UWA UWACE...

By BatulMamman17

267K 31.4K 7.2K

Uwa uwace... ku biyoni ku sha labari. More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
37
38
39
40
41
42
43
44
45
46
47
48
49

36

7.8K 746 299
By BatulMamman17

UWA UWACE...36

Batul Mamman💖


Addu'ar samun rahama da kyakkyawan makwanci ga iyayen 'yan uwa da muke tare. Sisters Teema (mahaifi), Hadiza Yauri (mahaifi) da Hashal (mahaifi da 'yan uwa maza uku). Allah Ya jikansu da rahama Yasa sun huta.


***
Da sallamar da ya san babu mai amsawa ya murda hannun kofar dakin. Fitila a kunne take da alama cikin sauri aka manta ta. Ga kaya watse a ko'ina. Riguna ne da wanduna harda kwalaban turare na jiki da na kaya. Salihi ya yi ajiyar zuciya ransa duk babu dadi. Da kunnuwansa yaji Mubashir yana waya da abokinsa suna shirya yadda zasu fita party shadayan dare. Bai yi masa magana ba domin yana son tabbatarwa kansa Mubashir din zai je ko kuwa. Fitar da ya yi niyya ya fasa ya zauna a gidan ba tare da sanin dan nasa ba.  Goma da rabi kuwa sai gashi ya fita daga gidan da sand'a a zatonsa babu kowa sai Ummule da ta dade da kwanciya.

Wata leda mai kyau Salihi ya gani a saman tebur din da Mubashir yake ajiye tarkacen makarantarsa. Ya dauka ya bude yaga sababbin takalma kala biyu da risit din sayayya. Abin da aka kashe na sayayyar ya girgiza shi. Bill ne na dubu casa'in da yan canji a sayayyar kaya. Shi dai bashi da kudin da zai iya bashi ya yi sayayya mai tsada haka. To a ina ya sami kudin?

A dakin yayi zaman jiransa har bacci ya kwashe. Goshin asuba ana tsaka da kiran sallah sai gashi ya shigo da sand'a. Rufe kofar yayi da sauri ya murda mukulli sannan ya kwantar da bayansa a jikinta yana ajiyar zuciyar tsira.

"Allah Ya soni Baba bai tashi ba"

"Ko kuma ni Ya soni da na kwana a dakinka ba."

Wani wawan juyi Mubashir ya yi a matukar razane yana kokarin murda mukullin kofar ya fita amma ya kasa. Ilahirin jikinsa babu inda baya ji yana rawa.

"Juyo ka dubeni Mubashir."

Maimakon ya juyo sai ya cigaba da kokarin fita har Salihin ya tadda shi inda ya juya masa baya. Hannunsa dake rike da mukullin ya kama ya rabasu da yatsun nasa. Sau daya ya murda su duka suka ji sautin budewar kofar. Mubashir dake faman gumi zuwa yanzu ya sake kama hannun kofa wannan karon. Shi fa burinsa ya bar gaban uban ko ta wane hali. Saboda shi da kansa ya san cewa bai taba yin laifi kwatankwacin wannan ba, shi yasa hankalinsa gabadaya ya tashi. Gani yake suna hada ido zai gano duk abubuwan da suka wakana a wurin party din.

"Irin wannan patin kuke kira till dawn ko?"

Shiru babu amsa daga Mubashir kuma har yanzu hannunsa yana jikin hannun kofar amma ya daina murdawa.

"Ban hanaka zuwa ba jiya bayan na gama jin shirinka da wani a waya."

Ras, ras, ras...haka gaban Mubashir ya cigaba da faduwa yana sauraron mahaifinsa a tsorace.

Salihi ya daure zuciyarsa iyakar dauriya saboda warin hayaki iri iri da yake ji a jikin Mubashir. Da wahala idan bai sha kayan maye ba ko tarkacen hayakin. Sassauta murya ya yi sai ka rantse kuka ne zai kwace masa a kowane lokaci.

"Tsakaninka da Allah Mubashir idan ka kwatanta abin da akayi a wurin da kaje da tarbiyar addini da ma maslahar zamantakewar dan Adam kana tunanin Annabin Rahama zai yi maraba da kai?"

Fada, mari, zagi, tsinuwa ko duka sune abubuwan da yasa rai dasu. Ko kadan bai yi zaton wadancan kalaman ba. Daga kai ya sami kansa da yi ya kalli babansa. Duk wani zafin kai na matasa sa'anninsa sai ya kufce masa. Rashin kunyar da aka koya masa koda zata baci irin yanzu yaji babu guda da zai iya. Allah SWT Yafi komai da kowa. Sunansa kadai da aka ambata gami da kwallar  disappointment a idanun mahaifinsa sun dagula masa lissafi. Ba yadda ya iya dole ya girgiza kai a matsayin amsa ga tambayar da aka yi masa. Ta yaya ma zai yaudari kansa yace inda yaje bai sabawa musulunci ba?

Kogin tunanin da ya fada da mabambantan yanayin dake bayyana a fuskarsa kowace dakika sun sanyaya ran Salihi. Alamu ne na cewa tarkonsa ya kama kada. Da shirinsa ya shigo dakin Mubashir domin yana fata yau ta zama rana ta farko kuma ta karshe da irin wannan fadan zai shiga tsakaninsa da dansa. Wayarsa ya kunna har yanzu suna tsaye a bakin kofar ya kunno abin da yake so ya nuna masa. Bidiyo ne wanda ke nuni da jama'a suna jam'in sallah. Bayan kamar sakan goma anyi kabbarar dagowa daga sujjada amma wani matashi a sahun gaba bai tashi ba. Koda aka sallame aka duba ashe rai yayi halinsa. Mutane suka yi ta kabbara da ambaton Innalillahi.

Mubashir bai san lokacin da ya soma kuka wiwi ba yana cewa,

"Baba kaga fa ya rasu"

"Kamar haka ne ajali ke riskar kowane bawa a lokacin da bai yi zato ba. Da ace naka lokacin yayi a jiya karshenta da sai dai yanzu a kirani inda kaje party ace inzo in karbi gawa" tsigar jikin Mubashir ta tashi da tunanin hakan kawai.

Salihi kuwa  dafa kafadarsa ya yi suna fuskantar juna.
"Abin tunani shi ne da ace kaine na cikin bidiyon nan da kila har nima na koma ga Allah ina bada labarin mutuwarka. Kai nayi imani 'yan bakinciki sai sun mutu saboda sun san cewa nayi babban rabo. Ranar lahira mune 'yan hura hanci saboda nayi dacen samun dan da Allah Yake so har ya karbe shi a sujjada. Haka zaka karbi cetonmu ka kaimu aljanna idan ayyukan alkhairinmu sunyi karanci" Sai da ya ja numfashi sannan ya dora da "da kuma ace ka mutu a wurin patin haka zanyi ta boye fuska kada idon sani su ganni. Kuma ina mai imani da cewa zan dawo gida nayi ta gillawa mutane karya. Ba zan taba yarda a san a inda ajali ya riskeka ba. Kaga anyi biyu babu. Ka tafi a banza ka bar ubanka zai tafi a hofi tunda ya zama makaryaci"

Jikinsa Mubashir ya fada yana kuka duka jiki na bari. Salihi ya dinga bubbuga masa baya da rarrashi. Sai da ya kula nutsuwa ta zo masa sannan ya yi masa tambayar da ta zo masa a ba zata.

