Lawh-Al-Mahfouz

By TajawwalAlRuwh

2.6K 672 265

Ina hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da ku... More

01: Hadiza.
02: 1996
03: 1996
04: 1996
05: Ibrahim
06: 1996
07: 1996.
08: 1996.
09: Hadiza
10: Ibrahim
12: 1996.
13: 1996
14: Hadiza.
15:1996
16: 1996
17: 1996

11: 1996.

121 39 14
By TajawwalAlRuwh

Biki na saura kwana biyu ranar Yaburra ta tashi da sassafe ta futa. Koh sallan asubah ba a tada ba sanda ta futa daga gidanta ta sama qawarta a tashar mota inda suka kama hanyar Kukawa gun wani malami da aka musu kwatance, wanda shi kuma a nasa tsari baya ganin baqi sai da safe koh dare. Suna isa Yaburra ta isar ma boka da qudirorin ta, harda kukan ta dan ya tausaya mata ya taimaka mata ta kwatar ma diyar ta mijinta da kanwar ta ta satar mata. Nan da nan boka yace ta kwantar da hankali sannan ta dauka cewa buqatar ta tamkar an biya mata shine. Kudi ya caje ta masu yawan gaske ta sauke masa su kan ya fara mata aiki.

"Kinga wannan" ya fadi yana miqa mata wani magani da ya daure shi da igiyar doguwa "Karbi ki dora shi a qugun ki yanzun nan" jiki na bari Yaburra ta karba ta miqa ta dora shi a qugun ta kamar yadda ya fadi. "Ga wannan kuma ki saka a hammatanki". Ya miqa mata wani maganin. Karba tayi ta saka a cikin hammatar ta kamar yadda ya fadi sannan ya miqa mata wani qullin maganin a leda kan yace. "Ku tashi ku wuce. Kada ki kuskura kicewa kowa komi daga yanzu in kun futa nan da maganin a jikinki har ku kai gida. Lokacin zaki cire ki dake su daban daban su zama gari. Na qugun ki zaki barbada so uku a miya ki kira sunan diyar taki da sunan shi saurayin. Na hammatan ki kuma zaki barbada shi so daya tal amma a cikin abinci mara miya sai ki kira sunan dayar yarinyar so tara ki basu su ci. Da zarar ta ci wannan abinci saurayin zai ji kiran da kika masa bazai taba samun sukuni ba har sai ya zo anyi auran su". Dariya duka sukayi na jin dadin abunda boka ke fadi.

"Ita kuwa dayar yarinyar tana cin wannan abincin ke bama mutum ba, koh bunsuru bazai qara muku sallama bakin qofar gida neman ta ba".

"Wannan kuma". Ya fadi yana nuna dayan kullin da ya bata "Sai ranar da ita diyar taki zata hadu da shi saurayin sai ta zuba shi a ruwan wankan ta tayi wanka da shi amma ta saka baho ta tara ruwan wankan sai ayi masa dahuwa da shi ya ci. Me raba ta da shi sai mutuwa". Murmushi boka yayi musu da haqoran sa da suka dawo yellow sabida rashin kula.

Godiya su Yaburra suka fara zubawa boka suna ta sa masa albarka. Boka yayi dariya kan su tafi yace "Baiwar Allah kan ki tafi sai kin ije jingina". Ya fadi yana washe baki.

"Jingina kuma malam bayan kudin da na biya". Dariya yayi kan yace "Ehh sai an ijewa Aljana Naja'atu jingina dan yaranta ne zasuyi wannan aikin. In wani abun ya faru kikayi wani kuskure aikin be je daidai ba zasu qone in kuma suka qone sai sun sha jinin Biladama kan su warke dan haka kan ki bar nan sai kin bar mata jinginar mutum daya daga cikin zuri'a  da Allah ya baki sabida tsaro". Kallon juna Yaburra sukayi da qawarta, Yaburra ido na neman raina fata dan ita duk duniya ba abunda take so kamar yaranta. Har ta fara cewa qawar ta bazata iya ba qawar tayi maza tace da ita "Dallah can wawuya. Menene zai tafi ba daidai ba? Yau kika saba barbade ne Yaburra? Ai cewa yayi jingina sai in wani abu ya faru ne zaa buqaci jinin. Ki bada sunan Hamza kawai mu tafi".

"Hakane koh?". Yaburra kamar wawuya ta fadi qawar tace "Ehmana. Mu da muka san sirrin tsiya". Suka sha hannu kan suka juya ga boka ta fadi sunan d'an ta Hamza harma da sunan mahaifin sa. Kan azahar sun koma cikin gari sun isa gida. Gidan dama ba kowa sai yara dan dama baqin Yola a can gidan su Haji Modu aka sauke su dan Yaburra tace koh taron bikin bata so ayi mata a gida a bata mata gida haka nan Haji Modu ba yadda ya iya sai can gidan ya sauke baqi kuma ya maida taro.

