Su Faiza da Hauwa, ma sunyi kyau haka su Ya kamal da Ya Nura.

Khadija da bishira ba sun yi kyau anyi barin kudi an sha rawa.
Sai sha daya suka tashi.

Ranar Alhamis akai kamu, wani yadi ta saka wanda duk jikin sa stones ne. Mutli colour. nai adon ja. head takalmi da mayafi.

Tana shiga ganin taron jama'a yasa ta fashe da kuka. Ummu ma kukan ta fashe dashi ganin ga ranar auren ta amman Abbun su baya nan.

Kowa yazo yan uwan Abbu na ma duk sun zo.

Ranar ansha kuka kamar me.
Ranar an yi kamun gargajiya in da aka raba mufici da kaski da turarukan ruwa.

Ranar juma'a akai yinin Ummu. amarya tai kyau cikin purpke din material me kyau. Ranar ma idanun ta jawur.

Inda Mutane suka halarta sosai amarya tayi kyau kamar ka sace ta ka gudu.

Amman ita kadai tasan ciwon da take ji.

Asabar akai dinner. Har Abokan Ya Haidar sun zo inda amarya ta saka pink din kaya da adon milk. Ango ya sha milk din shadda.

Fadar irin kyau da kudin da aka kashe bata lokaci ne.

Ya Haidar duk ya zuba mata ido dan ya kasa dauke idon sa. Sannan daga ganin ta yasan akwai abinda ke damun ta dan yaga yadda take dafe kirji ko dan cije baki.

Kasa yin shiru yayi,
"Baby na lafiya kuwa?"
Dagowa tayi ta kalle shi.

Murmushi ta saki,
"Ba komai."

"Anya kuwa Baby. Kinga idanun ki sun fada."
"kar ks damu kirji ne ka ciwo kawai."

"Muje asibiti kenan."
"A'ah! Zai daina ne."

"To kinsha Maganin kine."
"A'ah in an tashi zan sha."

"Allah sauwake.!"
"Ameen!"

"Gobe fa za'a kai min ke ko."
Murmushi kawai tayi.

"Baby na gobe kin zama mallakina."
"Ya Haidar ka bari man."

"Shikenan nayi shiru."
Hannun ta ya kamo yana taba zanen lallen ta.

"Abin nan yayi kyau."
"Ya Haidar ka bari."

"Dan na yaba da kyan lallen."
"A'ah rike hannun nawa da kayi."

"To na saki shikenan."
Kai kadai na daga.



*INDABAWA*
[11/20, 1:05 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY

By *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾





page *47*



Ranar Lahadi daurin aure tin Asuba Hafsat ta tashi da wani matsanaicin zazzabi ga ciwon kai.

Daurewa take har akai mata kwalliya.

Shigowar Abbi ita ta kara ruda ta. Dan tana falon Ummu a zaune, ya shiga.

Cikin bedroom ya shige Ummu ta bi bayan sa.

Ina daga falo na jiyo har gagin sa.
"Kin jini ko. Wallahi yanzu zan je kuma sai na sa an daura da Shehun da ba kwaso. Dan haka ki kira ma ki fada musu."

Daina ji komai tayi. Ji tayi ta daina gane komai sai ta fara kokawa da numfashi ta fadowa tayi daga kan kujera ta kife a kasa. Numfashin ta ya dauke.

A fusace ya fito a dakin ya fice a gidan ya sa Shehu ya shirta ya biyo shi dan agundin.

Karfe sha daya dai dai aka daura auren *Hafsat  da Ya Haidar*

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now