: 1996.
12: 1996.
13: 1996
15:1996
16: 1996
17: 1996

14: Hadiza.

169 39 11
By TajawwalAlRuwh


Tun da aka kirani cewar Umma ba lafia gaba daya na rasa sukuni. Duk da ance jikin da sauki na kasa samun kwanciyar hankali na san kuma nayi na gan ta da kai na ba dan haka na fara hada yar travelling bag qarama. Na hada yan kayan da zanyi using for a few days na jera a ciki. Kan Ibrahim da Bibi su dawo daga aiki na gama shirye shiryen tafia na Maiduguri dan har flight ticket na siya.

"You're always so thoughtful my love" Ibrahim ya fadi yana kissing saman kai na. Dawowa yayi ya samu na riga na gama shirin komi na tafia Maiduguri. Sai dai tafiyar namu babu Bibi sabida aikin ta. Itama tana dawowa aiki ta hada nata kayan, tare muka bar gida. Ita ta kama hanyar zuwa gidansu Muhibbah inda zatayi spending few days zuwa lokacin da zamu dawo mu kuma driver ya wuce airport da mu. Kan ayi sallar isha'i muna garin Maiduguri, driver din gidansu Ibrahim already an aiko shi airport yana jiran mu.

A duk da na ziyarci garin Maiduguri, sai na sama kaina da tuno da memories masu yawa. Wasu masu dadi, wasu marasa dadi. Da wanda zasu saka ni murmushi, wasu ma har su saka ni dariya wanda zanyi ta yi har sai cikina ya kusa qullewa, wasu abubuwan kuwa da na tuno sai dai na share hawaye daga idanu na. Yanzu zaman mu a mota samun kaina nayi da lumshe idanuna, na saki wata murmushi ina reliving wasu memories. Nayi murmushi ne ba dan abunda nike tunowa na farin ciki bane, nayi murmushi ne dan whatever it was i was thinking of ya riga ya wuce, ya zama tarihi a rayuwa na. Dago kai na nayi na ga Ibrahim gaba daya hankalin sa na kan wayar da yike ansawa. Gaba daya concentration dinsa na kan wayar sabida abunda yike tattaunawa me muhimmanci ne, abu ne da ya shafi aiki. Hannu na na dora kan nasa na dan shafa shi hakan ya sa ya juya ya kalle ni yayi mun murmushi kan ya sake maida attention dinsa kan wayar sa. Ba a wani jima ba muka iso gidan su Ibrahim. Gidan da ke dauke da memories da yawa na farkon rayuwar auran mu da Ibrahim.

Gidan qato ne haddade, da ka ga gidan ba sai an fadi maka cewar mutanen da ke cikin sa mutane ne masu arziki ba. Girma da haduwar gidan kadai ya isa ya sa mutum ya fahimci haka. Bayan main house din, akwai two other smaller apartments cikin gidan wanda yan uwan Ibrahim biyu ne ke zaune ciki tare da iyalan su. Main house din kuwa nan ne sasan suruka ta, Hajia Falmata nan kuma muka wuce kai tsaye. Koh da muka shiga a cike muka sama sasan Umma, surukan ta da jikoki harma da sauran yan dubiya duk sun zagaye da ita. Kowa yayi murnan ganin mu musamman ma Umma wadda muna shiga na isa inda take zaune na rungume ta. Yadda Umma ta dauke ni da irin kauna da kuma kulawar da take nuna mun yasa a duk lokacin da na kasance tare da ita nike ji tamkar ina tare da uwar da ta haife ni ne.

"Ina kishiya?". Ta tambaya da bata ga Bibi ba. Tun kan nayi magana Ibrahim ya bata ansa cewar mun bar Bibi a kaduna sabida yanayin aikin ta. "Iyyeeh! Gaskia Kishiya an girma, Tabarakallah".

Kayan abinci aka fara shigo mana da su duka muka ce sai mun gabatar da Isha tukun zamu ci. "Mu je dakina kiyi sallan". Umma ta fadi tana riqo hannu na kan ta ce masu aiki su biyo mu dakin da abincin. Muna shiga na fada bandaki nayi alwala kan na futo Umma har ta shimfida mun sallaya. A koh da yaushe bata taba gajiyawa da hidima ta, indai ina tare da Umma bata kaunar taga nayi komi. Duk sanda ta gan ni rasa inda zata sa kan ta take yi dan murna, wannan shine irin son da Hajia Falmata ke yi mun.

Ina cin abinci Umma na zauna gefe na tana mun hira. Da mun hada idanu zata yi mun murmushi mu cigaba da hirar mu. A haka Ibrahim ya shigo ya same mu shima ya zauna ya fara cin abinci daga plate dina. A wannan yanayin, duk wata damuwa da tashin hankalin da nike ciki yan kwanakin nan duk na nime su na rasa. Naji zuciya ta babu komi in ba farin ciki ba.