"A ina ka sami kudin da kayi waccan soyayyar? "

***

Bacci mara dadi Uwani tayi sakamakon abubuwan da suka faru a gidan Munzali jiya. Da suka dawo gida tare da Asabe tayi mamaki sosai da Innayo bata tambayeta daga ina suke ko dalilin fitarsu tare ba. Kalmar 'kema 'yarki ce' da Munzali ya yi amfani da ita lokacin da yake cewa ba zai roketa rufin asirin Qibdiyya ba tayi mata karan tsaye a wuya. Makomar rayuwar yarinyar a gaba ya sanyata cikin damuwa. Shikenan rayuwarta ta baci tun yanzu? Sai kuma nata 'ya'yan da basu wani dameta ba suka fado mata. Anya ta ma san wani abu cikin rayuwarsu sama da dan abin da ba a rasawa? Irin abin da kowa ma zai sani muddin ya zauna dasu. Ita dai a matsayinta na uwa ba za ta dorar da komai ba. Babbar 'yarta Amira ta tuna. Yarinyar da har almajiri take sawa yi mata tsarki lokacin da take karama saboda bata son tashi daga kemis dinta. Sai ta bawa almajirinta mukullin gidanta ya tafi ya gyaro mata jiki su dawo. Kudi ne kawai a gabanta sannan bata son mai aiki mace don kada ta dauke hankalin mijinta. Ta biyun kuma Anisa a lokacin tata kuruciyar wani kanin Salihi da yake karatu ta sakarwa ragamarta. Sai da Salihin ya yi mata tatas lokacin da ya farga. Idan ma da mugun nufi kila har anyi an gama. Yaran basa kaiwa shekara biyar take barinsu su fara wanka. Saboda ita ce Uwani ina kika fito neman kudi, ina zaki neman kudi. Mubashir ne ma ya dan samu kulawa a matsayinsa na dan fari kafin ta gaji ta watsar. Duk wannan tunanin sai ya kare a inda take ganin cewa ai kudi take nema musu.

'Kudin da baki iya kashe musu' zuciyarta ta tuna mata.
'Kudin da suke neman salwanta a banza?'

Kamar an tsikareta haka ta tashi firgigit ta janyo wayarta. Nambar Habibu ta dannawa kira ta kara a kunne. Ta shiga har ta katse bai dauka ba. Ta cigaba da gwadawa missed calls sun kai goma zai gani amma  duka shiru. Lokaci ta kalla sai taji bari tayi masa uzuri kila bai tashi ba. Nan kuma ta canja akalar kiran ga Salihi. Kiran yaje gareshi lokacin da Mubashir cikin kuka ya fada masa da kudin wa yayi sayayya. Sam bata yi la'akari da cewa yanzu ake sallar asuba ba. Kudadenta kadai take tunani.

Yana amsa kiran Uwani ta hau fada kamar ta ari ba. Bakinta yana kumfa saboda tsabar bala'i amma ko jan numfashi ta gaza yi.

"Wallahi Salihi ka fadawa matarka ta dawo min da kudadena da sarkoki. Ba yau muke tare da kai ba na san baka taba daukar min komai ba idan baka dashi.  Ka fada mata ta dawo dasu idan ba haka ba police station zan kai maganar nan su kwatar min hakkina"

Ba speaker Salihi ya saka ba amma yadda Uwani take daga murya babu abin da Mubashir bai ji ba. Jikinsa sai ya sake yin sanyi. Kunyar mahaifinsa ta sake lullube shi. Hannu yasa ya karbi wayar ya kara a kunnensa.

"Umma ni na dauki kudin da sarka sai dai abin da ya rage babu yawa."

Yana gama magana ya mikawa Salihi wayar ya shige bandaki. To shi ma dai Salihin bai ce komai ba ya katse kiran ya fita yin alwala.

Uwani tafi minti biyar a zaune da waya a hannu. Ta san waye Salihi. Ta san abin da zai yi da wanda ba zai yi ba. Sanya Mubashir karbar laifin da ba nasa ba baya cikin abin da zata taba yarda zai yi. Idan ta kure zai iya karbar laifin amma ba dai yace wani ya karba ba.

'Mubashir?' ta dinga maimaita sunan a zuciyarta kamar yau ta fara ji.

"Kai! Ina! Sata?"

"Idan kin gama surutan ki tashi kiyi alwala ko ki rufe mana baki muyi sallah a nutse"

Juyawa tayi taga Innayo akan abin sallah. Bata san lokacin da ta shigo ba. Da azamarta ta tashi amma ta kasa fita yin alwalar. Kanta ya dauki mugun caji ne yana daf da bugawa. Yadda zuciyarta take zafi ko duka aka yi mata da itacen darbejiya ba za ta ji wannan radadin ba. Ayi maka gagarumar sata kuma ka gane dan cikinka ne ya aikata? Kamar sakarya haka ta dan tsaya galala da ta tuna yace abin da ya rage saura kadan. Tuntuni satar bata wani dameta ba saboda tasa ran Ummule ce. Ko ana tsiya tsiya sai ta fito da kudin domin kararta zata yi. A kwato mata kudinta sannan a nunawa Salihi kuskuren tunanin zai iya mata kishiya ya kwana lafiya. Jikinta, zuciyarta, ruhin dake rike da ranta da ma tunaninta a take suka koma na kankanuwar yarinyar dake tsananin bukatar mahaifiyarta. Ji tayi kamar an mata tsirara duk sanyin duniya ita yake duka. Uwa ce kadai zata fahimceta ta suturta ta. Aikin da take takama dashi karshenta sun rabu kenan, kudin da ya rage dan cikinta ya sace. Kudin Hajji kuma wani sashe na zuciyarta mai dan hankali ya dage akan ta nemi Habibu komai rintsi. Zargin da mijinta yake masa ya sanyata wasiwasi. A zatonta a dake ta soma magana, bata san tun a kalmar farko komai nata ya ruguje ba. 

"Kiji wani abin mamaki Innayo. Sata aka yi min ta kudade masu yawa da 'yan sarkokina  wai amma Mubashir yace shi ne. Ni kuwa me nayi masa da zai min sata irin wannan? Na wahala sosai ina hada kudin nan" sai hawaye sharrrr kamar famfo.

"Allah Ya kyauta. Matsa zan tayar da sallah."

Uwani ta girgiza kai ta dafa kafadun Innayo "baki gane ba Innayo. Ba labari nake baki ba ya faru ne a gaske. Kudin nan dashi nasa ran biyan KNUPDA su sakar min gidana. Bani da komai duk na kashe a gini da biyan Hajji. Wurin aikin ma sun dakatar dani saboda mugunta irin ta masu kudi."

Salima da Zara duk sun ji maganganun Uwani. Salima sai ta kasa hakuri ta shiga dakin. Da Innayo suka hada ido saboda ta juyawa Uwani baya tana share tata kwallar. Kwalla ce ba ta tausayin Uwani ba kadai harda ta kara ganin girman Allah. Soyayyar 'ya'yanta bata hanata hango cewa abin da ya sami Uwani harma da matsar bakinta ta tonawa kanta asiri duk yana cikin sakayyar Allah ba. Irin wannan lokacin take ta jiye mata. Halin rayuwa ya juyo wanda zaisa ta dawo gareta ba domin Allah ba.

Kai Salima ta girgiza mata don ta daina hawayen sannan ta da daga hannuwanta sama tana dariyar takaici.

"Allah Ya jikan Hasiya ba don ta mutu ba. Ta ce Allah Ya hadaki da babun da kike yawan kira watarana. Yau gashi kun gamu har ta fara saka ki kuka. To kadan ma kika gani wallahi" tayi kwafa da karfi "Baki ga komai ba. Uwa? Ke har kina tunanin kin ci bulus kenan akan hawayen Inn.."

"Salima ya isa!" Innayo ta fada tana riko hannunta.

Hannun ta janye ta cigaba da tsayuwa a gaban Uwani.

"Ki barni in sauke mata kafin Hasiya taji banyi komai ba tayi min Allah Ya isa." 

"Nace ya isa haka. Idan kuma kema shaidanun ne dake shi yasa ku ke neman hanani yin sallar asuba to Bisimillah"

Bayan tafiyar Salima har Innayo ta idar da sallah Uwani tana tsaye. Da gaske kanta ya rikice har bata iya gane mai yake faruwa a kusa da ita. Zuciyarta ta kasa rabe mata tsakanin sace kudin da wanda ya sata wanne yafi dimauta hankalinta. Kai a takaice ma duk wani labari mara dadi da ta samu game da dukiyarta sai yanzu ya yi zaman dirshan a kwanyarta kamar wadda ta farka daga magagin bacci.

*

Da Innayo ta idar da sallah ta zauna tana addu'o'inta amma hankalinta yana kan Uwani. Abin da take gani shimfide akan fuskarta yafi karfin damuwa sai dai a kira shi tashin hankali. Tausayinta ne ya tsirga mata. Sai kuma kamar wadda aka girgiza tayi kokarin kawar da tausayi daga zuciyarta. Uwani ce fa! 'Yar cikinta wadda ta wahaltawa amma ta dinga wulakanta ta. Kalmar wulakanci ita ta dace da duk abubuwan da ta dinga yi mata a baya. Ta tuna mugun ciwon hakorin da idan ya tashi sai ta kusa fitsari a jikinta. Amma Uwani ta rufe ido tace bata da kudi. Kuma taki kaita ganin likita don kada a alakantasu da juna. Duk wata soyayya da uwa zata yiwa da itama tana yiwa Uwani, amma hakan ba zai sa zuciyarta ta kankare mikin da ta bar mata ba. Ba za ta taba yi mata baki ba amma ta san cewa lokaci zai musu alkalanci. Tana so Uwani ta rarrabe tsakanin zare da abawa, me yiwuwa hakan zai sa tayi hankalin da ta jima tana yi mata fata. Da wannan ta mike domin tunaninta ya karkata zuwa ga autarta magamin kukanta. Hasiyatu mai zuciyar zinare. Hasiya takwarar Asiya matar da ta gagari shaidancin Fir'auna. Jarumar matar da ta zama majinginar Annabin Allah Musa AS. Ita Innayo taga ranar sanyawa yaro sunan magabatan kwarai. Ta kasance cikin farinciki domin kuwa da kyawun hali da addu'a gashi matsalolin gidan Hasiyan sun kau. Suna cikin ganiyar samun rufin asiri, ana saka rai da samun lafiyar Abbas, gashi zuciyar Ayaah ta karkato daga hudubar shaidan. Sannan uwa uba ga rabo Allah zai basu na zuri'a.

"Salima idan kin sallami 'yan makarantar (yan matan 'ya'yanta) nan ki zo ki tayani yiwa kanwarki dambu."

Zara sai tayi saurin tashi ta goya 'yarta "Kawo in yi mata Innayo."

"Yi zamanki kada ki kwasar mata sanyi sanyin safiyar nan"

Kwance goyon tayi ta kwantar da ita a kusa da Salima.
"Gata nan bari inje in taya Innayo aiki"

Bata jira cewarsu ba ta fice. Tana isa rumfar da suke amfani da ita a matsayin madafi ta dinga share kwallar dake bin idanuwanta. Ita Zara me zata ce da duniya banda NAGODE. Ta koyar da ita darasi mai wuyar fassara. Mijin da take takama dashi har take wulakanta mahaifiyarta dominsa ya juya mata baya. A zahiri ya nuna mata har yanzu yana sonta. Amma ko kusa yaki sab'awa mahaifiyarsa akanta. Yaki kawo mata 'ya'yanta sannan yaki sanyawa jaririyarta suna. Innayo ce ta tsaya mata har tayi masa magana akan haka. Wayarsu ta karshe da ita bayan ta gama sauraron bayaninsa abu daya ta fadawa Zaran wanda ya sakata zubar da kwalla.

"Biyayya yake yiwa mahaifiyarsa wadda komai rashin dadinta gareni da tawa 'yar dole muyi hakuri. Ita Uwa ta wuce tunanin duk mai tunani. Allah ne kadai Ya san fadi tashin da tayi dashi kafin ya kai yanzu. Idan na ce ya sab'a mata dominki ina ganin ban yi musu adalci ba. Ki mikawa Allah lamuranki ki zuba ido ki ga yadda Ubangiji Yake shigarwa bayinSa fadan da yafi karfinsu"

Da yammacin ranar Innayo tayi sadakar kosai tayi tawassuli dashi akan nemawa Zara zabin alkhairi.

Kukan da tayi a ranar ko digo bashi da nasaba da halin da take ciki da mijinta. Hawayen na nadama ne da dana-sani. Sai kuma tsantsar godiya ga Allah da Ya ara musu rayuwa ita da Innayo din. Dole ne tayi amfani da wannan damar ta daidaita da mahaifiyarta.

Bata ji isowar Innayo ba sai muryarta da taji tana cewa "kin tuna lokacin da ake cewa kin fi kowa iya girki a gidan nan? To kiyi mata farfesu da naman kazar can na firij, ni kuma zanyi dambun. Duk na wanda tafi ci to mai shi tafi iya girki sai a daina cika mana baki."

Zara ta juyo da murmushi mai hade da hawaye. Innayo din ma da guntuwar kwallarta domin kuwa ta dan jima tana kallonta.

Abin da ba kasafai mutanen da suke yi ba Zara tayi a lokacin. Rungume Innayo tayi tana cigaba da kukanta. A haka take magana da dusashshiyar muryar da ta cakude da kuka.

"Don Allah Innayo ki ce kin yafe min. Ba wai don na koma gidansu Maryam ba. Sai don kawai wannan kullutun hakkin naki da na daukarwa kaina ya sauka daga kirjina"

Ta dago kai tana mai nuni da kirjinta.
"Na sani sarai cewa ban kyauta ba amma kaina na yiwa ba ke ba. Don Allah ki yafe min."

Innayo ta dan tura baki duk ta rikice da kunya "to cikani don Allah kada a ganmu"

"Sai kin ce kin yafe"

"Zara zan ci kaniyarki fa. Cikani nace"

Zara ta cikata tana dariya kasa kasa.
"Baki ce komai ba."

Innayo ta numfasa tana kallonta tana girgiza kai tare da murmushi.
"Indai nice ki sani cewa hatta waccan yayar taku mai rangwamen tunani na dade da yafe mata. Babban burina dama bai wuce ku fahimci kuskurenku ba. Wallahi Zara ba kudinku nake so ba. Ku din da na haifa a halin maraici ba uwa ba uba ku nake so."

Kwalla ta sake taruwa a idon Zara. Innayo kuwa sai tayi gaba ta fara tattaro abubuwan da take bukata na girki. Yau dai gidan Hasiyan zata je da kanta ba aike ba.

Da suka gama Maimuna ce ta daukar mata kwandon da aka zuzzuba abincin. Kiranta tayi a waya tace ta nemi izinin mijinta yau sai gidan Hasiya. Zara da Saliman sun so zuwa ta hana. A cewarta bata son yawo kawai don suna gida. Wuraren shabiyu suka fita.

***

Awa guda da fitar Ayaah, Hasiya ta kula da 'yar pos dinta a inda ta durkusa ta zuba mata kunu. Dauka tayi ta bude taga 'yan kudaden da basu kai dari uku ba a ciki. Ta san ba za su wuce kudin motarta bane ta manta a gida. Idan kuwa haka ne in ba a kai mata ba karshenta ta dawo a kafa ko ta kare da rance. Wannan ma bai dameta ba sai da taga takardar da Ayaah ta nannade kudin WAEC dinta a ciki dubu sha biyar. Daren jiya Honorable ya bata saboda yau din ne rana ta karshe da zasu biya. Duk da tana jin jiri haka ta daddafa bango ta tashi tana kiran Murja da Ummita.

"Don Allah wata cikinku ta zo tabi Ayaah makaranta da pos dinta da ta manta."

Murja ta ce yanzu suka yi waya da wata mata zata zo kitso. Ummita na jin haka ta san ita ce mai zuwa. Hanzarin shiga wanka tayi ta fito ta shirya da sauri. Bata son lokacin break ya yi taje ta wahala wurin neman Ayaah cikin dalibai. Idan ta isa da wuri ajinsu kadai zata nema.

Ta gama shiri ta fito Honourable ya bata kudin adaidaita suka ji sallama. Direban Minister ne wato Abdulkarim.  A soro suka hadu da Honourable Habu ya mika masa wani envelop.

"Oga ya ce jiya likitan Abbas ya turo masa. Gwaje gwaje ne da ake son ku sake kai shi ayi yau dinnan. Idan sakamakon ya fito zasu gane aikin da za ayi dole sai an bude kan ko kuwa irin wanda ake soka na'ura ne tayi. Ya ce kuje kai tsaye ya biya kudin."

Honourable Habu ya ma rasa irin na'u'im godiyar da zai yi. Shi kuwa direba fadi yake ai bai ga komai ba cikin dimbin alkhairin wannan bawan Allah.

Direban na fita Ummita ta fito. Riga da siket ne a jikinta na atampa. Ta yane kanta da mayafin pashmina wanda ya sha jiki ba laifi. Sai dai a wanke yake ya kuma sha guga.

Ta hango mota a farkon layinsu ikayar inda mota ke tsayuwa amma bata yi mata kallo biyu ba ma. Kanta a kasa tana tafe hankalinta yana kan cimma titi da wuri ta sami abin hawa. Bayanta gefenta taji ana horn sai ta kara rabewa kusa da kwatar dake gefe, a zatonta ko ta tsaya akan hanyar motar ne. Sake horn aka yi ta kuma matsawa. Da aka yi na uku sai ta juya baya cike da tsiwa. Direban na bude kofa ta ce,

"Malam ko kwatar kake so na fada ne sannan ka sami hanyar wucewa?"

Ganin dan dattijon da ta gaisar dazu tare da mahaifinta sai kunya ta kama ta. Kasa tayi ta rissina mayafinta ya rufe mata gefen fuska ta sake gaishe shi tare da bashi hakuri. Murmushi ya yi don ko da ya dameta da horn din sai da Maigidansa ya ce kada ya firgita 'yar mutane.

"Shigo a rage miki hanya"

Girgiza kai tayi da sauri "Baba zai yi fada. Na gode"

Abdulkarim yaji abin da tace sai yaji ta burge shi. Idan bai yi kuskure ba ita ce Ummi babbar diyar Honourable. Bude bayan ya yi ya fito da kafarsa daya ya tsaya.

"Zo muje a fara sauke ki ina sauri ne."

Yawu ta hadiya da kyar da taga mai maganar. Sake yin kasa tayi zata gaishe shi ya ce,

"Shigo motar sai mu gaisa"

Ummita ta daburce "Allah Baba da Anti Hasiya sun hana"

Abdulkarim sai ya dauki waya ya kira Honourable Habu. Yana tsaye bai mayar da jikinsa ciki ba har wayar ta shiga. Gaisawa suka yi sannan ya kada baki ya ce,
"Tare muke da Mal. Amadu amma sai nace kada ya fada muka ina mota saboda bana son ka fito da safe haka. To yanzu mun hadu da Ummi nace ta shigo mu kaita inda zata je amma taki. A takaice dai neman izini na kira"

Honourable ya dan ji nauyi domin harga Allah baya son take dokarsa. Sai dai kuma yana kyautata zato ga Ministan. Ba wai kuma don sakar masa bakin aljihu da yayi yanzu ba.
Tuntuni bai taba saninsa da mugun hali ba. Duk da dadewarsu basu hadu ba, baya jin zai kira shi domin neman izinin cutar masa da 'ya.

Dariya ya yi ya ce "Tana karkashin ikonka babu ruwana."

Kallonta Abdulkarim ya yi tana kallon kasa ya ce "to sai ki bar kirgen kasar kizo mu tafi ya bayar da izini"

Ummita ta dan tsuke baki tana mamakin salon yadda ya yi mata magana kamar yaji haushin kin shigarta.

Daya barin ta zagaya zata shiga amma ga mamakinta sai taga kofar baya a bude. Direban ta kalla galala tana ware idanuwanta ta dan rage murya ta nuna kofar a tsorace.

"Wai nima bayan zan shiga?"

"Baki yarda da azkar dinki na safe ba kenan, ko baki yi bane kike wannan tsoro?"

Mamakin wannan Minista yana neman zauta ta. Shi da yake abokin babanta ya akayi yake yi mata magana kamar ta yiwa tsaranta laifi? Kuma ma da wane kunnen yaji abin da ta fada a hankali.

Dan murguden bakin da tayi duk akan idon Abdulkarim din. Dariyarsa ya gimtse don kuwa da gayya yake yi mata magana a haka. Baya son ta shigo a darare kamar tana tare da uba. Bashi da masaniyar ko anyi mata miji amma haka nan yake jin wani kwarin gwiwar tunkararta. Idan da mijin a hannu sai ya hakura. Bai san lokacin da dariya dai ta subuce masa bane a yayin da ya hangota ta kai hannu baki tayi tofi. Ba kunya tabi jikinta ta shafe ta kuma tofawa motar sannan ta shiga da kafar dama gami da Bisimilla da dan karfi. Har ta shiga yana dariya.

Mal. Amadu ma sai da ya dara. Ta zauna a dofane tana kallonsu. Dariyar masu kudi ma daban take, babu sauti mai karfi ko hargagi ta ayyana a ranta. Tambayar da ya yi mata ce ta maidota hankalinta

"Wai me da me kika karanta kika tofa mana ne?"

"Su Au'zu bi kalimatillahi...." Sai tayi azamar dora hannunta akan labbanta "ba daku nake ba. Tunawa nayi ban yi ba kafin na fito"

Hannu ya mika mata yana murmushi "to sai ki bani abin sadaka ladan yi miki tuni ko. Don da farko na zata mu kike tofewa don kada mu gudu dake."

Mayafi ta janyo abin da ya lura ko dabi'arta ne ta rufe rabin fuska tana dan murmushi.

"Wai ya sunanki ne?" Ya tambayeta saboda yana son sake jin muryarta.

"Ummita"

"Ummi-ta? Tawa kenan ko ta mutane da yawa?"

Hanjin cikinta taji ya yi wani juyin waina a tanda ta manta da kunya ta kalle shi cikin ido. Ba shiri ta sauke nata ta dukar da kai kamar mai shirin kwanciya akan cinyarta. Basu sake magana ba sai kwatancen da take yi har suka isa makarantar. Ga mamakinta dana  Mal. Amadu sai suka ji Abdulkarim yace a jirata.

Ta kusa minti ashirin a cikin makarantar kafin ta fito a guje tayi bakin titi. Shaf ta manta da wanda ya kawota kuma yake jiranta. Hannu bibbiyu tasa tana tsayar da adaidaita sahu. Abdulkarim na ganin yanayinta harda hawaye kwance a fuskarta ya fito da sauri.

"Ummita"

Ganinsa yasa kukan nata ya karu. Ta dawo da baya suka hadu domin shi din ma nufota ya yi. Kafin ma ya tambayeta ta fada masa abin da ke faruwa.

"Ba a ga Ayaah ba. Wai ta kusa awa biyu da fita fitsari har yanzu bata dawo ba. Kuma ga jakarta a ajin. Anje duka bandakunan da lab da ko ina bata nan" shirun sakan biyar tayi wani tunani yazo mata "ko dai aljanun bandakin sun dauketa?"

"Bama mutane ba aljanu Ummita?" Abdulkarim ya tambayeta yana kada kai don kada ta saka shi dariya a halin da ake ciki "Muje bandakin mu duba. Allah Yasa dai kin iya rukiyya sai na tsaya daga bayanki ko?"

Duk da tashin hankalin da suke ciki bai hanata fassara shi a ranta ba. 'Mutumin nan ba dai bakar magana ba'. Ita da kanta kuma ta hango wautarta ta ce,

"Ko masu satar mutane" ta dan tafa hannu irin na ta canka daidai "ai fa an ga kana zuwa gidanmu shi kenan za a fara kawo mana hari."

Abdulkarim bai ma san lokacin da ya ya balla mata harara ba.

"Ji mun yarinya. Ni kuma zaki dorawa laifin?"

"To ai ..."

Kai ya girgiza kawai ya ce ta zo su koma cikin makarantar. Suna tafe zuwa ofishin Principal ta daga waya zata kira gida ya hanata. Idan sun san aihinin me yake faruwa sai su fada. A haka hankula ne zasu tashi babu sanin madafa.

