FARHAT. its all about love and romance

1.5K 44 0
                                    

💥🔥💥🔥🌹🌹
FARHAT
💥💥🔥🔥🌹🌹

Writing by ummee yusuf(maman yusuf).

Page 6

FARHAT kenan amma asalin sunan ta aisha bukar alibe.ya daya tilo ga shahareren mai kudi kuma dan kasuwa da yayi fice anan cikin gida naija da kasashen ketare.

Alh bukar alibe ya kasance asalin borno state kanuri ne shi gaba da baya .auran soyayayya suka yi da matar sa hjy kaltuma duk da ta kasance shiwa arab,sai dai allah ya jarabce su da rashin haihuwa tsawon shekara 12.kwasam rannan allah ya albarka ce su da samun ciki,murna wajan ma uratan ba a mgn.haka suka ci gaba da rainon cikin har allah yasa ya kai watan haihuwa,ranan wata safiya hjy kaltuma ta tashi da nakuda sai dai ba a dauki digon lokaci ba ta sunkuto yarta kyakkyawan gaske mai kama da mamar ta sak sai duhun baban ta da ta dauko.

Ranan suna anyi bidiri sosai dan naira taci kashi.taci sunan kakar ta na wajan baban ta wato ya aisa,shine ake kiran ta da farhat(mai fara a kenan).

Alh bukar ya kasance ba inda ba a san shi ba wajan taimako da son mutane sosai yake taimakawa talakawa,dan haka baka raba gidan sa da jama a sai dai in baya gari.

Farhat kuwa tun tasowar ta bata da abin ki irin talaka,ta raina talaka ko Yan aikin gidan su hkr suke da ita.lokacin da ammin ta ta tara gane halin ta kuwa hankalin ta ba karamin tashi yayi ba,Dan ita da mijin ta ba mai irin wannan halin.

Bata yi wata wata ba ta fara tsawatar mata da nuna mata illan hakan sai dai ko kadan farhat bata daukan wannan nasihan ammin nata.ko a skul ba kowa take kulawa ba sai Dan wane da wane,shiyasa tun tasowar ta bata da wasu frnds.kwata2 frdns dinta 2 ne kacal ramlat yar gidan wani ambassador ce said Ruky yar gidan shehun borno.

Allah ya bata kuri da son nuna ita din wata ce a duk inda take,lokacin da Ta gama sec skul,burin ta daya ne wato fita abroad karatu tana ganin bata da matsala ganin yanda abban ta yake daukan nauyin karatun yaran mutane tare da fitar dasu bare kuma ita yarsa tilo.amma abin mamaki lokacin da result dinsu ya fito,ta samu 9crdt cike da dauki tacewa abban ta ita London take son zuwa karatu tunda shima business dinshi sun fi yawa a can.Abba yace Ai shi ko kano baza ta je da sunan karatu ba bare abroad,shi ba haka a tsarin shi mace tayi nisa da gida da sunan karatu.

Bori sosai farhat ta tayar Wanda tasan ada in tayi abban ta kome take so zai mata amma Ga mamakin ta wannan karon ba nasara da haka dole ta hakura ba Dan taso ba.ta fara a nan uni maid,tana level 100 tana karanta business admin. Dalilin haka ta kara tsanan talaka a ganinta basu da zuciyan nema sai dai inutum ya nemi abinsa suzo su same shi maula.shiyasa ta musu lakabi da poor beggers.Bama kaman masu fita karatu da taimakon abban ta toh duk tafi tsanan su.shiyasa ta Dora damaran yaki dasu.

In kana neman pretender ko actress in ka samu farhat toh ka gama.in kaga yanda takewa masu zuwa Neman Taimako gidan su a gaban iyayen ta baza ka taba yarda cewa tana kin su ba.

Ammin tana kokari wajan bata tarbiya na gari duk da takasance ita kadai ce gareta. bata dauka wani shagwaban ta ko kuma tana gani tayi wani Abu ba dai dai ba tayi shiru,fada take mata sossi ko in ta kama dukan ta ma tana yi

Tsabanin abbanta da yake shagwaba sosai,yana matukar ji da ita.shiyasa take abinda taga dama in yana gari.

In taga masu Neman Taimako sun zo wajan abban ta, duk yanda zata yi taji taimakon da suke nema sai tay.in taji taimakon wani abune toh ba zai dame ta ba amma in taji na fita karatu ne zata nuna goyan baya tare da jin dadin ta.da Zaran sun kebe dasu sai tayi musu wulakanki da rashin mutunci tare da Jan kunne akan su janye ,in ka dauka toh ka tsira amma kayi taurin kai kuwa su hadu ita da frnds dinta suyi maka Sharrin da yafi karfin ka.

A ganinta tunda ita da take yar Sa ma bata je ba toh inda Sanin ta ba Wanda zata bari ya tafi sai dai a bayan idon ta.

Lokacin da ta shiga unimaid,samari sun yi ta tururuwan sonta amma ba Wanda ta taba kulawa saima rashin mutunci da wulakanci ya raba su.shiyasa in kana son kan da mutunci ba zaka je mata da sunan so ba.son kurin ta da son a Sanin ta yasa in suka je cafeteria cin abinci sai tasa anyi mata bill na wayan da suka ci abinci a wajan duka ta biya shiyasa masu kwadayi da son bati suke kiran ta da UNIMAID STAR.

Muddin ka kirata da wannan suna ko me kake so zata yi maka shi cos dama kudi ba matsalan ta bane.shiyasa take taka duk Wanda taga dama,a Cewar ta ita tafi karfin samarin Maiduguri,kai ita a naijan ma bata Ga Sa an auren ta ba.

FARHAT   Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang