RAWANIN TSIYA | ✔

Oleh fadeelarh1

59K 7.6K 4.7K

Halinta na girman kai, rashin kunya da wulaqanci su suka sanya ya tsane ta.. baya qaunar ya bude idanuwa ya g... Lebih Banyak

PROLOGUE
Chapter One
Chapter Two
Chapter Three
Chapter Four
Chapter Five
Chapter Six
Chapter Seven
Chapter Nine
Chapter Ten
Chapter Eleven
Chapter Twelve
Chapter Thirteen
Chapter Fourteen
Chapter Fifteen
Chapter Sixteen
Chapter Seventeen
Chapter Eighteen
Chapter Nineteen
Chapter Twenty
Chapter Twenty-One
Chapter Twenty-Two
Chapter Twenty-Three
Chapter Twenty-Four
Chapter Twenty-Five
Chapter Twenty-Six
Chapter Twenty-Seven
Chapter Twenty-Eight
Chapter Twenty-Nine
Chapter Thirty
Chapter Thirty-One
Chapter Thirty-Two
Chapter Thirty-Three
Chapter Thirty-Four
Chapter Thirty-Five
Chapter Thirty-Six
Chapter Thirty-Seven
Chapter Thirty-Eight
Chapter Thirty- Nine
Chapter Fourty
Chapter Fourty-One
Chapter Fourty-Two
Chapter Fourty-Three
Chapter Fourty-Four
Chapter Fourty- Five
EPILOGUE

Chapter Eight

893 149 65
Oleh fadeelarh1

~© 2021
RAWANIN TSIYA
BY FADEELARH1
All Rights Reserved

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

BUGAJE INDUSTRIES
KANO- CENTRAL

Zaune suke a conference room wuraren qarfe hudu da rabi na yamma.

Paapa, Hafeez, Hanifa da Unit heads na Comapny din..

Sadiq ne ya shigo yana fadin "sorry for keeping you waiting.. Clients din namu ne sai ahankali"

Hanifa wadda take zaune kusa da Paapa ce da danna mishi harara yayinda sauran heads din suke fadin "it's okay Sir"

Paapa ya nuna mishi kujera wadda take opposite ta Hanifa yace "ai ni na so kawai ayi forfeiting deal din tunda na ga murdaddun mutane ne.. were you able to convince them in the end???"

"Yes Sir.."

"Well done Son.."

"Thank you Sir" ya fada tare da zama kan kujera

Gyaran murya Paapa yayi sannan ya kalli Hanifa yace "toh Baby, tell us why you called for this emergency meeting"

Cike da mamaki na ga Sadiq ya kalli Paapa sannan ya kalli Hanifa wadda itama shi take kallo..

Wai dama ita ta kira meeting din? for what??

Hanifa wadda ta miqe tsaye ce tace "dama ina so in fadi muku cewar Sadiq is not who you all think he is.."

Gaba daya aka ce "what??"

Paapa wanda yake kallon Hanifa cike da mamaki yace "Baby me kike fadi haka??"

Gani nayi Sadiq yana ta shafa kanshi da hannuwan shi biyu non-stop.. da alama baya son inda zancen Hanifa yake zuwa.. He knows cewar whatever it is, it has to do with receipt na Bristol da ta gani a ofis dinshi dazu.

hmmmm...

"Yes Paapa.. Sadiq sata yake yi maka a kamfanin nan"

Tun kafin ta rufe baki kowa ya cika da mamaki yayinda na ji wasu suna fadin "subhanalillah" wasu kuma suna fadin "what??" yayinda saura suke ta qus-qus...

Sadiq dai a wannan karon duqar da kan shi kawai yayi cike da haushi da takaicin abinda Hanifa ta fada..

A ran shi kuwa fadi yake yi "this garl must be very stupid"

Paapa wanda shima ranshi yake a bace ne yace "Ke Hanifa lafiyar ki kuwa??? akan wane dalili zaki tara mu ki ci ma Sadiq fuska?? how can you accuse him of stealing?? shin kin san ko waye Sadiq kuwa??"

"ofcourse na sani Paapa, Abubakar Sadiq Bunza is a thief" ta fiddo copies da tayi na receipt din Bristol ta miqa ma Paapa sannan ta miqa ma Head of Marketting wanda yake zaune a gefen ta shima ya gani sannan yayi passing round.

