BABI NA SHA UKU

3.7K 366 1
                                    

Kasa ida kallon tayi, nan take ta saki camera ta cigaba da kuka, she can't just believe it wai Momynta ta rasu, yanzu bazata kara ganinta ba kenan? Shikenan yanzu batada me santa. Su Uncle Musaddiq sun daina santa tunda har suka barta wajen Gwaggo.

Kashe cameran tayi taje ta maidata inda ta daukota, dawowa tayi kan gadonta ta cigaba da kuka; daganan baccin wahala me cike da mafarkai ya kwashe ta.

Cikin bacci taji an daka mata duka, "Tashi dan ubanki kiyi sallah, kin kwanta kina bacci kamar dangin asara," ta tsinkayo muryar Gwaggo na fadin haka, kuma tayi hanyar fita. "Saura ki ki tashi wallahi, in dawo inci uwarki shegiya dangin mayu," ta kara fada, hade da banging kofar.

Badiyya kwakwalwarta tayi mata zafi, she's still a kid, bata taba experiencing wadandan abubuwan wahalar ba a rayuwa, batasan cewa akwai cruel mutane haka ba a duniya.

Kuka ta fashe dashi, dan ba haka Momynta ta saba tana tadata sallah ba, kuma yanzu tana mafarkin Momynta ta dawo, ta fada mata karya suke mata cewar ta mutu, kafin ta maida mata amsa Gwaggo ta tashe ta.

Tana cikin kuka ta tuna cewar Gwaggo idan ta sameta anan ba karamar wahala zata sha ba, sumu sumu ta mike ta wuce tsakar gida domin yin alwalla. Tayo alwallar ta dawo, sai rawar sanyi take; kasan cewar an fara sanyi.

Har tazo zata shiga daki Gwaggo ta kwala mata kira, "kiyi maza kiyi sallar, ga wanke wanke can kiyi mani, idan kin gama ki share tsakar gidan," fadar Gwaggo, domin a cewarta yanzu ta hutu, kamar yadda Larai ta bata shawara, ta cigaba da wahalar da ita da aiki, har ta gaji ta gudu wajen dangin uwarta. Ita dama badan tanaso ta dauko ta ba, saidan Ahmad ya bukaci hakan, kuma bazata iya ce mashi A'a ba.

Badiyya goge kwallar da tazo mata tayi, da hanzari ta shiga daki domin gabatar da sallar ta, tana gamawa ta fito ta fara wanke wanke, bayan ta idar kuma ta kama share tsakar gidan, bayanta sai rikewa yake. Tanayi tana kuka, dan ita a rayuwarta bata taba kwatankwacin irin wannan aikin ba, komai Momy keyi mata, ko kuma Ladi me aiki, amma yau gata tana sharar tsakar gidan Gwaggo. Ni kam nace yarinya bakiga komai ba.

Da kyar ta gama sharar nan, ta koma dakinta wajen takwas na safe, ba karamar gajiya tayi ba, kirjinta sai heaving yake kamar me asthma.

"Ina kike? Ko shikenan kin gama aikin," fadar Gwaggo cikeda kumfar baki. Ita kuwa Badiyya tanajin haka tayi maza ta kwanta a tunaninta idan taga tana bacci zatayi kyale ta.

Ba'afi minti uku ba taji an watsa mata ruwan sanyi a jiki, firgigi ta tashi, hawaye na fitowa daga cikin idanunta. Wannan wace irin rayuwa ce?

"Ki tashi dan uwarki kije ki share wajen awaki a boys quaters, ko ni kike nufin zanyi sharar wajen," Gwaggo ta fada, tana harararta kamar idanunta zasu fado.

Badiyya rau rau tayi da idanu, "Gwaggo bafa ki fada mani da can ba," ta fada tana goge hawayenta da tafin hannunta.

"Iyyeh! Lallai yarinya ta biyo halin uwarta, yanzu ni kike maida ma magana Badiyya? To dan uwarki ki tashi kije ki share wurin. Kuma daga yanzu ayyukanki kenan, kullun sai na kara maki wasu," Gwaggo ta fada, tana matse mata kunne. Badiyya ta saki kara "Gwaggo dan Allah kiyi hakuri," ta fada tana kuka.

"Maza ki tashi ko sai naci uwarki," ta fada tana hankada ta. "Kuma ki cire wadannan kayan, dan idan kikayi mura bazan baki magani ba."

Badiyya tana hawaye haka ta cire kayan jikinta ta chanza wasu sannan ta fita domin share wajen awakin.

Bayan ta gama tazo ta zauna, domin wata irin yunwar azaba ke cinta, bata taba kaiwa karfe tara na safe batayi breakfast ba, amma ya zatayi? Dole sai Gwaggo ta bata.

"Koni zanzo in kawo maki breakfast din?" Gwaggo ta fada daga falo.

