KURMAN GIDA

Autorstwa rashmarrka

10.2K 646 49

Love story Więcej

page 1
page 2
page 3
page 4
page 5
page 6
page 7
page 8
page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 14
15
page 16
page 17
page 18
page 19
WASA FARIN GIRKI
page 22
page 23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34

page 21

291 26 3
Autorstwa rashmarrka

🏨KURMAN GIDA 🏨

        Na
Rashida Usman
     (Rashma)

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

Page 21

بسم الله الرحمن الرحيم

  Har ta shiga cikin gida tana masifa ita dai Salma batace mata komai ba sai kallo da ta bita da shi gajiya ta yi ta shiga gidan su zaune ta sami baban ta ya dawo daga aiki har ƙasa ta duƙa ta gaida shi sannan ta cire hijabin ta ta shiga Kitchen ta karɓi aikin da Umma keyi ita kuma ta fito tana share zufa kusa da Baba ta zauna "wash Allah na duk jikina ciwo yake min."

    "Sannu ai kuna ƙoƙari girki ba abu bane mai sauƙi bare gaki da lalura ai kin kusa sauka ki huta."

   Murmushi ta yi tana shafa cikin ta da ya zama titsetse haihuwa yau ko gobe "tabbas na tabbata haihuwa rabo ce sai wanda Allah ya so yake bawa sannan kuma sai lokacin da ya ga dama yake baka kaga fa Baban Salma magani wane iri ne bansha ba akan nasami ciki amma duk a banza saida lokacin ta ya yi sannan na samu."

   "Haka ne wani rabonsa yana nesa wani kuma kusa yake mu ƴan Adam dama munada gajen haƙuri akan abinda muka ƙwallafa rai."

  Haka suka ci gaba da firar su saida aka kira salla sannan Baba ya yi alwalla ya fita koda ya dawo Salma ta gama jera komai cikin kwano ɗaya suka ci dukan su uku cikin farin ciki da jin daɗi  kwantawa Salma ta yi akan cinyar Umma tana shafa cikin ta ta ce "my baby kaci tuwo ka ƙoshi babu abinda kake so?"

   Aiko kamar ya sani ya motsa murmushi ta yi har sautin ta na fitowa yawwa my baby tunda ka ƙoshi ka gyara kwanciyar ka zan baka labarin abubuwan da nayi yau." Dariya ta yi sannan ta fara ce wa "my baby yau da safe naje makaranta boko koda naje na makara hakan ya saka akayi min bulala saida nayi kuka hakan ya sa kaina ya yi ta min ciwo kuma ina dawowa naje islamiyya na iya hadda hakan malamin mu ya bani alawa kuma na kawoma taka da aka taso makaranta muka haɗu da Fadila muka dawo ta re shine na samu Umma na saka mun kai aiki bari naje na ɗauki ma taka sweet kasha."

   Aikuwa ya motsa dariya ta yi har jerin haƙoran ta suna bayyana girgiza kai Umma ta yi ta ce "ni kam bansan yaushe Salma zata girma ba shekara sha bakwai amma kullum sai ta ɓara takeyi."

   Dariyar jin daɗi Baba ya yi yace "ki barta mana ai sun saba firarar su tuna daga lokacin da ta san kinda ciki."

   Sweet ta dawo da ita guda biyu ɓarewa ta yi ta ce "Umma ha."

   Ba musu ta buɗe ita kuma ta saka mata komawa ta yi ta kwanta ta ɗora hannu akan cikin daga nan bacci ya yi gaba da ita kwalliya Fadila ta caɓa ta saka wani wando da riga wando iya gwuiwa rigar kuwa iya karta cibiya gashin ta ttare ta ɗaura shi a tsakar kai sai ya sauko yanata yawo a gadon bayan ta   ko sallama bata yiwa kakar ba  ta fita  wata danƙareriyar ce ta faka ƙofar gidan su bataji kunyar mutane dake zaune a gurin ba ta shiga mota suka ja suka tafi sunyi nisa  da tafiya kamar waɗanda zasu bar garin Kano ya ce "wai haryanzu ƙinƙi shawo min kan ƙawar nan taki?"

    "Saminu kenan kai angaya ma shawo kan Salma abune mai sauƙi Salma fa ba irin sauran ƴan mata bane da nake ƙawance da su na sati biyu uku   sun bani yarda amma Salma mun kwashe shekara biyu da ita amma ko bakin titi bata yarda ta raka ni."

