💠💠💠💠💠
*©® 2018.*
*♡INA MAFITA?¸.•💥*
_{Gajeran labari)._
*BASED ON A TRUE STORY*
*WRITTEN BY.*
HAWWA MUH'D USMAN
(REAL-SMASHER).
Devoted to:wad'anda suke cikin k'uncin rayuwa irin wannan,da fatan Allah ya kawo muku sauk'i a al'amuranku ameen.
Bestowed to:Maimounath Ousman Gagara (O.G),Jamila Musa (Meelat Musa),Halimatus'sadiya Muhammad (Leema),Sainah Usman (Oum Meenal),Amina Umar Fana (Aufana),Aneesat Abubakar Rimi (Oum Ayman) & Halima Sahad.
🅿1⃣
Na kasance yarinya Y'ar kimanin shekaru ashirin da uku (23),a wasu lokuta da suka gabata matsayin yarinya mai matuk'ar kamun kai wadda a duk lokacin da na fita daga gidanmu bana ko da iya d'aga kai na kalli mutanen dake hada-hada akan hanya,kada kuyi tsammanin na ce a baya kuyi tunanin na sauya,a'a har yanzun ma da nake baku wannan labarin ba chanjawa nayi daga halina ba,sai dai akwai abunda nake so ku fuskanta game da labarina. Mun kasance a gidanmu muna da yawa wasu muna uwa d'aya,wasu kuma uba d'aya,haka zalika muna da wad'anda muke ciki d'aya ma'ana dai uwa d'aya kuma uba d'aya,babu buk'atar ambaton adadin y'ay'an gidanmu abunda nake so ku gane kawai shi ne mak'asudin abunda yasa nake baku labarin,wanda ya faru kimanin shekaru shida baya. A cikin shekara ta *2012* ne komai ya faru wanda wannan shekara ta zomin da wani babban al'amari daya faru da a kullum ina bak'in cikin faruwar hakan kuma ina zubda hawaye a duk lokacin dana tuna,a wannan shekara ta dubu biyu da sha biyu bayan na kammala makaranta sakandire,kimanin watanni sun biyo baya da basu da yawa,sai ya zamana wani mak'ocinmu ya nuna yana sona,kasancewar akwai wanda nake so a lokacin da har n riga an mana baiko sai nak'i amince masa saboda har ga Allah bana sonsa ko a zuciyata kuma na tabbatar da hakan kamar yadda kowa na gidanmu yasan da haka,ko bama haka ba ai an rigada an a ni ga wani daban wanda nasan bai kamatama na sake kula wani ba. Lokacin daya fuskanci bana sonsa sai ya kasance ya nunamin kamar bai damuba,kuma ko da gidansa na shiga baya nunamin komai saboda mun saba sosai da matarsa kasancewar tun tasowata naga iyayena tare da su,har ya zamana duk wani aike ko wani abu makamancin haka daga shi har matarsa sunfi jin dad'in aikena kaf a yaran gidanmu,ni kuma dama tun tasowata Allah baisa na kasance cikin yara masu k'yuya ba,haka kuma kyautatawa dai-dai gwargwado nakan yiwa matarsa a matsayinta na babba,kuma har lokacin daya furta yana sona ban chanja daga yadda nake ba,lokaci yaci gaba da tafiya inda mahaifina ya sa ranar aurena a k'arshen shekara da saurayin da na nuna ina k'auna,kwatsam wata rana sai wannan mak'ocin namu ya tare ni lokacin zan shiga gidansa yana fad'in "Batoul ni kika nuna bakya so ko...?" Nan nayi shiru ba tare da na tanka masa ba,hakan da nayi ni ban saniba ashe yaji haushina ne,sai naji yana sake fad'in "Shi kenan kiyi duk abunda kikaga dama,amma ki sani har kullum ni ina sonki,kuma ina da burin mallakarki a matsayin matata..." Shiru yayi yana saurarena ko zance wani abu,sai dai nanma banyi magana ba,kaina kuma a k'asa ina wasa da gefen hijab ena,cikin b'acin rai ya kira suna na,wanda jin yanayin daya ambaci sunan nawa yasa ni kasa d'agowa sai dai kuma na tsorata sosai dajin furuncinsa inda yake fad'in "Shi kenan tunda bara kiyi magana ba,amma ki sani ke da aure har abada,wallahi sai dai kiga anayi,ke barima kiji na tak'aice miki gaskiya ko saurayi tsayayye kin bar yinsa.." Yana zuwa nan a maganarsa sai kawai ya wuce ya barni nan tsaye a daskare na kasa motsawa,tsoro duk ya cikamin zuciya jikina babu k'wari na ja k'afafuna na fice daga soron gidan nasa dama a nan ya tare ni naje shiga,fasawa kawai nayi na koma gida tare da k'ulewa can k'uryar d'akinmu,wanda tsoro ya hana ni fad'awa kowa abunda ya faru dani,take kuwa zazzab'i mai zafi ya rufeni dana kasa tantance na mene ne.
