Lawh-Al-Mahfouz

By TajawwalAlRuwh

2.6K 672 265

Ina hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da ku... More

01: Hadiza.
02: 1996
03: 1996
04: 1996
05: Ibrahim
06: 1996
07: 1996.
08: 1996.
09: Hadiza
10: Ibrahim
11: 1996.
12: 1996.
14: Hadiza.
15:1996
16: 1996
17: 1996

13: 1996

129 45 13
By TajawwalAlRuwh


Nan da nan labari ya isa gidan biki cewar yaron Yaburra ya rasu. Nan yan biki suka dinga qarasawa gidan dan yiwa Yaburra ta'aziyya. Ba a bar gawar ya kwana ba nan da nan aka yiwa Hamza sutura aka kai shi makwancin sa Yaburra sai kuka tana kaicon ta ana ta kokarin rarrashin ta.

Gefen su Ibrahim suma gidansu taro suka yi na azo a gani duk da Hajia Falmata tace baza suyi wani babban taro ba sai amaryar su ta sama sauki tukunna. Da yamma yan uwa na jiki suka tafi asibiti suka duba Hadiza suka samu an bata magani tana ta barci. A nan suka sama labarin abunda ya faru da Yaburra suka ce aikuwa zasu qarasa gidan dan yi mata ta'aziyya.

Wani irin kallon takaici Daada tayiwa gashin Hadiza sabida irin askin kaskancin da Yaburra ta mata. Reza sabuwa ta samu ta kwashe ragowa gashin tas dan wani sabo ya taso. Yan uwan Maryama sun sha baqin ciki iri iri, sun sama kan su da yin dana sanin barin yaran a karkashin kulawar Haji Modu. Su kuwa Baba Azumi idanun su sun qara budewa, abunda ya faru ya ankarar da su cewar dole a tashi da yiwa Haji Modu addu'a dan ya rabu da asirin da ke tasiri a kan sa.

Mutane sun cika a gida Shatu ta fara ihu tana fadin "Maman mu ce ta cuce mu. Maman mu ce ta yi silar mutuwar Hamza". Tana kuka tana ihu kamar wadda ta zauce mutane suna riqo ta. Yan uwan Yaburra ne suka samu suka jawo ta aka rufe ta a cikin daki. Ita dai Yaburra tana gefe tana zubo da hawaye silently, wani sabon wutar tsanar su Hadiza da Fusam na ruruwa a zuciyar ta dan sune silar rashin Hamzan ta. Da ba dan su ba da Hamzan ta yau yana tare da ita. Alwashi ta dauka na raba su da duk wata farin ciki a cikin rayuwar su. Zata cigaba da azabtar da Fusam tunda Hadiza yanzu ta bar gidan amma itama zata san yadda zata yi da ita ta koya mata hankali.

A yammacin ranar Ibrahin ya wuce asibiti. Be tafi tare da kowa ba, shi daya yaje asibiti dan asalin sa ba wasu abokai gare sa ba, yan uwansa sune abokansa sai kuma abokan karatun sa wanda suke can qasar Canada. Yan kadan inda yike da su kuwa ba a wannan halin yike so su ga amaryar sa ba dan haka shi daya yayi tafiyar sa ganin ta. Koh da yaje har zuwa wannan lokacin tana barci.

"Yau barci take ta yi" Daada ta masa bayani "Jikin ya matsa mata jiya shine suka bata magunguna da allurai toh ina ganin su suka sa ta barci". Ta fada masa kan suka gaisa ta nuna masa farin cikinta tana masa Allah ya sanya alkhairi. Yan nasihohi ta shiga masa kan daga baya ta masa godia wannan babban taimakon da ya musu ya auri Hadiza zai dauke ta daga hell inda take da kuma kokarin da ya ce zai yi dan karbo Fusam sabida sun san koh sunce su zasu anshe ta Haji Modu bazai taba bari ba, amma dai kan su tafi zasu gwada luck din su su gani. Sai da suka gama magana tukun ta tashi ta futa daga dakin dan ta bashi privacy.

Kujerar da ta miqe daga kai yaje ya zauna, kusa da Hadiza. Karo na farko kenan a rayuwa da Ibrahim ya riqe hannun Hadiza cikin nashi. Ya jima yana kallon dan qaramin hannunta cikin nasa da ya fi girma. It looked perfect, like it was meant to be there all their life. Murmushi yayi kan ya kalli fuskar ta, looking peaceful in her sleep. Ya san ba jin sa zatayi ba amma hakan be hanasa yin magana ba.

"An daura auran mu Hadiza. Kin zama matata". Hakan ya kuma sa shi murmushi a zuciyar sa yana jin wani sabon so yana ratsa dukannin gabobin jikinsa. Kumatun ta ya shafa kan ya sake riqo hannunta ya zauna shuru, a million thoughts going through his mind, all happy thoughts about him and Hadiza, about the life they'll start together in ta warke, about the love and memories they'll share, the family they'll start. Tunanin ba qaramin annushuwa ya saka Ibrahim ba dan sai murmushi kawai yike ta saki. Da ka gansa ranar ka san yana cikin walwala.

Ya kai minti talatin zaune da ita bata farka ba har ya miqe ya futa daga dakin ya sama Daada zaune a waje ya mata sallama yace zai koma gida. Ga abinci nan ya kawo tayi kokari ta ci. Godia ta masa ta sa masa albarka kan ya wuce ita kuma ta koma cikin dakin. Hadiza bata farka ba ranar sai tsakar dare, nan da nan Daada ta hada tea ta dinga bata har ta sha ya ishe ta ta koma ta kwanta tana ta murmushi ita daya. Mafarkin Ibrahim tayi barcin da take barci, shi ke sa ta murmushi gashi kuma auran su da aka daura ranar. In ta tuna yanzu ta zama matar shi sai taji wani sanyi a ran ta, musamman yadda Daada ke qara yabon Ibrahim din tana fadin irin sa'ar da Hadiza tayi da samun sa. Nasiha ta fara mata akan Allah ta riqe shi amana da zuciyar ta tsakakkiya, tsakanin ta da Allah kada ta taba yin abunda zai cutar da shi dan shi din masoyin ta ne na asali.

Hadiza bata ji labarin rasuwan Hamza ba sai kashe gari da safe. Kuka sosai tayi dan a cikin yaran Yaburra shine dan dama dama. In aka cira aiki da yike yawan sa su shi be cika musu ihu koh ya dake su ba. Hasalima shi wasu lokutan ya kan siyo abu ya basu a sace ba tare da Yaburra ta sani ba koh kuma ya basu kudi yace su boye. Sai zuwa azahar Fusam ta zo tayi murnan ganin Hadiza ta qara samun sauki, karayar da ta samu a wurare har uku ne dama sai an dan dau lokaci kan su warke. Ribs dinta sun karye, sannan hannunta daya ya karye da kuma qaramar yatsar hannun hagun ta.

Rungumar juna suka yi da Fusam, sunyi kukan murna sunyi dariyar farin ciki. Fusam ta nunawa Hadiza farin cikin ta akan auran da tayi ita kuma Hadiza ta qara qarfafa mata cewar In Shaa Allah Ibrahim da mahaifin sa zasu yi iya kokarin su dan ganin Haji Modu ya yarda Fusam din ta dawo hannun Hadiza da zama. Murna ya gama lullube Fusam. Sai da ta ci abinci ta qoshi tukum ta fara ba su Daada labarin abunda Shatu ta dinga fadi da yadda ta dinga yin abu kamar wadda ta fara sabon hauka. Duka suka yi Allah ya kyauta da kuma tir da hali irin na Yaburra.

Normal rayuwa ya cigaba bayan auran Hadiza da kuma rasuwar Hamza. Ana sati guda daidai da bikin sauran yan uwan Maryama suka koma Yola aka bar Daada wadda ke jinyar Hadiza dan tana asibiti har zuwa wannan lokacin. Fusam kuwa tana zaune gidan ubanta sai dai Yaburra tana fama da rashin dan ta bata koh shiga sabgar ta. Suma gefen su Ibrahim normal abubuwa suka cigaba da tafia, yan biki sun watse. Ibrahim yayi hutun sati guda kan ya koma bakin aikin sa, zuwa lokacin yana gab da gama bautar qasar sa. Ba ranar da baya zuwa asibiti duba Hadiza, most times ma so biyu yike zuwa; da safe ya ga ya suka kwana sannan ya koma da yamma ya sha zaman sa har sai ya fara jin barci koh ita Hadizan ta fara jin barci tukun ya musu sallama ya koma. Kusancin su nata qaruwa kadan da kadan.

Sati biyu daidai Hadiza tayi a asibiti aka sallame ta aka ce mata sauran jinyar a gida zata qarasa shi har ta fara amfani da hannunta. Nan da nan su Baba Azumi suka yi shawara da Daada cewar zasu maido da ita nan gidan nasu a cigaba da jinya har ta gama samun sauki kan ayi maganar tarewa. Sosai Daada tayi na'am da shawarar tace zata qara zama da Hadiza kan ta koma Yola. Abunda basu sani ba shine Ibrahim already yayi nasa shirin tare da mahaifan sa. Sai ranar da aka yi sallaman suka zo Hajia Falmata ta gabatar musu da nasu qudurin.

"Tunda dai yanzu anyi aure. Yarinya ta dawo amanar mu, tana karkashin kulawar Ibrahim hakan din ya sa muke ganin jinyar ma mu ya kamata muyi. Kunyi iya kokarin ku yan sati biyun nan muma dan Allah ku bamu damu nuna kalar namu kulawar akan ta. Ibrahim kuma ya fara sauke nauyin da Allah ya rataya yanzu a wuyar sa". Hajia Falmata ta fadi. Sosai kowa aka yi na'am da shawarar surukan Hadiza na tafia nasu gidan da ita har zuwa sanda zata sama sauki ta tare a nata gidan. Ganin yanzu Ibrahim din ya fi su iko da Hadiza ya sa ba yadda suka yi suka amince dan haka a yammacin ranar Ibrahim yaje ya dauko su ya dawo da su gida. Maraba sosai aka yi da ganin su, aka yi musu tarba na mutunci. Daki guda musamman aka shirya a cikin gidan dan dawowar Hadiza gidan. Satin su daya da dawowa daga asibiti Daada ta kintsa ta koma Yola. Ranar su Hadiza da Fusam da ta zo mata sallama sun sha kuka. Alkawari Daada ta musu cewar in an kwana biyu zata dawo ta duba su. Itama Hadizan tace in ta sama lafia zata zo ganin su, musamman kakarta da ta dade bata gan ta ba.