Hayaniya sukaji tun kan su shiga cikin gida. Koh da suka shiga dambe suka ga ya kaure tsakanin Fusam da Shatu. Ana ta kokarin raba su an gagara Fusam ta danne Shatu a qasa tana ta kai mata naushi. Qawar Yaburra ce tayo kan su ta jawo Fusam ta jefar da ita gefe kan ta daga Shatu wadda ta ruga gun mahaifiyar su a guje tana kokarin mata bayanin abunda ya faru a harshen kanuri. Takaicin Shatu ya sa Yaburra ta kai mata wani irin mari wanda sai da ya razana masu tsaye a wurin. Masifa ta fara mata itama a harshen yare tana fada mata taji kunya da ta bari yarinya yar shekaru sha bakwai ta kai ta qasa tana bata kashi. Sai da ta gama da Shatu ta daka mata tsawa cewar ta wuce su shiga ciki tukun ta juya ta kalle Fusam da ke jikin Hadiza ta riqe ta tace musu "Toh karya tayi! Ba tsumman kuke sanye da shi ba. Kuna da suturan da ya wuce tsumma. Almajiran banza". Ta fadi kan ta juya sai dai kan ta wuce ciki kalaman Fusam suka tsayar da ita cak.

"Ehh! Munji muna sa tsumma. Amma ku ma a cikin tsumman kuka zo nan gidan, Baba ne ya maida ku mutane. Da kudin uban mu kuke saka kaya masu tsadan da kuke da su yanzu kuke cin abinci me kyau har kika sama bakin yi mana gori. Yar gidan matsiyata!". Duk yadda Hadiza ta dinga kokarin rufe ma Fusam baki tayi shuru ta qi sai da ta gayawa Yaburra abunda ke ran ta.

Yaburra ta kai minti guda tsaye a wurin maganar da Fusam ta fadi yayi shocking dinta. Qawarta ce ta fara yin kan Fusam Hadiza na kokarin kare ta tana basu haquri kan Yaburra ta qaraso sai dai koh da ta zo madadin ta kamo Fusam sai Hadiza ta finciko ta fara kifa mata mari ta sa qafa ta hankada ta qawarta ta cigaba da tattaka ta da qafa kan Yaburra ta dau icce ta dinga bugun ta da shi. Fusam na kuka tana kokarin jan Yaburra amma qawarta ta kamo ta ta riqe ta gam. Yaburra bata bar bugun Hadiza ba sai da ta lura kamar ta suma tukunna ta jefar da iccen ta wuce ciki tare da qawarta. Ihu Fusam ta dinga yi ta zo tana kokarin tayar da Hadiza amma shuru dan haka ta ruga waje tana ihun a kawo mata agaji. Gidan maqota ta shiga matar gidan ta sako gyale ta shigo ta sama Hadiza kwance a sume. Ruwa ta yayyafa mata tana kokarin farfado da ita amma shuru dan haka ta futa neman samari su taya ta kamo Hadiza a kai ta asibiti. Yaburra na jin haka ta futa ta saka ma qofar gidan su sakata kan ta kawo kwado ta saka ta tafi da mukullin tace babu wanda zai futa daga gidan. Koh da matar ta dawo haka suka dinga buga qofar shuru. Fusam na kuka tana roqon Yaburra cewar dan Allah ta buda qofar kada yar uwarta ta mutu.

"Dan darajar Allah Yaburra. Ni na miki laifi, ina ruwan Hadiza? Meyasa kuka mata duka?". Ta dinga kuka tana fadi. Koma tayi gefen Hadiza tana jijjiga ta tana kuka tana fadin "Dan Allah Hadiza ki tashi kada na rasa ki yadda na rasa Mama da Ali. Dan Allah bazan iya rayuwa ni daya ba". Ruwa ta kawo ta kuma yayyafawa Hadiza har sai da ta ga ta fara motsawa tukun. Hawaye kawai ke malala daga idanun Hadiza da sun kumbura. Fuskar ta yayi sumtun, jikinta duk jini. Duk yadda Fusam ta so taimaka mata Hadiza ta kasa miqewa ta kasa motsa hannunta da ya karye. Nan suka bare duka in ba kuka ba ba abunda suke yi. Su kam maqota da suka yi suka yi suka gaji sai daya daga cikin su ta saka danta matashi ya wuce can kasuwa ya kirawo Haji Modu dan dama su maqota sun san irin abubuwan da Yaburra kewa yaran.

Haji Modu naji hankalin sa ya tashi ya hau mota ya taho gida. Jin horn dinsa ya sa aka yi sauri aka buda gate ya shigo. Yaburra na jin sa ta futo tsakar gida inda Hadiza ke kwance tana hawaye tana wayyo Allah Hadiza sannu. Koh da ya shigo nan ya same ta tana ganinsa ta miqe ta ruga wurin sa a guje tana fadin "Haji na. Alhamdulillah da ka zo Haji na". Tun kan ya tambaya abunda ya faru ta ce "Ka ga Hadiza na neman ja mana abun kunya. Bayan tace mana ta aminta da wannan yaron Haji tun safe yau yarinyar nan ke mun tsiya iri iri a gida wai zata kashe kanta in muka mata aure da Ibrahim". Fusam na kuka take juya kan ta tama kasa cewa komi, itama Hadiza runtse idanu tayi tana hawaye. Duk yadda ta so magana bazata iya ba dan a lokacin ba qaramin nauyi bakin ta ya mata ba.