A ofishin Principal din banda ita akwai malamai biyar ana ta mayar da zance. Kowa ya shiga rudani har wasu suna cewa a tashi yaran kowa ya tafi kada a hada dasu. Yana shiga mutum uku suka gane ko waye. Da radar da bata buya ba suka sanar da ragowar. Nan da nan kuwa aka dinga raba idanu tsakaninsa da Ummita wadda ke biye dashi sau da kafa. Kallon ne ya tunzura shi kafin ma ya tambayi ya ake ciki ya fara da bayanin da ya baiwa Ummita dasu kansu mamaki.

"Wannan 'yar tsohon Ubangidana ce. Mun dade da rabuwa sai kwanakin nan Allah Ya sake hadamu. Yanzu ma daga gidansa nake kuma da izininsa muka taho nan."

Principal sai ta hau borin kunya "ranka ya dade me ya kawo wannan bayanin?"

Ya dage kafadu sannan ya ce "zuciya abar banza ce wani zubin. Yanzun nan sai ta shiga yiwa mutum sake sake ta sanya shi zargi a gurbin da bai dace ba."

Kowa kuma sai ya shiga gyara tsayuwa ana gyaran murya. Bai kulasu ba ya tambayi ba'asin sanda aka farga da batan Ayaah.

Bayanin da aka yiwa Ummita aka sake yi masa. Ya gyara zama tamkar a ofishinsa ya nuna wani Malami.

"Kirawo min Maigadinku"

"Su uku ne"

"Duka su biyoka sai ku saka wasu malamai a wurin saboda kada yaran su fice"

Masu gadi duk sun tsumu kowa ya rantse bai ga fitar wani bako ba ko na dalibar da ake magana a kai. Guda cikinsu yafi kowa dagewa aka rantsuwarsa. Gashi a shekaru alamu sun nuna ya girmi wadancan sosai. Yadda ya gabatar da kansa ya sanya Abdulkarim dora masa ayar tambaya. Dalilinsa kenan ma na daga waya yace zai kira Kwamishinan 'yan sanda domin a zo ayi bincike.

Hakuri aka soma bashi ya rufe ido yana fada akan sakacinsu da amanar 'ya'yan mutane.

"Idan sun zo zasu tafi da masu gadin a kullesu na a kalla sati koda an ganta kuwa. Wannan ai sakaci ne da rashin sanin aiki."

Dan dattijon maigadin yana jin haka ya soma muzurai. Rashin fara'a da ya gani ko digo a fuskar bakon nasu ta tsorata shi. Haka kawai da iyalinsa azo a kulle shi yana zaman zaman sa.  Hularsa ya cire ya dan firfita fuskarsa wadda ta soma tsatatsafo da gumi sannan ya rankwafo a gaban Minista.

"Yallabai ai ba ayi haka ba. Yarinya dai  babu wanda ya saceta. Duba min nan..." Ya zaro wata kodaddiyar naira dari biyu "ka gani wani matsiyacin Alhaji ne yazo da katuwar mota ya dauketa. Wannan abar ya iya bani don na barta ta tafi da alkawarin zata dawo kafin a tashi."

Dan ofishin Principal a take ya karade da sallallamin malamai mata da fadan malamai maza. Dattijo kamar a cinye shi danye. Principal ta ce barin aikinsa yazo domin bata san tun yaushe ake haka ba.

"Wallahi Hajiya yanzu ma tsautsayi ne. Wata yayi nisa nayi haka ne da tunanin zan dan samu na cefane. Ni yarinyar ko wayewa da fuskarta ma banyi ba sosai."

Ummita dai sai kuka kawai take yayinda Abdulkarim ya ce ba zai tafi ba har sai 'yan sanda sun zo.

***

Goshi Suhaib ya dinga murzawa ya rasa wane irin tunane ya kamata yayi. Ta ina zai fara nemanta? Baya son Munzali duk da ya san 'yar yayarsa ce amma yana gudun halin da zasu shiga kafin a ganta.

"Idan ta bishi kanta ta yiwa" ya furta a zafafe. Sai dai kuma can kasan zuciyarsa ya san cewa ba zai taba iya kawar da kai ba. Haka kawai yana zamansa yarinyar tayi masa karan tsaye a rayuwa. Banda mahaifiyarsa da kanne babu wata mace da ya taba damuwa da shirginta sai wannan yarinyar mai idanu a tsaye.

Mota ya shiga ya zauna ya bar abokan aikin Danliti da mayar da zance. Kusan minti goma ya yi kansa na kan sitiyari yana tunanin mafita kafin dabara tazo masa. Waya ya dauka ya kira nambar Ayaah yana ta addu'ar ta dauka.

***

Kokarin danne tsoro Ayaah take yi amma ya bayyana karara. Ta fara nadamar biyo shi tun kafin su bar layin makarantarsu amma ta rasa bakin cewa ya tsaya ta sauka. Banda ragon azanci ta yaya ma zata je gaishe da suruka da kayan makaranta? Idan matar mai hankali ce tana ganinta karshenta tayi mata fada.

"Wai ina zamu je ne naga muna yin bayan gari."

"Walalamb'e" Danliti ya bata amsa kai tsaye.

"Walame?" Ayaah ta tambaye shi da sauri don tana jin kamar bata ji me yace bane da kyau.

Danliti ya sake maimaitawa wannan karon harda dariyarsa.
"Kada ki damu Baby. Yanzu zaki gani da idanunki."

Tun daga Hotoro ta daina gane ina suke tafiya. Ta dai ga wani roundabout daga nan suka yi hagu gefen wani gidan mai. Jikinta ya yi sanyi kalau kamar mara lafiya. Gashi yau gabadaya tsoronsa ma take ji. Suna zuwa kofar gidan zata gudu kawai. Don kada ya gane ta kakalo murmushin dole. Ana haka 'yar wayarta ta soma vibrating. Bata san nambar ba amma da sauri ta dauka. Don ta san yanzu da wuya idan ba a fara nemanta ba.

Danliti bai damu da wayar da zata amsa ba saboda ya gama yanke hukuncin cewa ko me zai faru yau sai ya kusanceta. Ikon a hannunsa yake kamar yadda ya fadawa kansa.

Da sallama ta dauki wayar, muryarta tana dan rawa.

Suhaib yana jin yanayinta wani abu ya taso masa a kokon rai.

"Ayaah kina tare da Danliti? Zaki iya magana sosai?"

"Eh amma ba zan iya ba" ta amsa masa tana kokarin kin kallon inda Danliti yake.

"Kin gane ni ko?"

"Eh"

"Good, ki saurareni da kyau kuma kada kiyi abin da zai gano ki. Mutumin da ya daukeki wallahi makanike ne yanzu ma ina garejinsu. Mutumin banza ne.  Ya fadawa abokin aikinsa zai zo daukarki ya kaiki inda zai..." Sai ya kasa karasawa.

Ayaah ta sake tsorata sosai jikinta ya soma rawa. Yawu ta hadiya da kyar a hankali ta ce "ba na fada miki mumminsa zai kaini na gaisar ba? Yanzu muna hanyar gidansu ne. Kar ki bari a gane bana aji kinji"

Ba karamin burgeshi yaji tayi ba. Ga tsoron yana iya rarrabewa cikin zancenta amma a haka ta fada masa abin da ya dace ya sani.

"Na fahimta. Ki kokarta ki turo min address din inda kuke ta sms saboda kada ya gane."

"In sha Allahu. Ni dai ki dauko min jakata ki jirani a bakin gate ko an tashi."

Danliti ya dan kalleta ya murmusa yana kiran "Baby na kenan! Ki gama wayar nan ki fada min kalaman da zasu sanyaya min rai"

"Kiji min dan iska..."

Saboda yanayin da take ciki murmushi kadai ta iya yi amma duk da haka Suhaib yaji sautinsa. Shi kuwa gogan ya zata dashi take.

"Dariya ma na baki?" Suhaib ya ce yana shan kunu

"A'a. Don Allah ni dai kiyi sauri. Zan turo miki nambar registration din tawa ki cike min form din."

Kafin ya ajiye wayar ya sami kansa da cewa "Ki kula da mutumcinki Ayaah. Kada ki yarda ya taba min jikinki."

