" Nasani hafsat har yanzu kina san shaammaz ina rokon Allah ya daidaita tsakaninku" kallonta takumayi tana me sharar kwallan daya zubo mata tace " Mero bana fatan sake zaman aure da shaam,ko a mafatki naganni matsayin matarshi lallai senayi adu'ar tsari daga mugun mafarki had'eda yin sadaka, har kwanan gobe ina san yaa shaam sedai a yanda na fahimta sam wannan bashi bane mafita agareni,so tari zakiga abubuwan damu y'an adam muke so basu suke zamtowa mafakar alkhairi agaremu,yaa shaam ko banda asiri ba sona yakeyiba kuma tsana ta zahiri,nidai wlhy kinji na rantse miki nidashi har gaban abada,ina dai masa fatan alkhairi" jinjina kai mero tayi "To Allah ya kawo miki muji na gari me qaunarki" "Ameen" ta fad'a ataqaice sannan ta kwanta ta runtse idonta......

*Bayan sati biyu*

Shaam durqushe agaban daddy da abba haris dasu momy harma hafsat wacce dominta aka tara zaman,kasancewar wai shaam yace ze aureta kuma ze barta harseta qarasa karatunta a india,kowa yayi shiru yana kallon ta tsuniyar daddy domin kuwa ilahirin jama'ar wurin kallon me bada tatsuniya suke masa harya idar,hafsat dai batace qala ba kazalika bata koda girgiza da zancen ba tunda taga yana mata bata dagawa be dena kiranba ta tabbatar cewar lallai da wata aqasa..... Kallon su Abba yayi yayi wani malalacin murmushi sannan ya kalli hafsat yace "y'ata nasan bazaki tab'a watsan qasa a idoba,ina sauraronki menene naki ra'ayin ni duk abunda kikeso shi zan miki" kallon shi ta dago tayi ido cikin ido suna had'a ido abba ya gano ta shaqa,ta nisa sannan tace idonta a qanqance

" Bazan sake fad'ar abunda zan fad'a a yanzu ba,abu d'aya nake san kusani shine,dukkanin abinda kukaji zan ambata yanzu babu wasa kokuma wani abu makamancin raini aciki,kuskurewa qa'idata d'aya ka iya janyo lalacewar komai musamman idan na aikata abinda zan aikata idan aka kuskuremun qa idar" shiru ta danyi kowama yayi tsit taci gab

"Ni bazawarace ba budurwaba kuma a tsari na addinin musulunci nice dakaina nake da haqqin zab'awa kaina mijin aure a yanzu,bazan lamuncewa zab'in kowa ba tsarin addinina zanbi, kuma wlhy summa tallahi bazan tab'a komawa auren shammaz ba,ko gawata akayi kuskuren daurawa aure da shaam ban yafewa wanda yayi ba koda mahaifinane kuwa, idan aka qarabtayarmun da zancennan wlhy na sanya qafa nashiga duniya nida gida har abada,idan dame tantama kuma ya gwada tada zancen kuga ikon Allah, ku tambayeshi kuji dalilansa naqin zama dani idan dai basankai kuke sanyi ba ai bazaku qara cutar saba kamar yanda kukayi abaya,da bakinsabyace dani ya tsaneni!! An cuceshi da aka had'ashi aure dani,da bakinsa gashinan zaune ya kalli tsabar idona yace dani Babu tabinda ze zauna da mace bushashiya ni menakedashi,mena ajiye ajikina ina fama da qasusuwa,da bakinsa ya kalli tsabar idona yace dani na dena mafarki ze tab'a had'a shimfud'a da banza irina bushashiya,ashe nidin nan icce ce a idonku,ashe bajini a jikina,ashe qarfeceni bansan dadin mijiba,idan har baku sani ba toku sani yau nasha baqar wahala rayuwa da miji fanko,ina da aure an kawar dani sabida gudun wannan yaso ya cillani gayinta banda a litttafan hausa da fina finai ina kuka tab'ajin anyi aure shekara daya amma namiji be taba koda riqe hannun matarsa ba duk sanda kuka ga jikina da nashi ya hadu tofa duka ne,kuma da bakin sa ya sanar mun cewar bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane,shine ina makauniya zan dauki kaina inkai daidai bakin rijiya,sabida bana tsoron afkawa aciki,toku sani ina tsoro!! Na rantse da Allah kona rasa mujin aure bazan auri yaa shaam,ninan ni kadaice na san baqar wahalar danash a hannunsa,a ranar dana samu matsala dakaina na roqeshi akan waze aureni idan yasaken ya taimaka ya maidani gidansa,bud'ar bakinsa se cewa yayi dani be soni sanda nake da lapiya ba se yanzu dana dawo nakashashiya,bayan shine silar lalacewar rayuwata da quruciyana kowa namun kallon bazawara!! Kullum zancensa d'aya ya tsananeni yana tunasar dani bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane,shine yanzu ze bazamo kome ya gani ajikina oho!!! Ko kuwa dai yanzu zan iya wasa a bakin rijiyar tunda naqasa ta tafi oho!!! D'aukacin mutanen parlor dinnan ku shaideni ranar dazaku qara zuwamun da zancen komawa gidan shaam kun rasani kenan har abada!!!!""