"Ummaaaaaa" na fadi da muka hada ido da Umma naga ni take ta kallo. Murmushi tayi kan tace "Naji dadin ganin ki ne Hadiza yar albarka". Kan nayi magana Ibrahim ya riga ni "Kin fada mata?". Ya tambaye ni. Shuru da nayi ya basa ansar tambayar sa.

"Menene ba a fada mun ba?". Umma ta tambaya.

"Yanzu duk yadda kuke da Umma dama baki fada mata ba?". Ibrahim ya fadi in a dramatic way "Ai nayi tunanin kan ki fada mun ma ita kika fara fadawa". Yayi murmushi kan yace Umma ta kawo kunnen ta kusa ya fadi mata "Amma in na fada miki sai kin bani tukwuici". Sai da Umma ta yarda zata basa tukwuici tukun ya kai bakinsa daidai kunnen ta ya mata rada. Hamdalan da naji Umma ta fara ya sa na sunkuyar da kai na, lokaci guda naji kunyar ta ya kama ni. Sujudus-shukur Umma tayi ta dago tana zubda hawayen farin ciki tana fadin "Ashe ina da rabon ganin wannan ranar ni Falmata. Allahu Akbar Kabeeran, Alhamdulillah". Ta fadi tana share hawayen ta. Nima ban ankara ba naji hawaye sun fara zubowa daga idanu na, kai na a qasa nayi kokarin boye hawaye na amma already sun riga sun gani.

Umma ce ta jawo ni jikin ta tana fadin "Alhamdulillah. Alhamdulillah, Allah mun gode maka". Da kanta ta fara share hawayen fuska na tace dani "Ya da kuka Yar albarka".

Tun kan na ansa Ibrahim yace "Ai aikin kenan yan kwanakin nan. Babu ranar da bata kuka". Kallo na tayi ta kuma jawo ni jikinta tana fadin "Murna zakiyi, Allah ya ansa mana addu'ar mu. Ya bamu abunda da aka dade ana nema". Shuru nayi ina ta sauraron nasihohin Umma.

"Ashe wannan qiba da kyaun da aka qara me dalili ne". Ta fadi tana dariya. Kai na na dora kan shoulder dinta, feeling shy of her all of a sudden.

Addu'o'i ta fara mana da fatan alkhairi "Allah ya kaimu lafia. Allah ya nuna mana zuwan abunda zaa haifa lafia. Allah ya kawo da yawa bayan shi koh ita. Allah ya qara kuma so da fahimtar juna, da kuma yawan kwanaki ku raini 'ya'yan ku tare". Babban yatsar right hannu na na saka na fara goge sabbin hawayen da suka fara zubo mun. Addu'ar Umma ya saka na fara feeling emotional all over again.

"Aikam gobe da safe zan bada sadaqah. Alhamdulillah". Umma ta qara fadi tana ta jin dadi. News inda muka yi sharing da ita ya sa kulawar da take nuna mun ya qaru. Mun jima sosai a dakin Umma tare da ita dan har sai past midnight tukun muka mata sai da safe muka futo muka wuce dakin da muke sauka a duk sanda muka zo Maiduguri.

Muna shiga Ibrahim ya janyo ni jikinsa yana fadin "Back to where we started". Yar dariya nayi na qara shigewa jikin, nayi settling a arms dinsa. Dukan mu shuru mukayi, in my mind I was recollecting memories of the first four months of our married life, months inda mukayi spending a wannan dakin. Mun kai ten minutes tsaye a haka kan Ibrahim yayi releasing dina from his arms.

Na jima rabona da gidan mu. A qalla shekaru na kusan biyar yanzu rabon da na taka qafa a gidan, tun rasuwar Baba. Hakan ya sa yau nike ta jin gaba na yana fadi as i sat in the backseat of a sleek BMW, driver na tuqa ni zai kai ni gida. Ji nike kamar na cewa driver din ya juya mu koma na fasa zuwa but deep down, in my heart of hearts I knew i had to go. I need to.

Lokacin da na dauka rabona da gida be sa na daina kula da yan uwana ba. Duk wata dawainiya tasu wanda na saba ina musu ban daina ba har ma da abubuwan da basu tambaya duk ina yi. Zuwan ne bana yi, it was always so hard on me duk sanda naje. Ganin gidan, ganin mutanen gidan, tuna abubuwan da suka dani a gidan. It was always so hard shisa Baba na rasuwa na dauke qafa ta. Time to time kawai nike kokarin kiransu a waya na ji ya kowa yike.

"Hajia mun iso". Driver ya fadi, bringing me out of my trance.

Ibrahim ya so mu zo tare amma nayi reasoning da shi cewar i needed to go alone, maybe some other time in mun dawo sai muje tare. I needed to go alone for my first visit after so many years. Dogon numfashi na ja kan na buda qofar mota na sauko.

