A SOYAYYAR MU

By hijjartAbdoul

4.1K 74 0

Be tashi ya ga mace a gidan su ba, rayuwar su gaba ɗayan babu mata idan kaga mace a gidan to auro ga akayi ha... More

Shimfiɗa.
1
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49
50

2

138 2 0
By hijjartAbdoul

   

Cikin  dare ya tashi da zazzaɓi gashi da wani irin raki rashin lafiya ko yaya ne indai yana ciwo to sai ya nuna bare wannan da ya haɗu da damuwar maganar da za'a faɗa masa,  wanda ya rasa ina ta nufa bare kuma ya san abin yi,  kasa cigaba da zama yayi shi kaɗai yayi ya fito, ɗakin su Al-ameen ya shiga ya kwanta a kujera sai dai kuma wani irin sanyi yake ji kafin kace me ya fara rawar sanyi, lokaci guda kuma jikin sa ya rikice.

Kusan lokaci guda suka tashi suna kunna lamp ɗin dake gefen su.

"Sajjad".

Suka faɗa a tare suna nufo shi, Aliyu ne ya fara taɓa shi da sauri ya ɗauke hannun shi tsabar zafin da yaji jikin sa yayi, kafin ya ƙara kama shi ya zaunar shi yana zama a gefen sa.

Al-ameen yace, "ko ruwa sanyi za'a goge masa jikin sa dashi ko zazzaɓin zai ragu".

Aliyu yace, "Ko mu kira Daada ba?"

Al-ameen yace, "A'a Daada da wannan daren? Kar hankalin Anty ya tashi".

Ganin yana neman kwanciya yasa shi, kwantar dashi a cinyarsa yana shafa masa kai, bargo Al-ameen ya ɗauko ya rufa masa ya ɗauko Pcm ya bashi tare da maganin malaria, Aliyu ya zuba masa ido, jini ɗaya ba wasa ba, ko yane dole sai kaji kana san ɗan uwan ka bare su biyu kawai Mahaifiyar su ta haifa duk da babu shaƙuwa a tsakanin su amma akwai wata irin soyayya dake tsakanin sa da ɗan uwan sa shi kan sa yasan yana yi masa wani irin so da shi kan sa be yiwa kan sa ba, sai dai ko da wasa be taɓa nuna hakan ba, saboda irin gidan da suka ta so yasan da ace su biyu ne a gidan su ya tabbatar da soyayyar da yake masa sai ta fito fili.

A hankali ya fara ƙoƙarin kwantar dashi ganin ya sami bacci, amma ko kan sa be gama ɗauke wa ba ya damƙe hannun sa tare da ƙara shigewa jikin sa, ajiyar zuciya ya sauƙe yana ƙara gyara masa rufar da bargo, ya jinjina da kujerar, a haka bacci ya ɗauke shi, shima ba kuma farkawa ba sai da Al-ameen ya tashe shi sallah har lokacin Sajjad na bacci, daƙyar ya kwantar da shi saboda irin ƙwaƙumar da yake masa, yana ajje shi kuwa shima ya tashi. Koda sukayi sallah kasa baccin yayi kawai kwanciya yayi maganar bawan Allahn nan tana dawo masa a rai. Be san gari ya waye ba sai sa yaji muryan Anty da Mama suna magana da alama sun sanar masa, zaune ya tashi yana kallan su.

Daada yace, "Ka tashi ka shirya mu tafi asibiti".

Mama tace, "Ashe baza'aje ba, kamar ka manta jinyar Sajjad wanka ma yi masa ake".

Ummi tace, "Wallahi kuwa, ba abinda yake sai sallah ita ma da anayi nasan yi masa za'ayi".

Aliyu yace, "Sai shegen ragwanta ba, jiya be barmu munyi bacci ba".

Anty tace, "Allah sarki Auta na, rabu da su kaji ko? Ya jikin?"

Ya faɗa tana hawa kan gadan da yake shi kuma ganin haka yasa shi kwanciya a kafaɗar ta.

Inna tace, "sai kuyi sauri ku tafi asibitin kar jikin ya rikice ku shiga uku".

Su duka suka rangaya suka tafi asibitin amma banda Inna, Baba dake sa wuri ya fita be ji labari ba sai sa suka je asibiti dan haka  asibitin shima ya nufa lokacin har an sa masa drip ya sami wani baccin.