Jikin kowa yayi sanyi yayinda abba haris ya zabgeta da albarka,shaam kuwa ya saka kuka wiwi wai ta taimaka masa....to phaaaa..

Zaune suke idata Uncle say a babban parlor na gidan daddy se shagwab'a takeyi wai bazata koma india ba,shi biyeta yakeyi ya saba haka sukeyi da qannenshi sesu sakashi gaba abu beje yazo ba su saka masa kuka

"Haba dan Allah uncle say,idan kuma na tafi bazan qara ganin kaba fa" murmushi yayi yace "Dan Allah hafsat ki dena rigimarnan,bakya ganin khairi batayi haka ba? Ke komai se kace jin jira,komai rigima komai kuka,na sanar miki akwai wani coirse dazanyi a india na shekara daya kuma nxt montj zanzo,tunda kunfara school seki koma kafin nazo" turo bakinta tayi waje " Ni dai jiranka zanyi bazan iya juran rashin ganin kaba na tsawon wata ni yanzu im used to you over,i just cnt imagine my self with out you around" Murmushi ya sakar mata "Nima haka beauty amma ya zamuyi yanzu idan namiki aure ya zakiyi? Sekice dani zaki tafi" B'ata fuska tayi

"Ni nace dakai zanyi wani aurene,ni bazan taba aureba aje ana dukana,maza basuda kirki wlhy" janyo hannunta yayi shi yarigada ya saba da al'adar indiyawa yace

"Beauty banasan wannan mummunan tunanin dakika sakawa kanki,sam be dace kina cewa bazaki qara aure ba,adu'a zakinayi Allah ya kawo miki muji na gari me qaunarki tsakani da Allah" kallonshi tayi ido cikin ido tace

"Ni koba wannan ba bazanyi aureba,idan nayi aure mijin baze bari ina ganinka kullum ba,nikuwa that will be d worst thing that will happen to me ever,i just cnt imagine my self living a day with out u" murmushi ya sakar mata yana nazarin kalamanta sannan yace

"yanzu dai naji,amma ki daure ki koma school Allah zan siya miki sabon waya da sabon laptop da sabon ipad kuma zan siya miki sabon kaya ma,na zuwa school madam gayu" tana murmushi tace "Thank you for that,buh bana buqatar komai daka lissafa i just need u beside me,idan wannan baze samu ba,zan haqura nace haka Allah ya tsara" sakin hannun mata yayi yace yana miqewa "Thats very good of u gold,zancen waya kuma i already bought one for you, samsung s8 your favorite product,yana mota muje nabaki " miqewa tayi tana ihu tamkar ta rungumeshi,say akwai principles seyaga dama suke riqe babbar waya fa!! A hanyar fita suka had'u da yaa shaam,uncle say ya miqa masa hannu su gaisa,dakyar ya bashi hannu sannan yace " ke hafsat wai an sanar miki kowane mutum kika dakko secikin gida ake kaishi haka akeyi?? Ga guest parlor can kuje amma se ciki,ba wani privacy kuma bare ma" kallon mamaki say ya masa ita kuwa taja hannun say batare data koda kalle shiba domin kuwa ita alqawari tayi idan yayi sallama zata amsa,ita kuma tashigo koda shi kadaine a wuri zata masa sallama amma bazata taba yi masa magana ba,koda ze mata bazata kulashi ba, gabansu yasha sekace wani dolo yace "ke badake nake magana ba?" say ne yace "kayi hakuri Dr. Shammaz inshaa Allah bazan qara zuwa muku gidan bama gaba daya bare kayi fadan bare ya shiga ciki" kawai se hafsa ta saka masa kuka

" look uncle say,lemme just go n pack my things im going back to my Abba's house,im tired of this mesa daga zuwa hutu,Allah bazan kuma dawowa Niger ba sena gama school" hannu ya sanya ya dauko mata mayafin daya fadi ya rufe mata kanta sannan yace " Ina sauri ne gold,muje na baki wayanki" wani kishine ya tasowa shaam yace kai din dan iskan inane dazaka taba ta?? Dama iskancin dakuke kenan ko?" sosai rayuwar say ta baci ya wuce su zuwa mota,ya shige ita kuwa hafsat bakin ciki ya hanata koda motsi daga inda take se kallon say takeyi kunyarsa dukta rufe ta,hannun ta shaam yaja ya mannata da kofar parlor din yace " Ke wlhy ko zaki mutu sekin koma gidana wlhy ki sani wannan kayan dakika tara sena mora,bazan bari banza ta wuce niba" kallonshi kawai takeyi harya gama ya saketa batace dashi ci kanka ba,rayuwarata intayi dubu tota baci,haka ta zauna ta dinga kuka tana kiran uncle say yamma yaqi dagawa gaba daya ta damu da fushin sa,tsinuwa kuwa shaam yashata cikin kwando dubu....

Koyaya zata kaya a wannan bada qalar,gamu gani dai.....

Mom Nu'aiym ce🔨

BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho BaneΌπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα