GIRMAN KAI

1.5K 69 14
                                    

*GIRMAN KAI...*
        ('''RAWANIN TSIYA''')

*Na*

*Aisha Alto*

*Wattpad-@AishaAlto019.*

     '''Sadaukarwa Ga My Sweetheart, My Aminiyar Ƙwarai, My Ƙawar Arziki, Ta Gaban Goshin Aisha Alto, My Jinin Jiki, My Sisi Of Life JANAF🥰'''

    *Bismillahir rahmanir rahim*.

'''page'''...S

Ta daɗe a kwance tana rusa uban kuka, kafin da ƙyar ta iya lallashin kanta tai shiru, taja jiki a hankali ta miƙe tsaye ta ɗauki pant da pad d'inta dake ƙasa ta maida sannan ta ɗauki bomshort d'inta ta riƙeshi a hannu bata ko bi takan rigarta daya yaga ba ta fice daga ɗakin a haka tana ɗan ɗingisa ƙafarta tana tafiya a hankali hawaye na zubowa daga cikin idanunta.

Yana zaune a falo da goran ruwa riƙe a hannunsa yana sha, ta zo zata wuce ta gabansa bata ko juya ta kalli inda yake ba, dan sosai taji zafin wulaƙancin da yay mata, wata irin tsanarsa take ƙara ji sosai a cikin zuciyarta, har ta kai bakin k'ofar ficewa daga falon taji yaja wani irin dogon tsaki kafin ya fashe da wata irin dariya har yana dukan kujerar da yake kai, bata ko tsaya ta sauraresa ba ta fice da sauri ta nufi ɗakinta, tana shiga ta wurgar da wandon dake hannunta ta nufi toilet tana ayyana irin muguntar da zatai masa dan ta rama wulaƙancin da yay mata.

A haka tai wanka da ruwa mai zafi ta gyara jikinta sannan ta ɗaura tawul ta fito, duk abun da take yi dauriya ce kawai take, dan duk motsin da tai sai taji hannunsa na yawo a ko'ina na jikinta yana shafata, kamar a lokacin yake taɓa ta, duk jikinta a mace yake, a haka ta gama shiryawa ta saka wata ƴar yaloluwar doguwar riga mai hannun ves ta fesa turare sannan ta yafa ɗan ƙaramin gyale a kanta ta ɗauki wayoyinta da key ɗin sabuwar morarta da Abba ya aiko mata da ita ta zira takalmi ta ɗauki ATM CARD d'inta ta fice daga ɗakin.

Fitowarsa kenan daga wanka yana tsaye a gaban mirror yana goge ruwan jikinsa, yaji fitar mota daga gidan, da sauri ya ƙarasa gaban window ya ɗaga labule, hango maigadi yay yana rufe ƙofar get ɗin, alamun har an fice, da sauri ya dawo a gurguje ya shirya cikin shigar ƙananan kaya da suka karɓi jikinsa sukai masa wani irin mugun kyau, ya fesa haɗaɗɗun turarukansa masu sanyin ƙamshi da sanyaya zuciya, ya kwashi wayoyinsa da makullin mota ya fice daga ɗakin ya nufi harabar gidan, ganin babu sabuwar motar da Abba ya aikowa da Ramlat a parking space yasa ya gane ita ce ta fita, wani irin takaici ne da haushi ya kama shi, kenan yawo zata ci gaba da yi mai a gida, to kuwa zaiyi maganinta, zai sauke mata duk wani abun da ke kanta, zai nuna mata nan ba gidansu bane da take sakin jiki tai duk abin da ranta keso, shi ba zai ɗauki wannan iskacin nata ba, dan shi ba lusarin namiji bane, zai saitata dai-dai.

****

A ɓangaren Ramlat kuwa wani haɗaɗɗen tsadadden restaurant taje a cikin gari tai ordern lafiyayyen abinci taci ta ƙoshi, ta biya kuɗin ta fito ta shiga motarta taja, har ta nufi hanyar zuwa gidansu sai ta taka burki da sauri ta duba agogon wayarta, ganin ƙarfe 1:30am. Yasa ta dafe kanta cike da baƙin ciki dan tasan yanzu haka Abba yana nan a gidan dan yau lahadi baya zuwa ko'ina, jiki ba ƙwari ta juya kan motar ta nufi gidansu Fauzah dan Aisha bata nan tayi tafiya, har ta kusa ƙarasawa kuma sai kawai ta fasa kamar an hanata, ta juya ta kama hanyar komawa gida.

******

Fitowarsa kenan daga masallacin jikin gidan bayan ya idar da sallar Azhar, ya hango shigowar motarta cikin layin a guje. Kamar zai shige cikin gida sai ya lura da wata baƙar mota dake bin bayanta, harɗe hannunshi yay a ƙirjinsa dan bai san fitarta ba, kuma ga wani rakiyar da yaga wani na mata, zafi yake ji kasan ransa amma tsabar iya bariki yay kamar baya jin komai.

Har ta shiga gidan parking mutumin yayi ya fito har inda Saif yake tsaye ya miƙa misa hannu suka gaisa, sannan yace “Don Allah ko zaka min sallama da yarinyar da ta shiga cikin nan? Ina son magana da ita.” 

GIRMAN KAIWhere stories live. Discover now