page 27

2.3K 205 103
                                    

💖KINA RAINA💖








By Sawwama A.







Wattpad @sawwama14







Page 27.





Yana shirin magana ta dakatar dashi ta hanya katse kiran,fadawa tayi kan gadonta tana mai da numfashi a hankali ta tashi zaune tana kiciniyar cire hijab dinta dan dama ta idar da sallah ne.

Har ga Allah tayi fatan ace babu maganan auran wata a tattare da khalid da tafi kowa farin ciki,khalid shine mijin da zata aura kawai ta samu kwanciyar hankali ba tare da tuno da wani marwan. Tun ba yau ba ta san khalid yana da hikima da tsari na lallaba diya mace ya iya tarairaya,iya bi da macensa ya sa ta fara sonshi kafin tafiyarta cyprus kafin marwan ya shigo rayuwarta.

Marwan ba kowa bane face fasiki dan da ta biyewa marwan kilan da tare da dansa ko diyarsa yanzu, gaba daya in ta duba kudu,gabas,da arewa sai ta ga sam marwan bai dace da rayuwarta ba,marwan ba mutumin kirki bane duk namijin da zai so ya kebe da macen da ba muharramarsa ba lallai dan iska ne. Ita ko me ya rufe mata ido har ta fada soyayyarsa? Ko da yake kadan daga aikin samarin shaho sun san duk ta yanda zasu bi su cusawa mace soyayyansu daga baya su zame su barta da ciwo a zuciya.

In ta zauna tana tariyo rayuwarsu sai ta ga ba komi bane face iko da gadara marwan ya nuna mata a zamantakewarsu,ya koya mata karban yancinta a wajen wasu amma sam bai koya mata karban yancinta awajensa baya mayar da ita kaman baiwarsa yana ordering dinta around,she cant believe she even let him chose her clothes.

Tafukan hannunta ta saka ta rufe fuskanta dashi wannan abin kunyar har ina? Saurayi ba miji ba ita kuwa wata irin sakara ce? God! She was so neive amma dai wallahi marwan ya rainata chai! Allah ya hadashi da mace dai dai dashi.

Murmushi tayi tana picturing marwan da mace iron lady a fili tace "tab ashe ko za a kona gidan,wannan iyayen son girman." How she wish yanzu zai zo yaga yanda rayuwarta ya canza lallai zai sha mamaki she is not more that nieve miemie.

Wow! Miemie! It has been so long that someone called her with that name sam bata yarda da taga wani ya dau hanyan kiranta miemie zata dakatar dashi

Akwai wani lokaci da ta shiga sahad tana wajen kayan shafe shafe wata cute yarinya da bata fi 2 years ba tazo tana ja mata riga tsugunawa tayi tana kallon fuskar cute yarinyan fuskanta dauke da murmushi ta ja kumatun yarinyan tare da tambayanta ya akayi
Hannu yarinyan ta bude mata alamun ta dauke ta tana shirin yin magana taji wani murya mai kaman na marwan yana kwala kiran miemie bata sani ba ko yanayin yanda marwan ke kwala kiranta ne mutumin yayi amfani dashi ya sa taji muryar yayi mata kaman na marwan ko muryan marwan din ne dan juye juye ta fara tana neman ta inda muryan yake fitowa.

Da gudu taga wannan yarinyan ta nufi inda muryan yake maimunatu bata lura ba tana kokarin ganin mamallakin yarinyan nan ta bugewa wata hajiya basket dinta da sauri ta bata hakuri tare da kwashe mata ko da ta gama babu su babu alamunsu haka taje ta biya kudin kayanta ta fita a cikin mota wajen zaman passenger ta hango yarinyan hannun wata farar mata suna zaune amma babu kowa a mazaunin driver.

Kwarai maimunatu ta so ta tsaya taga mahaifin yarinya sai taga rashin amfanin yin hakan.

Numfashi ta sauke tuno inccident din kila ma marwan ne,kila yayi aure har ya haihu dariya tayi tana tunanin ta yaya ma marwan zai sawa diyarsa sunanta ai wanda yake da muhimmanci a rayuwarka shi kake yiwa takwara ta ayyana a ranta.

Karan da wayarta yayi ne ya firgitar da ita da sauri ta janyo wayar tana mamakin dalilin da zai sa mufliha ta kirata da daren nan dama dai mubeena ce wannan sarkin surutun.

Cikin nutsuwa ta amsa kiran da dariya mufliha take magana tace "yi hakuri maimuna na kiraki da dare." Murmushi maimunatu tayi tace "no ba komi ya su ikram?"
"Lafiyansu kalau,yauwa maimunatu zaki iya tuna uncle dinsu ikram da kika gani ranan a office dina?"
Dan jim maimuna tayi tana so ta tuno ranan "wanda ya zo kina shirin fita ranan da su ikram suka yi mid term break?"

KINA RAINAWhere stories live. Discover now