    Bakiyi dai yanda zakiyi ba tayaya za'ace anbaki aiki shekara biyu ki kasa kammala shi zan sami wata ta yi min wannan aikin dan nima wacce ta saka ni tana yimin magana."

   "Wai dama mace ke nemanta ne?"

  "Eh mace ce ke son a kawo mata ita wai tagan ta a tv tana karatu shekenan ta ɗauke hankali ta tana so ta shana da ita."

Dariya Fadila ta yi tana cewa ba mai daɗin za'a bata ba kenan yaushe zan tsaya da wata mace ni rame itama rame to me za'a soka min kenan."

   Dariya ya yi yace "Allah shima da ɗi idan kina so zan haɗa ki da Hajiya inaga idan kika ƙware bazaki ƙara sha'awar namiji ba."

"A'a barni da inda nafi ƙwarewa. Wai ina ɗan iska nan ya shiga ne?"

   Wai gowa yayi ya kalle ta "wa fa kike nufi?"

"Hassan wanki babban bargo mana aiki na masa ya ƙi ya biya ni."

  "Lallai da sauranki yarinya ai ya wanke ki ya yi gaba shi ɗin ne zai biya ki ko H.M baya shakka bare kowa a nan."

   "Allah haɗani dashi sai mun kwashi ƴan kallo dashi."

Dariya Saminu ya yi  "ni wannan tsakanin ku ne muje na ɓata wannan wanka dan naga jarumar tawa sai kuka takeyi."

    Dariya ta yi  ta ɗora hannu akai aiko taji ta harba "kai Saminu ka cika kwaɗayi."

   "To ai kece sai bakiga irin shigar da kikayi bane kallifa ƙirjinki kilama kaine kawai a ciki."

   "Naji muje bana son dogon bayani kuma kayi sauri ƙarfe goma ne diner ɗin."

   Agogon hannu sa ya kalla ya gana takwas yace "inada awa biyu cikakki."

    Gidan sa suka nufa tun a mota suka fara watsewa hakan ya saka mai gadi yi musu ƙuri dan shima A ne take yaji dizayar sa na tashi fitowa daga motar sukayi hannu sa cikin rigar ta bakin su a haɗe da haka suka ƙarasa cikin gida basu dawo hankalin su ba sai gurin sha biyu na dare rai ta ɓata "ka gani ko yanzu ai an tashi daga dina ɗin."

   Ƙara janyo ta ya yi jikin sa ya ce "to ai shikenan bari kawai mu ƙarasa dama ɗan ɗanawa nayi."

   Daga haka ya tashi cikin kitchen ya shiga ya haɗa liptop ya shanye shi duk zafin sa daga Kitchen ɗin yana hango mai gadi yana ta sukuwa dariya ya yi  kawai ya koma ɗaki har ta fara bacci faɗa wa ya yi akan ta a taƙaice dai wannan daren basu runtsa ba cikin sauri take shirya wa tana saka kayan ta na makaran sai kallon ta Umma keyi  ana cikin haka taji bayan ta ya karɓa mata kamar ansaka kibiya an caka mata rumtse idanu ta yi duk yanda taso ta daure kasawa ta yi wani irin zufa ke tsiyayo mata duk inda hankalin Salma yake ya tashi kamata, ta yi  da nufin miƙar da ita amma ta kasa ba shiri ta fara kuka wiwi da gudu ta fita ko ɗan kwali babu a kan ta yarinyar da ko mayafi bata sawa amma yau cikin tashin hankali ko ɗan kwali babu a kan ta bata zarce ko ina ba sai shagon baban ta yana ganin ta cikin tashin hankali ya rufe shagon sa ya bi bayan ta a nan ɗakin Salma suka sameta kwance kama ta ya yi domin su kaita asibiti girgiza masa kai ta yi, ta ce "a'a baban Salma ni nasan tawa ta ƙare dan Allah ga Salma nan da abinda zan haifa kada ka bari suyi maraici a duniyar nan sannan ka cika min buri na da kullum nake gaya ma."

     "A'a Umman Salma bazaki mutu ba insha Allahu sai kin aurar da Salma da hannuki."

