Book 1

3K 104 13
                                    

Typing🖊

               BAYA BA ZANI🥥🥥🥥🥥🥥🥥
  

By
Fadeela Lamido

  
  Wattpad fadilalamido

    ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

   *® _PEN: WRITER'S  ASSOCIATION_*

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

           

______________________________________

*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________

https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

   Bismillahi Rahamanir Rahim🖊

                
                  1-3

__________________________________________________________

........Abdullahi kasheni zakayi ne?, Wannan wanni irin wasa ne?, Wayo wuyana makorona, nashiga uku.......
Cikin tsanin haki wadda aka Kira da suna Abdullahi yace, gobema ki kara, Allah yaso ki ne kinban tausayi wlh dasai kinyi kuka zan barki"

    Karasa fincike rigarta tayi dake rike ahannnunsa Kuma wlh saina gayaka da Hajiya, kokarin Kara rukota yake cikin tsananin sauri ta kwasa da gudu ta fice dakin"

    Abdullahi kuwa fuskar sa cike da annashuwa ya sakko daga kan katifarsa yana lekenta ganin ta rufe kofar yasashi murmushi yana fadin waya gaya miki, labilen ya sake tare da komawa kan katifarsa ya kwanta"

Asma'u! ke Asma'u! Ina kika shiga Kuma?

    Wata tsohowa ke fadin haka yayin da take dire ledojin hannunta akasa da alama cefane tayo"

    Dobe dobe tafara yayin da ta nufi bandakin taji ana zare sakata daga cikin dakin ta dan haka ta juyo ta zubawa kofar ido"

    Kyakyawar yariya ce tsaye abakin kofar, wacce bazata wuce 16years ba, kanta babu kallabi yayin da gashinta yai wacce agadon bayanta"

     Karasowa tsohuwar tayi tana fadin, meyasame ki kikayi wujiga wujiga haka?

    Hannu tasa ta share zufar dake kwance afuskarta, ba Yaya Abdullahi bane ya shake ni, ya murdemin wuya kamar zai karya😭

   Subuhanallahi, me kika masa?

    Oho mishi"

   Tsaki tsohowar taja tare da daukan kayan miyanta tana kokarin juyewa ga roba tana cigaba da fadin"

    Kema ai bakyajin mgn, nace Miki ki daina shigewa Abdullahi saurin hannu garai aigashinan kinji ajikin ki"
  Idanu tabi tsohowar dashi tana me mata kallon abin da zakice kenan?, Harara ta zafgawa tsohuwar sannan ta Kara fitowa ta zauna ta zunbura baki, zuciyarta cike da haushi"

   Aikace aikacen tsohuwar keyi yayin da jefi jefi Asma'u ke zabga mata harara irin wadda ake Kira aikin banza harara adohu"

    Misalin karfe 6 na yamma tsowar ta gama duk aikace aikacenta dan haka ta nufi dakin Abdullahi tana me kwala masa Kira"

   Cikin yanayin irin na wadda bacci yama mugun kamu ya amsa, jin ya amsa yasata juyawa tare da daukan buta domin yin alwalan mangariba"

     Abdullahi kuwa fitowa yayi sanye da jallabiya Hajiya kika barni naita bacci baki tasheni ba har gari ya fara duhu"

BAYA BA ZANIWhere stories live. Discover now