FARHAT. its all about love and romance

4K 124 4
                                    

💥🔥💥🔥🌹🌹 *FARHAT* 🌹🌹💥💥🔥🔥

Writing by Ummee Yusuf( Maman Yusuf)

Page 1-5

BISaMILLAHI RAHMANIR RAHIM
Zaune take agaban tangamemen dressing morrown ta da yake shake da kayan shafe shafe hade da kayan Make up perfumes masu tsadan gaske. Katon dakine na gani na fada an kawata shi da royal bed pink colour wanda yasha shimfidu masu taushin gaske. komai na dakin pink and white ne dakin ya matukar tsaruwa tamkar kamar na wata amarya. Kana gani kasan na yar gatace
Shafe shafenta take cikin kwanciyar hankali daga ita sai dan karamin towel iya karsa cinya daya kuma ta nade gashinta dashi .bata dauki dogon lokaci ba ta gama shafe jikinta da lotions masu kamshin nan ta fara kwlliyarta cikin iyawa da kwarewa. Nan da nan ta kara kyau na musamman koda yake dama itadin kyakkyawa ce sosai,ba fara bace bt skin dinta yafi na wani farin kyau cos chocolate colour ce irin na black Americans din nan.gata da round face Wanda ya dace da manyan idanunta mai dauke zara2 eye lashes. ga gashin giranta mai yawan gaske,hancinta bai cika dogo but ya kawata face dinta sosai.
Sai da na tsorata da ta kunce towel din kanta saboda yawan gashin kanta mai tsantsi da tsayi gashi baki tsidik dashi.hand dryer tayi amfani dashi wajan busar da gashinta. parking din gashi tayi bayan ta shafesu da mayuka masu kamshi da tsada. wajen sip dinta ta nufa ta bude side din inner wears dinta,ta saka komai white sannan ta dawo side din gowns dinta ,tana Mazarin wanne zata saka yau ta ciro wani light blue taga bai mata ba ta Villa shi kan bed nan ta kara ciro wani black shima Kara cilli tayi dashi.
Haka ta rinks cilli da kayan da kyar ta samo wani arabian gown maroon and black yasha stones ta gabanshi tasa ta yane kanta da veil din Wanda shima maroon and black ne,fashion jawllery ta saka tare da feshe jikinta da perfumes masu dan karan kanshi kallon kanta ta tsaya yi a mirrow tana murmushi, cos ita kanta tasan ta hadu over fari tayi da ido tare da rike Dan waist dinta tace (how dare u, u don't hv d right 2 luk so beautiful like dis)smiling takarayi,kan side drawer ta nufa ta kwashe phones dinta ta zuba su awani hadadden black handbag.arean Adana shoes nata ta wuce gasu nan birjik Kala2 masu kyau sun kai kusan 50 duk kuwa high hills ne da alamu sune favorite nata.wani disiner black shoe tasa aciki tare da fitowa cikin sauri2 cos ganin ta kusa makara.

Sauri2 take saukowa daga steps din,ta kusan tsakiya suka hadu da ladi mai aikin gidan su sai dai duk wani aiki nata ladi ce maiyi mata. cikin rawan jiki ladi ta durkusa ta gaishe ta,rankwashi ta sake mata a tsakiyan kai ba tare da ta amsa gaisuwan ba. kasa kasa ta fara mata mgn tare da mata kallon kaskanci tace "ban hana ki durkusa min a palour ba ko sai ammi ta fito ta ganki?" cikin sauri ta mike tana bata hkr hannunta kuma na sosa inda tasha rankwashi. "
Habibty hiran me kuke ne keda mutuniyarki haka?" Juyowa sukayi atare suna kallon ammi da take saukowa ynxu cikin shiga na alfarma fuskanta dauke da murmushi,kamo hannun ladi tayi tana yar dariya tace "ammi kema kinsan in mun hadu da ladi hiran mu bata karewa,ko ladi" tace tana kallon ladi da ta kakalo murmushin dole "nasani bt kinsan zakiyi late ko?muje kiyi b/fast ki wuce skul ok? " ammina tace tana karasa saukowa. Har ta sauko kuma ta waiwayo tana kallon ladi da ta kasa gaba balle baya tace "yauwa ladi nayi miki ajiya a dakina" "toh ngd" ta amsa mata tana kara hawa saman dama tasan da ajiyan,bakomai bane face gyaran bedroom dinta take nufi cos tafi kowa sanin halin uwar dakin nata kamin ta shirya sai tayi kaca2 da dakin.tana isowa cikin katon plourn nasu wada yasha kayan alatu dan fadan irin tsaruwan shima bata lokacine.ammi ta tarar tana amsa waya bata tsaya a palourn ba,dining area ta wuce taja kujera ta zsuna.yafalta mai kula da lamarin kitchen din gidan ta da wani madaicin tray mai dauke da cups dasu plate ta ajiye akan table din.kokarin durkusa mata ta fara dukda ta girmeta nesa ba kusa ba,mugun kallo ta watsa mata shi ya hanata durkusawan da tayi niyya.
Ganin amminta na zuwa yasa tayi rutsunawa tace" yafalta inda wattu!" baki na rawa yafslta ta amsa kana ta gaida ammi wacce isowanta kenan fuskanta dauke da fara an ganin yarta na jan masu aiki a jiki.kujera taja ta zauna kusa da yarta serving dinsu ya falta ta matso dan tayi amma ammi ta dakatar da ita tace "habibty serve us." baki ta dan turo na irin ta tsani aikin nan but ba yanda ta iya dole ne tayi ko ammi taci ubanta ga abbanta mai tare mata baya nan.cikin lokaci kadan tayi serving dinsu chips ne da scamble egg wit liver source,tunda suka fara ba wacce tayi mgn kadan taci ta mike tana shirin daukan handbag dinta.wai har kinyi me?ammi ta tambayeta tana kallonta.na koshi tace a takaice,girgiza kai ammi tayi tace bansan ranan da zaki canza ba ace mutum kwata2 baya cin abinci.shagwabe face dinta tayi tace allah ammi ina ci fa,hmmm wannan abinda kikayi shine cin abincin?shiyasa kike nan kaman a hure ki ki fadi.dariya tayi ta dauki hndbag dinta tare da hugin din amminta tace im off ammina sai na dawo.allah ya tsare nd make sure kinci wani abu a skul ammi ta bata amsa insha allah ammi tace tare da ficewa daga palourn zuwa compound din gidan wanda yasha flowers kala2 direct parking lot ta wuce ta shiga wani hadadden matanta black colour sai sheki take.hanyan gate ta nufa tana drving a hankali bamodu mai gadi yana ganinta ya mike da gudu ya wangale mata wagegen gate tare da gaishe ta amma ko kallo bata ishe shi ba,tayi wucewarta girgiza kai yayi yana takaicin halin yarinyan.drving take a hankali cikin anguwan su na new g.r.a har ta fito bakin n.u.j nan naga tayi parking ta fito da wani black sunglass ta manna a face dinta wanda ya kara fito da kyanta.wani plate din music naga tasa tare da kure volume.nan ta figi motan a 100 tayi hanyan unimaid.

FARHAT   Where stories live. Discover now