   Wani irin nishi ta yi sai ga kan baby ya fito ƙanƙame shi ta Salma na gefe tana ta rusar kuka ganin Ummanta keyi ba'a jima ba ta haifi yaron kyakyawa duk murna sukeyi basu ankara ba sai gani sukayi tana rufe idanu cikin ɗimaucewa Salma ta yi kanta tana jijiga ta kukan jariri kuwa ya karaɗe ko ina da ƙyar Umma ta buɗe baki ta ce "Salma kimin alƙawarin bazaki watsar da tarbiyar da nayi miki ba ki kare mutunci ki na ƴa mace na roƙe ki kada ki watsar da tarbiyar da na miki ga ƙaniki nan na bar miki amana ki kula da shi."

   Kalima ta fara jini kuwa kamar an buɗe famfo haka yake malala koda Baba ya dawo da mata keke nafef Umma ta cika Salma na rungume da ita sai kuka take yi bata ma san ta rasu ba ɗaga ta da Baba zeyi ya ji ta yi nauyi hakan ya saka ya kai hannu kan hanci ta yaji ba numfashi  cikin tashin hankali yake girgiza ta amma shiru kake ji "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Umman Salma."

   Amma ina ga yaro yana ta tsala kuka  zani ya ɗauko ya rufeta sannan ya ɗauki yaron dake kwance ya miƙa wa Salma ya ce "ki riƙe shi bari na gayawa Kakar Fadila taso ta kimtsa yaron."

   Daga haka ya fita ko kallon ta bai yi ba bai jima ba saiga shi ya dawo jaririn ta karɓar ta yanke cibiya sannan ta yi masa wanka ta kimtsashi sai ga shi ya yi bacci   tuni ya sanar da ƴan uwa da abokan arziki da kansa ya mata wanka tunda basuda wasu ƴan makusanta makwanci ta aka kaita kwana uku suna amsa gaisuwa mutane suka watse a nan ne mutuwa ta dawo musu sabuwa Salma ke masa komai duk yanda Baba ya so ya kawo mai kula da yaron taƙi har akayi kwana  arba'in a nan ne mutane sukata bawa Baba shawara ya yi aure duk da babu tsarin haka a rayuwarsa amma haka ya yarda aka ɗaura masa aure da wata bazawara ƙasan layin su take mijin ta ya rasu .

    **** **** ****

   Ƙofar samu ta buɗewa Hayat  yanzu hankali Momma ya kwanta matsalar ta ɗaya Mubeena da ta yarda su ko neman su bata yi  ko yanzu zaune take a ɗaki tana tunani sallama Hayat ke ta yi amma bata ji ba shigowa ya yi yagan ta ta yi ta gimi kusa da ita ya zauna ya dafa ta sannan ta dawo hankalin ta "haba Momma wannan wane irin tunani ne tun ɗazu inata sallama baki jiba."

    Numfashi ta sauke ta ce "ya akayi auta na?"

    "Momma Suwaiba ce ta haihu yanzu an sami baby girl shine nazo nagaya miki kina ta tunani."

   Murmushi ta yi tana faɗaɗa fraa'ar ta tashi ta yi tana danne damuwar ta kamota Hayat ya yi ƙura mata manya idanu sa ya yi  wanda tun yana yaro haka yake mata sai ya gano tana damuwata "ya Momma na me yake damun ki ne."

    Hawayen da suka cika mata idanu ne ta share ta ce "Auta na tunani halin da Mubeena take nakeyi bata neman mu bare nasa e hali take."

    Numfashi ya sauke ya ce "Momma ki kwantar da hankalin ki idan da tana cikin damuwa da yanzu ta nememu na gaya miki zata dawo idan taji wahala bata san wa take aure bane."

   Fita ya yi dan ma kada kada ta tamye shi bayan sa ta bi ɗakin Suwaiba suka shiga tana kwance Hassana na gefen ta Fatima kuwa tana riƙe da baby sai washe baki takeyi  da fara'a Momma ta karɓi yarinyar tana sumbatar ta "sannu Suwaiba Allah ya ƙara lafiya ya kuma baki lafiyar shayarwa."

   Amin suka amsa dukan su Suwaiba kuwa kuka ta rushe da shi kusa da ita Momma ta zauna sai Hassana ta miƙe tsaye "haba mana Suwaiba ki gode ma Allah da ya sauke ki lafiya ina roƙon Allah ya baki miji na gari."

    Hawaye ta share tana cewa "Momma wane namiji ne zai aure ni a haka babu shi Momma Allah dai ya yafe min."

