Muje Zuwa

MS INDABAWA
[11/20, 12:43 AM] Antty😍: MIJIN UMMU NAH
TRUE LIFE STORY
7

writting by MARYAM S INDABAWA

Dis page is for you, Khadijat Taiyeb Na'abba, khady en mata.
Allah ta kawo miji na hakri Sis Khady, kawata ina sonki.




Hajiya Mariya na cikin takaba aka gane tana da ciki dan wata 4, dan haka watan ta biyar ta haifi dan ta namiji, ta sha kuka inda tace a mayar mata da sunan marigayi, haka kuwa akayi, ibda aka sawa yaron sunan Alhaji Muhammad suke kiran sa da Sabeer,

Satin yaron 2 ya rasu saboda fama da yake da ciwon ciki, Hajiya Mariya ta sha kuka sosai, dan sai alokacin take kara kukan rashin mijin ta da ua rasu.

Dan tana tuna lokacin da take masa zance haihuwa, take cewa ko ta gama haihuwa ne tinda lokacin Khadija na da shekara 7, yakan ce mata kika sani kk ya'yan da zan haifa kenan.

Ko da aka raba gadon Alhj Muhammad, mahaifan sa duk ya'yan suka barwa kamfanonin, kuma suka bukaci da a cire Hajiya Mariya daga ciki ya zama malakin su Hafsat da Khadija kawai.

Wai a zancin su anan shine, kar tayi aure ta haihu, ya'yan ta su shiga cikin gadon dansu, saboda suna son jikokin su, su samu ingantaciyar rayuwa kar su tagaiyara a rayuwar su.  Wannan yasa suka sa a fitar da ita.

*********
Manema dayawa sun fitowa Hajiya Mariya amman sam ko kula su batayi, da yake gidan Yayar ta ta koma ita da ya'yan ta Hafsat da Khadija.

Alhaji Mahmud wanda yake a mazainin mahaifinta, wato mijin yayar tane, yace, dole fa tayi aure tinda bata wuce auren ba dan a lokacin shekarun ta 30 a duniya.
anan take ce masa tana son a nema mata aiki, tinda Alhj Mahmud a ma'aikatar ilimi yake aiki.

Shekarar Alhaji Muhammad daya da rasuwa, Alhaji Mahmud Mijin yayar Ummu, ko ince mariqin ta shima Allah yayi masa rasuwa, Hajiya Mariya har tafi matan sa da Ya'yan sa kukan rashin sa, dan da shi ta bude ido ta gani a matsyin mahaifinta.

yana rasuwa takardar daukar Ummu nah aiki ta fito, Ummuna tayi farin ciki sosai, haka ma Ummi yayar ta,

Anan Gwangwazo aka samar mata makaranta, bayan an share zaman makoki ta fara zuwa aikin ta da nasariri masu yawan gaske, haka suka cigaba da rufawa kan su asiri, duk wata ita da Ya Muktar zasu siyo kayan abincu da kayan bukatar gida.

Shekarar Alhj Mahmud daya da rasuwa Ummi yayar Ummun mu ta rasu, innallillahi wainna illahor rajiun, mutuwar nan ta daki Ummu nah, dan jinya ta kwanta sosai, wannan yasa Mahaifiyar Ummu nah dauke ta daga nan gdn yayar tata, ta maidata gaban ta da zama,

Sai da Hjy Mariya ta dade tana jina sannan ta samu sauki ta koma bakin aikin ta, ko da tace, zata koma gidan marigayiya yayarvta sai aka hanata, wai tinda wadanda take gunsu sun rasu tai zaman ta hannun mahaifiyar ta.

Haka ta hakura amman duk wata in anyi albashi tana siyan kayan abinci da kudi ta kai musu.

Hafsat sunan kakarta ta wajen Ummun ta aka saka mata.

Ya'yan Ummi da yake duk sun girma kuma ana zaman lpy yasa suka zauna a hannun kishiyar Ummi, wato Umma.

Sai da Alhaji Muhammad yayi shekara 5, amman Ummu bata kula kowa.

Ana haka ne wani Alhj Umar ya fito yana son Ummu nah,
Alhj Umar yace shi dan kasuwa ne, sannan yana da mata daya amman ta rasu da marayun ya'yan sa mata 2, wanda yace suna hannun dangin mahaifiyar sune.

Hajiya Mariya tayi na'am dashi in da aka daura auren su, na family house din su ya kai ta, amman ita a bene take, bangaren ta daban, katon falo ne sai dakin bacci guda 2 da kitchen da bandaki.

Mijin Ummu nahWhere stories live. Discover now