"Subahanallah Allah ya sauwak'e ubangiji ya kare gaba nima yau nake saka ran sallamar insha Allah da zarar an sallameni zanzo gidan naduba Amrah".

"To Yaya Allah ya k'ara maka lafiya".

Daga haka sukayi sallama, bayan Ummah ta ajiye wayar ne ta kalli Abbdallah tace; "ashe har gurin Yaya ka shiga neman Amrah?".

"Wllh kuwa Ummah nashiga har ma mun gaisa sannan nafito".

Murmushi tayi sannan ta kalli Amrah tace; "tinda anbamu sallama ai saiki tashi mu wuce gida tinda ba komai zamu d'auka ba".

Tashi Amrah tayi tana ta k'ok'ari gurin ganin ta had'e k'afofinta tayi tayi tafiya dai dai amma abun ya gagara dole sai dai tayi tafiya kamar mai d'ingishi, ganin haka da Ummah tayi ne ya sata saurin kamata suka fice daga d'akin, da kallo Abdallah ya bita domin shi dai abubuwa da yawa ne aransa na farko babu rauni ajikin Amrah wanda zai nuna alamun tasamu hatsari ne, ko yar kujewa babu na biyu kuma babu inda nata yake ciwo sai k'afa lallai wannan abin dubawa ne, amma koma miye zaiji daga baya idan ma likitan ne be duba ta da kyau ba sai ya kaita wani asibitin da wannan tinanin dai har suka isa gurin motar daga nan suka d'auki hanyar gida.

*********    ***********    *********

Mama Hindatu ce zaune a gaban bokan da k'awarta Altine ta rakota gurinsa kallon su yayi sannan yace; "ku fad'i abinda yake tafe daku".

"Dama boka aiki nakeso ayimin akan wani yaro da yake tare da yarinya k'anwar mijina har akwai maganar aure ma atsakanin su, to so nake a juyar da wannan soyayyar daga kan Amrah ta dawo kan yarinyar wajena Salma".

"Menene sunan yaron?".

"Sunan sa Abdullahi".

"To za ayi miki aiki sannan ina fatan wacce ta kawoki ta sanar dake k'aidar aikin mu?".

"Eh ta sanar dani kuma nazo da kud'in da za a nemo duk abinda ake da buk'ata".

"Ku ajiye ku tafi za ayi muku aiki nan da kwana uku ki dawo ki karb'i sak'o".

"To boka mungode Allah ya saka da.......keee! Ba akira mana Allah anan kinsan da Allah kika zo gurinmu neman temako ku b'ace daga ganina kufita da baya baya".

Jikinsu ya na rawa suka soma fita da baya domin tsawar da boka Urdu ya daka musu ta firgita su sosaiii suna fita daga bukkar suka kwasa aguje domin atsorace suke.

**********   *********   ***********

Tinda su Ummah suka dawo gida Amrah ta shige d'akin ta tak'i fitowa kuma tak'i cewa da Abdallah komai duk maganar da zaiyi sai dai ta kalleshi da ido, Ummah kuwa duk tana lura da yadda Amrah take share Abdallah dan haka yau ta yanke shawarar samunta domin taji abinda ke faruwa.

Yau kimani kwana uku kenan da dawowar su Amrah daga asibiti kuma yau ne Ummah ta samu Amrah kan maganar Abdallah, kallon Amrah Ummah tayi tace; "wai Amrah me yake faruwa ne tsakaninki da yaron nan Abdullahi? Duka a 'yan kwanakin nan naga duk maganar da zai yimiki bakya amsa masa sai dai ki rik'a binsa da ido to ina son sanin abinda ke faruwa?".

K'asa Amrah tayi da kanta domin harga Allah ba tasan abinda zata fad'awa Ummah ba, dan ita dai tayiwa kanta alk'awarin bazata fad'awa Ummah abinda Abdallah yayi mata ba saboda abin yayiwa bakinta nauyi, kuma taga shima Abdallah bashi da niyar furta abinda ya faru tsakaninsu sai ma wani rena mata hankali da yakeyi ya na nuna baisan abinda ya faru ba.

"Wai Amrah tinani me kikeyi haka? Nayi miki tambaya baki bani amsar tambaya ta ba saima kika tafi wani tinani na banza".

"Yi hak'uri Ummah sannan kuma babu komai tsakanina da Abdallah kawai bana son yawan hayaniya ne shiyasa kikaga inayin shiru idan yamin magana,  saboda da zarar na kulashi zai isheni da surutu".

"To amma dai wannan ba dalili ba ne dan haka bana so na k'ara ganin kiyi masa irin haka".

"To insha Allah Ummah bazan sake ba".

Daga haka suka cigaba da hira irin wacce 'ya da uwa sukeyi atsakaninsu.

Kamar yanda boka ya cewa Hindatu ta koma bayan kwana uku ta karb'o sak'o to hakan ce ta kasance domin yanzu ma sune zaune a bukkar boka Urdu yayinda ya mik'awa Hindatu wani laya yace;

"Wannan zaki binne abakin k'ofar gidan su Amrah da zarar Abdullahi ya tsalaka wannan layar shikenan zai daina son Amrah soyayyar zata koma kan Salma".

Karb'a tayi cikin murna da farin ciki domin bata da burin da ya wuce rayuwar Amrah ta wulak'ance sallama sukayiwa boka Urdu sannan suka fito cikin sauri suka nufo cikin gari.

Da misalin k'arfe 5:30pm Abdallah ne da Amrah zaune a tsakar gida gefe guda kuma Haseep ne yake wasa, Ummah kuma bata nan taje dubo Kawu Sageer dan a sallemeshi yanzu yana gida.

Kallon Amrah Abdallah yayi yace; "nikam princess dan Allah ki fad'amin gaskiyar abinda ke faruwa dan wllh ko kad'an ban yarda wai me mota ne ya bigeki ba,  kuma nasan bakya yimin k'arya dan Allah a yau ma inaso ki sanar dani gaskiyar abinda ya faru dake plss".

"Hmmm wllh Abdallah kana bani mamaki saboda kana k'ok'arin nunamin kamar bakasan abinda ya faru tsakanina da kai ba, to ina so kasani idan ma zaka b'oyewa wasu ni baikamata ka nunamin baka sani ba saboda ni akaina ka aikata, amma kasani ni nayi maka uzuri domin nasan soyayyarka agareni gaskiya ce amma kuma bansan meya kaika aikata zina dani ba, idan natina lokacin daka keta min mituncina abin yana d'agamin hankali sosaiii bansan dalilinka nayin haka agareni ba amma koma menene kai kasan kayanka kawai abinda nakeso dakai shine ka turo ayi magana asaka mana rana domin ina gudun ka sake maimaita abinda kayi agaba amma indan akayi auren shikenan".

Cikin tashin hankali had'i da firgici Abdallah ya mik'e tsaye ya na fuskantar Amrah domin acikin idanunta ya hango tsantsar gaskiyar abinda take fad'a, durk'usawa yayi agaban ta tare da furta innalillahi wa inna illaihiri raji'un, Allahummah ajirni fi musibati, kallon sa Amrah tayi taga yanda hawaye yake zuba a idanun sa tamkar mace cikin tashin hankali tafara magana;

"Subahannallah dear lafiya kuwa? Me ya faru kake kuka? Dan Allah kayi min magana idan ba so kake zuciyata ta buga ba, dan yanzu ba komai zuciyata zata iya d'auka ba dan Allah kayimin magana".

D'ago jajayen idonsa yayi ya sauk'e su akanta yaga yanda lokaci d'aya ta birkice saboda ta ganshi yana kuka, murmushin k'arfin hali yayi sannan yace; "Amrah har yanzu kina sona?".

"Ina sonka sosaii Abdallah soyayyar ka ita ta sanya nakasa sanarwa da mahaifiyata asalin abinda ya faru tsakaninmu saboda banaso tayi maka mummunar fahimta".

"Nagode Amrah da wannan soyayyar da kike min duk da na aikata babban lefi kuma lefi mafi muni agareki amma baki tsaneni ba saima kariya dakike k'ok'arin bani nagode sosaii kuma nima insha Allah Allahu bazan baki kunya ba idan kin amince nanda sati biyu za a d'aura mana aure".

"Na amince Abdallah domin auranka shine babban burina".

Tashi yayi yana yi mata murmushi yayi mata sallama kan zai dawo da daddare, yana fita ya ciro wayarsa daga aljihunsa ya danna kira a number da aka rubuta *ABDALLAH* da manyan bak'i........✍🏻

_ina yimana barka da juma'a_

                    _*🌹SHATU CE🌹*_

*#Comment*
*#Vote*
*#Share*

_*Aysha Idris Abdallah*_

MATAR ABDALLAHWhere stories live. Discover now