page 27

2.3K 189 2
                                    

*🌞HAFSAT ELHAM🌞*

Billy Galadanchi

Haske writer's Asso💡

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.
Sadaukar wa ga k'awata Hafsat Abubakar qaya (Elham).

27

Kan wani yayi magana Elham ta saki wani razananniyar qara

"Nashiga uku momyyyyyyy......" Dafeta yayi yace "Haba Elham menene abin ihu Bakima ji waya rasu bafa" ganin bata hayyacinta se kukan take taqi ta kulashi ya sanya ya tallafota jikinshi "Jijjigata yayi yace " Blossom ki nutsu mu Shiga cikin gida tukunna kinji" hannu ya sanya akan lips nashi ya girgizawa driver d'in kai alamar karya fad'a waya rasu d'in,sosai yashiga rud'ani kasancewar besan waye ya rasuba idan ko momy ce lallai da babbar matsala,a haka dai ya d'aura ta akan kafad'arsa suka Shiga ciki,a parlor momy mutane sunyi yawa har bazaka iya ratsasu ka shiga cikiba,juyawa sukayi da nufin zuwa sashen su aikam se ganin Fulani Habeeba sukayi da icce qaton gaske "Wlhy bazan yadda ba yanda ya Turo aka kashemun faruk daga dawowar shi haka shima zan kasheshi Mugu kawai azzalumi" hafsa da Abdul da suka kasa gane inda zancenta ya dosa se suka tsaya sororo suna kallonta,da gudunta ta saka wannan uban sandar ta kwad'a wa Abdul a kai,take ya zube wurin a asume,kallonta Hafsat tayi cikeda rud'u sannan ta mayarda dubanta zuwaga Abdul dake kwance jini na masa zuba a kai,durqusawa tayi tama kasa kukan dayazo mata duk wani tunani nata ya tsaya chack baya yi gabaki d'ayan jinin dake zagaye ajikinta yakai saqonni cikin kwanyarta ya dena yawo,a hankali ta saka hannu ta jijjigashi "Yaa Abdul" ta kira sunanshi a hankali ganin be motsa ba ya sanya ta dafe cikinta atake tasoma ganin jiri,isowar momy kenan da sauri tayi kansu,dafata Elham tayi sannan cikin kuka tace "Yaa Abdul momy wlhy zasu kashe mun shi,kalli fa Haj Habeeba ta kwala masa wannan mugun iccen,na rantse da wanda rayuwa ta take hannunsa idan ta kashemun. Yaa Abdul na sena kasheta nima,sekuma ta qara dafe cikin koda ta kalli kafafunta tafara bleeding over,wani sabon kara ta k'walla take itama ta zube wurin asume,mutane sun riqe Haj Habeeba ana mata Nasiha amma ta kafe lallai seta kashe Abdul,kai tsaye momy sawa tayi aka wuce dasu asibiti tana sharar kwallah tabi bayansu........Allah ya tsare Elham bata samu miscarriage ba Abdul kuwa buguwane kawai,shine ya soma farkawa ganin momy akanshi ya sanya a hankali yace " momy dan Allah sanar dani wai meya ke faruwa ne ??" Kallonshi tayi cikeda ban tausayi tace "Babana wlhy qaddarorine,kaga Faruk ne ya dawo jiya da safe ni bama nida lapiya, wlhy da safe koda hadimansa suka je b'angaren sa ganin ya jima be fito ba Sefa gawarsa suka tarar an dab'a masa wuqa a qahon zuci,shine fa Habeeba ke ihun Kaine ka kasheshi karya gaji sarauta" dafe kanshi dake Sara masa yayi

"Wai ita wannan matar yaushe ne zatayi hankali,bazata barni ma Inji da mutuwar wulakancin gudan jinina ba seta zomun da wani salon iskanci wlhy wannan karon ko me martaba be isa ya hanani hukunta Habeeba ba abinta ya isheni,na shiga uku Farouq yanzu ya zanyi...." Rarrashin sa ta soma yayi seda ya hakura sannan yace "Momy ina Elham ?" Dan shiru kan can tace "Elham zazzabi takeyi tana wancan d'akin am bata gado" zabura yayi ya zare qarin ruwan da aka d'aura masa "Momy ta kani na ganta mana dan Allah ina ne d'akin?" Tana yunkurin hanashi amma ina seda yafita dole ta bishi sukayi d'akin, koda sukazo baccinta takeyi amma yaqi komawa d'akin sa sanda ta farka,a gaban momy ya rungume abarsa suka fara hawaye

