Lawh-Al-Mahfouz

By TajawwalAlRuwh

2.6K 672 265

Ina hanya? Ina mafita? Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta? Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da ku... More

01: Hadiza.
02: 1996
03: 1996
04: 1996
05: Ibrahim
06: 1996
08: 1996.
09: Hadiza
10: Ibrahim
11: 1996.
12: 1996.
13: 1996
14: Hadiza.
15:1996
16: 1996
17: 1996

07: 1996.

122 34 17
By TajawwalAlRuwh


Kashe gari Haji Bukar ya iske Baba a kasuwa da maganar da yayi da Ibrahim. "Magana dai tana nan sai dai an dan sama aqasi". Haji Bukar ya fara.

"Toooo... Aqasin mene fa abokina". Haji Modu ya tambaya.

"Yaro dai da yazo gida yaga wata yar wajen naka yace hankalinsa ya fi kwanciya da ita". Dariya duka suka kwashe da shi.

"Toh ai duk bata baci ba". Haji Modu ya fadi "Burin mu dama a qara karfin zumunci. Wannan bazata zama matsala ba ai abokina. Wacca yar nawan kenan ya gani dan ka san wanda suka taso din su uku ne akwai Hadiza akwai kuma kanwar ta Fusam".

"Ita Hadiza yike son a bashi izinin ya qara sanin ta, in an sama fahimtar juna sai mu sha biki".

"Ai wannan ba matsala bane, zan yi magana da iyalina a daren yau in na koma gida koh zuwa gobe in yana da lokaci yana iya zuwa su gaisa a dan fara sanin juna".

"Hakan ma yayi. Dama abunda ya kawo ni kenan, barin sauri na koma office kan mutane su fara zuwa nema na". A haka sukayi sallama da juna Haji Modu yana sai yaji daga Ibrahim din gobe, Haji Bukar yayi assuring abokinsa cewar zai turo sa kuma.

Sosai Ibrahim ya sama kansa da yin farin ciki da mahaifinsa ya kirasa da dare ya masa bayanin yadda sukayi da mahaifin Hadiza. "Gobe da yamma sai ka shirya kaje. Zasu saurari zuwanka". Godiya Ibrahim yayiwa mahaifinsa ya tashi ya wuce zuciyar sa cike fal da farin ciki.

Su kuma can a nasu gefen Yaburra ta daka tsalle sama ta duro tana buga hannu a qasa tana baza ayi haka ba. "Haji na ka taba ganin inda kanwa tayi aure ta bar yayarta. Takan me zai sa Hadiza tayi aure kafin Shatu kuma ma dai wanda asali aka ce yazo gun yayarta. Gaskia idan be son Shatu ina ganin gara an haqura da maganar, Kace musu Hadiza ba a shirya mata aure ba. Ai yarinya ce kwata kwata nawa take. Shekaru sha takwas fa!".

"Koh sati daya ba a yi ba nan kika gama cewa ta haqura da karatu in miji ya futo ayi aure, yanzu kuma kice in koma in ce musu aah bayan na riga na amincewa abokina. In zama mutumin banza a idanunsa? Aah kam Yaburra, yaro zai zo ganin Hadiza gobe in sun fahimci juna muka saka rana ayi musu aure. Ita kuma Shatu in Allah ya kawo rabon ta itama muyi mata auren ta tafi gidanta. Ai ba addini bane yace kanwa bazata iya aure kafin yaya ba kuma in ba naki ba Yaburra kan auran ya taso qilan itama Shatu wani ya futo mata sai a hada su biyu". Ita dai Yaburra duk bata gamsu da wannan bayanin ba, tana ganin ta ya Hadiza zata riga yar ta aure kuma auran ma a gidan hutu. Da me ta fi shatun ta da zai ce ita ya fi so. Hawayen takaici ta goge tace toh shikenan ba wai dan ta gamsu ba sai dan bata da yadda zata yi. Amma ta san dole ta sake komawa Benisheik gun malamin ta dan kamar asirin ta ya fara rage tasiri kan Haji Modu. Ta san dole ayi aiki a qara karkato mata da hankalin sa sannan a rusa wani zance na aure tsakanin Hadiza da Ibrahim Bukar Baba-Ganah. Ba yadda zata bari Hadiza taje aure gidan hutun nan ta bar nata diyar wadda gashi tana neman shiga shekara na ashirin da hudu ba manemi.

Baba da kansa yayi sallama qofar dakin su Hadiza dan mata bayanin komi. Bayan sun ansa ya shiga ya zauna qasa tare da su, Fusam ta taho da sauri ta kwanta kan qafar sa sai a lokacin Baba ya san da zazzabin da take yi. Damuwa sosai suka ga ya shiga, rabon da suka ga Baba ya shiga damuwa akan lamarin su har sun mance haka ya sa su jin dadin, suka fara having hope din cewar koma me Yaburra ta yi wa mahaifin su ya fara warwarewa. Haquri Baba ya ba Fusam yace da safe zai aiko mata da magani in ta sha ba sauki sai taje asibiti. Fusam ta so fadawa Baba abunda Yaburra ta mata amma Hadiza ta dinga mintsilin ta tana mata ido cewar kar ta fadi ta ja musu matsala. Hakan nan ta haqura tayi shuru bata ce masa komi ba. Amma ranar suka kasance cikin farin ciki ganin yadda Baba ya nuna damuwan sa da lamarin su. Dama indai so ne baza suce mahaifin su baya son su ba, aqasin da aka samu shine Haji Modu mutum ne mara zama sosai a gida kullum akan kan hanya neman halalin sa dan kula da iyalin sa sannan kuma mutum ne shi mara maida hankali sosai akan abubuwan da ke faruwa cikin gidan sa. A ganinsa matar sa tana riqe masa yaransa tsakanin ta da Allah, wannan saken da yayi kuma shi ya sa Yaburra ke samun damun musguna musu ga kuma asiri da kowa aka fi yarda da Yaburran tayi masa dan wasu abubuwan da yike yi da wuya ace da yina cikin cikakken hayyacin sa zai aikata. Tun zuwan ta gidan a amarya, Yaburra da ta lura da yadda ya dau son duniya ya dora kan yaranshi, da kuma yadda kullum be da maganar da ya wuci na matar shi da ta rasu, sannan kuma ta lura da cewar ba wai dan yana son ta ya aure ta ba sai dan yana buqatar mace a gidanshi wadda zata riqe masa gida dalilin auranta kenan, hakan ya sa Yaburra ta bazama bin malamai neman asirin da zata mallake Haji Modu da shi ya zama sai yadda ta so zaa yi a gidan.

Tatsuniya ya shiga basu suna nishadi suna dariya. Qarar dariyar su da Yaburra ke ji na qara hura mata wutar tsanar su a zuciyar ta. Sai da ya gama hirar da zai yi da su tukun ya juya zuwa ga Hadiza yace mata "Wurin ki nazo". Tattaro hankalin ta tayi ta maida attention dinta zuwa ga mahaifin ta. "Kinga baqon da yazo wajen yayarki jiya?". Juya masa kai tayi.

"Madallah" ya fadi ya dan tsaya jim kadan kan ya cigaba da magana "Ya zo ne jiya bisa umarni na da na mahaifinsa wanda ya kasance abokina, kun san abokina Haji Bukar da ke zuwa nan ai". Duka suka ansa da ehh. "Toh dan wurinsa ne kuma mun so hada shi da Yayar ku Shatu sai dai kuma jiya da yazo ya ganki Hadiza yace kin fi kwanciyar masa a rai". Mamaki sosai maganar ya ba ta, wai ita Hadizatul-Kubrah ta kwantawa wanda yazo gun Shatu a rai, toh ta ya?. Kwata kwata so nawa ya ganta da zai ce ta kwanta masa a rai?.

"Dan haka mun yi shawara da Ummanku, mun kuma yarda mu bashi dama yazo ku sama fahimtar juna. In kun daidai ta sai ayi muku aure koh". Ya fadi yana yar dariya ita kam Hadiza ta sunkuyar da kai sabida kunya da nauyin maganar da Baba ke mata. "Me kika ce?".

"Indai har ka aminta da shi Baba kuma ka yarda yazo bani da ta cewa na san bazaka mun zabin da zai cutar dani ba". Albarka Baba ya shiga sawa diyar nasa dama ya san bazata taba bashi kunya ba dan dama be taba sakawa Hadiza doka ba ta take koh ya sa ta yin abu taqi yi. Hadiza yarinya ce wadda samun irinsu yayi wuya, tana da jin maganar iyaye koh da kuwa abun be mata ba baza a taba gani a fuskar ta ba bare har tayi qorafi a kai. Hakan ya sa a kullum take fin cutuwa a hannun Yaburra unlike Fusam wadda wasu lokutan takan dan karban ma kanta 'yanci.

"Madallah, Allah yayi miki albarka ya kai rahamar sa kabarin mahaifiyar ki". Duka suka ansa da Aamin. Har ya miqe ya musu sai da safe zai wuce ya dawo ya miqa mata kudi cewar tayi amfani da su tayi girkin tarban baqon ta gobe. Godiya tayi ta amshi kudin shikuma ya fice daga dakin.

Takaici ya bi ya lullube Yaburra kashe gari, ga haushin abunda Haji Modu ya mata ga haushin ranar gaba daya ya qi futa ta samu ta koyawa Hadiza hankali. Hakanan ba yadda ta iya tana kallo suka shiga kitchen kamar yadda Baba ya umurta tayi shirin abunda zata tarbi baqon ta da shi. Da yamma yayi ta shirya tsaf cikin kayan ta masu dan kyau dan duk kayan ta sun kode sun mutu. Koh Baba yayi musu dinki Yaburra kwacewa take ta hana su. Gara ta ba yaran yan uwanta hakan ya sa su da kaya sai sallah sallah kuma sallar ma in an siya musu me tsada take komawa kasuwa ta sanjo musu da masu arha. Sauran kayan su masu dan kyau kuma yawanci wanda dangin mahaifiyar su ke aiko masu ne sabbi da kuma na kwance. Suma in Shatu taga wanda suka kyau a ciki dolen su su bata. Hasalima in an kawo kayan sai Yaburra ta deban ma Shatu wanda suka fi kyau kan ta basu sauran.

