Wannan karon ita ce ta tashi tana neman hanyar guduwa bazata iya jurewa wannan kallon da Uncle Awaisu yake mata ba.

Hannunsa ya ware "Give me a hug kafin ki fita please."

Tsayawa tayi kanta a kasa tana wasa da hannuwanta.

"Kinga komai na tambaya bakya yi ga yaji kin hadani dashi"

"To ai kunya nake ji"

"Bari nayi miki yadda kika koya min"

Ta bayanta ya tsaya ya rungumeta yadda tayi masa wancan lokacin da zai tafi. Da yake ya fita girma da tsaho sai ya rufeta gabadaya ya mata rada mata a kunne
"Ke special SS dina ce Umm Ruman. Allah Yayi miki albarka"

Amin tace a zuciyarta. A zahiri kuwa tace "Uncle idan na fadi ma'anar SS din zaka taimakeni don Allah"

"Toooohhh wane irin taimako kuma. Ko me kike so fada kawai zakiyi"

Kwanukan abincin ta nuna masa.
"Idan na fita dashi fada za'ayi min kila harda duka ma"

"Maganin wannan kawai ki kwana a nan shikenan"

Dariyar da taga yana yi ce tasa ta gane tsokanarta yake yi. Ta tabbatar idan Mama ta ga wannan miyar ko bata ji a jikinta ba kunnenta zai bada labari don bayan fada idan ta kama shi ta murde bata da hanyar tsira.

"Don Allah kace ya zama assignment irin yadda na baka"

Yayi murmushi "Ya zama Umm Ruman, me SS yake nufi?"

Sai da tayi kamar mai tunani kada yace tayi saurin canka sannan tace "Son So"

Ya girgiza kai "sai hakuri ni Sabuwar Sarauniya nake nufi. Jeki kawai idan kinga zaayi miki fadan ki gudu nan" kan katifar ya koma ya dan kashigida. Hankalin Rumana a take ya tashi. Dama shi take tunanin zai rufa mata asiri gashi ta kula kamar bai damu ba.

Awaisu yana kallonta yana dariya.
"Jeki mana idan an gama ki dawo ina son magana dake"

Mamaki take yi amma kuma tasan dama can idan sunyi laifi baya cikin wanda zaka zo wurinsu ya hana a hukuntaka. Sai dai yayi rarrashi idan anyi hukuncin. Duk wanda ya hana a hukunta to fa sai dai idan ya tabbatar mutum bashi da laifi. Kanta ta dan rangwada gefe muryarta tana dan rawa "na tafi Uncle"

Yana danna waya yana dariya ciki-ciki yace "sai kin dawo SS dina"

Ta durkusa zata dauki tray din "yau tun safe kunnena na dama ke dan zafi gashi Mama ita kunne take murdewa. Uncle kana da panadol idan ta murde zazzabi ya kamani sai ka bani"

Wannan karon da kyar ya iya danne dariyarsa "idan kinje ki bata kunnen hagun tunda shi kalau yake maybe bazaiyi zafin da zaki yi zazzabi ba"

Anya kuwa Uncle yana ma sonta ko da ba son so ba ta fada a ranta. Har wani dadi yake ji ga Anti Ummukulsum itama duk wasanta da yara ta iya duka.

Hadiyar yawu tayi da kyar ta tuna rankwashin da Antin ta yiwa Iman jiya saboda ta fasa mata plate. Harda sakin ajiyar zuciya ta sake cewa "bye bye Uncle"

"See you SS" yace daga inda yake.

Tafiya ta rinka yi kamar wadda kwai ya fashe mata. Ko dai kawai tayi tuntuben karya ne kwanukan su zube. Amma kuma masu kyau ne kila ma na baban su Iman Antin ta zuba abincin a ciki. Tana wannan tunanin har Awaisu ya kusa zuwa inda take bata kula ba. Tray din ya karba ya dawo da fuskarta daidai tata.

"Kin canka daidai Son So din Uncle Awaisu. Yanzu me kike so ayi da miyar nan kada a taba min mata"

Murmushinta kamar gonar auduga tace "zuciyata kamar ta fito don tsoro daurewa kawai nayi"

KASHE FITILAWhere stories live. Discover now