"Blossom na menene? Meya sameki haka?" Tama manta da wata momy hannun ta ta saka a saman wuyanshi tana shafawa a hankali "Bayan wannan matarne takeso ta kashemun kai,kagafa wannan qaton sandar ta buga maka,Allah ni idan har ta qara tab'aka sena rama maka muguwa ma da ita" rungume abarsa yayi ita dai momy murmushi kurun takeyi Elham ce takuma cewa

"Yaa Abdul gobe zamu tafi London din ko?"

"Noo princess sekin haihu tukunna" shagwab'a ta soma yi wanda ya sanya ba shiri momy tabar musu d'akin ganinfa dukkansu ba wanda yasan da zumanta acikinsu

"Hubby wai ni waye ga rasu ne? Nagane momy ai d'azu tamaji sauqi" k'ara rungumeta yayi sosai "Habeebty se hakuri faruk ne akazo har cikin masarautar nan aka kasheshi jiya" zabura tayi ta dafe k'irji sosai ta sona kuka dakyar ya rarrasheta tayi shiru,sosai taji wannan mutuwar ta faruk musamman dayake ita dashi basuyi rabuwar dadi ba sam.

A haka dai aka kammala zaman jana'iza yayinda Habeeba ta daurawa Abdul alhakin kisan faruk wanda kowa yasan haukanta takeyi sabida tun farko shi Abdul baya san sarautar balantana ma yayi kisa akanta.........

Har cikin Elham yashiga watanshi na haihuwa suna Niger wannan umarnin mahaifin Abdul ne, wata rana da yamma Elham ta tashi da labor ita kad'ai Abdul yaje Kano amma a ranar ze dawo da kanta takira momy ta sanar mata tanajin labor ne yazo mata aikam cikin ikon Allah segashi momy da kanta ta karb'i haihuwar agida sabida koda tazo har kan baby ya soma shirin sulmiyowa ta sunkuco little princess d'inta kyakyawa me matukar kamanni da ita,har sumar kan babyn irin nata tayo,cikeda murna aka sanar a fada take agun me martaba yayi umarni da azo masa da babyn aikam take yabata kyautar wani katafaren kamfanin sa na saqa,kuma ya bata sunan momy,dama a fada suke zama tunda cikinta ya tsufa,se Wuraren 9 Abdul ya qaraso a fusace yazo gidan yana zuwa yaganta zaune a parlor itada wasu hadimai

"Sannu da zuwa yaa Abdul?" Tace dashi tana me kallonshi ko duban inda take beyiba yace "yauwa" atakaice ya wuce ciki abinshi,mamakine ya kamata ta miqe ta baiwa dayar babyn ita kuma tabishi ciki yana daga cikin wardrobe tace "yaa Abdul lapiya dai kashigo cikin gida ranka abace?" Cikeda fusata yace

"Bansaniba tsabar rainin hankali shine tun karfe hudu nake kiranki amma baki daga ba kuma har yanzu baki kirani back ba,ko kinaso...ya zaro kanshi daga wardrobe d'in yana mata magana atake yayi hooking gani ba ciki a jikinta,da sauri yazo ya riqeta da mamakinshi yace " Blossom yadai?" B'ata rai tayi "kaci gaba da masifan da kake mana,banda haka ina fama da labour zaka zo kanamun masifa,Allah ni banmasan inda na wurgar da phone naba,kuma fa nasha wuya,shine kokace ina Baby" wara idonshi cikeda mamaki "Blossom wai da gaske kin haihu? Wlhy babu wanda ya sanar mun hasalima ban lura ba ciki ajikinki ba se yanzu,me kika haifa mun ina babyn?" Murmushi tayi "Baby girl tana hannun hadima adama" wani uban tsalle ya daka yana ihun murna da gudu ya ruga parlor hadimanma sunsha mamakin yanda ya manta da wani girman kan mulki ya sungume y'arsa yana tsallen murna..

*ku taya Nu'aiym da adu'a wlhy bashida lapiya*

Mom Nu'aiym

Hafsat ElhamWhere stories live. Discover now