A babban Falo ta same shi zaune. yaci wani yadi sai tashin warin wiwi yake.

Murmushi yayi da yaga shigowar ta.
Gefen kujera ta samu ta zauna.

"Ina yini?"
"Lafiya Ya gida."

"Lafiya lou."
"Uhmm daman wata magana nazo da ita."

"Ina jinka."
"Daman ba komai ya kawo ni ba sai nazo na fada miki ina sonki ne.  Kuma aure nake son muyi."

"Allah sarki! Sai dai kayi hakuri dan akwai wanda nayiwa alkawari. Sai dai zan maka adduar Allah baka mace ta gari."

Fuska ya hade ya wani sha kunu yana muzurai irin na yan daba.
"Ina bazai yiyu ba. Ni ke nake sso kuma ke zan aura. Kinji na fada miki ko kuma ki tsaya ki zuba ido ki gani."

Ya fice kamar zai tashi sama.

Murmushin takaici tayi dan tasan wanda zai turo shi.

Tasan ba kowa ya saka wa Shehu wannan tunanin ba sai *Mijin Ummun tah*

Dakin Ummu tayi ta fada mata duk abinda ya faru.

Ita ma Ummu murmushi kawai tayi tace,
"Ki kwantar da hankalin ki. Ki dage da addua Allah yana sane dake."

"Kinsan dai Ba wanda zai miki auren dole bayan an riga ma da an gama magana da iyayen Aliyu. Addu'a zaki kara mikewa da ita. Nima zan kara mikewa tsaye."

"Nagode *Ummu nah* " ta fada tana mikewa tayi daki.

Lallai Abbi u.yanzu na kara sanin ba son mu yake ba. In ba haka ba taya ana son auren miji na gari zai turon shehu.

Zuciyar ta taji kamar zata buga dan zagi da bugun da take mata.

Al qur'ani ta dauko ta fara karantawa. Dan tasan shine magani komai a rayuwa.

Tasan shi zai yaye mata duk abinda take ji da bakin cikin zuciyar ta.

Tana fara karantawa ta nemi abunda take ji ta rasa.


*INDABAWA*
[11/20, 1:02 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY



BY *Maryamm S Indabawa*
*Mans*


??HAJOW????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍??✍??✍??


Page *42*



Sister tah *Surry Arab* love u.

Ummu sudais. Allah kara mana dangon zumunci Ameen









Ummu ce ta leko, ta hange ta rike da Al qur'ani. Bacci ya dauke ta.

Karba ta yi ta maidashi ma ajiyar sa sannan ta fita.

Sai wajen magariba ta tashi. Alwala tayi ta tada sallah.

Bata tashi akan sallaya ba sai bayan isha'i.

Kitchen taje dan samun abinda zata ci.

Kwai ta tasa ta soya shi. sannan ta hada kunun alkama ta zuba masa madara da sugar.

Daki taje taci sannan ta kunna kallo.
Wayar ta ce tayi kara dubawa tayi,
Ya Haidar ne.

Cikin sanyin murya ta amsa mishi.
"Baby na lafiya kuwa?"

Abinda ya tambaye ta kenan dan jin muryar ta wata iri.

"Lafiya lou. Nayi bacci ne."
"Ok amman muryar ki tayi sanyi sosai fa."

"Kar ka damu."
"Dole na damu man."

"Hmm yasu Mamana."
"Lafiya lou."

"Ya aiki?"
"Alhamdulilah! Ya makaranta."

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now