👑 *GIDAN SARAUTA*👑
Written by *Zeeneert💕*
*Zeeneert* @wappad
Bismillahir rahmanir Rahim. In the name of Allah,the most gracious and the most merciful. Assalamualaikum Fam. Zeenertu tadawo for the second time to bless your screens with GIDAN SARAUTA. Labarin da dinne dai dakuka sani se dan abunda ba'a rasaba. I realize there's a lit bit of typos and what have you,gakuma dayawa danakeda tabbacin basu karanta labarin ba as the book was written when I was still a novice in a writing world. So here I am with the 2nd edition of labarin Almustapha da Asma'u and I hope da wanda suka karanta abaya da wandanda basu karanta ba will all join me on this journey for I assure you'll enjoy every bit of it.
Kamar kuma yanda nafada tun abaya littafin GIDAN SARAUTA kirkirarren labarine,everything you come across in this book are nothing but a pigment of my imagination and incase wata/wani taga/yaga yayi kama da yanayin rayuwarta/sa to shi ko ita susani akasi akasamu bawai da ganganba. Thank you
*Page One*
About the kingdom: Masarautar Zazzau
Masarautar Zazzau katuwar masarauta ce da inna tsaya misalta muku girmanta da kyawunta zamu kwana muna abu daya bamu gama ba. Cikin Masarautar garine guda dake daukeda bangarurruka daban daban kama daga kan Fada,bangaren sarki da iyalinsa,Waziri,Galadima,Fagaci,Sarkin yaki and every other rank inda kowa sashinsa ke tareda nasa iyalin according to their ranks and office. Kuyangu,bayi da Fadawa ma ba abarsu abaya ba! Sashi suke dashi guda inda suke gudanarda rayuwarsu bayan suntaso daga assigned portion dunsu. Kitchen kuwa fankacece suke dashi inda ake general abinci akaiwa kowani bangare nasu dukda kuwa kowani bangare sunada nasu private kitchen din acikin gida inkanaso kayi wani dan kunji kunjin ka ko kayan kwalama!akwai clinic wadatacce da makaranta da akayi musamman sabida ma'aikatan masarautar(Kuyangu,bayi and fadawa) da iyalansu dake benefiting.
Kodayaushe kashigo Masarautar every where is busy ana kai kawo. Fadawa na fada,kuyangu da bayi na wuraren ayyukansu,Dogaraye nabawa Masarautar tsaro dare da rana ayayinda Masu Masarautar daukansu ke aiki 24/7 wurin ganin sunkawo cigaba a Masarautar da al'umman gari baki daya.
Masarautar Zazzau na daya daga cikin manyan masarautu a yankin Africa bama a Nigeria kadaiba awancan lokacin. Sun kuma yi fice sosai sabida adalcinsu,sanin darajar dan Adam dakuma sanin dukwani tactics na iya mulki.
__________
Tafiya yakeyi ahankali kamar bazai taka kasa ba,kai kace tsoron taka kasar yake ayayinda yake sanye da kananun kaya. rigace baka da akamata rubutu da farar ink me take
"DREAM BIG" sekuma plain black jeans. Dukda he's looking neat and tidy kallo daya zakama kayan jikinsan kasan sunci duniya dan har kalar bakin yafara dafewa tsabar kodiya. Takalmin kafarsa kuwa irin local handmade shoes dinnan ne,sudin dai babu laifi haryanzu da kwarinsu.
Acikin masarautar yake tafiya kuma tunda yashigo yake wuce dogarayen dake tsattsaye a haraban masarautar suna gadi anma cikinsu babu wanda yayi yunkurin bashi girmamawan daya kamata sema wani kallo dasuke binshi dashi wasu acikin su na kuskus a tsakaninsu,ko kallo basu ishe shi ba barema yasan sunayi,kodayake yasan sunayi din he just decided to act like he doesn't!
inda sabo harya saba dankuwa kullum haka abun yake! Sede inbe fita koya shigo Masarautar ba irin treatment dinda suke mishi kenan. Haka yacigaba da ratsawa tsakankaninsu yana wucewa kanshi akasa haryabar inda suke sosai yanufi wani building dake can gefe acikin Masarautar,ko kadan kuma building din beyi kama da acikin Masarautar yake ba tsabar tsufansa da rashin kyaunsa. Ko yar plaster da penti da akeyi from time to time a Masarautar in antashi renovation shiba'a taba yimasa ba. Babu kafan mutane,babu dogaraye,babu kuyangu. Wurin shiru kamar kufayi inkuma ba anfada maka ba bazaka taba sanin akwai masu rayuwa agurin ba.
YOU ARE READING
GIDAN SARAUTA
FantasyA story of a young Prince and his Mother with two sisters who have been deprived of their rights by a very heartless woman #MAGAJIYA#.......
