Lawh-Al-Mahfouz

By TajawwalAlRuwh

2.9K 702 265

Ina hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da ku... More

01: Hadiza.
02: 1996
03: 1996
04: 1996
05: Ibrahim
06: 1996
07: 1996.
08: 1996.
09: Hadiza
10: Ibrahim
11: 1996.
13: 1996
14: Hadiza.
15:1996
16: 1996
17: 1996

12: 1996.

123 49 20
By TajawwalAlRuwh


Su Hadiza haka basuyi barci ba dan duk jikin ta ba inda be mata ciwo. Fusam na gefen ta in ba kuka ba ba abunda take yi. Ta rasa me zata yi ma Hadiza. Haka suka lallaba har zuwa wayewar gari tukun ta futa ta dinga gudu har ta isa gidan kakkanin ta. Nan ta zube dakin kishiyar mahaifiyar Haji Modu dan asalin mahaifiyar sa Allah ya mata rasuwa dan haka Baba Azumi ita suka sani a matsayin kakar su. Samun ta suka yi zaune tare da yayar mahaifiyar su da suka zo daga Yola suna karin safe suna hira. Zubewa tayi jikin Baba Azumi ta barke da kuka tana kiran sunan Hadiza. Nan da nan hankulan su suka tashi. Sai da hawayen ta suka tsakaita tukun ta musu bayanin komi dalla dalla tun kan ta gama Daadar su ta fara share hawaye tana wayyo mutuwa, in ba mutuwa ba da ya raba Maryama da yaranta da yaushe zasu shiga irin wannan halin. Nan da nan suka miqe daya daga cikin qannin Haji Modu da ke zaune a kusa da iyalin sa Baba Azumi ta aika aka kirawo mata ya dauke su a motar shi zuwa gidan Haji Modun. Koh da suka isa Haji Modu ya riga ya wuce kasuwa ita kuma Yaburra dama yana sa qafa ya futa itama ta fice wayon bin bokayen ta. Ta tafi gun bokan ta na cikin gari dan jin koh akwai taimakon da zai mata.

Kuka duka suka shiga yi ganin halin da Hadiza ke ciki ana gobe bikin ta amma ace an mata jina jina haka har an karya mata hannu. Nan da nan qanin Haji Modu ya dauke ta ya wuce asibiti da ita. Kan Baba Azumi tace ya wuce kasuwa ya kirawo mata Haji Modu. Gado aka ba Hadiza doctor ya hau kanta aka fara treating dinta. Ba a wani jima ba Haji Modu ya taho asibitin Baba Azumi ta rufe shi da masifa tana qorafi akan yadda yayi sake da lamarin marayun yaransa. Kare Yaburra Haji Modu ya shiga yi ya dinga bawa su Fusam laifi. Hakan ya kuma dagawa Baba Azumi hankali dan ta san Yaburra bata bar Haji Modu haka nan ba, babu uban da ke cikin hayyacin sa zai dinga ma yaran da ya haifa irin abubuwan nan musamman ma in aka yi la'akari da irin son da yike nuna musu a da.

Sai da ta gama jaraba tukunna tace masa sai yaje ya sama magabatan Ibrahim ya musu bayani koh za a daga bikin ne. Koh da yaje ya sama Haji Bukar ya fadi masa abunda ke wakana, sosai Haji Bukar ya jinjina maganar sannan yace In Shaa Allah zai magana da Ibrahim. Immediately ya sa aka yi aike zuwa inda Ibrahim ke bautar qasa dan a sanar da shi abunda ya faru kuma sannan a fada masa Haji Bukar din na son ganinsa. Gaba daya abunda yike yi ya tattara ya ije a gefe ya wuce asibitin duba Hadiza kan ya wuce gida. Ganin halin da Hadiza ke ciki ya sa Ibrahim kwalla, gaba daya Yaburra tayi disfiguring dinta, jikinta duk a kumbure, fuskar ba kyaun gani amma hakan be rage son da Ibrahim ke mata a ran sa sai ma qaruwa da son yayi, yaji ya mugun qosa ya aure ta ya dauke ta daga gidan ubanta. Hawayen da ya dinga kokarin riqewa sai da suka sauko da Fusam ta futo rakashi tana maida ma shi yadda abun ya faru. Haquri ya bata ya qarfafa mata kan ya ciro kudi ya miqa mata ya wuce yace mata da dare zai dawo.

Yaburra kuwa koh da taje wurin bokan cikin gari fatattako yayi yace bata zo wurin sa neman magani ba, tana so ya warware mata aikin da wani ya mata. Sai da ya kwashe mata albarka tas kan yace mata baya ma kaunar qara ganinta a gidanshi tunda ta raina aikinsa ta koma neman wani malamin. Daga nan gidan Talatu ta wuce amma tun daga bakin qofa da Talatu ta hango ta ta buya tace ma yaranta suce bata nan an mata rasuwa ta tafi can Bama garin mijinta ta'aziyya sai tayi sati guda kan ta dawo. Jiki a sanyaye Yaburra ta bar gidan Talatu. Futowa tayi daga inda ta boye tana fadin "Matsiyaciya! ya miki kyau. kullum sai dai nayi ta yawon raka ki gidan malamai kina sauke musu kudade ni koh sisin ki bana gani na ci. Kya ji da shi, ina zan iya komawa wurin malam ya hada dani".

Rasa abun yi ya sa ta wuce gidan kanwarta wadda suke yawon malaman tare dan jin nata shawaran. Nan da nan yar uwar nata ta shirya tace mata suje gidan malam Gobe da nisa ta san shi bazai rasa basu mafita ba. Koh da sukaje boka ya duba ya duba ya fada musu cewar gaskia bazai iya karya wannan asirin ba, hasalima babu wanda zai iya karya shi sai shi wanda yayi shi. Kuma tabbas kamar yadda ta bada sunan Hamza inda bataje anyi saurin karya asirin ba zata rasa shi kuma diyar ta Shatu na iya samun matsala sosai akan maganar aure. Kuka Yaburra ta fara tsakanin ta da Allah tana ta fadin ta gama yawo ta lalace. "Shikenan Hadiza ta gama dani. Uwar su ta riga ta musu asiri kan ta mutu, sun gama dani".

Kanwarta da ke gefen ta ke fadin "Dama wallahi fulanin nan asirin su ba qaramin ci yike ba. Shegun yara". Tare suka dawo nan gida suka shige uwar daka suna ta tufka da warwara. Gaba daya bata ma lura da rashin Fusam da Hadiza ba a gidan. Har yamma suna ciki, sai da suka yi shawaran kashe gari da sassafe zasu tafi Kukawa kawai duk inda gidan boka Zalimu yike su nema a san yadda za ayi. Suna cikin wannan shawaran aka yi sallama abokan Hamza an riqo shi an maido shi gida wai ya yanki jiki ya fadi a filin kwallo. Nan Yaburra tayi wiqi wiqi da ido dan ta tsorata, kada dai aikin boka ne ya fara bayyana. Kanwarta ta kwantar mata da hankali cewar jiri ce kawai ba wani abu bane. Madara ta kadawa Hamza ya sha kan ya shiga dakinsa ya kwanta ita kuma ta fito ta raka kanwarta kan ta shiga kitchen sai lokacin ta lura su Fusam basa gidan baa dora tukunya ba da rana bare na yamma.

Tana cikin zage zage Haji Modu ya shigo ya fada mata cewar an kwantar da Hadiza a asibiti kuma yana ganin auran da za a dora gobe za a daga zuwa sanda zata sama sauki. Murna sosai Yaburra ta shiga yi dan ta san wani opportunity ta samu, tunda za a daga bikin zata sama lokacin yin sabon asiri gangariya. This time bazata yi mistake ba.

Shikam Ibrahim koh da ya koma gida ya sama mahaifinsa ya masa bayanin komi sannan aka gabatar masa da shawarar Haji Modu be katse mahaifin nasa ba sai da ya gama magananshi ya tambaya opinion din Ibrahim tukun. Gyaran murya yayi kan ya fara magana yace ma mahaifin sa baya son a daga auran, gobe In Shaa Allah aje a dora auran sa da Hadiza ta cigaba da jinyar ta in ya so in ta sama sauki sai ta tare. Sosai Haji Bukar ya ji dadin hakan dan dama shima hakan ya so amma yace sai yaji daga Ibrahim din tukun. Bayanin komi yawa iyayen sa abun be musu dadi ba duk tausayin su Hadizan ya kama su suka ce aikam ya kamata a dora auran as soon as possible. Labarin kuma da ya ba iyayen sa yasa suma suke ganin ya kamata a dauke itama Fusam din daga gidan.

Bayan isha duka yan gidansu Ibrahim suka cika motoci biyu aka tafi asibiti duba Hadizan. Siyayya irin abubuwa da aka fi riqe ma marasa lafia suka yi aka tafi ma Hadiza da shi sannan sukaje suka musu kyautar kudi wanda da kyar aka yi da Daada kan ta karba kudin tayi musu godia. Suna zaune basu tafi ba Haji Modu ya shigo bayan ya gaisa da kowa Haji Bukar ya ja shi gefe ya fadi masa decision dinsu basu so a tsaya da zancen auran. Hakan yayiwa kowa dadi aka dinga ma juna fatan alkhairi.

Koh da Haji Modu ya koma gida Yaburra ta riga tayi barci. Barcin da bata samu tayi ba yan kwanakin ne ya mamaye ta, gashi kuma dama kashe gari tana da tashi da wuri dan zasu kama hanyar Kukawa dan haka Haji Modu be samu ya sanar da ita maganar daurin auran ba. Tana tashi kashe gari da wuri wuri ta shirya koh haduwa bata yi da Haji Modu ba bare ta tambaya izini ta kama ta fice daga gidan ta wuce gidan kanwarta suka kama hanyar Kukawa. Sun dan sha wahala kan suka gano gidan boka sai dai kuma a lokacin da suka gane gidan rana ta fara futowa dan azahar ta kusa kuma shi dama be ganin baqi in rana ta futo. Roqo suka dinga yi amma inaa. Iya alfarmar da ya musu shine da ya aiki dan sa yace yaji me ya kawo su ta ma yaron bayani ya shiga ya fada masa sannan ya aiko da yaron da ansa cewar ta koma gida kawai ba komi. Hakan ya kwantar ma Yaburra da hankali tunda har boka yace ba komi ta san ba komi din ne.

"Kin gani ba, ke kin cika damuwa. Qilan yayi hakan dan ya tsorata ki ne. Kin san suna haka" suka tafi da kanwarta suka cigaba da hirar su Yaburra na karyo goro tana jefawa baki dan hankalin ta ya gama kwanciya yanzu. Koh da ta shiga samun gidan tayi shuru ba mutane sai Shatu da ke daki kwance tana ta sharar kuka. Lokaci guda hankalin Yaburra ganin Shatu na kuka, qarasawa kusa da ita tayi tana fadin "Shatu na lafia?". Murya qasa qasa Shatu ta fada mata dazun nan aka dora auran Hadiza da Ibrahim Bukar Baba-Ganah. Wata iriyar ihu Yaburra ta saki tana jifa da dankwalin kanta.

"Ba tana asibiti ba" ta fadi hawaye na zubo mata Shatu ta kwashe komi ta fadi mata kan tace mata su Mairam suna can gidan taro. Tsakani da Allah Yaburra ta zauna tana taya diyar ta kuka kanwarta na rarrashin su tana fadin dallah kada su damu.

"Me aka yi aka yi Hadiza? Sai kace bokaye sun qare a garin Maiduguri". Kanwar Yaburra ke fadi "Sai mun hanata jin dadin auran. Wallahi zamu taso ta gaba da tsinannun qafafun ta zata baro auran. Kada ki damu Shatu na". Ta dinga rarrashin su.

Sabida baqin ciki da hassada Yaburra ta kasa leqa gidan da ake taron biki duk da ba wani babban taro aka yi ba sabida rashin lafiyar Hadizan wadda take asibiti kuma zata dan jima a asibitin dan har haqarqarin ta Yaburra suka karya mata ba hannu ba kawai. Ranar haka daga ita har Shatu kamar marasa lafia suka kasa komi, abincin ma da aka aiko musu daga gidan biki kasa ci suka yi dan hassada. Cikin takaici Yaburra tayi fatali da kwanukan abincin. Har kanwar Yaburra ta tafi suna daki zaune. Yaburra kamar wadda ta fara hauka sai suna zaune sai ta fasa ihu tana fadin "tabdi. Hmmm". Shatu ita dai tana ta kuka abunta dan sosai Ibrahim Bukar Baba-Ganah ya gama tafia da imanin ta gashi kuma a karshe ba ita ya aura ba, Hadiza da bata fi ta iya gayu da sa kaya masu kyau ba ita ya zaba.

Wani irin sauti me kama da gurnani da Yaburra ta fara ji ya sa ta futowa tsakar gida. A guje tayi hanyar dakin Hamza ta same shi a qasa yana ta amayar da jini. Ihu ta fasa tana kaicon ta shikam Hamza sai kuka yike yana ce mata kamar jikinsa na ci da wuta. Shatu ta shigo dakin da gudu itama ta fara ihun ta futa waje tana neman taimako. Nan da nan aka taimaka musu aka wuce da Hamza asibiti har zuwa lokacin be daina aman jinin da yike ba. Jikinsa sai wani irin rawa yike sai kace me ciwon farfadiya can kuma sai Hamza yayi tsit, kamar ya samu barci sai dai koh da suka qarasa asibiti da shi rai ya riga yayi halin sa, Allah ya yiwa Hamza rasuwa. Yaburra itama ta dandana rashin d'a. Barewa tayi a qasa ta dinga ihu tana kuka tana birgima a qasa mutane na kokarin riqe ta. Already an kira Haji Modu ya zo asibitin dan a dau gawar Hamza a tafi a fara shirin yi masa sutura.

End Of Chapter 🎉🎊

Wani hisabin tun a duniya ake yin sa🥁dama su Hausawa sun ce 'Alhaki...

Someone should complete it for me Abeg😂🤣

Gashi an dora auran Hadiza da Ibrahim kuma fa🕺

Na muku laifi ne? No votes no comments 😫😭 toh tsakani da Allah hutu zani😞😔

Continue Reading

You'll Also Like

146K 15.2K 18
[Sequel of 'MY SUBCONSCIOUS DESIRE'] Once again, a tale of desire and respect Once again, a tale of Rathod and family bond A multi-couple story. F...
261K 4.4K 62
This is an unofficial fan-made English translation of We are...คือเรารักกัน (We are... we are in love). Please do not re-translate to any other langu...
84.2K 3.5K 48
The MC may seem cringey in the first few chapters, but please give this story a chance. This story is an experiment, so I don't know how well it wil...
18.2K 1.3K 38
"You were magnificent, Satoru Gojo. I will never forget you for as long as I live." Satoru Gojo laid there, bisected in half, as if the universe itse...