"Sai wasu su koma gida ai anyi yawa haka, ku wuce aiki".

Bintu tace, "A barni zan kula da shi".

Hafiz yace, "baki da hankali shiyasa kika ce zaki kula da shi".

Yusuf yace, "Bata san waye Sajjad ba shiyasa tace haka".

Kumbura fuska tayi, tana hararan su.

Ummi tace, "ku faɗa mata waye shi da har take nema masa shishshigi".

Anty tace, "babu zancen shishshigi ko takwara? Ummi ki barta mu zauna tare".

Tashi sukayi domin tafiya aka bar Anty da Bintu. Sai azahar suka dawo har lokacin kuma be tashi ba abinci suka ci anan sannan suka koma matan kuma suka zauna nurse tace sai dai su fita saboda kar a dami marar lafiya, waje suka fita kuwa su dukan su. Wasa wasa har la'asar be tashi ba.

Mama tace, "Bintu je ki ƙara ganowa ko ya tashi".

Ummi tace, "wannan baccin de Allah yasa lafiya".

Anty tace, "Ai baccin shine lafiya indai a rashin lafiyar Sajjad ne".

Ita de Bintu tashi tayi ta shiga ɗakin, lokacin doctor na fitowa daga ɗakin. Idan sa a rufe kamar me bacci sai dai ba baccin yake ba tunani yake ko doctor ɗin zai sanar da Daada ko ba zai sanar da shi na duk da ya ɗaukar masa alƙawarin kada ya sanar da shi abinda ke damun sa domin yasan muddin aka sanar da Daada ko ƴan gidan su suka sani to ya san sai sun matsa masa ya sanar da su abinda ke damun sa, to idan suka tambaye shi ya ce musu me? yace musu wani mutum da ya manta sunan sa ko kuma yace musu wa?.....

"Ya kamata ka tashi baccin nan ya isa haka".

Tsaki yaja a zuciyar sa ya mai ƙara gyara kwanciyar sa tare da bude idan sa, ganin lokaci yaja a agogon dake ɗakin yasa shi neman tashi zaune sai dai kuma ba zai iya ba dan babu ƙarfi ko na sisin kwabo a jikin sa, rumtse idan sa yayi yana sauke ajiyar zuciya ganin haka ya Bintu zata ɗaga shi. Wani irin banza kallo ya wurga mata tare da jan tsaki da ƙarfi. Hakan yasa ƴar baiwar Allah komawa da baya ta fice tana mamakin sa to shi wai baya magana ne? amma ai taji shi sarai jiya yana magana ita ne baya son yin maganar, Anty taje ta kira ta zauna wurin su bata dawo ba.

"Anty ni kada yarinyar nan ta ƙara zuwa inda nake".

"To Baffalo( Sunan da take kiran Baban ta dashi) ko baka ji ba?"

Haɗe fuska yayi.

Yace, "Yi haƙuri".

Ƙwafa tayi masa sannan ta shiga ta haɗa masa ruwan wanka, ta fito tana masa faɗa.

"Wannan halin naka idan baka rabu dashi ba ina mai tabbatar maka da cewan zaka sha wahala a rayuwar ka, kai shikenan babu wanda ya isa ya raɓe ka sai ƴan uwan ka maza? Ka cigaba da abinda kake".

Ta faɗa tana fara cire maballan rigar sa.

"Akwai inda zaka je babu namijin da zai taimaka ba dole macen ce de, naga yadda zakayi a wurin, yarinya na san..."

"Haba Ummu Aliyu, za'ayi ace yaro baya da lafiya kina masa faɗa har haka?"

Mama ta katse ta tare da ƙarasowa inda take, ta cigaba da cire masa rigar.

A zuciyar yace,'ohh sai kace Maman bata fi Anty faɗa ba'.

Amma a fili ƙara langwaɓewa Maman yayi, Anty takaici ne ya ishe ta ta watsa masa harara ta fice.

"Mama a kira Yusuf ko Hafiz ya min wanka Allah bazan iya ba".

"Gasu nan sun zo suna waje ne".

Sai da ta taimaka masa ta kaishi toilet lokacin suka ƙara so, Hafiz ne ya masa wankan yana mita.

Yusuf yace, "gardi da kai ake maka wanka,wallahi kaji kunya".

