Budewa yayi wani zuben gold ne a ciki. Hannu na ya kamo, ya zura min.
Sosai yai mata kyau ya kara fito da hasken hannun na.

Sumbatr hannun ta yayi,
Sannan ya jawo ta jikin sa ya rumgume ta. Kasa janye jikin ta tayi.

Fuskar ta ya tallafo ya dawo. Idon ta ya kawo ruwa. Kallon juna suka na minti na sannan tai kasa da kanta.

Kanta ya kuma dagowa ya matso da fuskar sa. Gane abinda zai yi yasa na dukar da kai na.

Murmushi yayi ya kara rumgume ta, janye jikina nayi.
"Har Ga Allah ban son barin ki sai dan dole,"

Kallon sa nayi, sai nayi tausayin sa dan idon sa yayi jawur dashi.

Nima jinai zuciya na zaffi. Kamar na fashe da kuka.
"Kayi hakuri insha Allahu, nan da wani lokacin muna tare."
"Allah yasa. Allah nuna min wannan lokacin."

"Ameen."
Bude kofar yayi, muka fita rike da hannuna. Cikin dabara na zare hannuna. Har muka karasa gefen su Faiza,

Sai da mukaji an fara kiran suna sannan muka mike. Sai a lokacin naji kewar sa.

Dan bansan lokacin da hawaye ya fara zubon ba yana ganin haka ya dawo.

"Haba Baby ya kuma kuka. Kina son hankalina ya tashi ne, kiyi hakuri mun kusa kasancewa tare har karshen rayuwar mu insha Allah."

Ya jawo ni jinkinsa yana lallashi yana bubuga bayana. kara shigewa nayi jikin sa ina cigaba da kukan.

Shima idon sa yayi jawur, ganin nayi shiru yasa yakira Faiza da Hannu ta karaso ya mika mata ni.

Wajen Ya kamal ya isa ya rumgumeshi, dai dai karasowar su Hauwa kenan.

Hauwa ta karaso wajen mu tana dariya kasa kasa, Ya Nura kuma wajen su Ya haidar yaje ya rumgume shi.

"Kamal ga amana ta nan ka kular min da ita kar ka barta tayi kukan komai. In abin ya fi karfin ka ka sanar min. Ka kular min da ita."
"Kar ka damu kasan yadda muke da Hafsat ai baka da matsala."

Rumgume juna suka kara yi. Sannan ya koma wajen su Hafsat.

Da gudu ta karasa jikin sa ta rumgume shi.

Wajen su Faiza ya karasa da ita,
"Faiza ke zan bawa amanar ta dan wani satin su Hauwa zasu taho."
"Kar ka damu ya Haidar."

Dai dai kunnen ta ya kai bakin sa, rada yai mata. Sannan ya sake ta.

Murmushi tayi, shima haka. Ta juya ya tafi yana murmushi.

Yana dago musu hannu.

*INDABAWA*
[11/20, 1:00 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??



Page *38*

Dedicated to my daugthers.
yara na manyan gobe ina son ku ina kaunar ku Allah barmu tare.
*FADIMATU, HALEEMATU, AMINATU,(MEENAL) mamana ta kaina.*

So love u yarana.


Sai da muka ga tashin su sannan muka tafi.

Gidan Faiza muka tafi, dan ya Kamal yaki kaini gida. muna zuwa ban san lokacin da bacci ya dauke ni ba.

Suna sauka ya kira bata dauka ba. Text yayi mata

Sannan ya kira Ya Kamal yace ai bacci ne ya dauke ta.



Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now