"Lafiya Alamhamdulilah."
"Baby na sauran kwana nawa ne?"

"Me fa?"
"Ki zama mallakina."

"Ai yanzu ma taka ce ni."
"Haba da gaske?"
 
"Eh saura wata nawa."
"A'ah ban son zancen wata. Sati nawa zaki ce."

Dariya tayi. tace,
"To saura sati nawa?"
"Sati sha biyu."

"Ya Haidae kenan wata ukun dai kenan."
"Hmm ai ban san a ce watan ne. So nake naji an fara cewa sauran sati ko kwana kaza."

"Rai dai!"
"Haka ne, Allah nuna mana da rai da lafiya Ameen."

Sukai sallama.


Ko da Abbi ya zo Ummu ya rufe da fada dan me Hafsat za tayiwa dan yar sa haka to wallahi shi zata aura.

Ummu dai shiru tayi tana mamakin yaushe Abbi ya koma haka dan duk sai yanzu take ganin wasu dabi'u nasa. Dan duk abinda ya faru bata cikin hayyacin ta.

Jin take kamar a mafarki abun ya faru shiyasa take mamakin in taga yana wasu halaiya na daban.

Har ya karaci fadan sa da nuna isar sa ta sai Hafsat ta auri zabin sa

Kala Ummu bata ce ba sai kallo da ido kawai.

Shi a tunanin da ta dauka kamar yadda in yace abu kaza ne zata ta yadda ko va haka bane.

Gidan ya fice ya bari.

Ummu har gun Hafsat taje ta fada mata yadda Abbi yace.

Hafsat taso ta daga hankalin ta amman Ummu ta kwantar mata dashi tace,

"Hafsat kar ki damu kullum buri na da Addua ta ki samu miji na gari mai hankali wanda zai rike min ke amana to Allah ya amsa addua ta kuma nayi istahara naga da alheri dan haka ba abinda zai biyo baya."

Sai da ta gama lalabata da magan ganu masu dadi sannan ta kawo hiran abubuwan da take bukata na kammala karatun ta da aure.

Lissafa mata tayi suka qirga kudin da zara bukata.

Sannan da yadda biki zai kaya.

Kudi masu yawa suka kirga.
ummu tace,
"Hafsat baza a taba muku kudi ba. Wannan yasa na siyi filaye wanda in bikin ku ya tashi baza a taba kudin ku."

"Haba Ummu wai menen amfanini kudin namu?  Shin wai abun mu ba naki bane."

"Ba haka bane Hafsat. Ai nauyin ku akai na yake ni ya kamata nai muku ba kuba. In nai muku da kudin ku kamar ku kukai ne."

"Ummu ni fa na dade da cewa ki amince ki karbi kamfanonin nan mun baki amman kin ki."

"Kul na hane ki da kara tada maganar na. bani da burin da ya wuce na gan ku cikin kwanciyyar hankali da farin ciki. Yanzu in kun bani na mutu fa. Wanda bai cancanta ya shiga cikin dukiyar ku ma shiga zaiyi."

"Kiyi Hakuri Ummu."
"Baki kin komai ba. Allah miki albarka."

"Ameen."
"Aliyu ya fada mike ne. Nan da wata daya zasu je yin order kayan dakin ki. Anty Fatima wai dole sai naje."

"Mama Fati kenan. Sai Kije ai."
"Eh amman sai naga tashin ku tukkuna."

"Tashin mu kuma Ummu."
"Eh na biya muku umra keda Khadija da Khairat zakuje. in kun tafi sai mu hadu mu dawo tare lokacin sauran sati biyu kuyi final exam,"

"Masha Allah!  Alhamdulilah! Ummu. Allah saka Miki da alheri yasa ki gama lafiya. Ameen "

"Kar ki damu."
Rumgumeta Hafsat tayi tana mai jin farin ciki a zuciyar ta.

Tin da taji zance tafiyar su ta mai da kai kan karatun ta dan tasan in har sunje can ba lokacin karatu sai na ibada.

Dan bata manta zuwan su da Abbu da yace,
"Hafsat duk lokacin da kika ganki anan kada kiyi wasa da damar ki wajen yin addu'a. Ba ga ke kadai ba ga duk yan uwa musulmai. Nayi duba naga sai dai ban riku abu anan ba amman da na roka Allah ke amsa min. Dan haka ki nemawa kanki rayuwa mai kyau da inganci."

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now