   "Ooo wannan ƙanwar ta mu ba jaruma bace idan bakiyi shiru ba saina aura miki baba mai gadi mijin lantana."

   Dariya sukayi gaba ɗaya Fatima ta ce "amma ko da ka gwada mata bone ina wannan cikar ina Baba."

   Wayar sa ce ta yi ringing ya saka beyi magana ba ɗagawa ya yi "Sweethart ykk sai yau."

  "Ƙaniyar ka da Sweethart ɗin  ina airport ɗin Lagos kazo ka ɗauke ni marar mutunci."

   "Tuba nake gimbiya a gidan Abdullah gani nan tafe da gudu."

   Kallon Momma ya yi ya ce "halan ke kika gaya mata inda muke?"

   "Eh ai idan mun ɓoye ma kowa ai ita bai kamata mu ɓoye mata ba."

    "Shikenan Fatima muje ki raka ni mu ɗauko ta wai tana airport."

   A tare suka fita da sauri Hassana ta miƙe tana cewa "Momma bari naje na sama musu abinda za suci kafin su ƙara so."

    Cikin jin daɗi Momma ta amsa mata dan  tana mugun son Hassana tana mutunta da duk wani dangi ta cikin sauri Hassana ta haɗa dambun cus_cus da yaji kayan haɗi da soyayen nama akai sannan ta haɗa musu lemun abarba da kankana  sai farfesun kayan ciki da tayi ma mejego wanda yaji kayan yaji suma ɗibar musu ta yi ko kafin su ƙara so ta gama haɗa komai tea kawai ya rage ta juye hadari ya ne ya haɗu sosai hakan ya saka Hassana hankali ta ya tashi da tasan Hayat baya iya tuƙi cikin ruwa  mayafin Fatima dake kan kujera wanda dawowar ta daga aiki ta ajiye Compoud ta fita sai Safa da marwa takeyi har cikin ta ke juya mata tanajin kamar zatayi zawo yayafi aka fara tuni ta ruɗe ta kai bakin get ta buɗe ta leƙa babu kowa sai wasu jerin motoci da suka jero komawa ta yi ƙarfi ruwan suka fara tuni jikinta ya fara rawa horn yaki bata ma jira mai gadi ya fito ba taje ta buɗe masa ya shigo yana ganin ta ya yi murmushi ya ce "ki gani ko Sweethart na gaya miki yanzu tana can hankalin ta a tashe."

     Rufe get ɗin ta yi ta zo da gudu ta buɗe gurin da yake ta janyo hannu sa da gudu ta kaishi rumfar dake bakin ƙofar falo tana taɓa jikin sa rungume ta zeyi suka ji muryar Sweethart tana cewa "lallai ma mu mutu kenan ko?"

    "Ammi me yasa kikayi magana ai da kin barsu muma dai munkusa auren nan tunda wannan ɗan tatsin ya yi ai dole nayi aure."

     Murmushi Hayat ya yi yana shafa bayan kansa ciki Ammi ta shiga bayan ta suka bi Hassana kam sai sunne kai takeyi da fara'ar ta Momma tazo ta rungume ta itama murmushi ta yi tana mai jin daɗin haɗuwa da su  a nan Hassana ta gabatar musu da ruwa da abinci saida suka ci suka ƙoshi sannan suka dasa fira ɗakin Momma Ammi ta sauka shiko Amjad ɗakin dake kusa da na Suwaiba ya sauka wanka sukayi da sallar isha sannan suka dawo falo suka dasa fira Hassana kuwa ta can gurin Suwaiba ita da Fatima ita kuwa tana gefe tana cin Farfesa kayan cikin da akayi mata wayar Hassana ce ta yi ƙara da sauri ta ɗaga ganin momy ke kiran ta  "Assalamu alaikum my Momy."

    "Dalla gafara ba ita bace me yasa baki ɗaga wayata."

    Mtswwwwww "wai dan Allah Husaina me yasa kike da damuwa ne."

    "Ni ba waccen maganar na kira ki ba Momy ta ce sis love ta haihu gobe zan diro nide bazan jira su Mamy da Hajaju ba."

   Dariya Hassana ta yi ta ce "yawwa ƴar gari  koke fa amma kin wani dameni yaushe ne watan da zan haihu sai kace kin bani cikin ne."

