EL-BASHEER

By Nuceeyluv

21.2K 1.6K 16

EL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai k... More

EL-BASHEER 1-5
EL-BSHEER 6-10
EL-BASHEER 11-15
EL-BASHEER 16-20
EL-BASHEER 21-24
EL-BASHEER 25-28
EL-BASHEER 29-30
EL-BASHEER 31-33
EL-BASHEER 34-35
EL-BASHEER 36-37
EL-BASHEER 38-39
EL-BASHEER 40.
EL-BASHEER 41.
EL-BASHEER 42.
EL-BASHEER 43.
EL-BASHEER 44
EL-BASHEER 45
EL-BASHEER 47
EL-BASHEER 48
EL-BASHEER 49
EL-BASHEER 50
EL-BASHEER 51
EL-BASHEER 52
EL-BASHEER 53
EL-BASHEER 54
EL-BASHEER 55
EL-BASHEER 56
EL-BASHEER 57
EL-BASHEER 59
EL-BASHEER 60
EL-BASHEER 61
EL-BASHEER 62
EL-BASHEER 63
EL-BASHEER 64
EL-BASHEER 65

EL-BASHEER 58

584 45 1
By Nuceeyluv

EL-BASHEER*



Na
Nuceeyluv😘

58


Kissing dinta ya fara yi kota ina yana lasheta kamar ya samu sweet, kokarin cire mata kaya yyi dan hankalin sa ya fara tafiya ummi ta rike rigarta dan bata manta darensu na jiya ba, badan yaso ba ya saurara dan shima yana tausaya mata danma dai tanada dauriya ne kawai, shiru sukayi na wasu minutes kafin ummi tayi yunqurin tashi, toilet dinsa ta shiga danyin wanka, ta gama cire kayanta kenan taji ya bude kofar, wara ido tayi tace,
              "pls ka fita wanka zanyi"
ta fada tana masa alamar nuni da yatsa, gani tayi ya fara cire kayansa, bata manta haduwarsu ba ranar, tayi saurin jawo kayanta zata maida ya rike mata su, wurgi yyi da kayan ya dauketa cak ya tsunduma  ta cikin ruwan data tara shima yabi bayanta.

******
Koda su inna suka isa gida sai suka tarar da mlm sabo shigowar sa gidan kenan, binsu da kallo yyi lkcn da suke zama yace,
           "daga ina kuke haka nazo gidan ba kowa?" Inna tace,
              "daga wajen tsinannen yaron nan muke haruna"
mlm sabo yace,
             "meya hadasu harda zagi haka?"
              "Toh ba dole na zagesa ba? Wai sbd shi tantiri ne ya saki jamila" inna ta fada tana kumfar baki,
               "Saki?"
Mlm sabo ya fada hankali tashe,
               "Ehmana saki biyu yyi mata shine na sata a gaba nace muje ya cike sauran dan bamu gaji wulakanci ba."
               "Innalillahi wa'inna'ilaihin raji'un" mlm sabo ya fada yana rike kai yace,
               "haba saude ya da girman ki kike abin yara?"
              "Ban gane ba?" inna ta tmby tana tsare shi da ido, cikin jin haushi yace,
             "kin kashe mata aure mana memakon naji sasanci kikaje musu wannan abinda kukayi duk shiriritace wlh Mtwsss"
yaja tsaki,
              "Kai sabo yaushe ka fara canjawa ban sani ba? 'Yarka fa aka cima mutunci"
mlm sabo ya kalli jamila da tayi tsumu2 cikinsu yace,
             "ke tashi kibar nan"
sum2 tabar gun kuwa, kafin ya maida kallon sa kan inna yaga ta zare masa ido, abinda yaso fada ya makale sbd shakku daya darsu a ransa, cikin nutsuwa ya canja akalar zancen  yace,
              "ba canjawa nayi ba, gani nayi 'yan mata sunyi yawa a gari haka ma zawarawa, to ita Allah ya rufa mata asiri da aurenta kin tsinka mata shi ba'asan wanne kalar miji zata aura ba nan gaba."
Inna tace,
              "Idan dan wannan ne ai tazo gidan sauki, suma mazan akwai su dayawa a gari jamila son kowa kin wanda ya rasa tana gama idda zata samu miji kai kafin ta gama ma zasu fara taruwa ana jira sai wadda ta zaba."
Zuba mata ido yyi yasan jamila duk kamannin ta ta  debo ya girgiza kai kawai ya bar musu gidan.

