*UWAR MIJINA...!*
_(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)_
*Mallakar:JANAF*
*Wattpad:Janafnancy*
*Dedicated to my blood Sisters JANAF*
*Intelligent writer's Asso*✏
_*Kowani marubuci indai ya dora Alkalaminsa kan Takardarsa,ko Wayarsa,ko tap dinsa da niyyar Rubuta wani abu to yana da babban dalilinsa bawai iya yasaku nishadi bane A"a don ya baku wani darasin dazaku fadaku akai ne,walau darasin mai fitane daga farkon farawa,wallau kuma sai kun himmatu wajen hakurin karatu kafin kuci ribar abin....Da wannan dan bayanin nawa nake kira ga yan TEAM HIRAH DA MU"AZZAM,dasu dauki kaddara Abunda Allah ya rigaya ya rubutu babu mahalukin daya isa ya chanzasa,wannan itace KADDARARSU...Assalamu Alaikum Janafi*_💕
_Dedicated to my Childhood friend FADILAT FALALU MASKA...Tanque bby Sakallahu fiijannah_
*NO 23*
Daida lokacin kuma zahirah ta sheme akasa hannunta bisa cikinta tana salati da karfi,Cikin wani irin Rudewa mu"azzam yayi kan Ummi yana jijjagata ammh hankalinsa na kan zahirah datake mukurkusun ciwo.
Su karime ne suka isa ga Zahirah suna riketa suna jera mata sannu,Mu"azzam rumgume Ummi yayi yana kiran sunanta ammh ina ko Numfashi batayi Uwani ne tayi Dabaran Bude Fridge ta dauko Ruwa mai sanyi ta mikama mu"azzam tana fadin"zuba mata wannan yallabai, inaga fa Zahirah Nakuda ce"Tafada hankalinta tashe,cikin wani yanayi Mu"azzam ya shafama Ummi Ruwa Afuskar hau sau biyu kafin ta sauke ajiyar zuciya tana maida Numfashi daya da daya.
Idonta ta fara budewa taci karo da mu"azzam yana fadin"Plz Ummi..."Yafada kamar zaiyi kuka,Da hanzari ta dafe kanta lokacin da kalaman yarinyar ke mata gizo a kunnenta,Ture mu"azzam tayi da karfi kan tayi nasaran mikewa jirin na neman kara gada ita ya mike da Sauri zai tarota tace cikin karaji"kar ka kuskura ka tabani Ibrahim..."Tafada wasu hawaye masu dumi suna binta. kallonsa take cikin rashin hayyaci,idanunta sunchanza kala sunyi jawur kamar garwashi,lokaci guda ta maida idanunta inda zahirah ke mukurkusu,su karime na rike da ita suna mata sannu,kuka kawai takeyi tana salati.
Kallonta ta dawo kan mu"azzam wanda ke tsaye kamar wani tsohon munafuki,Mirmshi tayi mai ciwo kafin tace"Ni Suhaima,ni Suhaima,ni Mu"azzam kaci amanata ka sabama alqawari, kayi ma diyar wa"inda sukayi sanadiyar rugujewar Farinciki cikina,ka na so dole sai na hada zuru"a dasu ko.."? tafada tana kallonsa Rausayar dakai yayi ya bude baki zaiyi magana ta katseshi da cewa'Karka kuskura kayi min mgana Ibrahim kagama min komai naga sakayyar daukan cikinka danayi har na tsawon wattani tara,nazo na haifeka nasha wahalan Shayar dakai nasha wahalan Rainonka saboda kai nasha kwana da yunwa nayi fadi tashi na rayuwa don duk kai kasamu rayuwa mai inganci,yau burina ya cika kazama wani abu ibrahim ashe da abunda zaka sakamin kenan..."Tafada hawaye suna mata ambaliya.
Jikin mu"azzam na rawa ya durkushe bisa gwiwowinsa agaban Ummi idanunsa sunkada sunyi jawur shima jijiyoyinsa kansa sun mike radau kamar wanda wani cuta ta kama,gabadaya miyan bakinsa ya kafe yarasa mafita lokaci daya abubuwa sun taru sun mai yawa ya bude baki zaiyi mgana kenan karime tace"yallabai,hajiya ku taimaka akai zahirah Asibiti wlh Nakuda ce,kuma haihuwar Fari kada Asamu mtsala.."Wani sakaran kallo Ummi ta jefa karime dashi kafim ta daka musu tsawa tana fadin"Ku saketa munafukai,ko zata haihu billahil azim baza haifanmin wannan dan iskan cikin acikin gidanan ba,sai dai ta haifeshi cikin gidan Shettima..,kuficemin daga gani banzaye kawai.."Tafada cikin bacin rai tana wuci kamar mahaukaciya.
Gaban mu"azzam yafadu Ras lokaci daya yana kallon Ummi wacce tafara taku zuwa gabanshi daidai lokacin dasu karime suka fice hankalinsu atashe,jikinsu a matukar sanyaye,ga Tsausayin yar baiwar Allah zahirah,ga kuma mamakin Rashin Imanin Ummi,haba ko bata taba haihuwa ba,ita macece balle ma ta haihu tasan zafin Nakuda ammh dayake zuciyarta babu imani ko ajikinta.