   " Kin san Allah ko me zakice min bazan yarda bakida ciki ba dan nagani a mafarki na."

   "To sannu allaramiyya."

   Daga haka ta kashe wayar  dariya Husaina ta yi  ta kalli momy "Allah Momy tunda kikaga Hassana tana kwana_kwana wallahi ciki ne da ita."

   Murmushi kawai Momy ta yi dan ita kaɗai ta san raɗaɗin da take ji a zuciyar ta  har Husaina ta tashi bata sani ba Baba ma da aka gaya masa bai wani nuna damuwa ba kuma bai nuna farin ciki sa ba sai ɗakin sa da ya shige ya zauna ya rufe idanu yana tunani yana cewa "me nayiwa Manga da ta saka min da wannan  amma ba komai ai Allah baya bacci kuma yana ganin komai."

     Da dare baby Suwaiba ta riƙa kuka ta bata nono amma taƙi shiru har Momma ta zo ta karɓe ta amma taƙi shiru su Hassana suna sama basu san me akeyi ba  Amjad da dai kukan baby ya dame ya fito ya shiga ɗakin Momma ya gani ta goya ta a safa da marwa takeyi ga Suwaiba gefe ta zabga tagumi kallon Momma ya yi yace "Momma wai meke damun ta ne."

   "Ba abinda ke damunta sai rigima murmushi ya yi yana cewa kawo ta na duba ta nagani."

   Kwanto ta ta yi ta miƙa masa kallon ta ya yi take ta yi shiru ta ƙura masa idanu tana lasar baki murmushi ya yi yana manna mata kiss a baki baki Momma ta saki ta na kallon baby ta ce  "kajimin yarinya to ku ƙarata ni nayi nan dan bacci nake ji."

    Fita ta yi ganin ta yi shiro ya saka shi miƙawa Suwaiba ita aiko tana shiga hannu ta, tawani tsala ihu hakan ya saka ya karɓe ta take ta yi shiru ɗakin sa ya shiga da ita ya kwanta ya ɗora ta akan cikin sa take bacci ya kwashe shi ita kam ta dai lafe kawai Suwaiba ma kwanciya ta yi sai asuba yariyar ta sami bacci a hankali ya ajiye ta take kuwa ta tsala ihu da sauri ya ɗauke ta ya saka babban tawul ya goya ta ya na jijiga ta saida ta yi shiru ta fara bacci bayi ya shiga ya ɗauro alwala yana goye da ita ya yi sallah yana zagayen ɗaki da ita dan da ya yi kamar zai sauko da ita zata fara kuka har Momma ta zo ta same shi da ita me zatayi inba dariya ba  "kawo ta ayi mata wanka to kwanto ta ya yi yamiƙa mata take kuwa ta tashi daga bacci "o ni wannan yarinya wayo kamar misalin ta mazare kawai."

    Dariya Amjad ya yi yana mata kiss a goshi fita Momma ta yi da ita tun ana mata wanka ta yi bacci   dungure mata kai Momma ta yi tana cewa "ji ɗan baƙin da ya hana mana bacci jiya."

  Dariya Ammi ta yi "amma fa kinsan a kwai kyau dan ta fiki."

   "Ba wani nan kinga ta wai ita tasan mace ta san namiji wallahi jiya mukayi_mukayi yarinyar nan ta yi shiru amma fafir ta ƙi saida Amjad ya ɗauke ta sannan ta yi shiru tare suka kwana da ita."

   "Aifa ai shikam yanada wannan duk kukan yaro yana shiga hannu sa zaiyi shiru  ni ina mamaki wannan abu."

   Kwantar da ita Momma ta yi bayan ta gama shirya ta aiko tace bata san zancen ba Hayat da Hassana ne suka shigo shi cikin shirin fita ita kuma tana sanye da doguwar riga tamata kyau sosai da sauri ta je ta ɗauke ta amma taƙi shiru Hayat ma karɓar ta yayi amma ina gurin maman ta aka kai ta taƙi kama nono ma "oo gaskiya kun matsawa baby na duk kun jagwalgwala ta."

