"Har yanzu banga ta inda na can-canci wannan sadaukarwar ba? Har yanzu faɗuwata na ke gani da kuma raunina a duk lokacin da na ke tsaye a gabanki! Mutane da yawa suna cewa na samu Lu'u-Lu'u mafi daraja a rayuwata, a yayin da suke hasko min fuskarki a tafukan hannayensu.
   Na ɗauka Nasarata zata zo ne bisa dagewata da aikina tuƙuru, ashe ɗaukakata na gare ki.
Bana so na ci gaba da yin rayuwa sadaka da kuma ɗaga matsayin da ba gumina ba ne Nabeeha, wannan matsayin ba zan taɓa samunsa ba, domin zuciyata bata da kyan da zata kula da shi! Ba zan iya ci gaba da gani na akan matsayin da kika sadaukar min ba!" Ta ƙarasa maganar hawaye na sauƙa akan fuskarta, hawayen da take ganin kamar sun gaza wajen nuna damuwarta da kuma tsananin nadamarta.

     "Wa ya faɗa miki gwagwarmayar ba taki ba ce? Wa ya faɗa miki a matsayin sadaka na baki?" Ta yi saurin katseta, tana murmushi akan fuskarta, a yayin da take ƙoƙarin tsayar da hawayen fuskarta.
    Ɗagowa suka yi duka suna kallonta dan jin amsar maganar da ita kaɗai ce zata ba su.
     Ruƙo hannunta ta yi ta ɗora akan nata, sannan ta ɗan matsa shi da ƙarfin da ya rage mata. Zafin hannun nata na ratsa ko wata ɓula ta jikin Nabeela tana jin yana tatsa ko ina na jikinta.
   "Daga lokacin da na fara aiki sai nake ji a raina burinki nan wannan matsayin, ni bani da sha'awar samun damar da sunan da na samu. Hakan yasa na ci gaba da yin aiki kamar yanda nasan da ke ce a wannan matsayin za ki yi shi, zaki kuma so sunanki ya dinga yawo a duniya.
   Sunan ne yake futowa kawai a jikin aiyukan da nayi, amma zuciyata na cike ne da hasashen yinsa kamar yanda zaki yi. Yana kuma tuno min da abubuwan da kike yawan faɗa inda kin samu damar yinsa. Sai dai ban same ki ba, ban ji daga gareki ba har sai a ƙarshen watan da ya rage min."
  Murmushi ta sake yi tana lumshe idanuwanta "Ƙaddara ta daɗe tana bibiyar mutane da sauya musu arashin su. Lokacin da na yanke duk wani buri da kuma sa rai akan ganinki, a lokacin kuma ƙaddara ta bayyanar da sunanki a gabana."
  Idanuwanta ta sake lumshe tana jan numfashi, ba zata iya tuna yaushe ne ta yi doguwar magana haka ba. Kamar yanda ba zata iya tuna adadin lokutan da ta samu kanta fayau babu nauyi ba. Wata ƙila dama ce Allah ya bata, damar da take ji itace ta ƙarshe a gare ta. Sai dai ko ba komi burikanta ya cika, ta cika mafarkin da ta daɗe tana son tabbatarsa.

    Ƙara matsa hannun Nabeela ta yi, tana jin kamar za'a iya ƙwace mata "Ki sa hannu dan Allah!!" Ta faɗa cikin raunin muryarta da ta fara ja baya.
   A yanzu bata da zaɓi, duk yanda ta ke son ta guji faruwar hannunta akan takardun ba zata iya ba, karon na farko da Nabeeha ta roƙeta akan abin da ta saba bata ba tare da ta roƙa ba.
   Hannunta har rawa yake ta sa hannun, tana jin hawayenta na tsananta zuba a kan takardun.
  Har zuwa lokacin da ta gama sannan ta miƙa mata takardun. Da kai ta yima Na tsayen alama ya ƙaraso wajenta.
  "Ka kira Lutfi ka ba su suna jira dan Allah." Bai bari ta ƙarasa ba ya kara waya a kunnensa ya yi magana, ba daɗewa ya amshi takardun ya futa da su.
Mintuna uku ya sake dawowa ya matso kusa da ita yana shafa kanta da murmushi akan fuskarsa.
   "Na basu, sun tafi, duk da sun so ganinki  kafin tafiyar su."
  Ido ta lumshe tana murmushi, sannan ta kama hannunsa ta ɗora akan na Nabeela sannan ta ɗora ɗaya hannun nata akan nasa, hakan ya sa suka kalleta a tare, suna buɗa idanuwansu duka a kanta.
    "Ina da sauran burin da bai cika ba. Burin da yasa na yi nesa da ƙasata ya ƙara matsar da ni daga inda na ke." Ta yi maganar tana shigar da idanuwanta kan nasa, da ya ke jin kaifinsu da tasirinsu na huda zuciyarsa, wani shauƙin da ya daɗe yana ji akan su yana ƙara tasirantuwa a zuciyarsa.
    Nabeeha da ban take, ita kaɗai ce mace guda da yake jin soyayyarta a duk tsawon rayuwarsa.