Shi da ya fada ya yi mamakin karfin halinsa sai dai kuma yanzu ba lokacin hakan bane. Haduwar kwana daya ce amma zuciyarsa taki bashi hadin kan yakiceta daga tunaninsa.

Ita ma a nata bangaren wani irin nauyi kalamansa suka yi mata. Haka nan ta cije ta sake yanko karya ta fadawa Danliti bayan ta kashe wayar.
"Wai nambarmu ta NECO ake bukata daga ofishin Principal. Shi ne kawata ta kira don kada a neme ni."

Mutumin da ko sakandiren bai gama ba sam bai fahimci karyar ba. Hankalinsa bai bashi yasa ido akan abin da take rubutawa ba. Iya abin da ta gane a hanyar da suka bi da sunan unguwar da ya fada wanda bata ma rike daidai ba ta rubuta.

Suhaib ya koma wurin sauran makaniken ya karanta musu text dinta.

"Da mamaki dai amma wannan kwatancen ya dace da hanyar gidansa. A can unguwar Walalamb'e yake da zama"

"Muje ka nuna min"

Mutum uku ne suka shiga motar. Harda shugabansu cikon na hudu. Rayukansu duka sun baci akan abin da yake yi. Ga daukar abin hawan masu kawo gyara sannan kuma ya dauki mace yana shirin bata mata rayuwa.

*
Bangaren inda suka nufa wawakeken filin unguwa ne da gidaje tsilli-tsilli basu matse juna ba. Gidajen wurin kaf babu bene ma a iya ganinta. Duk sunfi kama da gidajen gargajiya. A takaice dai unguwa ce ta masu karamin karfi sosai. Cikin Ayaah ya sake kullewa da mugun tsoro a lokacin da faka motar a kofar wani dan tsakon gida.

"Ina ne nan?" Ta dan dake ta tambaye shi.

"Gidan mai ban ruwan fulawa a gidan Mummy. Kiyi hakuri zan shiga in duba shi ne yanzu na fito"

Tunda dai bai kirata ba sai taji dama dama a ranta. Fita ya yi ya rufeta a cikin motar ya shige gidansa da sauri. Mukullin dakin Rabilu abokinsa da ya bashi aro tun jiya ya manta a aljihu yazo dauka. Sun yi da Rabilun can dakinsa dake kusa da unguwarsu Ayaah zai kaita. Kuma idan shi Danliti ya gama biyan bukatarsa da ita shi ma mai dakin zai yi.

Kafin ya fito ta sake turawa Suhaib wani sakon.

(Ya kulleni a mota wai wani wurin zamu je ba inda na turo maka ba. Don Allah kayi sauri wallahi tsoro nake ji.)

(Ki kula da duk inda kuke bi ki sake turo min. Please take care of yourself.)

Amsar ta karanta ta gyada kai kamar yana kallonta.

A ciki kuma matar Danliti da murna ta tashi tana yi masa maraba ya doka wani uban tsaki da ya saka ta ja da baya. Naira dari biyu irin wadda ya bawa maigadin makarantarsu Ayaah ya jefa mata a wulakance.

"Gashi nan na san abin da kike yiwa kenan. Ke dai a baki kudi ku ci abinci da 'ya'yanki."

Hawaye taji ya taho mata tayi saurin tarewa da hannunta. Kudin ta duka ta dauka ta ce,

"An gode. Allah amfana"

Tsaki ya sake yi mata ya shige daki yana neman wandon da ya cire jiya. Ita kuma mayafinta ta zara a kan igiya. Ta goya karamar ta rike hannun mai wayon ta fice tana ce masa zata karbo kayan miya.

"Na ajiye mota a waje ta mutane. Kada ki kuskura kije kusa da ita. Ke dawo idan na tafi sai ki fita."

Sarai ta ji abin da yace amma tayi biris ta fita soro ta leka. Abin da tayi tsammani ta samu. Yarinya ce mai fuskar kamala a cikin motar. Takaicin halinsa ya turnuketa. Babu wani bakon abu a halayyarsa da bata sani ba. Bakon abin da shi bai sani ba tare da ita shi ne a yau ta gama hadiyar bakincikinsa in Allah Ya so. Komawa tayi cikin gidan suka yi kicibis a bakin kofa. Rai a bala'in bace ya dinga yi mata masifa.

"Me yasa kika fita? Da kika fitan me yasa kika dawo?"

Hakuri tayi ta bashi tana cewa taji kamar ya kirata ne. Sai da ya gama fadan ya koma dakin yana cilli da kaya.

"Me kake nema ne in tayaka?"

"Mukullin dakin Rabilu nake nema wanda na bari a cikin wando"

Kai ta jinjina tana tunanin wato can zai je da yarinyar. Dauko mukullin da ta gani da tana ninke wandon tayi ta mika masa. Haka ya warce shi a hannunta ya fita da gargadin ta jira sai ya tafi.

*
Sakon da Ayaah ta turawa Suhaib ya riske shi ne suna kurkusa da unguwarsu Danliti. Tun fitowarsu har yanzu bai fasa ambaton Allah cikin addu'a da fatan nasara ba. Da ya gama tura mata amsa ya sanar da abokan tafiyar tasa abin da ta ce. Guda a cikinsu sai ya ce su karasa gidan nasa. Kila suyi sa'ar samunsa ko su tambayi matarsa ina yake.

"Muna ma iya cewa ta kira shi ta ce anzo nemansa akan motar da ya dauka da 'yan sanda. Na san da wuya idan bai tsorata ba"

Shawararsa ta sami karbuwa suka karasa. Da yake Allah Maji roko ne sai gashi sun sami fiye da abin da suka saka rai.

Wanda ya bada shawarar ne ya yi sallama a kofar gidan. Ta fito da yaranta da 'yar ghana must-go wadda ta zubawa kaya. Ta ganinsa ta dan saki fuska suka gaisa. Ba tare da bata lokaci ba ya ce,

"Idan kin san inda Danliti yake ki fada min don Allah. Daga gyaran mota ya dauko motar wani mutum. Yanzu haka yace 'yan sanda zai kawo mana."

Sauke jakarta tayi daga dakalin kofar gidan tana cewa "ba zan fada ba don laifin nasa ya kara yawa a dukkan dakikar da 'yan sandan suka wahala nemansa. Sannan idan kun hadu ka fada masa ya aiko min da takardata."

A rikice ya ce "kiyi hakuri ki taimaka mana"

Su Suhaib suka firfito ta dubesu ta kau da kai.

Suhaib din ne ya tako gabanta ya dubeta a mutumce ya ce "don Allah ki taimakeni kada ya keta haddin 'yar mutane. Har makaranta ya bita ya daukota yana shirin bata mata rayuwa."

Da sauri ta dago kai tana mai tono yarinyar da ta gani.

"Bari na shiga adaidaita sahu ku biyoni in kaiku inda nake tunanin zai kaita"

Suhaib ya ce na gaban ya koma baya ita da yaranta su zauna. Su da suke makanikai basu fitar da warin jiki irin nata da na yaran ba. A haka kuma ba karamin kokari take ba. Duk albashin Danliti a cin banza da hofi sai yan mata yake karewa. Sabulun wanka da wanki sai tayi kamar ta ari baki. Ruwa ma iya na girki kadai yake saya mata. A haka take cancanawa suyi wanka bayan kwana bibbiyu ko uku. Ga zafin gari da ake fama.

Kai kawai Suhaib ya dinga kadawa cikin takaicin wai wannan matar aurece. Mace da ake son a mutunta amma ita ce nata mijin har yake da guts din zuwa kofar gidansa da yarinyar da zai nema ta gani. Kodayake ba kansa farau ba da ya tuna nasa uban. Neman tsari ya dinga yi akan fadawa wannan kaba'ira ta zina har suka kai kofar dakin Rabilu. Ya kuwa laluba aljihunsa ya bawa yaran dubu goma ya ce ga kudin mota. Bata cuci kanta ba ta karba tana ta godiya.