   Cewar Amjad da shigowar sa kenan karɓar ta ya yi ya ɗora ta akan kafaɗa bata jima basu ta yi shiru saida ta ɗan jima sannan ya miƙa wa Suwaiba a kunya ce ta bata nono ta sha ta ƙoshi take sai bacci fita sukayi aka bar Hassana ita ɗaya a gurin ta gurin ƙarfe biyar sai ga Husaina ta diro ita da Hajaju kasancewar jirgi suka bi cike da murna da ɗauki  Hassana ta tare su ɗakin Suwaiba suka tare babu yanda Hassana batayi ba su sauka sama amma suka ƙi Hajaju ta ci gaba da kula da su har sukayi arba'in   sannan sukayi haramar komawa fafir Hayat ya ƙi Hajaju ta koma ya ce ai tazo kenan tana ji tana gani  Husaina ta tafi bayan komawar Husaina su Baba suka zo shida iyalin sa sunyi murna sosai barin ma Hassana Momy kam saida ta yi kuka da taga yarinyar har ta fara wayo janta Momma ta yi ɗakin ta "Haba mana Maman Hassana meye haka kike yi ki ɗauki ƙaddara mana ki rungume ta Allah bazai tuzarta ku ba."

    "Ni ba wannan ke damu na ba kamar ɗayar da bansan wace uwa duniya aka kaita ba gashi bamu san inda Manga take ba yayan ta ma dai take gidan sa da mukaje cemin ya yi ganin Manga yanzu ba abu bane mai sauƙi domin kuwa ko shi bai isa yaje gurin ta ba."

   "Kar ki damu kanki insha Allahu tana hannu mai kyau."

   Saida Momma ta kwantar mata da hankali sannan suka dawo cikin jama'a bayan kowa ya watse ne Ammi ke tambayar Momma anan take gaya mata labarin da Hassana ta basu ta tausaya musu saosai  "aiko zanma Amjad magana idan yana ra'ayin ta basai ayiwa Baban nata magana ba kafin su tafi."

   "Wallahi da ko kin kyauta domin kuwa ina tausaya wa Maman su wlh."

    Washe gari Ammi ta yiwa Amjad tana masa magana take ya amince harda murnar sa aiko da ƙwarin gwuiwa Momma ta tunkari Baba da maganar da fari ƙin amince wa ya yi saida Hayat ya saka baki sannan ya Amince kwanan su biyu suka dawo cike da farin ciki Hajaju kuwa murje idanu ta yi ta bisu ta dawowar ta da sauri Fatima ke saukowa mayafi a hannu ɗan kwali ma a hannu suna zaune gaba ɗaya suna karya wa cokalin hannu Hayat ta karɓe tana cewa "auta bari nayi cokali biyu na makara kuma yau wannan ogan na mu zai zo."

   Tura baki ya yi ya matsa yana ture filet ɗin ya rungume hannaye take lokacin da yana yaro ya dawo mata dan haka yakeyi indai kaci abinci sa dariya ta yi tana shafa kansa ta wuce dan bata da lokacin kula shi gudu take sosai dan ba ƙaramin makara ta yi ba koda taje kuwa har ya zo cikin mutuwar jiki taje office ɗin dan abokan aikin ta suna gaya mata bayada mutunci ko kaɗan tana zama aka zo aka kira ta   da sanyi jiki ta shiga babban ofishin yana zaune hakimce.........


   Wayyo Hannaye na duk zafi suke min.😔😔😔😔

    Idan babu comments aje shi zanyi na huta ko kuma na maida shi na kuɗi da haka naga ruwan comment😡😡😡😡


   *ALLAH KA BAMU ƳAƳA MASU ALBARKA*

Czytaj Dalej

To Też Polubisz

67K 1.2K 16
Izuku Midoriya, formerly known as Yagi never had a happy life Ever since he was diagnosed as Quirkless, his life turned upside down His step-sister I...
217K 7.2K 38
After years of abuse Anastasia has shut herself within emotionless walls. Even if the physical and mental abuse have broken her to the high extent, h...
112K 23.5K 71
Arc(9)-Arc(14)+Real World+Extra အာဏာရှင်ကုန်းvsနတ်ဘုရားရှို့
52.3K 3K 48
ហេតុតែស្រឡាញ់បងស្រីសុខចិត្តមកបម្រីម៉ាហ្វៀដែរមានចិត្តឃោឃៅចំនួសបងស្រីដោយដឹងហើយថានិងមានរឿងអ្វីកើតឡើងក៏ប៉ុន្តែដែរធ្វើដើម្បីបងស្រី។តើនិងមានរឿងអ្វីបន្ទាប់ព...