BABI NA BIYU

10.8K 599 14
                                    

🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊
💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔
( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_)
             *NA*

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*watpadd:huguma*

© *haske writers asso*💡
(Home of expert and perfect writers)

*babi na biyu*


Hikimar ubangiji ce haduwar jini qauna da shaquwa tsakanin wane da wane,yakan sanya irin wannan jituwar da qaunar juna tsakanin bayinsa,hakan itace ta kasance tsakanin wadan nan bayi nasa guda uku wadanda suka fito daga mabanbantan yare har ma da qabila,wanda daya daga cikinsu ma suka samu banbancin qasar haihuwa a tsakaninsu

*Alhj yusufa adamu*

  Haifaffen jamhuriyar nijer,cikin garin DIFFA,garine dake da qarancin jama'a cikin duka qasar ta nijer,tattalin arziqin yankin ya ta'allaqa ne kan noma da kiwo,mazauna garin sun hada da hausawa,fulani da larabawa.

alhj yusufa na daga cikin jinsin fulani wadanda a nan mukafi kira da sadakar yalla,duk da yake ruwa biyu ne shi,saboda asali mahaifiyarsa na daya daga cikin larabawan dake zaune cikin yankin wanda auratayya ta hadata da adamu mahaifin alhj yusuf.

Bai fuskanci wani qalubale wajen samun auren rahinatu ba saboda suna da wani yanki na sarautar garin diffa,mahaifin adamu a lokacin shine wazirin sarkin garin na diffa wanda ko bayan rasuwarshi sarautar bata bar gidansu ba adamu dinne yaci gaba da jan ragamar,kasancewarsa d'a na fari kuma babba a gurin mahaifinsu.

Yusuf tun yana qaraminsa zuciyarsa da tunaninsa sunfi ta'allaqa ga harkar siye da siyarwa wato kasuwanci,wanda hakan shi ya zama sanadiyyar haduwar jininsu da qanin mahaifinsa muhammadou wanda ke kasuwancin dabino da cukui tsakanin nijeria da niger.

Yadda ya lura da hazaqar yusuf da qulafucinsa na son kasuwanci yasa ya fara daukarsa rakiya zuwa nijeria tun shekarun yusuf din basu taka kara sun karya ba,cikin qanqanin lokaci sai ga yusuf din ya zama cikakke kuma gogaggen dan kasuwa tsakanin nijeria da nijer.

Tun zuwan yusuf na farko qasar nijeria ta burgeshi,yanayin garin al'ummarsa wayewarsu da kuma mu'amalarsu da jama'a,musamman da ya soma shiga garin kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa,wanda da iyakacinsu sokoto katsina,harkarsa a kano sai tafi garawa ta kuma fi bada armashi kasancewarta cibiyar hada hadar kasuwanci,hakan ya sanya bayan cukui da dabino sai yake hadawa da mazarqwaila da sauran abubuwa da mu bamu da su.

A lokacin cikin kasuwar kwari suke sauka inda anan ya hadu da alhj *dalhatu attahir* wanda yake da makekiyar rumfa,nan cikin rumfar tasa yake ajjiye kayansa idan yazo kafin ya rarrabawa 'yan kasuwa da masu sara.

Kunsan hali sai yazo daya ake abota,yadda alhj yusuf yake mutum mai matuqar kirki,gaskiya riqon amana taimako da son jama'a haka alhj dalhatu take,nan da nan abota da shaquwa mai qarfi ta shiga tsakaninsu duk da bambancin nau'in kasuwanci dake tsakaninsu,saboda shi alhj dalhatu yana saida atamfofi  ne kala daban daban kaama daga qarama mai sauqin kudi zuwa mai tsada,sau tari alhj yusuf kan karbi atamfofin daga hannun alhj dalhatu idan zai koma qasarsa nijer ya tafi da su ya saida,ko kadan alhj attahiru bai karbar kudin atamfofin daga hannunshi har sai ya siyar ya sake dawowa nijeria duk da cewa bawai baida kudin bane babu ma zancan matsalar kudi tattare da shi da kudinsa a hannunsa,tafi tafi sai Allah ya sanuyawa harkar atamfar tasa albarka wanda babu dadewa ya bude babban shago na atamfofi zalla,ba'a dauki wani dogon lokaci ba shagon ya karbu cikin garin diffa da sauran maqwaftan garin,don wani lokaci wasu tun daga dosso tillaberi niamy ko zinder zaga ga sun shigo sari,hakan ya sanya ya sake bude wasu shagunan cikin wadan nan garuruwan,wadansu nashi shi kadai wadansu kuma shi da alhj dalhatu ne.

Dangantakar ZuciyaWhere stories live. Discover now