Hauwa tace, "Haba ukuti, kinsan fa kina da lalura amman kike neman sawa kan kidamuear da zata tayar miki da ciwon ki ko.kinsan an hanaki tunani."

Tayi shiru ta jawi hannun ta.
" Ya Haidar namiji ne da kowacce yarinya zara so ya zamo mijin ta."
"Nima dai haka na gani ban ga aibun sa ba. Ta komai yayu kivar wannan damuwar da tinani kiyi istihara yafi."

"Hmmm! ba komai wallahi tsoro nake ji na halin mazan nan. Amman zuciyata na yabawa da hankaki da nutsuwar shi da ilimi."

Tayi shiru idanun ta ya kawo ruwa.
"Kuna tayani da addua Allah ya zaban mafi alheri. Ban son na amince dashi abin yazo bai yi ba ya bata yan uwar takan mu, bans an da wane ido zan kalle shi ba ko Mama Fati."

"Kina tunanin mau kyau ki daina kawo wannan tunanin insha Allah zamu na miki addua ba abinda zai faru amsai alkhairi." Faiza ta fada tana kama dayan hannun nata.

"Kar ki damu indai addua ce kullun cikin yin ta muke sai dai fatan Allah ya amsa."
"Ameen Nagode."

"Ba komai kan mu mukaiwa." Daga haka suka dau hira da yan gyare gyare. Sai tamma muka tafi gida.

Hauwa a ranar Ya Nura yazo ya dauke ta.  Sukati gidan su sai ya rage sai ni kadai.

Washe gari Mami tace sam sai na gama hutawa zan koma gida. Ba yadda zan yi haka na hakuri.

Ba abinda Momy take bari na nayi daga kwanciya sai kallo da chat.

Sai da nayi sati ta barni na koma gida. Da kanta ta kaini da uban kaya. Sai gidiya takewa *Ummu nah*

*INDABAWA*
[11/20, 12:56 AM] Antty😍: *MIJIN UMMU NAH*
TRUE LIFE STORY


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*




?? *HAJOW* ????

??‍??‍????‍??‍????‍??‍?? *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* ✍??✍??✍??


Page *32*




Ya Haidar kuwa ya Kamal yace ya dan bani lokaci nayi tunani kar ya kirani ya dan janye jikin sa.

Waya dai baya kirana amman kullum text zai yi min safe, rana da dare.

Zaune nake sanye da jar riga da bakin siket dogo, kai na da na gyara. Ba dankali. Ina daki duk kewar hirar da muka sabayi da Ya Haidar ta isheni, ina son kira bana son wani abu ya biyo baya. danayi dailling zan kashe tin kafin ta shiga.

Sallamar sa najiyo daga tsakar gida ba kowa a gidan sai ni. Ni na amsa.

Babban falo ya shiga hijab dina na sanya nayi can falo.

Zaune yake sanye da bakin wando da jar riga mai dogon hannu sai waya dako hannun sa.

Da sallama na shiga, ya amsa yana bina da kallo.

Sosai na rikita shi dan kallo ya dinga bina dashi sai kace bai san ni ba.

Durkusawa nayi. Nace,
"Ina yini?"
"Lafiya lou Baby, Ya gidan."

"Gida lafiya."
"Ummu fa?"

"Ta fita."
"Haba dai kuma wajen ta nazo."

Kasan zuciyar sa kuwa cewa yake wajen ta yazo kuma ya ganta yaji dadi.

"Bari naje anjima na dawo."
"Bari na kawo maka lemo."

"A'ah barshi kawai."
"Dan Allah!" Na fada murya a narke kamar zanyi kuka,

"To shikenan."
Da sauri na fice. Dan bana son ya tafi nafison nai ta kallon sa.

Sosai yake jin ta har cikin ransa. Komai nata burgeshi yake yi. Ji yake kamar ya kamota ya tusa ta cikin jikin sa.

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now