"Ka jira ni". Na ba driver umarni dan bani da niyyar jimawa a cikin gidan.

A hankula nike taku na har na isa gate din gidan na buda na shiga. Wani irin sauti ne ya futo daga bakina involuntarily ganin gidan da aka birne cibi na a ciki, gidan da nayi spending childhood dina a ciki, gidan da na sha wahala da azaban rayuwa iri iri. The house hadn't changed much, duk da na sa anyi gyare gyare, an yi modernizing gidan.

Na dan jima tsaye a tsakar gidan as i went back in time, back to over twenty years ago. Ina kallon wurin da ake aikace aikacen gida na hango yan mata biyu, daya na wanki daya na doraya tana shanyawa. Aikin su suke suna dariya suna hira, suna fantasizing about rayuwa outside gidan mahaifin su da ya zame musu tamkar wani kurkuku.

Fading wannan memory din yayi as she walked into the room she shared with Fusam. The room that knew them than most people. The room that held so many secrets, knew of the so many tears and laughters they had shared. The four walls which knew of so many dreams, so many aspirations.

Murmushi Hadiza tayi tana share hawayen da suka fara zubowa daga idanun ta "We were such dreamers". Ta fadi out loud.

"Hadiza" Jin sunan ta ya sa ta juya "Ke ce?".

Matsawa kusa da me maganan tayi tana fadin "Ni ce" ta fadi tana kallon yadda shekaru suka qara nunawa a fuskar Shatu yan shekarun da tayi basu hadu ba. Shatu bata yi tsammani ba taji Hadiza ta rungume ta tana fadin "Long time sister".

Maganan da suka ji ana yi a tsakar gida ya sa matan yan uwanta suka futo tsakar gida. Cikin yan uwanta maza uku, guda daya ne kawai baya zama nan gidan da iyalin sa. Gaba daya ma Marwan ba a nan garin yike ba, aiki ya dauke shi har can garin katsina a nan kuma yike zama tare da iyalin sa. Amma da Abdi da dayan qanin ta Umar duk a nan gidan suke tare da families dinsu. Abdi da matar sa daya da yaransa biyar, shikam Umar matan sa biyu da yara hudu sai kuma tsohon ciki da taga uwar gidan sa tana da shi. Bayan su kuma sai Shatu da har zuwa wannan lokacin Allah be sa tayi aure ba. Shekarun ta arba'in da takwas kenan a duniya babu miji bare yara tana zaune a nan gidan kullum suna cikin rigima da Yaburra. Abun nasu babu wani dadin ji. Sai da suka gama gaisawa da matan cikin gidan tukun ta wuce gefen Yaburra.

A kwance ta same ta as usual dan kimanin shekaru goma kenan da Yaburra ta sama stroke wanda ya ja mata paralysis from her waist down. Bata tafia, bata magana bata komi sai da taimako. Tana ganin Hadiza ta miqo mata hannu tana kokarin magana duk da maganganun nata futowa suke kamar na yarinya qarama da ke kokarin koyon magana. Ba musu Hadiza ta wuce kusa da ita ta zauna. Zarnin da ke tasowa daga jikin Yaburra be sa Hadiza ta ji kyamar ta ba.

Halin da ta sama Yaburra a cikin ya mugun razana Hadiza dan kana ganin Yaburra ka san mutanen gidan basa bata isasshen kulawa yadda ya kamata. Duk ta rame, jikin ta ba komi sai qashi kana ganinta ka san bata samun isasshen abinci ta ci ga kuma kazantar da suke barin ta a ciki. Wannan dalili da kuma tunowa da abubuwan da Yaburra ta musu a baya ya sa Hadiza kuka. Tabbas Allah ba azzalumin bawan sa ba dan gashi tun a duniya Allah ya fara nuna ma Yaburra ayoyi iri iri.

Sai da tayi kukan ta har ta gaji tukun ta share hawayen ta ta juya ta kalla Yaburra. Kalamai uku ta furta mata kan ta miqe ta nufi qofa "I forgive you".

Karo suka kusa yi da Shatu da ke shigowa dakin dauke da tray din ruwan sha zata kawowa Hadiza. Da kyar Hadiza ta iya danne hawaye ta ce ma Shatu sauri take zata tafi amma zata dawowa very soon.

End Of Chapter 🎊🎉

Allah sarki rayuwa! Yaburra an zama abun tausayi 🤣😂

Salaam alaikum. Hello everyone, I hope duka muna lafia. Long time koh? Yeah Ikr, I've missed reading your wonderful comments😊🤗 bear with me for the long break.

Continue Reading

You'll Also Like

300K 21.8K 26
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
1.7M 141K 65
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...
333K 10K 81
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...
177K 6.5K 81
Not many people understood 12 year old Jessica, as a person and an individual. That doesn't include, however, her older sister, who Jessica adores w...