Yana fita jamila ta fito tana tura baki, inna tace,
             "kyaleshi muna nan dake sai yazo yana karamar murya idan yaga kin samu Alhji"
dariya jamila tayi tace,
               "harna hango ina fantamawa yadda nakeso"
             "sosai ma kuwa" inna ta fada tana dariyar itama,
             "Yauwa waini inna na tmbyeki?"
               "Inajinki"
inna ta amsa,
              "wai ya lbrn ummi ne tunda tayi aure tazo kuwa?"
Inna tace,
              "me zatazo tayi? Ai tun da akayi auren nasa sabo yyi mata gargadi karta soma zuwar mana gida dan mun gama bayarta kenan taje ta karata da wannan mahaukacin kilama ya gama karairaya ta dan inajin lbri a gari mahaukacin irin riqaqqun nan ne basajin mgni" dariya jamila tayi tace,
             "kai zanso ganin idon ummi yanzu haka ta lalace kilama har wankin kashi take masa hhhhh" tayi mgnr tana dariya, inna ma dariyar tayi, jamila tace,
             "aiko gobe zanje na gano mana rahoto" inna tace,
             "kwarai kuwa amma kiyi baya2 kar ya sauke haukansa a kanki" jamila tace,
              "ai dole ma nayi taka tsantsan"
ahaka dai sukaci gaba da gulmar ummi suna dariya.


••••••••
Washe gari ummi na gyara parlo yyinda el-bash ke zaune kan doguwar kujera yana bin duk wani move dinta da kallo, knocking sukaji ummi ta jawo hijab dinta ta saka, zuwa tayi ta bude kofar wara ido tayi tana mmkin wacce ta gani a kofar, farinciki ne ya kamata da fara'a tace,
             "oyoyo jamila" jamila tayi sakarere tana kallon ummi data canja mata lkci daya kamar ba itan ba, shigo mana ummi ta katse mata tunani, shigowar tayi tana me sake bin ummin da kallo tace,
                "ke anya mahaukacin kika aura?" Tayi mgnr tana zagaye ummi batare data lura da el-bash yana parlon ba, dan yake ummi tayi tace,
              "zauna mana jamila ko ruwa fa baki sha ba"
tayi mgnr tana juyawa hanyar kitchen,
         "kan uba"
jamila ta furta a hankali tana rike qugu, juyowar da zatayi taha El-bash kan kujera fuskar sa babu alamar fara'a ya gane fuskar matar tun ranar da suka kawo masa ummi ya fahimci akwai wata a kasa tsanin su abinka ga wanda yasan kan aikin sa.

Kusan diriricewa tayi, dan tayi mugun tsorata da ganinsa ga kuma mmki fal ranta dataga ya canja babu wannan qasumbar me yawa, yyi fresh dashi duk wanda ya ganshi bazaiyi zaton baida lpy ba.
            "Gashi"
taji ummi na mgn a bayanta. Adan kunyace ta juyo sbd ta tarar ta tana karewa mijinta kallo.
Basarwa ummi tayi bata nuna ta ganta ba, tace,
              "ga kujera ki zauna"
tayi mgnr tana zama itama. Zama jamilan tayi ta zubawa ummi ido tace,
                "wai ya naga abubuwa haka?"
Ummi tace,
               "kamar ya fa?"
               "Uhum yadda lbri yake zuwane ba haka na gani ba"
ummi tayi murmushi tace,
                "kinsan shi lbri idan za'a bayar dadine dashi mutum be sanin sanda zai kara mai gishiri."
Jamila ta tabe baki itafa ba yanda taso gani ba kenan, can tace,
               "kuma haka kike ta fama da wannan garjejen qaton a gida?" Ummi tace,
               "ban fahimceki ba?"
             "Toh ai gani nayi ba hankali har kika iya jure kashi da fitsarin sa" rintse ido ummi tayi tana tunanin yadda mutane suka kasa fahimtar El-bash yanda kasan A/C haka yake a waje zafi a ciki sanyi fahimtar da tayi masa kenan adan zamanta dashi. Yyinda jamila ta samu damar juyawa gefen El-bash tana kare masa kallo musamman data ga ya lumshe ido, tana ayyanawa a ranta inama ita aka bawa mahaukacin dan kallon fuskar sa kadai ya isa a zauna dashi.

Ummi na bude ta sake kama jamila na kallon el-bash, wani irin abu taji yazo ya tokare mata kirji da sauri tace,
              "jamila tashi muje dakina ki gani ranar da kukazo babu dama."
Dan yatsina fuska jamilan tayi bataso ta musa ummi ta gane asirin zuciyar ta dan haka tabi bayanta tana dan juyowa ta kalleshi a sace.

