Ganin ya dauke ni ya dira akan gado yasa na shagwabe fuska ina masa kukan shagwaba.

"Oh Sorry Habibaty da wasa nake miki."
Daga haka kuma ya fara lallashi.

Dago ni yayi muka tafi daining. Akan cinyar sa ya zaunar dani ya dinga bani a binci har na koshi.

Falo muka tafi yana tsokanata irin kukan da kiran Ummu da Momy da na dinga yi.

Murmushi kawai nayi nai kasa da kai na dan kunyar sa nake ji. Bama kuma ya kawon maganar jiya.

"Hafsat!'
"Uhmm!" Na fada kaina a kasa.

"Nagode sosai bisa halacin da dauriyar da kika yi. Gaskiya ke jaruma ce, na gode miki. Kin faran tan kin mallake zuciya ta banda burin da ya wuce in faranta miki Hafsat."

Kasa na kuma yi da kai na. Dago ni yayi ya hade bakina da nashi yana sumbata ta. Sai da yai me isar sa sannan ya sake ni.

Fuska na shagwabe, hawaye na zubo min.
"Lafiya Baby?"
"Ya Haidar! Ummu."

"Oh to shine kuma zakiyi kuka."
Wayar sa ya dauko ya kira number Ummu.
sai da suka gaisa sannan ya mika mata.

Bayan sun gaisa suka dan taba hira sannan Khadija ta karbi wayar.
Sun jima akan wayar Ya Haidar sai kallon ta yake yana jin dadin ganin ta cikin farin ciki.

Bayan sun gama ya jawo ta jikin sa yana shafa cikin ta.
"Baby na bacci kake?"
"Ya Haidar wane Babyn naka."

"Gashi nan kwance a cikin ki."
Ido ta rufe da hannun ta.
"Wa yace maka da Baby a cikina."

"Ni nasan dashi tinda ni na ajiye shi jiya."
"Uhmm ni ba komai a cikina."

"To shikenan yau zan yi ajiya ta a cikin ki."
"Kai Ya Haidar" na fada ina kokarin tashi a jikin sa.

Jawo ni yayi ya kara rumgume ni."Eh man!"

Ni dai shiru nayi dan ban son maganar ma sai kace bai san kunyar sa nake ji ba.

jijigani ya ringayi har bacci ya dauke ni. kiran Sallah da ake na azahar shi yasa na tashi.
Alwala mukayo ya tafi massalaci.







*INDABAWA*
[11/20, 1:18 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY



BY *Maryam S Indabawa*
*MANS*

🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾.





Page *72*










Zaman lafiya muke gudanar wa sosai na cire kunya na ringa kula da mijina dan ni kaina ina mamakin wani abun da nake masa. To in ban ba ya auro wata tai masa na zama koma baya.

Ina son Ya Haidar kamar yadda yake tsananin sona da kaunata. Sam bai son ganina cikin bacin rai ko damuwa. Kamar kwai akan Fa haka ya Haidar ya mai dani.

Kowa kokarin yake yaga yafi dan uwan sa kula da dan uwansa yake.
Har gasar yin abu muke duk dan wannan yace yafi son wannan.

Gaskiya nasan nayi dace da miji na gari wacce kowace mace zatai sha'awar auren sa.

Yadda ya Haidar yake min har mamaki nake ji dan yana shayar dani soyayyar da ban taba zaton samun ta ba.

Kudi kuwa kullum sai ya zube min su duk da ba amfanin da nake dasu. Komai nasa tare muke yi haka nan komai nawa tare muke.

Bama in weekend ne tare muke gyaran gida da girki bayan nan kuma muyi wanka tare kowa yaiwa dan uwan sa kwalliya.

Na yadda Soyayya gaskiya ce. Sannan sai da ita ake samun jin dadin zaman aure.

Mijin Ummu nahМесто, где живут истории. Откройте их для себя