Bayan sallar maghreb Ibrahim ya iso aka sauke shi a parlorn da aka sauke shi ran jumu'ah. Shima wannan zuwan shi daya yayi ba tare da Hamidu ba. Baba ne ya futo suka gaisa yana ina zai iya ganeshi in ya ganshi a hanya duk ya girma ya sanja. Sai da suka dan taba hira kan Baba ya miqe yana fadin "Barin turo Hadizan". Ranar da yike ba diyar ta yazo gani ba Yaburra koh karan ta leqo su gaisa bata yi ba tana cikin daki da yar ta sai habaice habaice suke yi.

Muryar ta me sanyi ya fara ji kan idanunsu suka hadu tayi saurin sunkuyar da kan ta. A hankula ta qaraso cikin dakin ta zauna a qasa duk da ga kujerun zama nan, Ibrahim yana ankare da yadda take aiwatar da komi nata cikin nutsuwa. Gaishe shi tayi a ladabce ya ansa mata fuskar shi dauke da yar murmushi. Daga nan zama suka yi shuru, shi Ibrahim be san me zai ce mata ba dan be taba zuwa zance ba a rayuwar sa itama kuma Hadiza haka ta rasa na cewa sabida baa taba zuwa wurin ta da sunan zance ba. Namiji ma dai be taba zuwa gida neman ta ba. A hanya kuwa dama in koh an tsayar da ita bata tsayawa sauraron su take wucewar ta.

Da taga dai shurun nasu ba me qarewa bane sai ta miqe ta wuce kitchen ta dauko kayan abinci ta kawo masa Fusam ce ta taya da wannan aikin itama ta shigo suka gaisa, lokaci daya Ibrahim yaji Fusam din ta shiga ransa. Gabansa ta dire tray din ta fara serving dinsa sai a lokacin ya sake magana.

"Ki zuba kadan". Toh kawai tace ta cigaba da aikin gaban ta. Tana gama zuba abincin kan ta miqo masa ya zamo ya sauko qasa ya zauna kan carpet. Murmushi ta masa kan ta ije plate din a gabanshi, shima murmushin ta kufce masa har sai da ta lura da dimple dinsa na gefe daya. Replaying murmushin Hadiza ya dinga yi a mind dinsa. Ba karya yarinyar tana da kyau.

Sai da ya fara cin abincin ya dan fara sakin jiki yana dan jan ta hira, ya tambaye ta akan karatu, ya tambaye ta koh shekarun ta nawa and koh tana da wani plan for her future. Tun Hadiza na kunya kunya har ta dan fara sakin jiki suka dan yi magana. Da sun hada ido zai mata murmushi sai tayi saurin kau da kanta sabida kunya da ya gama cikata. Ya kai awa guda a gidan kan ya miqe yace ya kamata ya koma gida. "Amma ranar jumu'ah In Shaa Allah zan zo".

"Toh barin kira Baba kuyi sallama". Kan ya ansa ta ta fice zuwa parlorn Baba ta fada masa baqo zai yi halinsa, tasowa yayi yazo sukayi sallama da Ibrahim yana ce masa ya gaida Iyayen nasa.

"Hadiza sai a taka masa koh". Baba yace mata. Ba musu ta raka Ibrahim har inda yayi parking motar shi. Cike da fara'a ta masa sallama ta dawo cikin gida ta wuce ta kwashe kayan abincin ta wuce dakinsu da shi ta zubawa Fusam dan ranar qin yin girki da su Yaburra tayi. Cin abincin sukayi sosai sauran da ya rage suka boye dan sun san yadda Yaburra ke qule da Hadiza ba lallai ta basa su abinci ba. "Kar ki damu yan canji sun rage cikin kudin cefanen da Baba ya bani. In na samu dama zan qaro mana yan abubuwa da su". Hakan ya sa Fusam murna, yan kwanan nan baza suyi kwanan yunwa ba.

End of chapter 🎊🎉

Labarin ya fara sugar koh tukunna dai?😅

Continue Reading

You'll Also Like

494K 31.4K 41
Let's see how different personalities mends with each other to form a beautifull bond together. Where the Eldest is calm and cold, Second is aggress...
434K 15.7K 44
Vikram, a senior officer, prioritizes his duty above all else, much like his father, ACP Rajendra. He has three siblings: one is an officer, and the...
55.5K 2.9K 51
The Rajputs well known as the most powerful and devil's for the people who tries to messed up with them people got goosebumps just by listening to th...
27K 3K 9
[Sequel of 'MY SUBCONSCIOUS DESIRE'] Once again, a tale of desire and respect Once again, a tale of Rathod and family bond A multi-couple story. F...