Yanzu kam babu bakin magana saboda jirin dake ɗibar sa kan sa kuma juyawa yake. A haka ya samu yayi sallah aka zuba masa abinci sai dai yana ci ya dawo shi  daman ba wani na kirki yaci ba Daada ne ya shigo yaga yadda yake ƙela amai abin gwanin tausayi, yana gamawa kuma ya kwanta aka sa masa drip.

Baba da suka shigo tare da Daada.

Yace, "yanzu haka babu abinda ya ci ko?"

Mama tace, "Ai bacci yake yi tun safen nan sai yanzun nan ya tashi shine yayi wanka yayi sallah yaci wannan abincin".

Daada yace, "Sallamar ku za'ayi ayi masa duk wani abu da aka saba yi a gida har ya warke ko kuwa de?

Baba yace, "Gaskiya de zai fi, tunda anan ɗin tarewa ake, ga kuma Inna ita kaɗai".

Yusuf yace, "Itama Inna sai ta..."

"Gidan ku Yusuf".

Baba ya katse shi, shiru yayi bece komai ba, Aliyu a zuciyar sa yace, 'ai ta saba daman'.

Sai da ruwan ya ƙare sannan aka sallame su, suka garzaya suka koma gida. Haka Sajjad yayi ta fama da zazzaɓi baya iya cin komai daga yaci sai amai dai-dai da rana ɗaya basu gaji da shi ba, shi kuma sai shegen raki baya iya motsa koda ɗan tsa ne komai yi masa yake har ta kai ta kawo alwala ma sai an ɗaura masa ahaka yayi sati biyu  suna jinyar sa a gidan nan Inna kuwa dmaan tsakanin ta da shi kallo ne sannu wannan bata haɗu su da ita ba daman yana yaron sa idan baya da lafiya ba sannu take masa ba dake ita a ganin ta rai mi ne da yaron  shiyasa sam bata san shiga harkar sa wai kar ya rena ta ita a ganin ta ma wannan jinyar tasa ƙarya ce. Wannan abun ba ƙaramin ɓatawa sauran ƴan uwansa rai yake ba, kawai de shiru kowa yayi abin na cin sa a rai musamman Aliyu da yanzu hira ma bata haɗa shi da ita dan Allah ya gani shi dai sosai haushin ta yake ji.

°°°°°°°°

Yau ya kasance sati biyu kenan Sajjad na fama da kan sa, sai kawo yanzu Alhamdulillah ya fara samun sauƙi domin babu laifi yanzu yana iya komai da kan sa kawai ƙarfi ne da jikin sa baya da shi sosai, sai dai kuma wannan damuwar har yanzu tana danƙare a zuciyar sa, ta wata zuciyar sa na san ƙara ganin wannan bawan Allah kai har ma san magana dashi yayin da wata zuciyar kuma bata san yin magana da shi sam.

"Yaya Sajjad ya jikin?"

Yaji Bintu tayi masa magana, tsaki yaja a zuciyar sa rufe idan sa. Daman a compound ya zauna ita kuma ta dawo daga makaranta. Zama tayi a kusa da shi.

Tace, "Wai meyasa baka san min magana, nifa ina san naga mun saba sosai".

Shiru yayi mata be amsa mata ba.

"Yaya Sajjad magana fa nake".

"Mtswwwww!

Yaja uban wani wannan tsaki.

"Wulaƙanci de Yaya Sajjad babu kyau".

Buɗe idan sa da yayi daidai da shigowar wasu yara su biyu sa'annin juna kowanne su hannun sa riƙe da alawa, da gudu suka nufo shi, shima ɗan murmurshi yayi yana gyara zaman sa.

"Uncle Daddy yace baka da lafiya kaji sauƙi?"

"Naji sauƙi Sadiq".

"To Allah ya ƙara sauƙi".

"Ameen Samir".

"Amma kunsa me?

A tare suka ce girgiza kai alamar a,a.

"Daga yau Pappi zaku ke cemin kunji ai".

"Eh munji".

"Yauwa to ku tashi mu shiga ciki ko?"

"A'a sai dai ka ɗauke mu".

"Wallahi bazan iya ɗaukar ku ba, ban gama warkewa ba".

Samir yace, "ka goye mu".

"Faduwa fa ba zan yi idan na goye ku".

Daƙyar suka yadda ya riƙe hannun su suka tafi. Da ido Bintu ta bisu kawai, babu abinda yafi komai takaici irin yadda baya kula ta, to meyasa ma baya kulatan?

