Farkon auren komai na rayuwar ta ya dauke mata, kama daga ci da sha, kaya ne dai bai taba dinka mata ba, Kudin albashin ta in tayi wa su Hafsat bukatun su sai ta kai banki ta ajiye sauran, dan duk wata ba abimmnda bata ajiye wa su Hafsat kamar yadda Mahaifin su ke musu, haka take yi musu, aje shopping ko aje wayon shakatawa.


A wanje mahaifiyar ta tabar sun Hafsat da Khadija, dan bata son taje damu ana wulakanta mu.

Zaman su Hafsat a hannun kakar su Baba Zulai, sam ba sa ji dadin sa, ko dan mai matan ya rasu ne, dan Abbu duk wata sai ya loda mata kayan abinci da kudi, in azumi yazo har kayan rabo yake bata tayi, sannan yayi mata dinki, to a lokacjn ba kamar su Hafsat duk jikokin ta tafi son su.

Amman yanzu sam, ko dinkin da ta sabayi musu duk shekara ta daina, sai dai tayi wa wadanda suke da uba, abin duniya ya rufe mata ido.

wannan yasa Ummu ke kashe musu kudi sosai tai musu kaya masu kyau da tsada, dan kwata kwata dangin Abbun su ko waiwayen su basa yi, bare su musu wani abun.

Ummu ita ta zame mana Uwa da Uban mu, ita take hana su kukan komai, dan komai na rayuwar jin dadi tana ajiye musu.

Wani abun wai Baba Zulai sai tana jin haushi dan Ummu ta mana abu, Ummu kance mata inban musu ba wa zai musu, kuma dan me nake nema.

Baba Zulai ganin ba yadda zatayi ta hana Ummi yi mana abu yasa ta fara hadamu da yan uwan Ummun mu, yau tace mun mata kaza gobe mun mata kaza.
Kullun ati tayi mana fada.

In mun fadawa Ummu sai dai tayi ta bamu hkri, takan ce zaman tare haka ya gada, amman mai hakuri na tare da Allah, Allah na sane da ku, kuci gaba da hakuri kullum nasihar Ummu kenan ga ya'yan ta.

Haka in sun zauna zatayi ta jan hankalin su akan kula da addinin su, da kame kansu, shi yasa suke so zama da Ummun su dan in dai suna tare tana yawan jan hankalin su da abjbda yake dai dai da wanda ba dai dai naba.

Uncle Tijjani ya dade da rasuwa, inda Uncle Ado yake da ya'ya 4, Anty Fatima kuma tana lagos tana Abuja tana aure da dan ta Haidar.

Hajiya Mariya a hankali ta dinga fuskantar halaiyar Alhj Umar.

Muje zuwa


MS INDABAWA
[11/20, 12:44 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
8

By MARYAM S INDABAWA
MANS

Wannan shafin naki ne Rabi'at Shuaibu Idiris, (Rabra) Allah raya mana ya'yan mu Ameen

Hjy Mariya a hankali ta fara fuskantar halin mijinta, ashe auri saki ne dashi, dan matan sa 3 duk ya aura ya saka ba wacce ta taba mutuwa.

Ta faron ya'yan 2, ta biyun yar ta daya, sai ta ukun da bata haihu ba suka rabu, kuma ashe buga bugar sa kawai yake yi ba wani kasuwanci sai kuma yar malamta da yake tabawa.

Halin kunci ya samu Ummu dan wani lokacin ko abinci basu dashi, wannan yasa, Ummu duk wata sai ta ajiye kayan abinci. Abinda bata sababa wai yanzu ita ke ajiye kayan abincin da zata ci.

Kullum ta tuna rayuwar ta, ta baya ta kanyi kuka, sannan ta godewa Allah dan ta san wannan jarraba ce sai dai tana fatan Allah bata ikon cinye ta.

Duk da haka MIJIN UMMU in ta siyo kayan abincun, in ta fita aiki sai ya auna yaje ya siyar ya samu na sawa a wayar sa, dan kiran yan.matan sa.

Ita dai Ummu hakuri kawai take da halin mijin ta, ga dangin sa ba son ta suke ba.

Ganin halin da ya'yan ta Hafsat da Khadija ke ciki yasa take son debe ya'yan ta, toh amman ba debewar ba ina zata ajiye su, dan ita gaskiya bazara iya kwaso ya'yan ta ta kawo gidan mijin ta ba, dan tasan yaran ta baza su sake ba.

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now