Yini jamila tayi a gidan koda taje dakin ma kasa zama tayi dan haka tace zata sauka kasa, ganin haka ummi ta riko hannun el-bash ta maida shi daki tana fita kuwa yyi dariya yanajin dadi a ransa ashe ummi na sonsa haka? Tunda ya hango kishi a idonta, takaicine ya kama jamila tace tafiya zatayi, ummi kuwa ta hado mata sha tara ta arziki,  har bakin gate ta raka ta, lkcn mlm sabo na zaune ummi ta matsa ta gaishe shi ya amsa mata sama2 babu sakin fuska kamar kullum, a sanyaye tabar gun tanajin wani iri a ranta,yyinda jamila tayi tafiyarta gida wani daci na taso mata arai, duk yadda za'a sai an aura mata El-bash ai ba cikinsu daya da ummin ba kazalika ba ubansu daya ba ehe. Haka tayi ta sakawa da warwarewa harta isa gida.


~~~~~~
Bayan kwana biyu, suraj ya kawo musu ziyara gidan shi da wata yarinya wacce bazata wuce sa'ar ummin ba anace da ita Aisha, lkcn ummi suna parlo tana kallo ta juya taga el-bash ya zubama kallon ido, sai taji ya bata tausayi a tunanin ta ita kadai keyi batasan kuwa shima kallon yake kamar ita. Suna hakan suraj sukazo, ummi da fara'a ta tarbesu shima el-bash murmushi yake batare da yace komai ba, kusa dashi suraj ya zauna ita kuma yarinyar me suna Aisha ta zauna kusa da ummi suna gaisawa, ummi tace,
              "oh sai yau suraj aka kawo min aysha" aysha tayi dariya tace,
             "kuma lefin shi ne" suraj yana dariyar shima yace,
             "au hademin kai zakuyi dan na hada ku?" Ummi tace,
             "ai gskyne"
suraj ya kama hannun El-bash yace,
              "bari naja abokina muje baya muma mu hada kai".
dariya sukayi masa a tare sukace,
                "kodai zancen kurame ba"
dariya el-bash yyi sbd ya juya musu baya bazasu ganshi ba, suraj yace,
             "hakan ma yafi dadi ya zuramin ido na gwalala masa ido"
daria suka sake yi masa be kara cewa komai ba sukabi ta corridor din kitchen inda zai sada su da garden din part din.

Suna tafiya Aysha tace,
               "ummi ko awaya bakya nemana, inason nazo gunki wlh toh abubuwan ne sai a slow yanzun ma dan kince nazo na miki kitso ne" ummi tace,
              "kinsan ba waya a hannu na, idan na rikema wazan kira tunda kullum muna tare"
cikin tausayi aysha tace,
            "Allah ya bashi lpy"
            "Ameen" ummi ta amsa tana fadin kafin su dawo,
             "kama min kan nawa wlh tunda nayi auren nan bega kitso ba" aysha ta cire gyalenta tace,
              "kawo kayan kitson nayi miki ko shida ne"
ummi ta haura sama ta kawo nan aysha ta dinga mata kitson sharp2 ta gama. Ummi ta tashi tace,
              "kai gsky ya kamata ki bude saloon aysha"
aysha tace,
                 "koh?"
              "Ehmana kitson masha Allah"
ummi ta fada tana shafa kai.

*Wacece Aysha?*
Aysha Yusuf budurwar Suraj ce wanda ake shirye-shiryen bikinsu nan da dan wani lkci, da tuni ma anyi bikin suraj ya roki Alfarma a kara masa lkci sbd aikin da suke gudanarwa musamman na a mutu ne ko ayi rai?? Yana gamawa za'a sha bikinsa, to el-bash ma haka yaso idan sun gama ya nemi macen aure sai gashi auren yazo masa yna tsaka da aiki to dama haka Allah ke ikonsa kana naka ne yana nasa kuma nasan shine daidai. Suraj da yawan lokuta idan yazo yana hada ummi da aysha a waya har sukayi sabo kamar sunsan juna, mutunci ne me tsafta ya kullu a tsakanin su.

••√√√
Suraj ya kalli El-bash yace,
         "jibi ne fah"
          "Insha Allah" El-bash ya fada yanajin kamar ya jawo jibin tazo kusa, suraj yace,
           "ya naga sai doki kke ko akwai wani abune?"
Dan murmushi El-bash yyi ya rike kirjinsa saitin zuciyar sa yace,
            "nan wajen ya kosa ya fitar da abinda ke ciki" da mmki suraj yace,
             "kai nifa ban gane ba"
El-bash ya harareshi yace,
             "Ummina mana na kosa na sanar mata *ABINDA KE RAINA* i so much love her" 
yyi mgnr yana lumshe ido yanaji a ransa inama ummin ya furtawa hakan, wata irin dariyar shakiyanci suraj yyi yana rike ciki yace,