"Sadiq ya saci kudi har N16.9m daga kamfanin nan ya biya kudin accomodation a Bristol Palace Hotel.. Shin salary dinshi har ya kai ya mallaki irin wannan kudaden?? what is he doing in a luxurious hotel anyway??? aaaah, No wonder ya karbi position din Finance Manager ya hana komai motsi.. sai da authorisation dinshi za'a iya fitar da kudi meanwhile yana kwasan kudi yana kashewa ba tare da an sani ba plus....."

"Shut up Hanifa..." Paapa ya dakatar da ita cikin fada yayinda na ga ta kalle shi cike da tsananin mamaki.

"Kina da hankali zaki zo cikin mutane kiyi ma Sadiq cin mutunci irin wannan?? dama kin fara aiki a kamfanin nan saboda ki sa mishi ido ne? da kika gano all these me ya hana ki zuwa wurina direct ki gaya mun?? do you have to come here and defame him??"

Tunda Paapa ya fara magana Hanifa ta daskare.. shin me Papa yake fadi?? asiri kenan Sadiq yayi mishi?? how can someone steal money from you sannan ga evidence nan and you still try to defend him??

"Toh yau zan fadi muku asali ko waye Sadiq" Paapa ya fada rai a bace.

Sadiq ne yayi saurin fadin "Please Sir, you don't have to.. mu bar maganan haka nan"

"No Son.. I told you tun farko muyi reconciling issue dinnan amma ka qi.. I think lokaci yayi da yakamata kowa ya san abinda yake faruwa"

Gani nayi Sadiq ya dafe kai yayinda yake ji kamar ya tashi ya falle Hanifa da mari..

Su kuwa Heads din sun natsu suna so su ji... Da alama dai su ma basu san komai game da Sadiq ba.. kawai sun wayi gari sun gan shi a matsayin ma'aikacin kamfanin..

Ni kuwa nace balle kuma ni da masu karatu... ah toh!!

"Abubakar Sadiq Bunza is the son of marigayi Abubakar Muhammad Bunza, Former Minister of petroleum na qasa mamallakin Bunza Oil & Gas wanda ya rasu shekaru kusan biyu da suka wuce"

Gaba daya dakin taron sai na ga kowa ya cika da mamaki yayinda ake ta kallon shi ana qus-qus.

Hafeez na ga ya sa ma Sadiq idanuwa shima cike da mamaki.. tabbas ya sani cewar Sadiq comes from a rich and sophisticated family domin kuwa yanayin rayuwar shi says it all.. toh amma bai taba sa ran cewar he is this stinking rich ba.. like he is such a simple, kind-hearted and down to earth kinda guy! Ta ya mutum yana da wannan matsayin a qasar nan zai zama this simple??

Hanifa ma zaro idanuwa tayi, qafafuwanta kuwa sun yi sanyi.. a sanyaye ta zauna kan kujerar ta yayinda ta sa ma Sadiq idanuwa..

Shi kuwa tunda ya dafe kai bai qara dagowa ba saboda takaici.

"da ni da mahaifin shi tare muka yi karatu a Stanford University a qasar America.. dukda a lokacin he was my senior, jinin mu ya hadu and we became best of friends. I studied business administration yayinda shi kuma ya karanci Petroleum Engineering. Bayan ya gama masters dinshi ne ExxonMobil suka bashi aiki and I am sure you all know that it's one of the best Oil & Gas producing Companies not just in America but in the world at large, Ya zauna a qasar America for over twenty years shi da iyalin shi... dukda ba qasa daya muke ba, abokantakar mu ta cigaba har lokacin da ya dawo Nigeria ya zo ya zama Minister of Petroleum na qasa.."

Girgiza kai na ga yayi sannan ya cigaba da fadin "Mahaifin Sadiq shine mamallakin Bunza Oil & Gas wanda nasan gaba dayan ku babu wanda bai san shi ba.. Kun sani cewar his business is beyond this country.. Ya rasu a sanadiyyar hatsarin mota da suka yi shi da matar shi (mahaifiyar Sadiq) akan hanyar su ta dawowa daga airport.."

Ya dan yi shiru tare da kallon Sadiq wanda kanshi yake a duqe har a lokacin sannan na ga ya dafa kafadarshi yace "Allah ya jiqan su da Rahama"

Gaba daya dakin taron suka amsa da "ameen"

"Me Sadiq yake yi a kamfanin nan?? na san dukkanin ku tambayar da kuke yi ma kanku kenan... idan bazaku manta ba wata goma da suka wuce Bugaje Industries yayi sinking wanda har ya kai mu ga shiga bankrupt.. dayawan ku kun sani cewar saboda haka ne aka kasa biyan salary dinku wanda har ya kai ga anyi downsizing ma'aikata.. We all saw it on the newspaper that I was about to sell the company in order to pay our debts until this gentleman showed up.."

