JARABTA 6-10

856 45 0
                                    

*🙆‍♀JARABTA🤦‍♀*

*🌈KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION🤝*

*©Zahrah Galadima (Noorul~Jannerh)*😘✍

*Dedicated to Aunty Fauxah ('Yar Amana)😍*

*بسم الله الر حمن الر حيم*

*Wattpad: Bint_Lajawa*

*6-10*

Sun gama class d'in ranar 'karfe 2, sun fito lectures ne Hussaina ta ce ma Mahnoor dan Allah zasu yi magana a online tonight. Murmushi kawai tayi tace "Allah ya kaimu. Hope ba wani laifin na aikata ba, dan na san bana rasa abin laifi".

Dariya Hussy tayi tace "haba dai Besty, its nothing serious fah."

Da haka sukayi bankwana kowa yayi nashi hanyar.

💞💕💞💕💞

Mahnoor na komawa gida Mommy ta sakata tayi wanka tayi sallah sannan ta sauko ta ci abinci. Tana gamawa ta tattara ta mi'ke tare da fad'in "Mum zan shiga ciki in d'an yi karatu sai in fito."
Kallonta Mummy tayi tace "A'a ki je ki d'auko books d'in ki dawo nan."
Murmushi kawai Mahnoor tayi ta wuce.

Suna zaune tare da Mummy tana karatu suna d'an hira sai ga Ibrahim ya yi sallama. Da gudunta ta tashi ta dira a gaban shi, kuma sai ta tsaya kallon shi. Mummy ce tace "Allah shiryeki, kin tsaya kallon shi ne bazaki kar'ba kayan shi ki shigar ba?". Cike da jin kunya ta kar'ba tare da cewa "sannu da zuwa Ya Ibrahim." "Yauwa" kawai yace yana dariyarta. Wucewa ciki tayi shi kuma ya zauna gaishe da mama. Mahnoor na dawowa Mummy ta ce ta kawo mishi abinci. Shafa kai yayi yace "Wallahi dama kamar kin san yunwa nake ji, kuma Mummy tun last week nake so in dawo kawai saboda girkin ki."
Dariya tayi tace "shikenan amma na san ba dad'ewa zakayi ba koh?"

"Eh sati 1 zan yi in koma".

"Tab gaskiya ya kamata ka kawo mana suruka, ko baka san ka girma ba? Ka ga sai ka samu mai kula da kai."

Murmushi kawai yayi yace "toh" ya mi'ke ya bi Mahnoor kitchen. Bin shi da kallo Mummy tayi, ta san kunyarta yake ji. A hankali ta furta "Allah ya albarkaci rayuwarka Ibrahim, ya baka mace ta gari."

Samun Mahnoor yayi ta gama had'a komai ma tana shirin fitowa ya kar'ba tray d'in hannunta yace "'kanwata kin san meye?" Girgiza kai tayi. Ya kama hannunta yace "zo muje ki raka ni part d'in Ummi nah in ci abincin a can." "Toh" tace ta bi bayan shi. Mummy na ganin wucewarsu ta girgiza kai saboda ta san ko wajen mahaifiyarshi be je ba.

Suna shiga wajen Aunty suka sameta a parlour tana yankan farce. Sallamar su ne ya sa ta d'ago ta maida dubanta kansu. Fad'ad'a murmushinta tayi tare da amsa sallamar.

Zama sukayi a carpet kusa da ita. Tambayar 'kannen shi yayi tace "Amina da Ahmad sun dawo school sun tafi Islamiyyah. Zainab kuma yanzu zata dawo". Suna hira yana cin abinci. Yana gamawa Zainab ta shigo da sallamarta. Tana ganin yayan nata tayi jifa da jakar hannunta, da gudu ta rungume shi kamar ta shekara bata gan shi ba. Gaishe shi tayi sannan ta nufi wajen Ummi. Hararta tayi tace "sakarya kina abu kamar wata 'karamar yarinya." Dariya tayi tace "Sorry mum I missed him sosai ne." "Ki je ki ci abinci ku shiga kitchen. Kai kuma kaje kayi wanka kaje masallaci." "Toh" suka ce Zainab ta wuce. Juyowa yayi yace ma Mahnoor "Lil Sis ku dafa favorite food d'ina, kuma ki shirya min labarai masu dad'i kin ji?" "Toh Big Bro". Murmushi yayi ya ja hancinta ya wuce. Tattara wajen tayi tace "Ummi zan shigo anjima" "Toh dear ina nan ina jiranki duk da na san saboda yayanki zaki zo". "A'a wallahi Ummi ai ina shigowa sosai yanzu school ne ba sau'ki." "Shikenan Allah ya taimaka." "Ameen Mum".

💞💕💞💕💞

After dinner duk suna zaune a main parlour har da Abbah, sun gama hira kuma dare ya fara yi. Mahnoor ce ta ja Zainab za su je su kwanta. Ibrahim yace ku jira ni mu tafi. Sai da safe suka yi ma iyayen nasu suka nufi part d'in Ummi. "Big Bro sai da safe" "Good night sisters. Gobe idan kun dawo school zan baku tsaraban da na kawo muku." "Toh Ya Ibrahim mun gode."

Har sun kwanta Mahnoor ta tuna ta saka chargy a parlour. Tashi tayi ta je ta d'auko, ta ma manta sun yi zasuyi chat da Hussy. Kunna wayar tayi, messages guda 3 suka shigo. Bata san d'ayan numbern ba sai kawai tayi ma Hussy short apology text sannan ta kashe wayar. Bathroom kawai ta shiga ta yi alwala. Sallah tayi raka'a 2 sannan ta dawo ta kwanta. Addu'a tayi musu ita da Zee, wacce tuni bacci ya kwasheta...

*-Ko mene Hussaina take so ta fad'a ma Mahnoor?* _Kip d fire burning🔥. Don't 4get to drop ur comments_




*.....1 Luv❤.....*





*#Noorul~Jannerh*😘✍

JARABTAWhere stories live. Discover now