      "A lokacin da idanuwana suka rufe nasan idanuwan duniya za su dawo gare ku, bani da tabbaci akan sanu kwanciya mai kyau da amsa tarin tambayoyin da za su zo gare ni a bayan babu ni. Amma idan kuka zama a ƙarƙashin inuwa ɗaya kalmar son kai da son zuciyar da nake tunanin ina da su za su ɓacewa idanuwana na.
  Ba iya yau kaɗai ba, nasan lokuta masu yawa na sha yin addu'a akan cikan wannan burin. Dan Allah Nu'aym ka maye gurbina da Nabeela a bayan idanuwana! Ka bata matsayin da ka bani a zuciyarka! Ka mata kallon da kake min! Wannan kaɗai nake buƙata a wajenka, wannan kaɗai nake so daga gareka! Na tabbata itace mace ɗaya da zata kula min da yara na. Itace mace ɗaya da zata zauna da kai ta so ka kamar yanda nake sonka.
   Ina so na ji a raina ban bar ɗayanku cikin neman madogara da samun mutumin da zai jingina da shi ba. Ina so na samu aminci a lokacin da mutuwa zata ɗauke ni a yayin da mutane biyun da nake so a duniya sun zauna ƙarƙashin inuwa ɗaya! Ku min alƙawarin zaku zauna a tare da juna? Ka mun alƙawarin maye gurbina da Nabeela. Dan... Allah .. Nu.. Nu'aym!" Ta yi maganar tana jan numfashi, muryarta ta fara sarƙewa daga saurin da take, kafin wani lokaci numfashinta ya fara marazanar barinta.

   "Dan Allah!" Ta yi maganar tana ƙoƙarin sakin hannunsu.
   Ruƙe hanunta ya yi gam akan nasu yana  jin sauƙar hawaye na ƙaruwa akan fuskarsa, ji yake kamar zuciyarsa zata iya tsalle ta faso ƙirjinsa.
   "Ba abin da zai same ki Nabeeha! Ba zaki mutu ki barni ba! Zan auri Nabeela kamar yanda kike so na miki alƙawari, amma kada ki mutu ki bar ni dan Allah!" Ya yi maganar a ruɗe yana jin kalmomin suna tafiya suna gujewa daga gare shi.

     Sai dai kamar ya makaro, dan baya jin akwai kalmar da zata iya sake futowa daga bakin Nabeeha bayan murmushin da ta masa tana lumshe idanuwanta da ƙoƙarin sakin hannunsa.
    Da sauri ya danna ƙararrawar da ke kusa da gadonta, yana dannawa kamar zai iya fasata saboda gani yake kamar bata isa inda ya kamata ace ta je.

    Nabeela da jinta ya yi ɗaukewar wucin gadi ya samu dawowa a lokacin da ƙaran ƙararrawar ya cika kunnenta.
  Gani take kamar mafarki ta ke ba wai gaske ba ne, duk abin da Nabeeha ta ke faɗa mata kamar kunnuwanta ne suka yi kuskuren ji kamar yanda suka saba. Ko kuma ruɗewar mafarkin da ta saba yi ne a cikin mafarkanta.
  Nabeeha ta bar mata komi, komi da ta mallaka harda mijinta tana kuma kiran zata mutu ta barta.
  Bata san ya akayi ba sai da ta tsinci wasu mutane masu fararen kaya na jan gadon Nabeeha suna futa da ita, tana kallon Nu'aym na binsu kamar zai tashi sama, gani take kamar shima yayi zaucewar da ta ninka ta ta.
  Da ƙyar ta cira ƙafafuwanta tana bin bayansu tana son ace ta kai inda suke, sai dai takunta baya gamsar da gangar jikinta, asalima kamar yana ƙara matsar da ita ne zuwa baya.
  Har zuwa lokacin da ta ga sun shige da ita wani ɗaki sun rufe musu ƙofar.
     Tana jin sautin kukan 'Yan uwan Nabeeha da kuma 'yan gidansu, tana jin kaiwa da kawowar da Nu'aym yake wanda ita ta kasa.
   Idanuwanta na tsaye a kan ƙofar ɗakin da aka shigar da ita ɗakin tana ga kamar idan ta lumshe idanuwata ƙofar ba zata buɗe ba.
  Bata san adadin lokutan da ta ɗauka a tsaye a wajen ba, sai dai taga ƙofar ta buɗe a karo na biyu. Likitocin sun fara futowa, ya yin da 'Yan uwa suka yi caa a kansu suna tambayar ya take.
  Daga inda take tsaye bugun zuciyarta na ƙaruwa, kamar zata faɗo daga maɗaukarta, tana jin lokacin da kunnunwata suka yi mugun ji daga bakin gajeran Likitan mai kakkausar muryar da bata taɓa jin irinta ba.
   "Ku yi haƙuri Allah ya amshi rayuwa Nabeeha Nameer! Ina miƙa ta'aziyyata gare ku!"

  Bata tsaya jin ƙarshen kalmar ba, bata kuma buƙatar jin ta'aziyyar da yake mata ba, sai dai tasan jinta da ganinta ya ɗauke ɗif, tana fatan wannan ne gani da kallo na ƙarshe da zata yi a rayuwarta.....

    🌹🌹🌹🌹🌹

    Alhamdulillah! Wannan ina fatan kun gyara zama! Ina fatan kun shirya amsar saƙon farko a cikin labarin ƘAWATA CE! Zan Girmama ku a cikin ko wani shafi na labarina, domin nasan akwai ƙauna da mutuntaka a cikin wannan tafiyar.

#ƘWTC
#DABANNE

   PLEASE SHARE

Oum-Nass

ƘAWATA CEWhere stories live. Discover now