Sadiq ya dago kai ya kalli Paapa yace "please Sir, is this necessary??"

"Yes it is son... na gaji da jin qananan maganganun da Baby take yi akan ka da yadda take wulaqanta ka... she needs to know cewar kamfanin nan was in a serious problem lokacin da take karatu a qasar waje and I was here struggling to send her pocket money, She needs to know cewar har ciwon zuciya na ya kusa zama ajali na if not for you that came to my rescue, she needs to know cewar kudaden da ake juyawa a kamfanin nan gaba daya da wadanda take spending naka ne... and yes yakamata ta sani cewar accusations dinta a kanka na ka saci kudi ka biya accomodation ba haka bane, she needs to know cewar you actually spent so much money to save her father's company..."

Gani nayi Sadiq ya kalli Heads na Unit din yace "gentlemen I guess this is where you should all take your leave.. it's close of business already so you can close for the day. See you on tuesday and enjoy your public holiday on Monday.. Happy Independence Day in advance and God bless Nigeria"

Gaba dayan su suka miqe cike da girmamawa suka yi musu sallama.. Duk sun fita suna ta mamakin labarin Sadiq da suka ji.. dukda basu ji qarashin labarin Paapa ba sun gane lallai Sadiq shi ya ceci kamfanin a lokacin da suka fada gwata.. instantly he earned more respect domin kuwa dayawan su sunyi losing aikin su a lokacin.. farfadowar da kamfanin tayi ne aka dawo da su.

Bayan sun fita ne Sadiq ya miqe ya dauki I-pad dinshi da wayoyin shi ya kalli Paapa yace "I am sorry Sir, I will have to take my leave too. Ka san har yanzu ina ta fama da project work dina gashi lokaci yana ta qurewa.."

Paapa wanda yayi murmushi yace "Okay Son.." ya miqe tsaye shima ya cigaba da fadin "..I am so sorry akan abinda Baby tayi maka.. I really am ashamed of everything"

Girgiza kai Sadiq yayi yace "it's okay Sir.. please dont be"

"but you never told me cewar ka kashe kudi dayawa haka wurin accommodation.. why didn't you take my offer na hayan gida da nace zan kama maka?"

"I am sorry sir.. for some reasons I prefer not to stay in a rented house"

"dukda haka Son, N16.9m kudade ne dayawa.. zaka iya siyan gida lafiyayye ma da shi ai"

Sadiq ya dan yi murmushi yace "haka ne Sir, but it's done already"

"toh shikenan Son, Allah yayi maka albarka"

"Ameen Sir, nagode"

Ya kalli Hafeez yace "take care Bro.."

Hafeez yana murmushi yace "You too.."

Ba tare da ya kalli Hanifa ba ya juya ya fita abinshi.

Hanifa wadda gaba daya tayi da-na-sanin dauko wannan zancen duk ta bi ta cika da kunya.. she wasn't even able to look Sadiq in the eye anymore har ya fita... Gaba daya confidence dinnan nata ya bace.