***

Da kuka Ummita ta shiga gida duk da irin gargadin da Abdulkarim ya yi mata akan tayarwa iyayenta hankali. Kasa daurewa tayi tana shiga ta fada kan Innayo tana kuka. Hasiya ta saki cokalin dambun da take ci ta tashi da sauri tana tambayarta me ya faru.

Maimuna da Innayo basu dade da shigowa gidan ba. Kuma hirar dadewar Ummita da rashin samunta a waya ake yi sai gata ta fado.

"Ki yi min magana Ummita me ya same ki?" Hasiya ta sake tambayarta tana hawaye tun kafin taji me ya faru.

"Anti an sace Ayaah. Har makaranta wani yazo ya bawa maigadinsu kudi ya tafi da ita"

Hankalinsu ashe bai tashi da kukan Ummita ba sai yanzu da tayi magana. Kan kace meye wannan gidan ya rude da kukan mata. Murja, Hasiya, Ummita da Maimuna babu mai rarrashin wani. Innayo ce tayi ta maza ta daure tana basu hakuri. Suna kukan suka ji sallamar Honourable da yaron da ya taya shi rike Abbas suka je aka yi test. Kukansu ya saka shi shigowa tun kafin su amsa. A nan yaji labari mara dadi. Gidan ya sake cika da Larai (mahaifiyar A'i) dasu Hasina kannenta. Sun zo duba Abbas ne saboda Honourable ya fada musu za ayi masa aiki. Wannan ya sake dagula lamarin domin fada ne kuma yaso kacamewa.

Larai tana kuka ta ce "Hasiya naji labarin kina da ciki ai. Wato kafin ki haifa zaki fara daidaita 'ya'yan marigayiya saboda kina tunanin samun gado tunda maigidan ya soma  farfadowa."

Hasiya bata iya cewa komai ba da yayyenta suka hada baki ana ta fada mata maganganu. Innayo ta hana Maimuna da ma Murja da Ummita din mayar da martani. Batan Ayaah ne a gabansu ba zantuka marasa amfani a gaban suruki ba. Maigidan kansa  kasa tsawatarwa ya yi saboda yawunsu da kuma damuwar da yake ciki. Tunda ya ce suyi shiru suka ki sai kawai ya fita zai tafi makarantar. 'Yar nutsuwar da ya samu ma ta biyo bayan kiransa da Abdulkarim ya yi suka shigo gidan tare. Shi ya fada masa case na hannun 'yan sanda ana bincike. Ko sau daya babu wanda ya yi tunanin kiran wayarta saboda gargadi da jan kunnen da Hasiya take mata akan zuwa da ita makaranta. Duk sun zata wayar tana gida saboda haka babu amfanin kiran.

***

"Shigo mana Baby" Danliti ya ce da Ayaah bayan ya zura mukulli ya bude dakin shagon Rabilu.

Rainin wayon nasa ne ya bata mamaki ta ce "ban gane in shiga ba? Ya zaka ce min zan je gaishe da mahaifiyarka ka kawoni nan?"

Hagu da dama ya dan waiga bai ga idon kowa a kansu ba kawai ya fizgota cikin dakin ya rufe kofa. Budar bakinta zata yi ihu ta rufe sakamakon tozali da hoton tsohon saurayinta Rabeel (Rabilun Danliti).

Cikin kidima ta ce "Dani dama ka san Rabeel?"

Danliti ya kwashe da wata irin dariya harda tafa hannuwa kamar biri a hannun mai wasa dashi.

"Idan ya shigo anjima zai yi miki bayanin da zaki gamsu. Ni nan cire hijabi zaki yi mu farantawa juna rai."

Kallonsa tayi taji dukkan wata tsana ta duniya ta tattara a kansa. Ga haushin rashin hankalinta da ta bari ya yi wasa da tunaninta.

"Ashe abin da aka fada min gaskiya ne duk da dama bana tunanin mai fadar zai yi min karya."

Danliti bai wani damu da maganarta ba ya kama kayan aron jikinsa ya soma cirewa. Ayaah ta juya ta fara dukan kofa da ihu taji ya daka mata tsawa.

"Juyo nan ki gani"

Ta juya a fusace ai kuwa tayi tozali da kakkaifar wukar da yake nuna mata. Shi ma cikin fada ya ce,

"Ki kama bakinki ko idan na gama wallahi in kashe ki in kashe banza."

Durkusawa tayi a wurin ta fashe da kuka "me nayi maka da ka zabi cutar dani?"

Kishingida ya yi akan katifar daga shi sai singileti da gajeren wando masu dan banzan datti yana wasa da tsinin wukar ya zuba mata idanu. Sau daya ta kalle shi taji amai ya taso mata. Wani uban gashi ne a hammatarsa wanda da gani har kitso zai yi.

"Bana son munafunci bayan na san kema kina so. Banda gulma me zai sa ki biyoni wai zaki gaishe da Mummy? Ni Innata tana kauyenmu."

"Naji na cuci kaina don Allah kayi hakuri ka barni na tafi"

Danliti ya sake yin dariya "dama ai ba kwana na dauko ki kiyi mana ba. Za dai mu gwangwaje a jikinki ne kawai mu kaiki gidan tsohonki." Kula ya yi kamar tana danne amai ya dinga dariya "wai nan kyamata kike ji? Tabdi. Yarinya wannan jikin yau zai kafa miki tambarin da har ki mutu ba zai goge ba"

"Allah Ya fika" ta ce cikin kuka tana tofar da yawu."

"Ke dai anyi azzaluma. Kina ta kada jiki a gabana amma kin kasa karasowa ki bani kasona? Ki taso kafin na farde kayanki da wukar nan"

Duk wata magiyarta bata yi tasiri ba. Gashi babu halin buga waya. Karshe kayanta ya umarceta da ta cire ta zo ta same shi akan katifar. Da taki ya taso ya kamata ya tsarge hijabin ya wurgar dashi. Ayaah ta fashe da wani irin marayan kuka mai ban tausayi. Duk wata hudubar Anti Hasiya ta dinga dawo mata. Matsatsiyar rigarta ya gani yana karewa surar jikinta kallo harda lasar labba. Ta sake dukawa tana bashi hakuri ya dagota ta mike ya dalla mata mari saboda ransa ya kai makura sannan hakurinsa ya kare.

"Ni ban daukoki domin na gwada miki karfi ba. Soyayya mai zafi nake son mu shayar da juna amma kin tsaya kina neman yi min taurin kai. Wallahi idan kika bari na saka miki karfi yau ko uwar da ta haifeki ba za ta ganeki."

Hankadeta gefe ya yi ya koma ya kwanta rigingine da wukarsa a gefe ya dauko tecno dinsa ya kunna wata mahaukaciyar waka ya kure sautin.

"To maza ki cire kayan ki zo muyi rawa."

Ayaah taga cin mutumcin da tozarcin nasa sun wuce tunaninta. Yadda zata samu ta karbi wukar hannunsa ma dabara ta kare mata. Bata daddara ba kawai ta juya tayi masa ba zata wurin dukan kofar dakin da hannuwa biyu, iyakar karfinta. Danliti ya taso a guje bayan ya jefar da wukar zai kamota. Iskancin nasa na matsorata ne domin kuwa yana tsoron 'yan layin su farga a dauki mataki. Sun saba kawo yan matan da suka amince ne ba jjc irinta ba.

*
Ayaah na wannan bugun Suhaib na gama mikawa matar Danliti kudi. Kusan a tare shi da tawagar makanikai da ita suka kalli kofar. Baiwar Allah sai ta kada danta tabar wurin. Duk lalacewa bata son yaron yaga ubansa a yanayin da ta tabbatar zai shiga na muzanci nan da dan lokaci.

Jikin Suhaib na tsuma ya karasa jikin kofar suna biye dashi ya soma bugawa iyakar karfinsa.

Danliti da Ayaah suka kalli kofar a tare. Dankwalinta da gashinta ya hada ya yiwa mugun riko dama yana shirin fizga yadda zata ji zafi aka yi bugun.

"Waye?" Ya tambaya muryarsa ta fito kamar ta kyanwa don ya tsorata.