            "Gske kke kuwa?" Bude ido el-bash yyi yana murmushi, suraj murna ta kama shi dan bayaso ummi tasha wahalar banza, cikin tsokana yace,
              "but when? How? Little ce fah."
El-bash yce,
              "toh sai kayi kuma kaifa iskancin ka nada yawa mtwss"
dariya suraj ya sake yi yace,
                "haba maida wuqar ai dole na tayaka murna yanzu ka shigo system din"
               "toh sharukhan uban soyayya"
El-bash ya fada yana hararar sa, suraj yace,
              "haba waneni ai ka wuce tunani na yanzu ni dan kallo ne"
El-bash yace,
                "kaga mu koma bangaren aiki."
Nan suka fara lissafin yadda zasu kasance a wajen.


°°°°°
A daren ranar haj suwaiba ta gama tsara yadda zasu dauke ummi, duk wani shirinta ta gama tsaf.

Yyinda a bangaren ummi haka kawai ta dinga jin faduwar gaba, tun safe takejin haka saidai faduwar gaban be tsananta ba kamar yanzu da dare yyi, harta kwanta ta mike dan a dakin el-bash take, batason tashin sa ta fita a hankali lkcn besan da fitar ta ba sbd bcci yake, ummi dakinta taje tayo Alwala sbd bugun qirjinta ya tsananta, ji take kamar akwai abinda zai sameta me muni dan haka ta kabbara sallah dan kai kukan ta wajen Rabbi,

kusan kwana tayi tana sallah hade da tilawar Qur'an duk wata addu'a data sani ba wacce bata karanta ba, ummi har asuba taje a takaice dai bata iyayin bcci a ranar ba, anan dakinta tayi sallah idonta duk ya kekashe babu alamun bcci jikinta yyi sanyi kalau.

El-bash be farka ba sai asuba anan yaga ummi bata nan, zaton sa toilet taje yaji ba motsi nan yasa a ransa kila dakinta taje dan haka shima ya fada toilet danyin Alwala.

Koda ummi tayi asuba bata fasa Addu'ah ba hankalin ta ya tashi sbd matsanancin faduwar gaba da takeji, sam bazata iya bcci ba da rana ta fito ta tashi ta gyara daki, bayan ta gama ta leka dakin el-bash taga yana bcci jawo kofar tayi ta gangara kasa, nan ta gyara parlon tsaf taje tayi musu breakfast tana tsaka da jera abincin ya sakko, murmushi tayi shima ya maida mata da murmushin yana wara mata hannu, zuwa tayi ta fada kirjinsa ya rungume ta yana kissing dinta. A haka suka karasa kujera ta jawo musu abincin.

Saida suka gama cin abincin taji wani irin nannauyan bcci yazo mata, kan kujera ta koma ta kwanta dan batajin zata koma sama dan idonta yyi nauyi. El-bash ganin ta kwanta ya gyara mata kwanciyar sannan ya haura sama sbd aikin da zasuyi gobe yana bukatar shiri mekyau.

Barinsa wajen keda wuya aka turo kofar parlon a hankali, ummi ta manta bata rufe ba, dan haka aka samu damar shigowa, mutum biyune masu shigowar kowa ya rufe fuska, haj suwaiba ce da erta sakina, wani farincikine ya kamasu da alama bazasu wahala ba, cikin sauri haj suwaiba ta ciro farin kyalle ta manna a hancin ummi, batare da bata lkci ba suka sungumi ummi wacce ta zama kamar gawa, har cikin mota suka ajeta,

lkcn haj suwaiba ta aiki mlm sabo badan tana bukatar aikan ba saidan bataso ya gani tunda ya hada dangantaka da ummi, sakina ta koma part dinsu da sauri yyinda haj suwaiba ta fice da ummi a tamanin.

El-bash besan wainar da ake toyawa ba saima yana aikine a jima yyi murmushi sbd gab yake daya balle zuciyarsa dan gayama abar kaunar sa ummi abinda ke ciki, jawo wayarsa yyi ya kalli hoton ummi daya dauka tana bcci, wayar yakai bakinsa yyi kssn dinta yana mannawa a kirji zazzafar soyayyar ummi na ninkuwa a ransa.

Continue Reading

You'll Also Like

Alina By ihidethisapp

General Fiction

1.5M 38.1K 75
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...
73.9K 3.5K 164
Mo Chen traveled to the Collapse World and obtained a character strategy simulator. In simulation after simulation, he conquered the conquerable char...
234K 14.2K 45
The feeling of being abandoned by one's own family was not unknown to Aadhira. She hates her family for abandoning her when she was only a newborn, l...
20.5K 1.8K 7
Wanna visit rajasthan than read this special book about my love Rajasthan 💗