Ibrahim ne ya dauke ta ya kaita tashar mota suka mata sha tara na arziki. Suna tafia a mota tana qara sa masa albarka tana basa shawarwari. Godia sosai ya mata ya mata fatan alkhairi.

Yaburra tunda aka yi auran har Hadiza ta gama zaman ta a asibiti bata taka qafarta taje dubata ba, a cewar ta itama tana makokin mutuwar dan ta.

Wato irin sabuwar rayuwa Hadiza ta fara a gidan surukan ta tun bata sakin jiki da su har ta fara sabawa dan sosai suka karbe ta. Sosai suke nuna mata kulawa, kannen sa suna tarairayar ta dan cikin qanqanin lokaci ita da kanwar shi wadda suke kai daya har sun zama kawaye kullum tare suke, Hansatu tana zuwa dakin da take dan taya ta zama ta debe mata kewa tunda bata futa koh ina bayan tafiyar Daada ma dakin ta dawo da kwana dan basa barin Hadizan ita daya sabida cikin dare tana iya buqatar abu gashi hannunta a karye. Shima Ibrahim wani irin sudden change yan gidan suka gani a wurin shi, zuwan Hadiza ya futo da wani side of him da basu taba gani ba. The side that loved to play a lot and loved to smile a lot. Sosai hakan yikewa mahaifiyar sa harma da kannin sa dadi. Ba kunya yike nunawa Hadiza matsanacin so da kulawa dan in dai ya dawo daga aiki straight dakin ta yike wucewa nan yike zama ya ci abinci, yayi komi a can. Weekend da ya tashi yike shigowa sai dare. Tun Hadiza na kunya kunya har ta fara sakin jiki sosai da shi dan lokuta da yawa zaka jiyo kawai sautin muryoyin su suna hira suna dariya duk da mostly Ibrahim ne ke hirar Hadiza na sauraron sa. Hankali da nutsuwar Hadiza ya sa kowa a gida ke qara son ta. Sosai Hajia Falmata ke nuna mata kulawa dan har ta wanka ita ke taimaka mata wurin yi, cin abinci da komi sai an taimakawa Hadiza amma haka nan basa gajiyawa da yi mata hidima. Tamkar diya Hajia Falmata ta dau Hadiza.

Duk ranakun zuwa asibitin ta kuwa kashe zuwa aiki da duk wani abu da zai yi ranar Ibrahim yike yi ya kai ta da kansa a duba lafiyar ta kan su dawo gida. Fusam ma a duk sanda ta dan sama dama musamman in tana dawowa daga makaranta tana biyawa ta duba Hadiza kan ta wuce gida. Hankulan su a kwance.

Wataran da tazo ne take ba Hadiza labarin wani yaron aminin Baba da ya zo daga can garin Yobe dan zama da su. Labarin sa Fusam ta bawa Hadiza da Hansatu duka tausayin sa ya kama su. Baakura ya rasa iyayen sa duka cikin kwana ashirin. Mahaifin sa ya fara rasuwa kan mahaifiyar sa ta bi baya. Rashin madogara ya sa ya taho har garin Borno da tambaya har ya gane gidan aminin mahaifin sa Haji Modu. Yana zuwa Baba yayi maraba da shi ya sa aka bashi dakin Hamza yace a nan gidan zai zauna shi ya dau nauyin riqe sa sabida shi daya tal abokinsa ya haifa kuma sosai a baya wannan abokin ya taimakawa Haji Modu a lokacin da yike buqatar taimakon sosai.

Ya kuma ji dadi dan duk shekarun da suka dauka not in touch sabida yadda suka zo sukayi loosing contact, abokinsa be mance shi ba tunda har yana bawa dan sa labarin sa wanda har ya sa yaron tasowa zuwa neman sa. Dole ma ya riqe masa dan sa duk da hakan be wa Yaburra dadi ba.

End Of Chapter 🎊🎉

Hello people ya muke duka. Hope we're still enjoying the story.

Don't forget to bombard me with votes and comments. They keep me going😥😫

Continue Reading

You'll Also Like

143K 6.9K 28
Hooked onto drugs, no family, no guidance or sanity until she met HIM. Cover Creds: @Triceynexttdoor ❤️ -BLICKY.
301K 21.9K 26
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
1.7M 55.5K 75
Alexander, James and Skye were triplets. They were stolen from their family at the age of 4. The family searched for them day and night never giving...
54.4K 3K 22
If you knew what it felt like to have your entire life upended, that was exactly what Isabelle felt like right at this moment. From finding out you h...