Yaya kabeer da shigowar shi hall ɗin kenan dan an kira shi a waya an sanar da shi ga ango nan ya shigo a buge ya tarar da abin da ke faruwa tun daga farkon kalaman ta har ƙarshe duk ya ji komai ni da ke ƙokarin zuwa wun salma in tambaye ta hala falmata yaya Aqeeb ke so ya yi shiru bai faɗa har ya janyowa kanshi wannan abin maganar da zuwa na wurin ta na saka hannu kenan da zumar jan ta gefe sai karaf a kunne na na ji muryar yaya Aqeeb yana kira na

"Aisha kar ki kuma kuɓce min for the second time mutuwa zan yi in kika tafi"?..

Abin da salma ke gudu kenan gashi ya faru wannan abu ya daɗa tunzira aunty mufeedah har ta kasa hakuri ta bangaje shi ta isa wun mc ta fisge mic ɗin ta fara sauke nauyin zuciyar ta

"She is the Aisha that stole my happiness ita ce yarinyar da Aqeeb ya ke son halaka kan shi saboda muguwar son da yake mata itace yarinyar da ta dasa min mummunar lamba a kundin rayuwata Aisha Murad koh toh Aqeeb nan na bariki shi halak malak ki je ki mai abin da ba zan iya yi mai ba ga ta nan ku shirya ta a cigaba da shagalin auren da ita"kaiwa nan ta cila mic ɗin ta yi hanyar waje da azama ya karasa wurin ta ya riko hannun ta ta fisge tare da kara sauke mai wani marin dan tana takaici da jin zafin abin da ya mata wato ta nuna ɓacin ran ta amma bai damu da bata hakuri ba instead ni ya juya yana tonawa sirrin zuciyar sa lallai ta tafka asara da ta kasa banbance mafarki da ainihin rayuwa

"Feedah feedah pls don't go ki min rai wallahi ba yin kai na bane kin gani kalle ni idanuwana son ki ne a ciki ba na wata ba believe me"..

Ya fara dawowa hayyacin sa already wuta ne ya dauke min na wucin gadi me zan ji me zan gani yaya Aqeeb kanin yaya kabeer di na ke so na dama yana so na ne koh dai wata Aishar ce ba ni ba noo that's not possible ba ni bace i was shock har kasa motsawa na yi yaya kabeer karasa shigowa yayi ya juyo yaya Aqeeb ya ƙura mai ido ya ce

"Aqeeb kalle ni kalli cikin idanuna ka ƙaryata min zancen da kunnuwa na suka ji pls"
Unfortunately yaya Aqeeb ba zai iya kallon cikin kwayar idanun yaya kabeer ba dan ba zai taba ƙaryata feelings ɗin shi akai na ba so sunkuyar da kai yayi ƙasa yana kuka

"Aqeeb talk to me ina jin ka"by then yaya kabeer ya fara losing patience din sa already da tensed voice ya kara tambayar shi karshe har daka mai tsawa yayi dagowa yayi shima ya daka mai tsawar

"Yes abin da kaji gaske ne Aisha Murad has been my dream my wife in my dream ita ce yarinyar da nake so tun ban san menene so ba a kanta na fara sanin garɗin so

Maruka yaya kabeer ya firgita nima haka da na dauka ɓatar hanya ce amma ashe da gaske ne ni ni Aisha yaya Aqeeb ke so anin mamaki da al'ajabi koh a wasa ban taɓa kawo hakan ba koh shi kanshi bai taɓa nuna min a zahiri ba toh how ta yaya wai ma duk ni ni daya nake da samari har uku ban san da zaman biyu ba sai ɗaya a xikin su abin da Abbu ya sanar da ni washegarin da na dawo daga Egypt ne ya fara min yawo

. "Aisha dama akan maganar yaron nan ne wato yahaya toh ban ɓoye mishi komai ba gameda neman auren ki kabeer ya yi da farko ya ji zafi har yake neman sanin dalili bayan ya san ya riga kabeer ɗin shigowa bai san cewa ina da masaniya akan sirrin shi da ya ɓoye min ba a matsayin shi na ɗan aiki na kuma ni uban gidan shi sirrin kuwa ba komai bane illah aure auren da yake yi kafin ya haɗu da ni duk auren da yayi matar bata wuce shekara ba a ga gawar ta ba koh ta mutu haka kawai koh ya mata duka sosai da zai yi ajalin ta daga wanda ya bani cikakiyar labarin shi ya sanar da ni cewa yara ƙanana yake aura duk wacce bata rasu kafin shekara ba toh sai ya mata dukan da zai yi ajalin ta tun ƴan garin ba sa ganewa suna bayar da auren ƴaƴan su har suka gane suka daina shi ɗin mutumin Nijer ne chan cikin wani yanki mai suna Tawa a cikin wata dajin kauye mai haɗari kuma ba komai yake yi da gawarwakin matan ba illah bayar da su ga abin bautar su saboda koh bai bayar ba lokaci na yi zasu amsa dan tarihin gidan su ya nuna an tsine musu tare da la'antar su duk abin da zasu yi ba zai taɓa yin ƙarko ba suna ji suna gani toh da aka kora shi a kauyen ganin yana nema ya zamo masu annoba shine ya bar garin ya dawo nan a kano ya fara sauka ya yi sa'ar samin mafaka har ya yi aure amma da yake abin na bin shi haka matar nan ta yi shekara ta rasu ganin haka sai ya bar garin kafin a gane shi toh shine muka haɗu da shi har ya zama ɗan aiki na wanda na fi aminta da shi dan yahaya na da hankali da sanin ya kamata amma da yake mutum tara ne bai cika goma ba shi irin nashi ƙaddarar kenan ko da ya min maganar ki babu jimawa na saka amin bincike akan shi na wahala kafin in san tarihin shi amma ko da na sani sai na mai shiru ban ce komai ba dan jira nake in ga ko zai bayyana da kanshi amma bai yi hakan ba ni kuma na yi ƙokarin rufe duk wata kafa da zai haɗa ku gudun kar ki sake jiki da shi yana ɗaya daga cilin dalilin da ya sa na amince da ki tafi karatu ƙasar Egypt da kabeer ya nuna yana son ki sai na amince dan in yi amfani da damar wurin sanar da yahaya cewa na aan sirrin shi bayan na gama bayyana mai komai akan shi da na sabi sai ya roki alfarmar in bar shi ya tafi wani wurin dan ko ya zauna a nan ɗin yana iya cutar da mu ba a san ran sa ba ban da zaɓi illah na barin sa ya tafi tare da bashi jari mai tsoƙa"...

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now