Wurin Inna suka shiga, anan ya ga Yaya Babba da Yaya ƙarami suna zancen su da Inna gaida su yayi ya sami waje ya kwanta.

Inn tace, "Ku bar matan ku mu tafi tare da su, idan yaso ku sai ku taho ana gobe ɗaurin auren".

Tashi zaune yayi.

Yace, "Inna auren wa za'ayi?"

"Auren wata ce".

Komawa yayi ya kwanta, yana jin su suna tsara yadda tafiyar zata kasance matan su tafi gobe su kuma sai ana gobe ɗaurin aure, to shima kuwa gobe zai tafi ƙafar sa ƙafar Anty. Daddare su dukan su suna main parlourn Mama suna maganar tafiyar.

Sajjad yace, "Nima gobe zan tafi".

Aliyu yace, "kai da baka da lafiya Sajjad? Ka bari idan munje sai mu dawo a washegari sai mu tafi a jirgi saboda kada ka jigata".

"Nidai wallahi a,a taab".

"Sai yadda Inna tace".

Mama ta faɗa tana ɗauko wani zancen. Tashi yayi ya fice daga parlourn ya tafi wurin Inna, ita kaɗai ce a parlourn nata tasa tv a gaba tana kallan BBC Hausa.

"Inna dan Allah kice gobe a tafi a dani".

"Idan kaje uban me zaka yi?"

"Inna idan na zauna a nan da me zan yi? Kuma na jima rabo na da Bauchi ai".

"Idan ka matsa sai kaje goben kasan sai kayi aikin gidan nan namu".

"Haba Inna, bafa ni da lafiya".

"Wannan kuma ruwan ka".

Koma yayi yace tace su tafi a goben, yana komawa ɗakin sa ya haɗa kayan sa, washegari da sassafiya sojojin da zasu kai su suka iso daga Jaji motar da aka ɗauko matan su Yaya Babba ya shiga ya zauna a gaba.

Ummi tace, "Ina Sajjad ɗin yake? Hala yana can yana bacci ko?"

Inna tace, "Wanne haka? Banda shi a tafiyar mu dan haka muje".

Kowa yayi tunanin be fito ba, amma sai dai basu san yana cikin mota ba, babu wanda ya sani sai Zaliha da Maryam haka suka tafi abin su suna hira dan sune ya ɗan saba da su be sama da matan su Abdulmajid kamar yadda saba da su ba, har sukayi bacci, haka suka share awanni suna tafiya basu suka iso ba sai azahar Inna gidan ƴan uwan ta aka ajje ta su kuma gidan su dake Bauchi aka kaisu ana ajje su Sajjad ya fice. Haka akayi ta hidindimu batare da Inna tasan Sajjad yana nan ba, yayin da Sajjad tun zuwan su ya kuma kwanciya wata rashin lafiya, bata tashi sani ba sai da Bintu ta sanar da ita, a lokacin bata ce komai ba  har aka gama ɗaurin auren da zasu tafi  ya fito domin tafiya.

Tace, "Sajjad anan zai zauna tunda ya jima raban sa da gida".

"Ni bazan zauna a garin nan ba".

Ya faɗa kan sa tsaye.

Aliyu yace, "Inna baya da lafiya fa".

"Ya iya faɗa min magana ai".

Baba yace, "Sajjad kayi hakuri ka zauna kaji ko?"

Yana ji yana kallo ƴan uwan sa suka tafi suka barshi, ya koma gidan ƙanin Baffa shima Kaka ne a wurin su tunda ƙanin kakan su ne ba laifi gidan ya masa daɗi sai dai rashin lafiyar dake damun sa ce kawai ta hana shi jin daɗin garin, yasan da Abba yana nan ba zai yadda ya zauna ba....





Continue Reading

You'll Also Like

179K 10.5K 40
The feeling of being abandoned by one's own family was not unknown to Aadhira. She hates her family for abandoning her when she was only a newborn, l...
1.7K 207 8
Ana kiranta Jidda Sufi, ƴar auta ga Governor Sufi Adam. Duk da jindadi haɗe da tsaron da suke dashi a matsayinsu na iyalan Governor bai hana wani mum...
418K 15.2K 192
Won Yoo-ha, a trainee unfairly deprived of the opportunity to appear on a survival program scheduled to hit the jackpot, became a failure of an idol...
52K 2.1K 18
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata...