Wata Rayuwa

By SAKHNA03

3.5K 459 59

Labari kan karamar budurwa data samu kanta cikin kangin rayuwa,!!!! Faryah karki taba barina ke tawace har ab... More

Chapter 01(Garin bardugu)
Chapter 02(Wata halitta)
Chapter 03(Inada mafita ๐Ÿค”)
Chapter 04(Daular Saraham๐Ÿฏ)
Chapter(05)waiwaye zuwaga masarautar saraham
Chapter(06)auren gimbiya safeenah
Chapter (07)Sabuwar rayuwa ๐Ÿ‘ผ
Chapter (08)meyake faruwa ?
Chapter (09)Dole sai ya mutu๐Ÿ˜ 
Chapter (10)ahah bana sonta
Chapter(11)zan bar nahiyata
Chapter (12)shi wa ?? Wanene shi ???
Chapter (14)Me yake shirin yimin ?
Chapter (15)wayyo mai na aikata haka ??
Chapter (16)ke tawace har abada
Chapter(17)An gudu ba'a tsira ba
Chapter (18) Zaki fara tarar manyan baki
Chapter (19) yarima SAHEEL
Chapter (20) Zazzabin dare kuma??
Chapter (21)zan ci amanar mijina๐Ÿ˜ฅ!!
Chapter (22)an turoni ne aiki
Chapter (23)barka da zuwa cikin ukuba!!
Chp (24)ehhhhhh!!!!!๐Ÿ˜ฒ
Chp(25)na shiga uku!!!!
Chp(26)bazaki koma ba....
Chp(27)wannan din menene?
Chp(28)ohhh allah!!!
Chp(29)ina yarima amam din?
Chp(30)karka koya masa mungun hali
Chp(31)kawai kuma??!!
Chp(32)ahhhhhj......!!!
Chp(33)tohh fahh!!
Chp(34)haduwar masoyaโคโค
Chp(35)na yarda da kai
Chp(37)ita ba baiwa bace
Chp(38)kina tantama neh??
Chp(38)bantan uban can
Chp(39)mu zuba mugani!!
Chp(40)ku kama ta!!!
Chp(41)hakan bazai yiwuba
Chp(42)Nagode maka
Chp(43)finally๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ

Chapter(13) ina so ka auri y'ata fahreeyah ???

61 13 0
By SAKHNA03

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

chp(13)
"saheel ina so ka auri y'a ta fahreeyah "
kallonta sukayi duk a razane ,kamar basuji mai take fad'aba ,
"umma me kike cewa haka ne ?"
"bazaki gane ba ke ,amma ina tunanin idan shiya ji zai iya fahimtata "
"ahah ummah kituna fah mai kikace "
sukad'ai suke maganarsu ,shidai tunda ya ji abinda yafito daga bakin huda bai sake magana ba ,sai binsu da ido dayake ,saida HUDA tazo gabansa tareda karyar da kai tana kallonsa ,
"bawan allah nasan a idonka zan kasance mai wauta wacce take yarda da wanda batasanshi ba ,sannan zan kasance mai san kai saboda yanayin abinda narokeka ,amma kasani kodaya bayanda kake ganiba ne ,ni uwace mai son tseratar da yar ta daga kangin dayake tunkarota ,ni uwace da banida wani buri sai ganin yata cikin kwanciyar hankali ,nasan fahreeyah ta baka labarin rayuwarmu ,haka kawai na tsinci kaina da yarda da kai bawan allah ,dan allah amincemin da auren y'a ta ,sannan ka tabba tarmin da cewar zaka kulamin da ita a wannan RAYUWAR ,narokeka "
tafada tareda sakin wani kuka mai tsuma zuciya ,wanda duk wanda yaji yasan ma'abocin kuka nacikin wani irin yanayi ,ganin kukan bazai mata bane yasa ta tsugunna akan gwiwoyinta tareda kama kafafunsa .
  Ganin abinda mahaifiyartata takeyi kuma wai,duk akanta yasata sakin itama kukan tareda durkushewa ,wai saboda tsabar kunci da rashin daraja ,mahaifiyarta ce take rokon wani ya aureta,ba dan so ba ,saidai dan ya taimakata ,
tana cikin wannan tunaninne ta ji muryar saheel yana fadin ,
"shikenan ummah na amince zan auri fahreeyah ,kuma nayi miki alkawarin riketa da amana ,matukar ina tare da ita kuma ina numfashi ,da sannu babu abinda zai sameta "
"nagodee d'annan allah yayimaka albarka ,yakumasa albarka a rayuwarku ,bazan taba mantawa da abinda kamin ba har abada "
fahreeyah ce itama ta share nata hawayen ganin ummah nata ta dora murmushi akan fuskarta .
Hudace ta zuya tare da shiga cikin gidan da suka tsaya a bakinsa ,binda sukayi suma har zuwa cikin gidan ,gidane karami mai dauke da dakuna guda biyu madaidata .
Suna cikin kalle kalle ne ,wani matum mai dan shekaru yafito daga dakin tareda amsa sallamarsu ,fuskarsa ce ta nuna almar mamaki kafin ya iso gabansu ,
"huda dama kina raye ?"
"ehh baba HASHEEM ,ina raye,yanzu ma  nazo neman alfarma ne gunka "
"allah yasa ba wajen zama zaki bukata ba,domin kinsa duk wanda yasaukeki a gidansa to hukuncin dake jikinki ne zai hau kansa shima "
"ehh ina neman wata alfarma ne daban ba wacce kake zatoba "
"shikenan ku shigo naji da mai kuke tafe "
shiga sukayi ciki ,tareda shaida musu abinda yake tafe dasu gabadaya ,jinjina kai yayi kafin yace ,
"shikenan zamu taimaka ,sai su zauna zuwa da safe za'a daura amman ,inaga kekam ki tafi saboda kar a samu matsala zamanki anan"
"ehh nasani baba  hasheem  indai zaka taimaka min dahakan banida matsala da wani abun "
karisa maganar tayi fuskarta dauke da damuwa ,da kuma dana sanin abinda ta aikata .
Bayan ta tafine yazuyo da kallonsa izuwa su fahreeyah kafin yace ,
"shikenan na amince zan taimaka muku da abinda mahaifiyarki ta bukata ,inajin tausayinta matuka ,saidai banida ikon bata muhalli a wajena,yanzu ga can daki ki kwanta kafin muga mai gobe zatayi "
  A wajen huda kuwa tana isa gida dakinsu ta lallaba ta shiga zuciyarta na dukan  tara- tara  cike da fargaba .
"KEEEE d'iyar fatara da tsiya maza ki fito za'a fara ciniki ,ai in fada maka kyakykyawace ta fad'a a taro ,nasan zaka sayeta da daraja ina fadamaka ........"
zancen tane ya katse ganin huda tafito daga dak'i ita kadai batare da fahreeyah ba ,
"kee kuma ina take ?ai kinsan bake na kira ba ko ?"
"eh fahreeyah bata nan ,dana tashi bangantaba nima "
"kutt mekkike nufi kinsaka baiwa ta ta gudu kenan ?"
"ahah tashi nayi bangantaba nima a dakin "
"DUK'ANA !!! maza kabimin sawun waccer tsinanniyar yarinyar ,kuma ka tabbatar ka nakasata kafin ka kawomin ita ,ke kuma ki saurari mummunan hukuncina ,dan nasan da hannunki akan hakan "
  A can kuwa wajen su fahreeyah bayan sun tashi da safe sun shirya ,sai kuma baba hasheem yakirasu zuwa wajen majalisar sa.
A zaune take a gefe a daya bangaren kuma saheel ne shima a zaune saikuma wasu mutanen suma masu yawan shekaru.
Shirye shirye aka farayi na daurin aurensu ,inda aka nemi amincewarsu gabadaya ,bayan sun gama shiryawa ne  aka fara da bayar da sadaki ,zoben hannunsa yamik'a mata batareda yace komai ba ,yayinda waliyyinta baba hasheem yakrb,a tareda shaidawa sai kuma aka fara siiga ............
Haka lamarin yakasance har aka gama abinda za'a yi ,baba hasheem ne ,yashiga cikin gidan yafito da wani kaya a hannunsa na mata ya mika mata  tareda cewa ,
"ga wannan kayan al'adane da'ke bawa kowace y'a a wannan dangin ,duk da abinda yafaru, yafaru ,dole kina da jinin wannan dangin ,ki kula da kanki ,allah ya baku zaman lafiya "
Yana fad'a yajuya yakoma cikin gida ,daga kanta tayi tana kallon fuskar saheel hannunta dauke da kayan da baba hasheem din ya bata .
Juyawa yayi yafara tafiya batareda yace mata komaiba ,itama ganin haka yasata binsa a baya tana tunanni a ranta ,
""to yanzu tare zamu dinga rayuwa kenan dashi ,meyasa naga kowa yatafi an barni dagani sai shi to ?,gidansa zan koma da zama kenan ? au ashe aure akamin nida shi ko ?""
jin irin abinda take fada arantane yasata sakin murmushi ita kadai ,shima anasa bangaren tunanin yake akan ,
""kai anya kuwa nine ?wai na amince da auren ta ,nidai banajin wani abu mai kama so a gameda ita ,sannan banji haushiba da'aka dauramin aure da ita ,to me yake shirin faruwane haka ?""
dahaka suna cikin tunaninsu da basu da mai basu amsarsa suka iso kofar gidan saheel din ,tsayawa suka yi kowa yana kallon kowa ,lokaci daya suka dauke idonsu a tare kuma ,.......
    😊😊😊,rayuwar gidan saheel zai zo muku a gaba shida matar tasa fahreeyah kuci gaba da bani goyon baya ,domin nasamu na dinga suburbudo muku shi 😊,.
  A dunga taimakawa da bamu
  #comment
  #vote

  SADI -SAKHNA ce

Continue Reading

You'll Also Like

13.7K 317 16
An alternate Jason Uchiha timeline
32.1K 1.3K 24
Basically, the sin of sloth got transported to the world of demons, reapers, and angles by her littler brother greed. Let's see how sloth have a new...
17.4K 763 29
In this story A boy named The same as the protagonist's name in his previous life a Boy named Satoru Mikami is and ordinarily Otaku High schooler H...
19.5K 786 12
In the starlit festivities of Penacony, she meets Caelus, a figure shrouded in mystery who shines as a beacon into her enduring night. He was her lig...