Dandano 2

3.1K 60 2
                                    

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_* _*ZAFAFA BIYAR*_🔥

*_DANDANO DAGA LITTAFIN,_*

*_BURI 'DAYA_*
_NA MAMUHGEE_

*_1_*

Bismillahir-rahmanir Raheem.

Sauri yake faman zubawa Amma yanda saurin nasa yake tamkar Yana gudune sbd yanda ko gani bayayi sosai ga babbar rigarsa sai cika takeyi da iska tana qarawa,

Da safe kafin yafita jin zuciyarsa yakeyi fes sbd tunanin yau ranar sa'arsace tunda zasuje maula gidan mai arzikin da yafi kowane mai kudin jahar kudi harma dana wasu jahohin saigashi masifar datafi ha'darin mashin bala'i ta afko masa Dan gwara yasan sama mashin yayi dashi ya zubar akan abinda rashin hakurinsa yaja masa ayau din,

Yana shanyo kwanar layin gidansa wani mugun zufa ya yanko masa ya tattaro kuzari da qarfin hali yacigaba da tafiya Yana kallon tarin kalolin 'yan ta'addar dake cike da qofar gidansa sun baje sunashan iskar makeken bishiyar durumin dake qofar gidan  kusan su goma Sha biyar kowanne da kalar mugun makamin dake soke cikin qugunsa ko wani sashe na jikinsa Wanda duk qaddara takaisa shiga huruminsu yanxune zasu yiwa rayuwarsa illa Kuma ba Wanda ya isa ya tanka sbd hukumar ma da ikonta suke aiki sbd zakinsu shine amintaccen yaron DIKKO DILLA.

Wasu daga cikinsu fuskokinsu cike sukeda zanen Sara ko Suka haka jikinsu kusanma Babu Wanda fuskarsa bazata saka mai qaramin qarfin jini zawoba sbd Sam babu alamar wasa atareda fuskokinsu ga wani irin warin daga da wiwi dake tashi tun daga farkon layin unguwar shiyasa yawanci duk Wanda yake Dan asalin gari yasan anguwar ba wurin ganganci bace anguwar sarki ZAKI NEYO ce Sam ba'a mata garaje.

Da gudu gudu sauri sauri yaqarasa shigowa gidan tsohuwar babbar rigarsa kalar ruwan madara data koma kalar brown tana sake dibar iska sbd sauri dayake diba kamar zai tashi sama musamman yanzu daya qara ganin bataliyar 'yan daban dake qofar gidansa kamar qofar gidan wani qaura.

Yana shiga tsakar gidan sbd tsantsar rudewar dayake ciki ya kwashi wani mugun tuntunbe saura qiris ya kife cikin garinda iya talatu ta shanya na kayan mata datake siyarwa duk da duk rabi garin kukane take zubawa sbd yayi mata afkin siyarwa.

Zaune take tana lissafin jarkar tsimin data Saida wadda duk rabi jollyjus ne ta zuba aciki shima sbd afki.

Kallonsa tayi amatuqar sheqe cikin takaicin yanda ya tashi goga mata asara ta hanyar barar mata da gari a 'dan hasale tace"

Wai meye hakane kaketa muzurai kana rawar jiki kamar 6arawon daya ha'diyi kunama?,
Yanzu wannan garin dakake Shirin bararmin kasan hasarar nawane zaka jazamin Wanda nasan ko shekara zakayi kana sana'ar taka ta mutuwar zuciya bazaka Tara kudin biyana ba inyi magana jarabben sarkin gidannan yace bayason hayaniya kokuma yakamamin dabbobi yasa ayanke masa inaji Ina gani qatti suci banza.

To wlh banshirya hasaraba kusa Dan haka kafita idona inrufe.

Takalmin hannunsa ya fitar daga cikin babbar rigarsa data gama jiqewa da zufa,
zufa na qara tsatsafo masa Yana zare qananun idanuwansa dasukafi kama Dana Chinese din hauren qasa yace"

Qaddara takaini daukar aron takalmin ZAKI NEYO wainda kikaji dahiru yace dubu biyar suke nafita dasu wlh sun katse fata fata duka qafar biyu gurin gudun mahaukatan Karnukan da alhaji dikko dillah yasa aka sakarmasa ga yan maula da mabaratan dasuka tarar masa qofar gidansa duk da tarin yan sandan dake gadin gidan.

Wani irin sabon qululun baqin ciki da takaicine ya quleta tana watsa masa wani mugun kallon takaici baqin ciki yahanata ce masa qala sbd duk iya quluwa da baci ranta yayi sbd sanin masifar da hakan zai jawo
ta miqe ta tahau tattara kan akuyoyinta da kajinta dake walwalarsu filin tsakiyar gidan Dan tasan yau akwai saukar aradu a gidan Dan yau ko butar gidan saita ci uwarta idanba Allah ya tsareba baresu
Akuyoyinta da kajinta kuwa tasan tsaf zai take mata kawunansu su mace abanza,
Tana zaman zamanta rukayya taje Lagos ko wata shegiyar qasar ta hado jini da kafirai kokuma qila wata qabilar anxo anhaife mata masifar daba ita kadai ta addababa har yan gari da anguwa Dan kuwa neyo ba ubanda baya tsoro da shakkarsa ga wani irin kwarjini dayake qarawa mutane tsoronsa.

ZAFAFA BIYAR(DANDANO)Where stories live. Discover now