Wani irin kallo Haji Modu yayiwa su Hadiza. Kan yace komi Yaburra ta qara da "Dubi yadda tayiwa Shatu jina jina" tana jawo Shatu "Duk dan taje kamo ta zata shige rijiya wai zata kashe kan ta. Wannan wana irin bala'i ne. Kai co na ni Zaynaba". Ta fadi sai hawaye take "Haji na tun kan aje da nisa ka tsaida auran nan kawaii. Yarinyar nan bata so".

Wani irin kallo Haji Modu ya mata cike da bacin rai "In maida kai na dattijon banza!? Bayan na gama sanarwa abokai da yan uwa? Kuma sannan in ruguzan abotan da tun kan a san da zuwan ta duniya muke yi da Haji Bukar. Wallahi bata isa ba". Haji Modu ya fadi yana kallon Hadiza cike da bacin rai "Ashe mutuniyar banza ce ke ban sani ba". Baba ya fadi Fusam na kokarin fada masa qarya Yaburra ke yi ya daka mata tsawa.

"Rufe mun baki! Mahaifiyar taku ke qarya?". Ya fadi rai a bace "Mutanen banza. Duk kulawar da take nuna muku butulcin da zaku mata kenan. Ita ke muku qarya?". Ita dai Yaburra tana gefe tana kukan gulma tana haushin Haji be ji shawarar ta ba na fasa auran, da abubuwa sun zo mata da sauki. Amma ba komi tana da plan B dinta.

Jaraba Haji Modu ya dingawa yaransa, koh a jikinsa halin da Hadiza ke ciki ya dinga musu bala'i iri iri. Daga baya kan ya fice yace da su "Wallahi wallahi Hadiza in kika ga an fasa auran ki da Ibrahim ran asabar sai dai in shi din ne ya fasa. Amma koh mutuwa nayi ban yarda ma a daga auran ba bare a fasa shi". Yana fadin haka ya fice koh sauraron Fusam da ke roqon sa ya kai Hadiza asibiti be yi ba. Yaburra da yaranta suka fice daki suna shewa da gwalo. Suna shigewa ita da qawarta suka tafa hannu qawar na fadin "Aikuwa Ibrahim ya kusa fasa auran Hadiza". Yaburra tayi guda tana fadin "Ya kamata mu fara gyara Shatu fa dan ni in so samu ne ran asabar din kawaii a dora aur...". Yaburra bata gama magana ba ta tuno da warning inda boka ya mata. Salati ta fasa tana fadin "Na shiga uku. Talatu na shiga uku". Ta dora hannun ta a sama kanta kan ta miqe ta fara kai komo a tsakar dakin ta.

"Boka yace kada nayi magana da maganin a jikina. Na shiga uku Tala". Kuka Yaburra ta fara qawar ta miqe tana kokarin kwantar mata da hankali.

"Yanzu zan je na duba yara koh. Ki kwantar da hankalin ki gobe sai mu shirya mu koma wurin shi muji yadda zaa yi koh". Talatu na fadin haka ta fice daga gidan ta bar Yaburra cikin tashin hankali. Daren ranar kasa barci tayi, bata qara tsurewa ba sai da ta zo ciro maganin hammatar ta taga babu, wurin dukan Hadiza ya fadi gashi boka yace kada ta kuskura wani ya ga maganin. Tsakar gida ta koma tayi duban duniya bata gani ba. Kasa barci tayi kuma koh da gari ya waye shuru shuru bata ga Talatu ba gashi ita ta kai ta gidan bokan bata ganin da kanta zata iya zuwa garin kukawa har ta gane gidan bokan.

Ranar koh tsinke Yaburra ta riqe faduwa yike sabida tsananin yadda jikinta ke rawa. Ta rasa zaune ta rasa tsaye. Koh abinci ta kasa ci, cikinta ya tsure sai shiga bandaki take ta yi.


End Of Chapter 🎊🎉

Yaburra ta shiga tension fa🤣😂 Koh me ke shirin faruwa haka🤔

Continue Reading

You'll Also Like

59.3K 1.4K 40
standalone ~ mafia siblings series "You can't make me stay here! I will get an emancipation." I yell. Flashbacks of the gun in my hand, the almost-de...
KASHI By stuckinatale

General Fiction

413K 20.5K 42
"So, Mrs. Kashi Abhay Pratap Singh..chalte hai. Goodbye..". Saying this, he left her broken in this world of betrayal. ~~~~~~~~~~ Kashi, a simple gir...
499K 10.7K 51
Two girls are exchanged at birth and are given to the wrong mothers and after 13 years the truth comes out Rosabella Rossi is different from her sist...
PARIWAAR By

General Fiction

48.7K 5.4K 45
Arjun Shergill is a 28 years old, well renowned businessman, who has a big loving family and two kids. He is a caring and utmost loving man. This sto...