Tanajin haka tayi murmushin murna, hade da wucewa falon domin yin breakfast din. Tana zuwa Gwaggo ta turo mata cup din koko da bread, tsayawa tayi tana kallon abincin da Gwaggo.

"Bazaki ci bane? Kin tsaya kina kallona kamar mayya," Gwaggo ta zabga mata harar hade da mata rankwashi bisa kai.

"Gwaggo bana shan koko da bread, ki bani kosai," Badiyya tayi raurau da ido, dan bata saba shan koko da bread ba, saidai kosai. Shima sai sunje Kankia ne suke ci sometimes.

"Ohhh Allah sarki ai ban sani ba, to karbi wannan," Gwaggo ta fada hade da mika mata tray din indomie. Takai hannu zata karba ta bige hannun, "shegiya kwadayayya kamar uwarta, yanzu da karba kuma zaki? Dalla matsa bani wuri, shegiyar yarinya mara tarbiyya. Maza ki shanye kokon nan tas ki bani kofi na," Gwaggo ta daka mata tsawa, aikau ba bata lokaci ta fara tura kokon tare da bread din tana kwalla.

Wajen karfa daya saiga Ahmad yazo, yana zuwa ta koma daki ta rakube, domin yanzu ta tabbatar ma kanta duk wanda ya buga Momynta a bango namiji ne, dan haka bazata taba zama tare da namiji ba. Koda kuwa Sultan am ne!

Kira Gwaggo ta kwala mata, hakan yasa ta fita falon badan taso ba, saidan yanzun wani irin bala'in tsoron Gwaggo takeji.

Tana fita ta iske yanacin abincin rana, kallonta yayi, "Badiyya zo muci," ya fada cikin shigar lallashi, da murya tausassa.

Kallon Gwaggo tayi taga ta zabga mata harara, maganarta ta jiya ta fado mata a rai, mikewa tayi jiki ba lakka ta karasa inda yake, plate dinshi ya ajiye gabanta tare da zama kasa kusa da ita, alamar suci tare.

Saida takusa minti biyar kafin ta saka hannunta cikin abincin, ci suke ba wanda yayi ma kowa magana, amma mistakingly idan hannunsu yayi brushing sai tayi shuddering, nan take numfashinta zai fasa sama sama, kamar zata shide. Domin ita yanzu a rayuwa tsoron maza take, gani take kamar zasu kasheta yadda suka kashe Momynta. Da dai yaga kamar zata kware tsabar tsoro, sai ya zare hannunshi cikin abincin ya bar mata.

Bayan ta gama ci ta kwasa taje ta wanke, ta dawo har zata wuce dakinta ya kara kiranta, "Badiyya zo mu zauna mana, ko gudun Dadynki kike yanzu?"

Batayi magana ba tazo ta raba nesa dashi ta zauna, shima dan tasan Gwaggo sarai idan ya tafi tana iya jibgarta.

Haka ya gaji da zaman ya tashi ya tafi bata ce mashi kala ba, Gwaggo sai janshi da magana take amma yaki kulata.

Tashi yayi yabar gidan, zuciyarshi na mashi zafi, rayuwarshi Badiyya ce abu mafi soyuwa a wajenshi, amma meyasa yanzu take gudun shi? Meyasa yanzu take jin tsoronshi? Meyasa ko kusa dashi bata san zama.

Badiyya mikewa tayi ta tafi daki ta kwanta, kamar jira take ta yada kafadarta kan gado; ai kuwa bacci yayi awon gaba da ita.

"Badiyya kiyi hakuri kinji, Allah yana tare dake, kuma komai yayi zafi yana tare da sauki," fadar Firdausi, tana share mata hawayenta.

"Momy ina kikaje kika barni gidan Gwaggo?, Momy meyasa zaki tafi ki barni," Badiyya ta rungume mahaifiyarta, tana matsanancin kuka.

"Kiyi hakuri Badiyya, ba'a san raina na tafi na barki ba nima, haka Allah ya kaddara mana," Firdausi ta fada soothingly tana patting bayanta.

"To Momy ance man kin rasu, Momy naga an buga kanki da bango, Momy waye ya bugaki?" Badiyya ta tambaya tana dagowa daga jikin mahaifiyarta.

"Gaskiya ne Badiyya na rasu, kuma bazaki kara ganina ba. Sannan nan gaba zaki gano wanda ya bugani da bango. Kiyi hakuri ya ta, Allah yana tare da ke," tana fadan haka ta bace bat.

Badiyya na farkawa daga bacci, hawaye shabe shabe kan fuskarta, tunowa da tayi Momynta tayi mata confirming tabbas ta rasu, anan take ta saki wata uwar kara, "MOMY!!!".

Votes da comments rinku sune karfin guiwata. Nagode.

RAYUWAR BADIYYA ✅ Kde žijí příběhy. Začni objevovat