Bayan Sadiq ya tafi ne Paapa ya kalli Hafeez da Hanifa ya cigaba da fadin "...Sadiq ya ga newspaper din da aka yi publishing labarin Bugaje industries... Saboda damuwa da na shiga a lokacin har kwanciya asibiti nayi a dalilin ciwon zuciya na da ya tashi.. Immediately yayi contacting dina tare da dakatar da ni daga siyar da kamfanin nan, ya ji haushi sossai na yadda irin wannan matsalar ta same ni amma ban fadi mishi ba tunda we have always been in touch tun bayan rasuwar mahaifin shi.. In taqaice muku zance Sadiq shine ya biya dukkanin bashin da ake bin kamfanin nan sannan yayi investing huge amount of money in order to bring the company back to life.. ba wannan kawai yayi ba, shi ya gano ainihin wanda ya cuci kamfanin from our records. Saifullahi ya dade a kamfanin nan, shine Finance manager tun lokacin da mahaifi na yake raye and ganin cewar he was very good I decided to let him continue ko bayan rasuwar mahaifina. Amma dayake dan adam butulu ne ashe yana ta shuka mana tsiya yana diverting kudin kamfani to his pocket ba'a sani ba. Ko da muka yi discovering cewar shine tuni ya bace.. an neme shi sama da qasa ba'a gan shi ba. Sadiq shi ya sa aka dawo da duk wani wanda aka kora daga kamfanin nan.. ya gyara package na salary, bonus da compensation.. Sadiq shine ya dawo da martabar kamfanin nan har ya qaro mana manyan clients ba a nan qasar ba kawai har daga qasashen qetare. He introduced so many new and unique business strategies to this company and its thanks to him we are doing very well. A yanzu haka Sadiq yana managing both Bugaje industries and Bunza Oil & Gas at thesame time shiyasa lokutta da dama yakan yi tafiye-tafiye. Yana managing Bugaje Industries ne in order to set things straight for a while. we didn't know who to trust with the finance management na kamfanin, he spared me six months of his time to train Yahaya wanda shine most trusted staff a kamfanin nan.. munyi testing dinshi several times and he came out clean shiyasa aka cigaba da training dinshi kafin ke Hanifa da kai Hafeez ku kammala karatun ku kuyi Joining kamfanin nan, learn everything possible and take over from him together with Yahaya.."

Muryar Hanifa tana rawa tace "kenan Paapa kamfanin nan ba naka bane... nashi ne?"

Murmushi Paapa yayi yace "the company is still mine baby.. Sadiq ya taimaki kamfanin nan ne don Allah sannan don amintar da take tsakanina da mahaifin shi.. babu wani wurin da ya nuna cewar Sadiq yana da share cikin kudin kamfanin nan.. everything is still in my name.. aiki yake yi ma kamfanin nan amma baya daukar ko sisi a ciki a matsayin salary da makamantan su. His name is not even on our Payroll.. Da qyar ya amince aka yi centralizing account din kamfanin yadda ko ni idan zan kashe kudi sai nayi requesting.. a cewar shi it's my company and I can spend as much money as I want but i said No. Dayake ya san he is here for just 6months shiyasa ya haqura ya qyale ni tunda we all know cewar after the 6 months, he will be out and kamar yadda yace -for good"

Paapa ya saki ajiyar zuciya yace "kin ji kadan daga cikin irin abin alkhairin da Sadiq yayi mana don haka instead of wulaqanta shi da kike yi, he deserves some respect from you.. he saved our company"

Ya kalli agogon hannun shi yace "ku tashi mu tafi gida.. it's close of business already"

Daga nan ya miqe ya fita abin shi yayinda Hafeez ma ya miqe ya bi bayan shi not without smiling at a confused Hanifa.

Aikuwa suna fita na ga ta fashe da kuka.. tambayoyi kala-kala ta fara jero ma kanta...

Yanzu dama duk kudaden da take kashewa na Sadiq ne?? kenan kamfanin Paapa dukda babu a rubuce, partially nashi ne??? kenan duk gorin da take yi mishi kawai kallonta yake yi a matsayin fool?? wannan abun kunyan har ina??

Wani littafi da yake kan conference table din ta dauka ta jefar da qarfin gaske tare da fadin "I hate you Sadiq.. I hate you for how you make me feel right now"

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Ghen ghen ghen..
It's getting more and more interesting abi??

Toh mai karatu,
atleast mun dan ji ko waye Sadiq.. amma fa akwai saura don haka zamu jira mu ji nan gaba..

Ga Hanifa dai ta tara mutane don ta wulaqanta Sadiq ta kunyata shi sai kuma reshe ya juye da mujiya..

Yanzu da ta gano cewar dukiyar da take taqama da ita ta Sadiq ce ya zata yi???

Shin zata sauke girman kan nata ne ko kuwa?
At this point, all I can see is she has been defeated.. ko akwai wani abinda kuke tunani zata iya yi???

What next???

Kindly Vote and Comment!
Tell me how it's going and where you think it's going..!!

See y'all in the next chapter!!

One Love❤
Fadeelarh1

Lanjutkan Membaca

Kamu Akan Menyukai Ini

6.5K 597 47
Labari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.
16.2K 756 36
He was never looking for love. In fact, Yang Jeongin didn't really care for it at the time. He was too busy with the responsibilities that came with...
240K 10K 32
This is the rewritten (better!) version of Boys Will Be Boys DISCLAIMER: This book will contain foul language and general idiocy. I started writing t...
27.4K 2.2K 53
Matar shige da zabinsa.. Read and find out 💃🥰