Ogansa ya yiwa Suhaib alamar ya yi shiru sannan shi ya yi magana da kaushin murya.

"Mutumin banza bude ka bani mukullin mutane don tare muke da 'yan sanda"

Yawu ya hadiya ba shiri " 'yan sanda kuma?"

Sake buga kofar Suhaib ya yi da karfi Danliti yaji kamar ya saki fitsari a wurin. Yana can hankalinsa a rabe da tunani bai farga ba Ayaah ta dauki wukar da ya yar sai kawai gani ya yi ta nuna shi da ita.

"Ko ka bude kofar nan wallahi ko na burma maka wukar nan a cikinka"

Shi ya jiyota, na waje ma kowa yaji abin da ta ce.

Jikin kofar Suhaib ya raba da sauri ya ce "Ayaah?" da taushin murya.

Kuka ta fashe dashi tsabar farinciki "na'am?"

"Kada kiyi abin da zamu yi regretting kinji ko?"

Kai ta gyada tana wani kukan ta dubi Danliti "ka bude ni"

Gaba kura baya sayaki. Wukar hannunta bata dame shi kamar jin muryar shegen yaron nan ba. Idan bai bude ba ma zasu balle kofar ne ayi masa abin da aka ga dama. Saboda haka babu yadda ya iya haka ya zura mukullin ya murda kofar.

Mukullin yana yin karar ta bude kafin ma ya zare sakatar da ya saka ta sama yaji sun yi baya tare da kofar. Wawan bugu Suhaib yayi mata da kafa sai da ya jijjigeta gabadaya ta balle. Ayaah na ganin hasken waje bata yi wata wata ba ta danna kai a guje sai ji tayi sun yi karo da mutum har suna shirin faduwa. Dole ya saka hannuwa ya tarota. Tsigar jikinta da nasa suka tashi lokaci guda da suka hada ido cikin ido karo na farko tun haduwarsu. 

Da sauri Suhaib ya sanya hannu ya rabata da jikinsa. Kallo guda ya sake yi mata ya runtse idanu. Rigarta ko kadan bata dace da ganin idanunsa ba balle na wasu. Bai yi tunanin komai ba ya shiga balle maballan shirt din jikinsa. Rigar dogon hannu ne da ita. Cireta ya yi ya rage farar T-shirt din jikinsa. Ayaah bata ankara ba taji ya dora mata rigar ta gaban kirjinta.

"Rufe jikinki ki jirani a waje" ya ce ba tare da ya kalleta ba. Da sauri ta fice kuwa ta koma gefe tana share hawaye.

Kansa tsaye ya fada cikin kazamin dakin mai warin kazantar kaya da ta fasikancin da aka jima ana yi a cikinsa. Da kafa ya doke kofar daga kan Danliti yasa kafarsa dake cikin hadadden cover shoe ya danne tsakiyar kafafun Danlitin.

Razanannen ihun da Danliti ya yi sai da yaje kunnuwan makotan shagon. Mutane suka firfito ana kallon ikon Allah. Ayaah kanta durkushewa tayi ta cusa yatsunta a cikin kunne. Tsinuwa da zagi kala kala daga bakin jama'a ana fadin yadda suka mayar da dakin dandalin yan mata.

Suhaib kuwa bai ragawa Danliti ba don ko kadan bai yi niyar cire kafarsa nan kusa ba. Ogan makanikan ne ma ya ji tsoro yaje ya riko shi.

"Yallabai ka yi hakuri ka bari a hadashi da hukuma kada ka dauki mataki a hannunka."

Kamar ba zai dauke kafar ba sai ya cire. Sauran mazan kamar su ya yiwa suka dinga sauke ajiyar zuciya. Suhaib ya shammacesu ya sake daga kafar kawai kuma buga masa. Ihun Danliti har yafi na dazu don suma ne kawai bai yi ba saboda azaba.

Biyu cikin makanikan suka leka waje wurin Ayaah.
"Ki zo ki yi masa magana kada yayi kisa"

A hanzarce ta tashi ta koma kofar dakin. Ta san sunan shi tunda kannensa sun fada taji. Amma bata san ita me ya dace ta kira shi ba. Wasu hawayen ta goge ta sami kanta da cewa,

"Yaya"

Suhaib ya juyo ransa a matukar bace
"Ban ce ki fita ba?"

"Ka zo ka kaini gidanmu don Allah"

Yadda tayi maganar da sanyin murya ya taba shi sosai. Cije lebensa ya yi don bai so barin Danliti haka ba ya biyo bayanta. Haka ya tasata a gaba har bakin motarsa don baya son kowa yaga bayanta. Da kansa ya bude motar har ta shiga sannan ya rufe ya zagaya barin direba ya zauna. Yana tuki yana kula da hawayen da take gogewa lokaci-lokaci da rigarsa mai kamshi. Sai da suka bullo titi ya yi mata magana.

"Ina zamu bi?"

"Dama"

Shiru ya sake mamaye motar na 'yan dakiku sannan ya ce,

"Ba kya jin magana ko? Abin da ya faru shekaranjiya bai isheki ba sai da ki ka biyo shi"?

Da jajayen idanunta da suka rine saboda kuka Ayaah ta dube shi.
"Kayi hakuri don Allah."

"Ya tabaki?" Ya tambayeta idanunsa na kallon titi.

Ta girgiza kai tana wani kukan. Ba don sun zo ba da yanzu tana can ya gama da ita.

"Dago kanki ki dinga yi min kwatance"

Umarninsa tabi ta dinga kwatanta masa har suka shiga layinsu. Nan ta tarar da motar 'yan sanda har biyu a kan layin.

"Kinga abin da kika janyo a gidan ko?"

"Ai ba zan kara ba"

Suhaib ya taka burki ba shiri ya kalleta "tunanin karawa dama kike yi?"

"A'a" ta amsa masa da sauri.

Da ya tsaya tare suka fito daga motar. Shi da ita duka kunyar suturar jikinsu ta kamasu.

"Kinga abin da kika ja mana ko?"
Kunkuni yake don bai san da yaya ma zai shiga gidansu ba. Tsayuwa ya yi a hanya yace ta karasa. Tayi narai narai da idanu za ta yi kuka.

"Don Allah kazo kayi musu bayani. Yau ina jin Baba sai ya yi min duka."

"Banda abinki Ayaah, ance miki bana so a dake ki ne?"

Baki ta bude amma bata iya cewa komai ba ta rufe. Ta zata ba zai karasa din ba sai gashi ya cigaba da bin bayanta har kofar gidan. A tsorace ta saka kafa sai ta dawo da baya. Gabanta ke faduwa bata san abin da iyayenta zasu yi mata ba.

"It will be okay. Ki shiga"

"Wallahi zuciyata kamar za ta fito ta baki."

Tausayi ta bawa Suhaib sosai. Bai san tun yaushe take ta kuka ba yau ga wani ta fara na tsoro. Rab'awa ya yi ta gefenta ya shiga kofar farkon sosai.

"Assalam alaikum wa rahmatullah."

Murya tafi biyar da ta amsa. Amma a ciki Ayaah ta bambance ta babanta da Anti Hasiya.







Continue Reading

You'll Also Like

77.5K 8.3K 63
Duniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin dun...
5.4M 719K 198
Main Story ( Completed ) ~~~~~~~°°°°°~~~~~~~ Title - Transmigrated into the film empreor's death-seeking finance (穿成影帝作死未婚夫) Author - Lin Ang Si (林盎...
1.3M 37.5K 65
ယော.. ကျွန်တော်ကလူတော်..ဒါပေမယ့် လူကောင်းမဟုတ်ဘူး။ စာရေးသူ၏ စိတ်ကူးယဥ်မှုဖြင့် ရေးသောကြောင့် အပြင်လောကနှင့်ကွဲပြားနိုင်သည်ကို သတိချပ်ပေးစေလိုပါသည်။ လ...
139K 9.2K 17
#9 in romance on 05/09/2016 "Wai ina son ki fada min, me yake damun ki ne, da za ki haddasa irin wannan fitina, sannan ki zauna lafiya, kamar ba abin...