Chapter 1

2.9K 121 1
                                        

⚜ *"AMANARMU"*⚜

*PURE MOMENT OF
LIFE WRITERS*

_By Ayshkhair_🤗

1&2

Zaune suke a mota kowanne da abinda ke sakawa aransa. Gefe guda Khadeeja Ahmad da Fa'iza Kabir Halima Hassan ne suka kurawa Zainab ido a in curiosity suna San tabbatar da hasashen su akanta . Kallo daya zakaiwa Zainab ka tabbatar da ranta a bace yake dasu musamman Humaira tafi jin haushin ta fiye da su Haliman masu son ganin kwaf akan iyayenta jinginar da kanta tayi tana kallon gefen titi. "Wannan shine karo na barkatai da Humaira ke mata katsalandan arayuwarta Wai shin ma Ina ruwanta da iyayenta ? Dolene sai tabi abinda take so ? Wannan ba komai bane illa tozarci Humaira so take ta tozartata gaban kawayen su ta nunawa duniya cewa ita din ba 'yar kowa bace sai 'yar nakasashshe talaka Wanda bashi da komai yake a karence a a gidan abokinsa. Idan har ba hakan take son nunawa ba Mai zai sa ta fadawa kawayen ta cewa baban ta ba lafiya ?" Tsakin data ja ne ya dawo da hankulan su kanta da sauri ta basar kallonta Humaira tayi cike da tausasawa "kiyi hakuri Zee Inshaa Allah Baba zai Sami lafiya ki kwantar da hankalinki komai zai zama lafiya" maimakon hankalin ta ya kwanta ranta kara baci yayi cike da jin haushin Humairan ta daga mata kai "wato ta Kuma so take ta nunawa kawayen su cewa da Baba suke Kiran babansu maimakon Abba ko Daddy .... Wannan yarinyar tana son illata da banzayen maganganun ta Wanda ita bata yarda ba waazi ne" tsayawar da motar tayi ne ya dawo da ita daga dogon Tunanin da tatafi motar har ta shigo cikin gidan jikin ta a sanyaye ta bude motar ta fito sauran kawayen su Su Halima suka biyo bayanta Humaira ce karshen fitowa Dan kafin ta fito tuni Zee tayi cikin gidan ranta abace binta Humy tayi tana kwala mata kira Kallon Juna su Khadeeja sukayi suka tuntsire da dariya cikin muryar dariya Halima tace "yau fa Zee karya ta kare, shegiya me son asani ke ba kowan kowa ba ya dillalin kashi" caraf Halima ta amsa "eh bakiga tunda muka shigo mota take cin magani ba ba abinda take tunani saboda yau zaa ga karyar ta banza mutum sai famkama da nuna kai Dan wani ne" gyada kai Fa'iza tayi "Ni wllh Humy tausayi take bani duk da bamu taba jin kansu ba, ita fa ba komai aranta gani take kawai damuwar rashin lafiyar mahaifinta ce tasa ta a wannan yanayin bata San abinda ke ran Zee ba sai Allah baka isa ka gane bayan ta balle gabanta" tsaki Fa'iza taja "koma meye dai yau sai mun duba mahaifinta ko Dan aminci shekara nawa muna tare ? Duk zaman da mukayi ba Wanda ya damu da rayuwar su banda yanzu ma da ita Humyn ta matsa ba abinda zai kawo mu Dan Allah kadai yasan dalilin yasa Zee bata San aje gidansu" ganin Humyn ta tsaya yasa suka saurara da hirar jiran su ta tsaya yi Dan Zee tuni ta shige gida. Ita kanta Humyn taso ta fahimci Zee din ta maza ta kauda Tunanin Dan bata San yi mata mummunan zargi. Sakin Fuska tayi suna karasowa suka jeru suna tafiya kowanne da abinda ke sakawa aransa su kam tsananin mamakin Zee ne ya cika su yanda kiri kiri take abu kamar wata karamar yarinya to Wai shin me take nufi ne ? Ita kam Humaira tunanin ta ko dai har yanzun damuwar rashin lafiyar Baba ke damunta ? Anya kuwa ? Yarinyar da Sam bata damu da iyayen nata ba, asali ma Humyn ko Momy ne ke mata fadan ta shiga ta gaidasu duk da a cikin gida ne sai tayi sati bata leka iyayen ba wataran ma Maman da kanta take zuwa ganin Zee .... Tsayawa tayi da tunanin saboda tambayar da Fa'iza ta katseta dashi "meyasa Zee ta kyalemu duk da tasan Dan ita muka zo gidan nan ?" Rasa amsar bata tayi Dan ita kanta bata San abinda ya samu Zee din ba "hmmmm Zee tana da matsala Humy, ko ma meye ne zata ga rashin mutunci Dan wllh sai na fesa mata shi, ita din banza ban da ke da ban shiga na gaida Baban nata ba, banza kawai" shiru Humy tayi Dan bata da bakin tanka mata haka suka shiga gidan suka tadda Baba jingine da bango Mama na tsakar gida tana shara ganin su yasa ta saki Fuska "Aysha sannu ku da zuwa! Ku shigo" zubewa suka yi kusa da Baba suna Kallon sa a tausaye gaishe ta Mama sukayi ta amsa suka gaishe da Baba kai ya daga musu Dan ko yayi maganar ma bai zama lallai su jisa ba addua sukai masa na Allah ya kara lafiya har sun Mike Mama tace "Ina Zainab din take" a raunane Humaira ta amsa da "tashiga gida" gyada kawai Mama tayi "in kin koma kice mata tazo Ina son ganinta" da "to" ta amsa suka fito har bakin mota Humaira ta raka su Khadija tai musu sallama ta shigo cikin gidan ranta abace yau kam Zee ta tabata da yawa Kuma sai tagane kuskurenta a babban falo ta tadda Momy na Shan juice tana kallon tv a zumbure Humy ta wuce da Mamaki Momy ta tsaida ita "Lafiya Aysha?" " Momy Zee ce, kawayen mu suka zo duba Baba shine ta kyalesu tun a mota bayan munzo gida Kuma ta shigo nan ta barni da su sai Ni na kaisu suka gaisa da Baban" in da sabo sun saba da halin Zee Amma yau kam ta bata Mamaki "meyasa tai musu haka ? Lallai bata kyauta ba Kuma ranta zai baci" wucewa Humairan tayi dakin su ta tadda Zee ta cire uniform tana latse latse a waya a fusace Humy ta fara masifa "wannan wanne irine haline ? Halin rashin mutunci mutum yazo duba mahaifinka ka wulakanta su wllh wannan ba rayuwa bace Zee kin canza hali" ko kallanta ba tai ba bare tasa ran zata amsa ganin haka yasa Humyn fisge wayar wani banzan kallo Zee tai mata a kufulance kamar zata daki Humaira ta fara magana "meye matsalarki ? This is my life and my parents na taba fada Miki Ina neman shawararki ? Ki kyaleni haka naga damar tsara rayuwa ta..." Ka tseta Humy tayi da Mamaki "ban Miki magana akan iyayenki ba, na Miki ne akan wulakancin da kikaiwa su Fa'iza Kuma kin San su sarai ba kyaleki zasuyi ba, ke kika sani idan ba zaki canza ba nima ba zan canza ba dole innaga abun magana sai nayi, Kuma kisani maganar nan har kunnan Daddy Dan sai na fada masa, sannan kije Mama nasan ganinki" tsaki Zee tayi tabar mata dakin Kallon ta Humy tayi tana mamakin halin ta Wanda Sam bashi da kyau ba Wanda ya fuskance ta har Dan Zee baudaddan haline da ita a falo ta tadda Momy xaman ta kenan Momyn ta hau yi mata fadan abinda tayi kara kuluwa tayi "ita kenan kullum itace Mai laifi, meyasa Humaira ke son fadawa kowa laifinta Dan kawai a tsaneta ? Wani haushin Humaira ne ya kamata dolene ta taka mata birki dan bazata dau wannan rainin ba. Maganar momy ce ta dawo da ita daga tunanin da takeyi "dan Adam Yana da daraja bai kamata kiyi musu haka ba ko Dan Baban ki da suka zo dubawa, meye laifin Wanda ya kula da wani sha'ani naka ? Hakan ba daidai bane Zainab kinaji?" Gyada mata kai tayi tana jin bazasu fahimce ta ba ne Sam bazasu gane inda ta dosa ba tayaya zata nuna nakasashshen tsohon cen a matsayin shine mahaifinta ? Hmmmm magana momy ta cigaba dayi "daga yau Zainab bana son nakaraji ance kinyi wani abun, bana so ina son kizama yarda yar'uwarki take ki dauki kowa a matsayin naki ki kuma mutunta kowa saboda dan adam daraja garesa baka San me gaba zata haifar ba." Ajiyar zuciya Zee tayi hade da gyada kanta "zankiyaye mom" ta fada a gajarce zuciyar ta na cen kan wani tunani da ya dade da mamaye ta.

AMANARMU Where stories live. Discover now