A hankali memorynta ya tuno da ranan da sauri tace "yeah yeah na tuno shi amma gaskiya ba zan gane shi ba." Dariya tayi tana ji muflihan tace "toh kai kaji" duk sai kunya ya rufe maimuna dan tana da tabbacin wanda ake magana akai yana kusa kuma yana jin abinda tace.

Cikin ina ina tace "kin san uhm zan fita ya shigo toh kuma ban kalli fuskanshi ba." Dariya mufliha ta kuma yi abinda da bata cika yi ba kenan tace "karki damu ai na san ba zaki kalle shi ba,toh dai ni tun ranan ya sani a gaba wai sai na bashi number dinki ku dinga gaisawa ina ta mishi wala wala toh shine fa yau ya zo ya ritsani wai sai na bashi number din shine nace bari in kiraki in tambayeki tukunna."

Shiru duk su biyun suka yi,mufliha tana sauraron taji amsan maimunatu ya yin da ita kuma take kokarin tuno fuskan saurayin ta kasa and ita ba wani shirib welcoming issue din wani saurayi take yi ba she already have enough on her plate...

"Kanina ne maimuna,uncle dinsu ikram ina mai tabbatar miki ba zaki samu matsala dashi ba he is an easy going person."mufliha ta katse mata tunani ganin shirun nata yayi yawa.

A hankali maimunatu cikin rausayar da kai tace "toh shikenan maman ikram tunda kin ga ba damuwa ki bashi number din nagode."
Cikin murna mufliha tace "ah ah wallahi nice da godia for doing me such favour kina da kirki da hankali maimuna and i want the best for you." Murmushi maimuna tayi cike da kunya tace na gode daga haka suka yi sallama.

Tana ajiye wayan wani kiran ya shigo unknown number ne har ba zata picking ba sai ta picking.

Ajiyar zuciya ya sauke daga daya bangaren yace "i thought ba zaki dauka ba."
Dan yamutsa fuska tayi tace "wake magana pls?"

"Oops sorry! Taheer ne,taheer ke magana." Kara yamutsa fuska tayi dan still bata gane ba tana shirin cewa wani Tahir? Yayi carab yace "pls forgive my manners,sunana Tahir kanin aunty mufliha uncle din su ikram."
"Oh! Barka da dare." Ta fada a sanyaye.
Murmushi yayi me sauti yace "barkanki dai gimbiya,ya kike ya shirin shiga weekend?" Dan tabe baki tayi tace lafiya alhamdulillah.

Daga nan kuma suka yi shiru dan sam Tahir bai ga fuskan da zai cigaba da yi mata surutu ba.

A hankali yace "i hope ba zan zama takura ba a gareki?" Sai a lokacin ta dan saki murmushi tace "no haba kar ka damu." Ajiyan zuciya ya sauke yace "toh nagode i promise you wont regret knowing me." Mai da kanta kan pillow tayi tana murmushi tace "toh Allah yasa ameen."
"Toh maimunatu tell me about you,who is maimunatu and how many hearts did maimunatu break?"
Dariya tayi wanda ya ji shi har cikin kwanyan shi tace "ni maimunatu! I have never broken anybody's heart." A zuciyarta kuma tace sai dai ni da aka breaking min nawa ya kasa warkewa.

"Toh ni dai ki ban labarinki." Ya fada a shagwabe murmushi tayi da alama wannan mutumin dan daru ne tana shirin magana call ya shigo wayanta dan cire wayan tayi daga kunnanta ta duba caller id din.
"Hello kina jina?" Ya tambayeta jin tayi shiru da sauri tace "eh ina jinka,dan Allah bara in dau wayan boss dina." Dan jim yayi yace "that will be mubeena ko?" Zuwa lokacin wayar ta katse tace "eh ita ce." A hankali yace "pls do me a favour kar ki fada mata about me yet sai komi ya kankama." Tattara giranta tayi tace "why will i tell her about you? She is my boss fa,hold on gata ta kara kira." Bata jira amsansa ba ta picking call din dan bata so wayar ta kuma yankewa.
Wayyo sorry maimunatu na kira ki late na katse miki tadi." Rolling idanunta maimunatu tayi mutanen nan da iya cewa sorry tace "ba komi,i hope dai lafiya?" Gyada kai mubeena tayi tace "lafiya ba lafiya ba,yayana zai sauka a Nigerai 2am na yau,saboda akwai board meeting da za ayi sannan ya gama abinda yaje yi rannan monday din nan za ayi board meeting din karfe 10am." Ta karasa maganan tana nishi kaman wacce ta yi tsere gira daya maimunatu ta d'aga tace "okey?"
"We have new investors and i need you to be there." Da sauri ta tashi zaune tace "ban gane ba,mubeena kin manta ni serving nake yi why should i attend the meeting?"
Numfashi ta ja ta saki kafun tace "saboda ina so ki zauna a kujerana in nayi aure so i want you to impress my brother bana so in bashi labarinki ya ga kaman ina tura ki ne i want him to see what you are capable of shi da kanshi ba sai an gaya mishi."

Zaro idanu tayi tace "toh ni me zanyi a board meeting? Mubeena zaki saka ni a tsaka me wuya."
Juya idanu mubeena tayi tace "keh! I am the boss here and u will do as i say babu abinda zaki yi a wajen meeting din banda abinda kika saba yi a ko wani meeting."
Ajiyar numfashi ta sauke tace "toh i will do just as u say."
"Good ranan monday zaki yi elegant shiga be in your best and come early zamu tattauna akan abinda zamu yi."

Tace "toh inshaaAllah,nagode Mubeena nagode da soyayyar a gareni."
"Tsk ke kika sani,ni sai da safe joor." Daga haka ta kashe kiran
Dariya maimunatu tayi tana girgiza kai sosai take mamakin son da mubeena take mata tana so ta sake da ita su zama kawaye sam ta kasa ba a jininta bane yin kawa ko jalila kullum cikin yi mata complain na rashin kirki take tana son jalila tana respecting dinta na tsaya mata da tayi a rayuwa.

Sms ne suka shigo wayarta daga wajen suitors din nata uku,ko wannensu na mata fatan tayi bacci lafiya murmushi tayi a fili tace maimunatu mai mutane.


Monday da sassafe maimunatu ta fita bayan ta jera adduoin samun nasara da abinda yafi alkhairi a gareta saboda haka nan tunda suka yi magana da mubeena kan meeting din zuciyarta ke bugawa lokaci lokaci sai taji gabanta ya fadi.

Daren lahadi da kyar ta samu ta rintsa saboda fargaban da ita kanta bata san na menene ba.

Da safe ta tashi ta shirya cikin dogon wandon suite peach colour sai yar karamar riga milk colour da ta saka ta tuck in dinshi cikin wandon da yake har rabin cikinta. Jacket din suit din ta saka wanda ya rufe saman ass dinta kadan babu maballi a gaban rigar so a bude yake kana iya hango rigar ciki milk kala,cover shoe ta saka milk kala ta yane gyale peach a saman kanta sannan ta saka glass me haske,babu abinda ta shafa a fuskanta daga powder sai lip gloss me glowing.

Sosai tayi kyau gwanin sha'awa jakanta ta dauka milk colour ta fita tana adduan Allah yasa daddy baya palo ta dauki karamar motarsa.

Allah cikin ikonsa babu kowa a palon da sauri ta dau key din ta fita tana addua.

Duk sammakonta ta iske motoci a cikin company din ciki har da motan mubeena kusa da ita wata farar jeep ce kirar benz tabe baki tayi dan ta san yau dole a ga manyan motoci a wajen.
Office dinsu ta wuce direct,kofar office din mubeena a bude yake har zata shiga sai ta fasa jin ba ita kadai bace.

Da sauri aka shigo office din wani saurayi ne dauke da jakan suits a hannunshi me tsada yana sanye da khakin sojoji gira daya maimunatu ta daga a ranta tace tooooh masu abu da abinsu securities din ma nashi sojoji ne.

Cikin rawar jiki sojan yace mata "is my oga inside? " tabe baki tayi tace mishi "i really dont know,nima yanzu na zo." Gyada mata kai yayi ba tare da ya nemi izininta ba ya kutsa kai cikin office din mubeena bata yi mishi magana ba ko ta hana shi dan wallahi bata shirya yin battle da soja ba.

Tana nan tsaye tana fito da aikinta taji tsawan da ya hargitsa mata hanjin cikinta.

"Will you get out of here? Does this look like my office to you? Useless fellow." Da sauri sojan ya fito ya wuce maimunatu dake tsaya a sandare tana kokarin tantance muryan da taji.

Bayan sojan tabi da sauri amma kash elevator din ya sauka stairs ta bi dan ta cimma shi ta tambaye shi wanene oganshi bata so ta tabbatar da abinda kunnanta ya jiyo mata.

Tana bude kofan elevator din da suma suka biyo ya bude mubeena da mufliha a gefe da gefensa

Lokaci daya idanunsu ya sarke waro manyan idanunsa yayi yace "WHAT THE UGLY FUCK!"









*A nan zamu dakata sai in Allah mai komi mai kowa ya kai mu bayan sallah Allah yasa muna daga cikin yantattun bayinsa yasa muga farko da karshen azumin nan lafiya and also pray for me Allah yasa karshen azumina kenan a gida🙈Allah ya biya mana buqatun mu baki daya ya sada mu da alkhairinsa ameen thumma ameen*

_i am going to miss you guys sosai wallah i love you so plenty_ 💕💕💕💕

KINA RAINAWhere stories live. Discover now